Amatulmaleek Hausa NovelHausa Novels

Amatulmaleek 36

Sponsored Links

Ko data gama dafa tea din ta shirya a sabon tea set ta Jere ta dauko ta nufi dining room din

Shigarta yayi daidai da shigowansa dining din Shima bayan dawowansa daga sallan magrib sanye cikin black Armanis sweatsets fresh kaman saurayi abinci yake buqata sbd tinda suka dawo Shima Yana sama Yana hutawa cikin lafiyayyar bacci.

Kallansa tayi da idanuwanta farare tareda Dan dauke idanuwanta tana qarasowa tareda gaidasa a natse cikin sanyi.

Related Articles

Idanuwansa Shima ya Dan kalleta dasu kafin ya amsa Yana zaunawa a natse.

Green tea tafara zuba masa yakai hannu ahankali ya dauka Yana sha kafin tafara zuba masa farar spaghetti da kidney sauce sai lettuce da scotch eggs.

Tana gama zuba masa zata juya ahankali ya Bude Baki ya furta

“Ya jikin?

Dakatawa tayi daga inda take tsaye tareda sauke numfashi ahankali ta juyo ahankali idanuwanta na dagowa zuwa ga kallansa Shima daidai lokacin ya ajiye cup din hannunsa ya dago ya kalleta.

Sanyi jikinta yayi gabaki daya ta kasa daga kafafunta daga inda suke,

Jin shirunta ya Sakasa kasa dauke idanuwansa akanta Yana tinanin Bata ji saukin bane.

Miqewa tsaye yayi ahankali ya dosota ta Dan yi Baya kadan tareda dafa kejeran dining Dake bayanta tana sauke idanuwanta qasa tasamu kirjinta da bugawa ahankali hancinta Daya wuni yau din ba qamshinsa Yana shaqan qamshinsa cikin sanyi.

Shi kansa Saida ya iso gabanta ya tsaya Yana kallan wuyanta yaga gurin ya warke gaba Daya Dan bazaiso maamah dinta Taga wannan abin a jikinta ba.

Dagowa tayi ahankali zata kallesa ya juya ya koma inda ya taso ya zauna yafara cin abincinsa a natse.

Juyawa tayi batareda ta tsaya cin abincin ba ta koma dakinta zuciyarta Naci da bugawa.

Zama tayi tareda yin shiru tsawon lokaci Sai data tabbatarda ya gama ta miqe ta fito taje ta Zauna taci abincin ta taso ta dawo daki.

Sallan ishai tayi tai brush kawai ta kwanta.

Washe gari da safe ko fitowa batayiba Saida tayi wanka ta fito taci abinci tana zaune likita tazo dubata,

Batai mamaki ba Dan haka cire rigarta tayi ta duba koina na wutan Taga sun warke ta sake Bata cream da zata ringa shafawa a gurin ta tafi
Tana tafiya Mr Jameel ya Aiko mata da sabuwar waya guda biyu tareda layin MTN da Airtel.

Daya kawai ta Bude ta zabi na MTN din ta Saka ta ajiye dayar Dan Batada raayin amfani da waya biyu lokaci Daya.

Maamah tafara kira a take taji zuciyarta tayi sanyi lokacinda taji muryan maamah din.

Sallama tayi a cikin sanyi da nutsuwa tana cewa

“Maamah”

Ita kanta maamah din Jin Amatun ya Sakata miqewa daga kwancen datake tana ambatar sunan Amatun cikin tsananin kulawa da kauna tace

“Amatu,ansiya Miki wata wayar ne?
Mr Jameel yace wayarki kin yar ne a makaranta shiyasa bana samunki duk kwanakin Nan inata tinanin yanda zanyi magana Dake kafin na dawo,
Kina lafiya?
Zuciyata ta kasa nutsuwa Amatu,
Kina lafiya?

Numfashi me sanyi Amatun ta saki Jin abinda maamah din ta fada dan haka a sanyaye tace

“Lafiya kalau alhmdlh Maamah,ya Husnah,yasuke ta fama da hakurin rashin?

Alhmdlh”

Maamah yaushe zaku dawo?

Numfashi maamah ta sake tana cewa inshallah satin Nan zamu dawo Daman munata Dan jiran Husnah ta qara kwanakin data roqa ne Amma inshallah satin Nan zamu dawo.

Shiru Amatu tayi tana rasa abin cewa tace
“Allah ya dawo daku lfy”

Rasa abin fadawa juna sukai sai sukayi sallama.

Haydar tafara kira sbd tafi riqe numbernsa akan ta Abdul Yana dauka yaji itace abinda yafara fada shine

“10 days kenan bamuyi magana ba,tayaya zakiyi 10 Days ba waya,meyasa??

Batasan kwanakin data dauka ba rabonta da murmushi ya sauka kan kyakkyawar fuskarta sai yau din Dan haka murmushi me sauti ta saki tana cewa

“Zaka fara ko?

Rasa abin fada yayi sbd mamakin yanda za’a barta 10days ba wayan da gaske sai kawai ya hau tambayarta lafiyarta suna gaisawa dayake Abdul na tareda shi sun fita ne sai kawai ya Saka handsfree suka hau wayar su uku cikin samun nutsuwa da sakewa da juna.

Ta jima tana wayar dasu kafin ta kashe ta fito Dan batason zaman shirun ta nufi kitchen.

Da ita sukai aikin abincin Rana suka gama suka jere komai ta wuce daki.

Abinda batai tsammani ba shine dawowansa gida da wuri Dan haka a gidan yayi lunch ya shige.

Abincin dare kuwa kusan itace tayi sedai suka ringa taimaka mata da wasu ayyukan harta gama aka Jere komai ta sake shigewa.

Sallah tayi da wanka ta fito ta dafa ruwansa da baa dafawa sai lokacin cin abincin.

Tana kaiwa ta ajiye tana fita Yana shiga yasan lokacin ta fice sbd qamshinta Daya Dan fara noticing yaji ya shiga hancinsa.

Abincin yaci ya gama ya fice.

Yana ficewa itama ta shigo taci abincin da qamshinsa kawai Daya bari a dakin.

Sabuwar rayuwar kaucewa ganin juna suka fara Kokuma ace tafara dashi Dan shi ta nasa bangaren rayuwar Daya Saba ce yake Akai banbancin Daya fara samu shine kulawan dayake samu ta bangaren cimarsa datakeyi,Wanda itama ta Saba aikinsu ne Daman can itada uwarta,
Ta bangare daya Kuma dole tinda baa ware me kulawa da bangarensa ba itace dole tazama me aikin bangarensa,
Zata tafi gyare ne bayan ta tabbatarda ya fice zata gyara komai ta kunna qamshi da ac ta fito.

Shi da kansa yasan itace me gyara masa bedroom sbd Babu Wanda ya taba bin ko hanyar zuwa bangaren nasa Koda mr Jameel dinsa ne.

Bedroom dinsa shine Wanda yafi kowanne bedroom girma a Mansion din,
Luxury gadon Dake dakinsa a tsakiyar dakin yake hakama tsarin bedroom dinsa daban yake Dana Kowa.

*******Wani nauyi ne yahau kan Amatun a kwanakin dawowansu na aikinsa Daya hau kanta dole tinda ba know hakama Babu babba me fadan yanda zaayi din,
Masu aikin na jiran cewanta ita Kuma batada me ce matan Dan haka Bata Ankaraba ta samu kanta da nauyin da duk matan aure take dauke dashi a gidanta na kulawa da komai na Wanda igiyoyin aurenta yake kanta.

A yanzu data samu kanta a wanna tsaunin hatta breakfast din dayake ci itace take fitowa tayi shiyasa duk safiya sai sun Hadu gurin hidimar cin abincin nasa.

Da farko Hakan Bai fara kamasa ba Saida tafara sabar masa da pen dayake amfani dashi idan ya dawo a tsare suke cikin tsari hakama komai nasa.

Maamah kusan kullum cewa takeyi zasu dawo Amma Basu dawoba Dan haka ta Dena ma tambayar yaushe zasu dawo.

Yau Bai fito ba tin safe sbd Babu inda zashi Amma Babu Wanda yasan yana gidan.

Ita kanta Amatun yau duk batada Wani kuzari sbd sanyi da akeyi Dan haka tinda suka gama breakfast ta dawo dakinta ta kwanta,
Masu aikin gidan ne kawai keta hidimarsu.

Mum Aisha ce ta dawo itama hankalinta gaba Daya baa kwance ba tafi sati biyu a cikin mummunan tashin hankalin rashin sanin inda Naufal ya shige,
Sam Bata samun wayarsa hakama zayyan yace Baya tareda shi,
Duk inda take tinanin samunsa ta bincika Amma Babu labarin inda yake Dan haka ta tattara ta dawo ba shiri saikuma ta tarar da sun dawo sabon mansion.

Kayan akwatinan sitirarta kawai ta kwaso itama Tayo sabon mansion din sedai tana zuwa securities suka dakatar da shigarta sai ankira mr Jameel yakira ASH idan ya Bada izinin shigowarta.

Mr Jameel bayan ankirasa Kai tsaye yaso Bada Daman abarta tinda ba itace ta aikata laifinba Danta ne Kuma haryanxu Babu ma Wanda ya sani sai Naufal din yaji sauki tukuna zaasan yanda za’a yi dashi Amma dai yace su Jira sai abinda ASH ya fada.

Kiran wayar ASH din yayi Amma duka biyun Babu Wadda aka daga Dan haka bazai cigaba da kiransa ya takurasa ba sai kawai ya kira numbern AmatulMaleek ya sanar da ita izinin ASH din ake nema akan shigowan Ms Aisha idan ya Bada dama.

Shiru tayi sbd batasan me zata ce ba hakama batasan tayaya zataje har bedroom dinsa ta samesaba.

Sake maimaita maganar Mr Jameel yayi Wanda Shima take tsananin ganin girmansa Dan haka ta sauko daga kan gadon datake ta zira slippers qafarta ta nufi hanyar dining room ta shiga kofar data zata shigar da ita palonsa.

Palon tsit Babu motsin komai daga qamshi me nutsuwa Se sanyi ke tashi Dan haka ta sauke ajiyan zuciya tareda nufar kofan bedroom dinsa kowanne takunta zuciyarta bugawa takeyi.

Tana tsayawa kofar bedroom din hannu Daya ta miqa zatai knocking kofar shikuma Yana Bude kofar hannunta ya Saka kirjinsa Dayake Bude Babu Riga a jiki sbd dogon wandon pyjamas ne tin na safe a jikinsa.

Fatar jikinsa Dake fara qal Babu tabo ko kurji kodaya tana daukan ido sbd lafiya da Hutu tayi saurin daukewa idanuwa gabanta na faduwa hakama tafin hannunta Daya sauka Akai ta dauke ahankali.

Shi kansa tsayawa yayi a gurin tareda kallan inda hannun nata ya sauka kafin ya dago idanuwansa dasukai ja da ciwon kan dayake fama dashi tin dazu ya zuba mata itama shi din ta dago a sanyaye ta kalla batareda ta motsa ba.

Fuskarta yake kalla a natse
Ta sauke nata idanuwan tareda Dan yin baya kadan.

Itace tayi qarfin Bude Baki a natse tace

“Mr Jameel na magana ne”

Bai iya magana ba Kai kawai ya gyada mata tareda juyawa ya koma ciki itama ta juya da sauri ta fice.

Wayarsa Daya ya koma ciki ya dauka yaga Kiran Jameel din ya Saka kiransa Kai tsaye.

Cikin nutsuwa Mr Jameel ya sanar dashi abinda yake faruwa a gate na mansion din.

Shiru yayi kafin ya Bada izinin shigowan nata aka Bude mata ta shigo.

Bayan shigowarta Babu abinda tafara cin karo dashi Daya girgizata shine sai dakin dasu khaltume suka Kai mata kayanta wato baa sama yake ba a qasa dakinta yake duk da babba ne da palonsa Amma Sam baa qasa tazo zama ba,

Babban shock dinta na biyu shine tararta Babu kowa a gidan sai Amatu wadda take sama Kuma Bata sauko gaisheta ba.

Su sallah da abinci zataci ta huta sbd gaba Daya a kwanakin cikin rashin Kwanciyar hankalin Neman Naufal take.

Su karima da Farida ne suka hau shirya mata kayanta a wardrobe da sauran abubuwan inda zaa ajiye mata su.

Qanqanin lokaci sun gama suna kokarin ficewa ne Mum Aishan data gama komai ta zauna zata ci abinci ta kira sunan Farida tana cewa

“Meya samu old mansion din naga harda wuta Wani bangaren yayi,garin Yaya?
Kuma tin yaushe su Husnah sukai tafiya ne??

Kallan juna karima da Farida sukai kowannensu gabansa na faduwa da shiga firgicin tambayar.

Dagowa tayi ta sake kallansu tana fara cin abincin a natse tace

“Tambaya nayi,Babu amsar tambayata ne Kokuma dama kuka samu da sake bayan tafiyata”

Qasa sukai da kansu Wanda Hakan ya Bata tabbacin akwai abinda ya faru din kenan Dan haka ta ajiye spoon din hannunta tana hadiye abincin bakinta ta da tsawa ta sake maimaita tambayar
cikin rawar murya da Farida tace

“Su Ms Husnah sunyi sati uku zuwa hudu da tafiya”

Abincinta taci gaba daci tana cewa

“Uhum gobarar Kuma fa garin Yaya?

Wannan Karan a tare suka amsa da cewa

“Sir Naufal ne ya kunnawa kitchen din wuta…..
#MAMUH#

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button