Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 13

Sponsored Links

13

*_BAYAN SATI BIYU_*

 

Related Articles

“Daddy game da maganar ahmad da aysha” mummy sa’adah ta fadi tana lanqwasawa daddy hular da zai fita da ita
“Uhmmm…ina jinki…tace wani abu ne?”
“Eh….maganar gaskiya yarinyar nan daddy sai nake ga kaman bata sonshi…bata fito kai tsaye ta furta ba….saidai yanayinta yadda ya nuna tana cikin damuwa,kasan kawaici irin nata ba zata fito kai tsaye ta fada ba” shiru daddyn yayi kadan yana nazari….yayin da mummy keci gaba da taimaka mishi yana shiryawa,bakinta fal da addu’ar Allah yasa zancan nata ya samu gurbi,don maganar gaskoya ba zata so ace dan hajiya larabar ya auri ayshan ba,ko don kare qimarsu a idanun sauran qawayensu
“Bari naje na dawo…sai muyi maganar”
“Shikenan…..amma dai gaskiya daddy kar muyi abinda zamu cutar da yarinyar,kaga tamkar amana ce a wajenmu”
“In sha Allah” yace mata.

Tana zaune cikin kujerun roba dake tsakiyar flowers din da aka qawata gidan da su,cikin kwanakin duk ta takure kanta saboda jarabawa,hakan ya sanya bata da wani cikakken lokacin kanta,tana jin bata da wani gata daya wuce karatun shi yasanya ba zatayi wasa da damarta ba,ta sani cewa duk randa ta kammala karatunta zaiyi wuya idan ba qauyensu zata koma ba,don bata ga wani dalili da zai ci gaba da zaunar da ita cikin gidan ba tana zame musu nauyi bayan duka dimbin halaccin da sukayi tsawon shekaru suna yi mata,don haka ba zatayi wasa da damarta ba,zata tsaya tsayin daka taga ta samu abinda ta samu wanda zata tsira da shi koda ta komawa can din.

Ko kadan bata ji tahowarshi ba saboda yadda hankalinta yayi gaba,daddyn shi ya soma ganota,a nutse ya karanceta,sai yaga ta rame din,wanda yake a badini karatun da take tuquru ne ya kawo hakan,bai mata magana ba ya wuce ganin tayi nisa cikin karatun ta.

Qarar bude get da fitar motar daddyn ita ta dawo da ita,ganin ya riga daya fice saita maida kanta taci gaba da karatunta.

????????????????

Qarfe sha biyu na rana yayi sallama da anninsa a filin tashi da saukan jirgin saman malam aminu kano,wadda zata wuce saudiyya don yin umara,shi da sulaiman da farouq suka rakata suka juyo,kan hanyarsu ta komawa company ya bawa drivansu umarnin su wuce jami’ar bayero don yiwa wani abokinsa zuwan na zata,Dr mansur amini ne da har gobe khalipha baya mance halaccinsa a gareshi,hakan ya sanya yake matuqar girmamashi.

Duk inda motocin su suka ratsa sai idanu sunyi kansu saboda kyau da yadda suke daukar idanu,guri na musamman suka aje motocin nasu,yana yunqurin fitowa ya hango tahowarta daga nesa,cikin hanzari ya maida qafarshi tare da rufe murfin motar,ta cikin baqin gilashin motar ya zuba mata idanu har tazo ta wuceshi bata sani ba,su uku ne ita da wasu yammata kamarta da alama qawayenta ne,sai data wuce sannan ya fito suka nufi office din DR kai tsaye.

Sosai yayi murna da zuwan bazatan da khalipha yayi masa,sun jima suna hira har haidar ya qosa ya fice acewarsa zai shiga capteria yaci abinci kafin su gama,don baiyi breakfast ba suka fito
“Saika dawo…amma karka bata mana lokaci,muna da abubuwan yi da yawa da muka baro a company ka sani”
“Zan dawo da wuri in sha Allahu” ya fada yana fita da dan sauri yana wulga qafarshi kamar zaiyi ball da wani abu.

Ita daya ce zaune saman table din,hannunta riqe da littafi tana dubawa,duk da rabin hankalinta na wajen aliya data zaunar da ita a wajen,kwata kwata zata iya irga yawan zuwanta wajen,don sam ba wajen zuwanta bane,jinta take duka a takure.

Bata ankara ba taji fallatsowar abu ta gefan fuskarta zuwa hijabin jikinta mai sanyi,da sauri ta daga kai dai dai sanda haidar ke fadin
“Subhanallah….sannu don Allah” sosai lemon ya bata jikinta,amma ba wannan ne ya dameta,ta handout dinta take,ganin bata dubeshi ba ya sanyashi sake cewa
“Am sorry pls madam kiyi haquri don Allah,wallahi ban sani ba….”
“Babu komai…” Ta fada cikin hanzari tana miqewa ganin yadda hankula suka soma dawowa kansu abinda bata so kenan
“La la la…..aysha garin yaya?” Aliya dake takowa zuwa wajen ta fadi tana duban haidar dake tsaye cikin rashin jin dadi,sam aysha bata kula da ita ba da tuni ta tareta,saboda sarai tasan halin aliyan
“Bai sani ba aliya…muje kawai” ta fadi tana son janye aliyan
“Amma dai malam baka kyauta ba….duba yadda kayi mata da jiki fisabilillahi”
“Aliyaaaaa….bai sani ba ya kuma bada haquri…muje don Allah” ta fada tana janye da hannun aliyar
“Am so sorry kiyi haquri” ya sake fada yadda zata jiyo
“Is ok” ta amsa ba tare data waiwayo ba,sauke ajiyar zuciya yayi bayan yaga sun fice,duk da aliya saidata juyo ta watsa masa harara,sam bai zaci zatai sauqin kai haka ba,yayi mamakin yadda ta nuna babu komai cikin sauqi tayi tafiyarta,dama har yanzu akwai yammata irinta?,komawa ya sakeyi reception ya sake order din wani abun shan yace su hado masa da abincin da yace yana so.

 

????????????????

Zaune take gaban daddyn tana sauraron bayaninsa,wanda batasan daga inda aka samo wannan hikayar ba
“Badon mummynki ta ankarar da ni ba aysha ai zan tsammaci kin aminta da ahmad dinne….tunda dai haka ne babu takurawa zan musu bayani su janye…Allah ya kawo miki wani na gari ya hada hankulanku waje daya” amsa masa kawai da amin,don bata da wani abin cewa,miqewa tayi zuwa dakinta tana jujjuya maganar daddyn,hakanan taji babu dadi har ranta,ita dai abinda ta sani batayi maganar kowa da ahmad ba baya ga aliya,bata ce tana so ko bata so ba,a daren abun ya dan dameta,amma da yake ba wani sanyashi tayi can cikin ranta ba zuwa safiya ta rage tunawa da abun,ta saka karatunta a gaba,wanda yake final exam ce suke dab da fara zanawa.

Wannan abu shi ya kusa kawo baraka tsakanin mummy sa’adah da mummy laraba,mummy sa’adah taso wanke kanta,amma da yake ba abinda mummy laraban bata sani ba na mummy sa’adan kallonta kawai tayi,hakan bai hana ahmad ci gaba da kiran ayshan ba.

Cikin wata guda suka kammala jarabawarsu,komai yazo mata a saqi fiye da yadda ta zata,saidai ba abun mamaki bane hakan saboda ita kanta tasan ba qaramin karatu tayi ba,sai fatan samun sakamako mai kyau ta yadda zata samu damar dorawa daga inda ta tsaya

????????????????

Qarfe biyar da rabi na yammacin ranar,tana kan hanyarta ta dawowa daga gidan anty halima babbar diyar mummy data aiketa,bata wani jima ba ta dawo don sam babu sabo ko sakewa tsakaninta da ita,saboda kusan halayyarta daya da asma’u,abinda ya rabasu kadan ne,kusan photocopyn ta ce asma’u.

Dan uban horn aketa maka mata tunda ta sauka daga napep ta gangaro layin su,a dan sace ta waiwaya,mota ce qirar pilot baqa wul,tun daga glasses har jikin motar baqi ne,sheqi kawai take da daukar ido,tsoro ne ya kamata saboda yanayin layin nasu da bai cika jama’a ba,hatta da habu mai trader da ba’a rasashi qofar gidan da yake aiki yau baya nan,hakan ya sanyata qara dan uban sauri cikin yunqurin isa gida ko zata samu ta tsere,saidai haqanta bai cimma ruwa ba,tana dab da qofar gidan ya samu nasarar tare mata hanya,cak ta tsaya tana maida numfashin tsoro har zuwa sanda mamallakin motar ya bude ya fito,matashin saurayi ne wanda kallo daya zaka masa kasan kudi ilimi da hutu sun ratsashi yadda ya kamata,sanye yake cikin dinkin shadda jamfa da wando kanshi babu hula,fuskarsa dauke da murmushi ya zagayo inda take tsaye
“Kinga na kamaki babu inda zaki kuma guduwa tunda kinqi tsayawa” tsoro ne ya sake kamata,ya kamata kamar yaya,idanunta ta dan zaro tana satar kallon gefe da gefenta ko zata samu wanda zaya ceceta,mahaukacin horn din da aka danna daga bayansu wanda ko qarar tahowar motar ita bata ji na ya sanyata zabura saboda tsoro,waiwaya sukayi duka su biyun ita da wanda bata mako san sunanshi ba suna dubanta,asma’u ce ta fito,tana sanye da doguwar riga ta atamfa mai gajeran hannu,wuyanta nannade da dan qaramin mayafinta,yayin da qafafunta ke saye da hillshoes,glass din fuskarta daya kusa mamaye rabin fuskarta ta zare tana dubansu tare da takowa inda suke
“Hafiz…..” Ta ambata da alamun mamaki,bai amsa ba kuma baida niyyar amsawa,don shidin ba wani ganeta yayi sosai ba
“Ke aysha me kike a nan….dalla wuce gida” ta fada cikin hargagi,daman jiran hanya take,sam tsaiwar bata yi mata saboda rashin sabo,saboda haka da hanzari ta nufi get din gidan ta tura ta shige,ajiyar zuciya ta sako sannan taci gaba da takawa a hankali zuwa ciki.

A falo ta tadda mummy zaune cikin lesukan da take saidawa
“Kin dawo?”
“Eh na dawo mummy….tana gaidaki”
“Lafiyarki qalau kuwa?”ta fada tana qare mata kallo
“lafiya lau” ta fadi tana miqa mata kudin data ciro daga jakarta ta soma yi mata bayani.

Suna tsaka da lissafi asma’u ta fado falon tana huci
“Mummy….ki jama yarinyar nan kunne,tana neman ta janyowa kanta abinda yafi qarfinta don bazance yafi qarfinmu ba” maida hankalinta mommy tayi kan asma’un tana dubanta
“Wani abu ne ya faru?”
“Sai data zauna ta jefar da jakarta gefe sannan tace
” kinsan da waye na gansu a tsaye kuwa?”
“Waye ne?” Mummyn ta sake tambaya tana yatsina fuska idonta kan asma’un
“Fahad mummy dan gidan IG fa?,batasan bata kai can ba?,zata debo abinda zaya zo yafi qarfinta,koda yake ita daya zaya dama wallahi,ke har kin isa tarayya da maza irin hafiz?,kinsan yawan matan dake sonshi,kyau da kudi?” ta qare maganar tana duban aysha da wani wulaqantaccen kallo,ajiyar zuciya mummy ta saki wanda ke nuna bata zaci abun baikai can inda take tunani ba,yayin da aysha ke rabe zaune a gefe guda kanta na kallon qasa,gaskiyar asma’u zalla take gani cikin maganganunta,gaskiya ne,ita din ba kowa bace,ita din batakai matsayin kowa ba,don me zata tsaya da wani?,don me zata tsaya da wanda ya amsa sunan wani?,to amma abu daya ya kamata a mata uzuri a kai,bata bashi dama ba,bata kuma saurareshi ba
“Ko aure zaki indo baki kai ki auri dan gidan IG guda ba,ko yace yana sonki bai san ainihin wace ke ba,koda ya sani kuwa to yaudararki yake…..ki bari miji dai dai ke yazo miki amma ba irinsu hafiz ba,don wannan yafi qarfin kanki” ta rufe maganar tana bayyana inda ta dosa kai tsaye daga qarshe
“Allah ya kyauta…ke saiki kiyaye” cewar mummy tana ci gaba da lissafinta,gefe guda na zuciyarta tana ganin dacewar abinda asma’un tayi
“In sha Allah” shine kawai abinda tace tana miqewa hadi da daukar jakarta ta wuce daki.

Kallo mai kama da harara asma’un tabi bayan ayshan da shi,taso tattauna zancan da mummyn amma sai ta fuskanci hankalinta na kan business dinta,bata wani tsawwala ba ta wuce nata dakin tunda ta cika burinta.

????????????????

Yammacin ranar lahadi ne wanda yake dai dai da kusan watanni uku da kammala jarabawarsu,sanye take da riga da skert na atamfa brown wadda aka yiwa ado da yarfin yalo,hijabi ne a jikinta wanda ya sauko mata iya gwiwarta,fuskarta babu adon komai sai powder da man lebe data shafa bayan ta kammala yiwa daddy da ya yini yau a gida abincin dare,ita daya ce zaune cikin lambun gidan saman wani lilo dake daure tsakiyar shukokin dake cike a wajen,sosai takeson wajen yana kuma burgeta,yana debe mata kewa ba kadan na,takan iya shafe tsahon a wanni a wajen ita daya bata komai sai tuna rayuwarta mataki zuwa mataki,har zuwa bigiren da yau ta kawota kai,sau tari idan aka nemeta aka rasa cikin gidan to tana maqale ne a wajen,wajene da mutan gidan basu damu da shi ba,ta alaqanta hakan da basu san sirrin dake wajen ba da irin ni’imar daya tara ba,yakan tuna mata rayuwarta ta qauye sosai,duk da cewa ba wani abun burgewa sha’awa ko dadi a ciki da zata iya dorarwa,a yanzu ma lilawa take kadan kadan,idanunta na kafe waje guda tana kallonshi,wayarta dake saman cinyarta tana fidda sautun karatun kitabuttauhid na malam ja’afar mahmud adam,ta nutsu sosai tana jin karatu hadi da fahimtarsa kamar tana gaban malamin,mayyar karatun addini ce,tana da bibiya da kuma kiyayewa,babu wani karatu da idan tana saurararshi yake sakata nishadi irin karatun addinin islama,kada ma ace hadisi take saurara,wanda yawanci tafi son taji karatun Dr ahmad BUK.

“Ke…kizo daddy na kira” ta tsinci muryar asma’u a tsakiyar kanta,batasan yaushe ta shigo wajen harta qaraso inda take ba,kanta ta daga tana duban asma’u dake sanye da fitted gown,kanta babu dankwali sai gashinta mai santsi dako yaushe ke cikin gyara yake matse a ribbom,kunneta maqale da earpiece wanda sanyashi ya zame mata kamar al’adarta,hakan kuma baya rasa nasaba da yawan jin kade kade da take da shi
“Tom” ta amsa tana tsaida karatunta
“Yauwa…idan mun shiga ki yiwa daddy godiyar mota” tana gama fada ta juya abinta ta wuce,sam ta mance wacce mota ma,sai data zo shiga cikin gidan data sake ganin motocin ta tuna,motocinsu ne da daddy ya musu alqawari ya kuma cikasu guda biyu ita da asma’un,tuni asma’u ta soma hawa tata,saidai ita ko lasisin zuwa kusa da motar bata samu ba bare ta hau ta tuqa,kasancewar a sanda motocin suka iso daddyn baya nan,tafiya ta kamashi na sati hudu,andai danqa mata muqullin ta riqe sau daya,bata juyashi sau biyu ba mummyn ta karba daga hannunta,daga ranar ba’a sake mata maganar ba,taga dai asma’u na hawa tata har makaranta sai data shiga da ita,ko sau daya bata sake tunawa da wani batun mota ba,bata a cikin lissafinta ko sau daya bare ta damu da lamarinta,bata manta ba a qauyensu ko jaki sai ta manta rabonta da hawanshi balle mota,tana can cikin uqubar data fi ta kurkuku,yaushe ma zata tuna da wani abu.

“Indon baffale” daddy ya fada a sanda ta gama gaidashi yana murmushi,sau tari yakan kirata da hakan Idan yana cikin nishadi ko yana son jefa murmushi bisa fuskar ayshan,duk da sunan yana da babban naqasu nashi na qashin kansa,amma har kwanan gobe tana farinciki da alfahari da shi,tunda ko babu komai DA UBA AKE ADO.

yadda daddyn ya maida yanayinshi kadai ya isa shaida maka cewa muhimmiyar magana ce zaiyi da su,hakan ya sanya kowa ya bashi hankali da nutsuwarsa a sanda ya soma magana
“Na godewa Allah daya nunamin lokacin da kuka kammala karatunku cikin nasara,ba shakka nayi alfahari da hakan yadda kuka kama kanku da mutuncinku,alhamdulillahi….toh,dukkaninku ina zaton ba wadda bata haure shekara a shirin ba…saboda haka abu na gaba da nakeson kowaccenku ta sani shine….aure nake da burin naga kunyi,a yanzu shine abinda ya rage muku,duk da ke indo bamuyi haka da ahalinki ba,munyi dasu zan maida musu dake a duk sa’ilin da aka kai wannan bigiren,amma na tabbatar da cewa ba zasu qi ko suyi jayayya da wannan batun da nake muku a yanzu ba,don suma ina da yaqinin shine hukuncinsu na gaba a kanki” a hankali taja hanci tana dauke tagwayen qwallar data ziraro daga idanunta,bata jin sun damu da rayuwarta bare suyi wani kyakkyawan tunani game da makomarta,ba wanda ya biyo sahunta tunda ta taho,ba wanda ya damu yasan inda take rayuwa,babu wanda ya damu da sanin wani hali taci gaba da kasancewa bayan barowarta mahaifarta,duk da tasan cewa basa maraba da hakan amma a qalla zata ji dadi idan wani ya bibiyeta da sunan ahalinta ne shi,ita dai tana godewa Allah da yaji qanta ya dubi rashin gata da galihu irin nata,ya jefo mata da daddy cikin rayuwarta a lokacin da take cikin tsananin buqatar matallafi,wanda zai jibanci lamuranta,bangon da zata dafa taji dadi
“Ammm….auta” ya kira asma’u
“Na’am daddy” ta amsa cikin fara’a
“Ina fatan kin samu wanda kikeso kun kuma daidaita kanku” kai ta kada cikin sauri
“Eh daddy…ka manta da hamid?…dan gidan alhj kutama?”
“Af….anyi haka,ja’ira ko kunyata bakiji ko?,ba zaki bari mamanku ta gaya min ba?” Fuskarta ta rufe da tafin hannunta tana dariya,shima dariya daddyn yayi kafin yace
“To ma sha Allah,babu damuwa,hamid ai dan gida ne,sananne ne…amma duk da haka zanyi bincike,zan nemeku daga baya ke da shi duka”
“Toh daddy” ta fada cikin murmushi,wani farinciki ke ratsata na daban,tana jin kadan ya rage mafarkinta ya tabbata,saura kadan ta shiga sahun manyan mata,wadanda za’a kira ko a nuna ace matar wane ce ko surukar wane ce,ahalin alhaji kutama ko qaramin yaro yasan nasibin da suke dashi bare babba,lallai zata tserewa sa’a nan kusa.

“Indo aisha…..kinsan hafiz?….hafiz yaron gidan IG….” Mummunar faduwar gaba ce ta ziyarci asma’u,ashe hafiz bai bar aysha ba,duk abinda ta fada mishi kan ayshan kenan bai masa tasiri ba,meke shirin faruwa?,lallai dole tayi wani abu,bai kamata aysha ta auri kwatankwacin wanda ita ta aura ba,har abada aysha na qasansu kuma zata ci gaba da tabbata a qasansu,ba zata yarda ko ta bari suyi gasa ko komanceceniyar jin dadin rayuwar gidan aure ba,yayin da qwaqwalwar ayshan ta tafi binciken mai sunan da daddy yake fadi,don ita harga Allah ta mance da babinsa
“Au hafiz daddy bai yarda ba?….kinji aysha ashe bai yarda da abinda kika gaya masa ba” ta fada cikin dariya dariya tana duban ayshan
“Kamar yaya?,me yake faruwa?” Daddyn ya fada fuskarsa na nuna alamun neman qarin bayani idanunsa tsakanin aysha wadda kanta ke qasa da asma’u
“Daddy kunyar aysha tayi yawa,dama na sani ba zata iya gaya maka ba,hafiz kafin yazo gareka ita ya soma samu yace yana so….to already akwai wanda takeso suka jima suna soyayya….infact sunma juna ma alqawarin aure,ta sanar masa shi kuma yace bai yarda ba,lallai shi ya ganta yana sonta,ba ruwansa da soyayyarta da wani tunda ba aure aka daura musu ba,tofa shine ya biyo ta wajenka” kai daddyn ke kadawa
“A’ah ba za’ayi haka ba….,ba yadda zanwa aysha auren tilas,shi wancan din ya sunanshi?,waye shi?” Tashin farko khalipha shine wanda ya fado ranta,babu wanda ayshan ta dace da shi irin khaliphan,ta tabbatar idan ta aureshi ayshan ta daina tarayya da ita cikin komai,tana da yaqinin bashi da qarfin da aysha zata samu jin dadin rayuwar aure makamanciyar tata ma bare irin tata,ba shakka yaron oga shine dai dai da aysha,qwarya tabi qwarya
“Sunansa muhammad abba”
“Ba komai…ki bani number dinsa,ni zan kirashi da kaina mu zauna nasan wayeshi” cikin sauri ta fiddo wayarta ta dauki wayar daddayn ta soma loda masa number khalipha.

Ji take kaman ba kanta ake maganar ba,tunda ita iya saninta dukkan maganganun da ke wanzuwa tsakanin daddyn da asma’u ba wanda tasan ya faru akanta,bata gane cewa da ita ake ba saida daddyn ya soma magana cikin tsokana
“Wannan kunyar indon baffale har yanzu bata ragu ba,fulatancinki na jikinki…kinje jami’a amma babu abinda ya ragu,yanzu badon Allah yasa ma’u tayi bayani ba na miki auren dole fa?” Ya qarasa maganar cikin sigar zolaya,wani sanyi taji yana ratsata a sanda ta fuskanci kanta ake dukka wadan nan maganganun,qwaqwalwarta ta tsaya da tuna komai bare ta samu abin fada,hakan ya sanya ta sake dunqulewa waje daya,yar dariya daddy yayi ga zatonsa tsabar kunya ke dawainiya da ita,kusan bata kuma gane meke gudana ba,daga qarshe dai ta fahimci daddy ya sallamesu,asma’u ta kama hannunta ta miqar tana zolayarta cikin kissa da kisisina,zolayar datake ganinta kamar a majigin kallon fina finai,saboda tsahon zamanta da rayuwarta da asma’un bata taba ganin murmushi kan fuskarta zuwa gareta ba,idan ko tayi murmushin to na mugunta ne ko cimma nasarar wani muradi a kanta
“Indon nan har yau daddy taqi ta waye wallahi,har yau indon qauye ce,na rasa ta yadda zan canza ta,tashi mu tafi karki nutse a wajen” ta ambata tana jan hannunta tana dariya,binta kawai tayi kamar wata shashasha har suka fice daga falon suka doshi nasu gefen.

_gaisuwa da godiya a gareku masoya na cikin grps namu na zafafa paid grp,da daurin boye grps_????????????????????????????

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA MAI BUQATAR SIYA ZATA TUNTUBI WANNA NUMBER*
0803811300

*DB*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button