Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 25-26

Sponsored Links

BMGJY 25-26

 

Taƙabbalallahu Minna Wa Minkum…..May Allah subhanahu wata’ala Allah accept all our Ibadah forgive our sins and purify our souls…Ameen Eid Mubarak…

Related Articles

*FOR SALLAH PROMO*

Don ci gaba da karanta wannan littafin ki biya ta 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank, ko hoton kati MTN ta WhatsApp number 09013718241 idan a Niger kike zaki tura katin Airtel na 400CF ta wannan number +227 95 04 58 22 sai kiyi screenshot ki turomin nasaki a group.

★★★~~~★★★~~~★★★

Miƙewa Jakadiya jayi ɗuwawu a salike ta fice ta nufi sashinsu a hanya suka haɗu da Larai ta jata suka nufi can bayan gidan Jakadiya tace “Larai bakina da salama nifa kaina ya kulle da wani abu dake faruwa a gdannan” zama Larai tayi tace “Akan Yarima Habeeb kikeson mgn ko? Jakadiya ina tsoronki uhm barima naja bakina na samasa saƙata bazakiji a bakina ba….”
Riƙota Jakadiya tayi tace “Zo fa muje ki gani” dakin Jakadiya suka shiga ta dauko zanin gadon ta ware mata ta rintse idonta da sauri Jakadiya tace “Ni kaina ya kulle yau da safe ya kirani yace na bata kulawa sannan na ajiye wannan za’a nemeshi yanzu kuma ya kuma kirana ya bani wannan to me hakan yake nufi? kodai fyaɗe yayiwa ƴar mutane?…..” Rufe mata baki Larai tayi tace “bazai kasance haka ba kinsan akwai jumurɗarsu da mai martaba akan auren wata bamagujiya da yazo yace yanaso Mai martaba ya kori ƙudurin harma yaci alwashin indai yana raye ya haramta masa ita har abada ko?”
Jinjina kai Jakadiya tayi Larai ta kara yin ƙasa da murya tace “Banfa tabbatar ba amma raina yana faɗamin itace wannan yarinyar to amma kuma ai Kilishi tace ƴar’ ƙanwarta ce to in hakane kenan ta bakin naki fyaɗe yayi mata?”

 

Yarfa hannu Jakadiya tayi tace “To biri yayi kama da mutum to amma kuma idan farko fyaɗe ne yanzu kuma da naje na tarar dasu a wani yanayi menene?” Hannu Larai tasa ta rufe bakinta tace “Uhm! Larai jikar me koko samawa kanki salama kar naje nayi ta albashi na” Jakadiya ce tace “Abin fah da daure kai ta bakin naki anya yarinyar nan babu wata ƙullalliya a ƙasa don alamu sun nuna Kilishi tasan komai”
Hanya Larai taci tana cewa “nikam abin faɗa na ya ƙare keda kike da abin taunawa saiki zauna kita tunanin rashin tabbas” harararta tayi tabita da masifa tace “Kedai kika sani tsohuwar kawai”

*******

Tunda ya fita ya barta kalamansa sukeyi mata yawo a kwanyarta zuciyarta tayi duhu suma a yau zasu tashi zuwa Umrah da dare lumshe idanunta tayi tace “lkc baija ba amma na fara gajiyawa da wannan ƙuntacciyar rayuwar yaushe ne zan bayyana matsayin mata kamar kowacce mata?”
Kawar da tunanin tayi ta hanyar ɗaga wayarta da take ring ta kara a kunnenta tace “Rasheedah!” Ajiyar zuciya Rasheedah Turaki tayi tace “Tun jiya da dare nake kiranki bana samunki yanzun kuma muryarki ta bayyana min kinada damuwa Habeebah Ni marainiya ce banida uwar da zan tattauna damuwata da ita da Allah ya haɗani dake sai naji na samu sauƙin wannan ciwon saboda kina bani shawara ta hankali ina kawo Miki matsalata kiyimin maganinta HH meye matsalarki don Allah?”
Lumshe idanunta tayi tasa yatsanta ta ɗauke hawayen fuskarta tare da ƙoƙarin kumbura zuciyarta da juriya tace “Kar…karki damu Rasheedah wannan damuwar lkc ne kawai zaiyimin maganinta ke meye taki damuwar don nasan kawai bazatasa ki rinƙa kirana a lkcn da nake cikin ƙila wa ƙalan rayuwa ba”

 

Jan zuciya tayi tace “Prince Habeeb Khalil…” Wata muguwar faɗuwa gaban Beebah yayi ta miƙe zaune tace “Ya haka? Meye yayi Miki…” Murmushi Rasheedah tayi tace “A zahiri baiyimin komai ba baɗini ne da matsala bansan komai game da soyayya ba tun ranar da muka zo da Captain gurinki idanuna yayi tozali dashi nakejin rayuwata tana cikin wani yanayi na neman tallafinsa wlh zuciyata ta kamu da muguwar ƙaunarsa ta yanda bantaɓajin zan iya hƙr dashi daidai da rana ɗaya ba…..”
Slow numfashi Beebah ya rinƙayi tana ƙoƙarin daidaita shi yana ƙara ƙwacewa kanta na wata irin sarawa tashin hankali na ratsa duk wata kofar jini ta jikinta cikin mutuwar jiki da rawar murya Tace.
“Hab… Habeeb Rasheedah!?” Cikin karayar zuciya Rasheedah tace “Yeah it’s true Habeebah inason cousins ɗinki Habeeb…..”

 

Rintse idanunta tayi tanajin kalmar inason cousins ɗinkin kamar watsuwar ruwan zafi a jikinta ta ajiye wayar kawai batare data iya sanya hannu ta kashe ba ta koma ta kwanta duk ilahirin jikinta ciwo yakeyi da haka Kilishi ta shigo ta sameta ta ɗago idanunta da suka kaɗa sukayi jawur ta saukesu akan Kilishi dasu Hudah Hudah ta matsa tace.
“Sannu Sis ɗazun nazo naji ƙofar a rufe halan kina bacci ne?” Iska ta furzar ta kawar dakai tare da sanya hannu ta share hawayenta wayarta nata ring ta kasa ɗagawa sai Khalisee ce ta ɗauka tace “Yane Rash?” Kallon Beebah tayi ta miƙa mata wayar ta karɓa ta kashe hakan ya tashi hankalin Rash wannan shine karon farko da Beebah ta kashe mata waya hakan ya hanata nutsuwa ta ɗauko mota ta fito batare da kowa ya sani ba ta nufo gidan sarautar.
A dakin Kilishi kuwa babu hankalin wanda bai tashi ba yanda duk dauriya da basarwa na Beebah ta kasa jurewa ciwon da kecin Zuciyarta ta kifa kanta saman katifa take wani kuka me cin rai, rarrashin duniya taƙi yin shiru ganin abin nata bana nutsuwa bane yasa Kilishi ɗaukar waya ta kira Habeeb yana gaban Mai martaba lkcn ganin me kiran yasashi miƙewa yana cewa “Shikenan Allah ya taimake ka amma fah bazan fasa jaddada maka ba banason wannan haɗin ku barshi zaifi alkhairi idan kuma kun dage kuyi abinda zai faru gaba kuma nima bansanshi ba saboda raita Habeebah kawai takeso…..”

 

Binsa Mai martaba yayi da kallo tare da ayyana abubuwa da yawa a ransa yaja ƙwafa yace “Bantaɓa hukunci Anja ba sai a kanka kasani Habeeb bazaka taɓa samun wannan bamagujiyar ba zansa a ɓatar da ita a duniya tunda ta kasance silar saɓawa umarnina”
Habeeb part ɗin Kilishi ya nufa ya ishe su sun sata a gaba sai aikin rarrashinta sukeyi da tambayar abinda yasata kuka amma taƙi magantuwa ya taka ya tsaya akanta suka janye ya tsugunna gaban gadon ya dafa kanta yace “Habeebatullah” janyewa tayi ya fincikota da karfi ta wuntsilo jikinsa ya ɗago kanta ya sanya Harshensa ya lashe hawayen tare da jorner bakinsa cikin nata ta saki ajiyar zuciya me ƙarfi tasa hannunta tana tureshi.
Kallon kallo aka shigayi tsakanin Hudah Khalisa da Rasheedah Da ƙirjinta yake bugawa da ƙarfi wani abu yana tasowa daga ƙasan Zuciyarta ta kafesu da idanunta cikin tsoro tace “Ya hayyu ya ƙayyumu….” Janye bakinsa yayi daga nata yana shafa sumarta yayi musu wani irin mugun kallo da basu Hudah ba hatta Rash Saida ƙirjinta ya buga sumsum suka fice daga ɗakin, yayi ƙasa da muryarsa yace “Meyene to ko tafiyar ce kikeso na fasa?” Ajiyar zuciya tayi ta girgiza masa kai yace “Uhm inajinki faɗi ayi Miki yanzu uwar ƴaƴana” sake lafewa tayi a jikinsa tace “Idan kace kanasonta mutuwa zanyi….” Da sauri ya dago a firgice yace “Wa?” Sharrrr hawaye ya sulalo mata ta janye a jikinsa tace “bansanta ba kawai inajin kamar wani abu na shirin faruwa dani da zai iya zama ƙarshen alaƙata dakai Hero idan na rasaka ina zan kama?”

 

Tausasan yatsunsa yasa ya rufe mata baki yace “don Allah ki bari banson wannan muguwar fatan naki Habeebah duk da cewa akwai ƙura a gabanmu amma bantaɓa jin akwai ranar rabuwa tsakaninmu ba wlh ko zan rasu akanki na shirya daga jiya zuwa yau na ƙara tabbatar da cikar darajarki wadda a duniya babu wata mace da zata zomin da kalarta inganta bare har na tantance, Wyf kin zama sirrina Nima na zama naki ke kaɗai wlhl Azeem matsayinki bazai taɓa daidaituwa da wata ɗiya mace a duniyar nan a zuciyata ba ki riƙe wannan a ranki duk inda Hero ɗinki yake yana tare dake a zuciyarsa…..”
Hugging ɗinsa tayi tayi kissing lips ɗinsa tare da lumshe idonta tace “Same to you and double love you….” Sake haɗe bakinsu yayi ta janye tanajin wani mugun tsoro saboda yanda taji Sandarsa tana wani yunkurin miƙewa ta kuwa shammaceshi tayi fit ta fice, yayi murmushi ya miƙe yana saita kansa ya fito parlourn bai ganta anan ba hakan ya tabbatar masa ɗakinta ta gudu….

 

Rasheedah ce ta buɗe ƙofar ta shiga ta tsaya jikin ƙofar ta zubawa Big hips na Beebah idanu itanma kallonta takeyi ta cikin mudubi Rasheedah ta tako ta iso bayanta ta tsaya idanunta kafe akan Beebah ta zatayi mgn tayi saurin dakatar da ita da cewa.
“Zan iya sadaukar da kowanne farin ciki banda shaƙuwata kuwa rayuwata Rasheedah ke ƴar gata ce koda mahaifiyaarki ta mutu ta barku cikin gata gaban mahaifinku me sonku da baku kulawa nikuwa nawa iyayen suna a raye amma sun barratani da kansu saboda bambancin addini al’ada da kuma aƙida da kuma uwa uba rashin sanin haƙƙin zuciya,
Rasheedah na yarda shine ƙaddarata abinda yake faɗamin kullum Nima nice ƙaddararsa bansani ba ko gaske ne duk da inajin a raina Bazaimin ƙarya ba yanajin fiye da abinda nakejin akansa. Rasheedah Habeeb Shine Rayuwata shine ƙaddarata kuma shine duniyata ki sani duk wanda ya shiga tsakanina dashi zai zama silar yankewar numfashina…..”
Zama Rasheedah tayi saman kujera saboda jirin da taji yana ɗaukar ta tace “Meye alaƙarki dashi?” Sunkuyar da kanta tayi tace “Mijina ne…..” “Wht?” Ta faɗa tana miƙewa itama ta miƙe tace.

 

Na daɗe ina faɗa Miki Ni matar aure ce kina banzatar da furuci na Rasheedah auren Hero shine ya kawoni Masarautar Dutse a matsayin ƴar aiki ya kawoni Kilishi tace nafi nan ta bayyana Ni matsayin tsatso cikin tsatsonta sunana matar aure ba kamar kowacce mata ba domin kowacce mata dangin mijinta sun santa a matsayin mata, Ni kuwa kilishi ce kawai ta sanni matsayin suruka amma ko abokaina su Hudah basusan matsayina a wajen yayansu ba duk da cewa sun jima da ɗora ayar tambaya akansa game da lamari na, kiyi hƙr bansan cewa zakis…..”
Rufe mata baki tayi tana murmushi tace “nice ya kamata na baki hƙr da nayi azarɓaɓin furta Miki kalamin daya tayar da hankalinki akan mijinki Wlh da wata ce ba ke ba da har gaban abada abotarmu ta watse kiyi hƙr Habeebah inda gaban abada na cire mijinki a raina zan tayaki addu’a ku rayu cikin aminci dashi…..”

 

_Idan kika karanta min littafi baki biyani ba ban yafe Miki ba, idan ka/ki karantamin littafi a YouTube batare da izinina ba Allah ya fitarmin da haƙƙina a kanki/kanka da gaggawa_
[5/4, 8:11 PM] AM OUM HAIRAN:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button