Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 16

Sponsored Links

16

 

A duniya babu abinda ta tsana ta gani kamar ni,ban taba ganin tsana qarara daga idanun wani dan adam zuwa wani ba irin wadda nake gani daga idanun mahaifiyata zuwa gareni”ta fada muryarta na rawa alamun gabar da tazo tana taba zuciyarta matuqa gaya fiye da duk labarin dukka wahal halun data sha a baya
“tunda ta bar gidanmu……” Sai ta kasa ci gaba saboda kukan daya qwace mata,tayi matuqar qoqarin riqe sautin kukan saidai ta kasa,hakan ya sanya ta qudundune kanta cikin hijabi ta soma sakin kukan nata bayan ta toshe bakinta.

Related Articles

Shuru khalipha yayi tamkar baya wajen,saidai idanunsa idan ka kalla har sun soma sauya kala kadan,wani abu yake hadewa mai daci daga harshensa zuwa maqogoransa,labarinta ya taba wani sashe mai girma na tashi rayuwar,saidai babban abun al’ajabin yadda qiyayya mai qarfi ta qullu tsakanin uwa da ‘yarta,garin yaya?,meye sanadi?,zaya so yaji amsa,baice da ita komai ba hakanan bai tsaidata ba har sai data rage kadan daga cikin radadin da take ji cikin zuciyarta,ta sanya hijabin nata ta soma goge fuskarta,hannunsa ya saka ya laluba aljihunsa da yake baya rabo da hanki,zaro shi yayi ruwan madara mai kyau da taushi da qamshi ya aje a tsakiyarsu,sai data kalleshi da idanunta da suka dan tasa saboda kuka sannan ta saka hannu ta dauka cikin sanyi tace
“Na gode” sai data goge fuskarta sosai sannan ta miqa masa,kai ya kada alamun ta riqe,bata sake cewa komai ba ta dunquleshi a tafin hannunta sannan ta miqe tsaye tana cewa
“Ina zuwa” bai ce mata komai ba har ta juya ta fice daga lambun,tana fita wayarsa daya boye cikin aljihun wandonsa ta dauki vibration,a hankali ya zarota yana duba mai kiran nashi,P.A dinsa ne da suka zo tare,ya latsa ya kara a kunnensa
“Sir…..har yanzu baka gama ba….we r waiting”
“Kuna iya zuwa wani waje kafin na gama,idan na gama zan kiraku”
“Okey sir” ya fadi suka katse wayar baki daya sannan ya maidata aljihun wandon ya sake hade yatsunsa cikin junansu kamar yadda yake a baya.

Daga nesa ya hangota dauke da gorar ruwa data lemo hade da cup,gabanshi ta qaraso ta zauna a inda ta tashi sannan ta tsiyaya ruwa da lemon ta aje gabansa,turasu yayi suka koma gabanta,yana nufin ta dauka ta sha,sai ta kauda kanta kadan don ba zata iya shan abu gabansa ba,don ba sabonta bane hakan bata iyawa,ganin bata dauka din ba ya sanyashi cewa
“Uhmmm….” Ta gane manufarsa,hakan ya sanya ta dora cikin muryarta mai sanyi
“Tunda ta bar gidanmu bata taba wucewa ta qofar gidanmu ko bayan gidanmu ba,gaba daya ta daina bin layinmu,hakanan duk wani abu daya hadata alaqa da gidanmu ta barshi,sau tari idan aka aikeni zan lallaba na tafi gidansu ummina,na tsaya soro ina leqenta,saboda nasan idan na shiga me zai biyo baya,duka ne kuma na shashi babu adadi,hakanan idan labari ya kai kunnen inna yelwa cewa naje gidan nan ma itama tana kamani ta daka iya son ranta,harda dungurin kai,akwai sanda irin haka ta faru,ummi na ta kamani ta nada sannan ta gaggayamin maganganu da a sannan na kasa gane kome take nufi,ina komawa gida da aiken da inna yelwa ta yimin itama ta kamani ta yimin duka,ina tsugunne kusa da turken awaki ina kuka sabira ‘yar kawu auwalu wadda ta dan girmemin tazo shiga bayan gida,tsaki taja bayan ta dunguren kai na
“dama zaki haqura ki daina bibiyar waccar tsohuwar taki mai baqar zuciya da shegen ruqo,don ba zata taba sonki ba saidai zaki koma cikimta ta haifoki cikin wani ahalin ba wannan ba” maganar tata ta tsayan a raina,nayita jujjuyata saidai na kasa fano bakin zaren,a sannan akwai quruciya tattare da ni saidai manya manyan laguzzan dana haddace basu da iyaka wanda ake gayan,wasu ina girma ina ganesu ina warwaresu,wasu kuwa har kwanan gobe bani da amsarsu bani damai zaunar da ni ya warwaren.

Qiyayyar da mamana kemin tayi grman da kaf qauyenmu sunsan me ake ciki,da yawan mutane abun na basu mamaki da al’ajabi,sai wasu suka soma min qazafin anya ba shege na tayi ba koma shine sanadiyyar sakinta da akayi asirinta ya tonu,kalmar shegiya na santa tun a qananun shekaruna….saboda akwai wata ‘yar qauyenmu data taba cikin shege ta haife,irin tsangwamar da naga ana nuna mata da ‘yar data haifa qarsge ma tabar garin nasan cewa ba qaramin mummunar abu bace,saidai gakan ya taimaka min qwarai wajen kare kaina da kare mutuncina wanda ba wanda ya damu da shi,kusan kalmar shegantaki daga gidanmu ta fito,daga bakin kakata ta soma fitowa.

Kullum ta Allah saina je gidansu ummi na labe a soro komai jibgar da zan sha idan ta ganni bai dameni ba,wataran naci kuka na na qoshi idan na hangota a tsakar gida,abu daya ne ya sanya na rage zuwa na janye jiki sanda ta furta cewa zata tsinen idan ba rabu da ita ba,na kuma san illar tsinuwar itaye wa yaransu ta sanadiyyar makarantar dare da na saka kaina nake satar jiki naje da daddare idan aikeni,inacin duka a nan ma da dunguri duk sanda naje na jima din,inda Allah ya taimakeni ba’a taba gani na ba cikin daliban bare aje ace an ganni a hanani zuwa tunda babu wanda yake zuwa cikin yaran gidan.

Allah ne ya hada jini na da malamin makarantar darenmu malam musbahu,yanayin rayuwar da yaga ina fuskanta ya sanyashi tausaya min sosai,yana taimakamin gun karatuna,dalili kenan daya sanya na zama zaqaqura cikin daliban,sau tari yakan ban sabulun wanka dana wanki,saidai baya bani zallar kudi,sabulu dai yana taimakan da shi,hakanan yana bani shawarwari wanda hakan ya taimakan qwarai wajen saitan rayuwata,shi ya tsayamin ya nema min makarantar gwamnati dake cikin garin takai,manyan daya hada inna yelwa da su shi ya sanya ta haqura badon son ranta ba ta barni,amma fa wani lokacin ma sai an fita break nake zuwa,watarana ma idan taso tana hanani zuwa,duk da hakan na samu karatu sosai.

A sannan aka tada zancan aurara da yara matan gidanmu wadanda suke sa’anni na ne,kowacce tana da nata saurayin amma banda ni,a sannan ma na sha cari da maganganu kala kala,sam ban damu ba don ba wanda nake kulawa ko ince ba wanda ke kulani saboda rashin gata da kuma qazafin shegantaka da aka yimin,nima hakan ya yimin,saboda babban burina shine naga na kammala primary na naci gaba,haka aka soma shirye shiryen auren su su biyar.

To ashe suna qwafe da malam musbahu,ranan da naje karbar sabulu wajensa wanda ban taba haka ba amakaranta yake bani bayan an tashi,ranar ma na matsu ne zan wanke unifoarm dina da ban samu damar wankewa ba saboda gobe monday.

Ihu muka ji wanda bamusan daga inda yake ba,ashe talle ce faccalar inna kulu,tana daga cikin masu matsanta min fiye da kowa

Tana kishi da ummina ko sanda tana cikin gidan fiye da kowa,hakanan suna shiri sosai da inna kulu,duk da shirin ba don Allah da ma’aiki bane,hakanan bai kai har zuci ba.

Kalaman da mukaji yana fita daga bakinta shi ya daga mana hankali dukanmu nida malam musbahu
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’una,malam musbahu….indo….ashe masha’arku kuke aikatawa?….dama abinda kukeyi kenan shi yasa ko yaushe kuke liqe da juna?…wannan wacce iriyar masifa ce….yauni talle naga masifa quru quru da idanu na” kafin kace meye wannan ta tara mana jama’a,fadi take
“Wallahi na gansu…..na gansu da idanuna turmi da tabarya” abinka da qaramin qauye dake mamaye da duhun jahilci cikin qwaqwalen mafi yawa daga cikinsu nan suka yarda,suka soma mana tofin ala tsine harda masu shirin dukanmu,ba shiri aka miqamu hannun mai gari a can gidan na kwana,a ranar naga tashin hankalin dama jima banga irinsa ba,duk da ban wani damu sosai ba saboda ni nasan cewa muna da gaskiya babu abinda mukayi,har wayewar gari zuwa yammaci maganarmu ake zuzutawa ana yayatawa cikin qauyenmu da kewaye,mai gari masanin ilimin addini ne,hakan ya sanya baiyi hukunci da ka ba saida yayi kyakkyawan bincike

Kowa ya shaidi malam musbahu hakan shi ya wankeshi ya wankeni a idanun wasu,yayin da wasu suka zauna daram kan zancan inna talle ciki harda ahalin gidanmu kafff,hakan ya sanya ma wasu daga cikin jahilan iyayen yara suka soma janye ‘ya’yansu daga makarantar,hakan ba qaramin bata ran malam musbahu yayi ba,dalili kenan daya sanyashi tarkata ya nasa ya nasa yabar garin,wanda hakan niba qaramin sake sakani yayi cikin halin ha’ula’i ba,don dama tun kafin yabar garin aka hanani zuwa makarantar,ko nan da can ma an hanani fita,ina turke a daki kamar akuya daure cikin mari,komai saidai a wurga min haka zan dauka naci komai muninsa idan naji yunwa ta kamani qwarai,duk wannan abun da ake ummina na cikin garin tana gidansu amma tamfar ma batasan me yake faruwa ba,ba motsinta ba gilminta,wannan shine abu na biyu daya sake dagulamin lissafin rayuwata,kuka nake ba dare ba rana,ina zaune a daki a daure,ba wanka ba wanki ba sallah,haka na dinga zama a dakin tsahon kwanaki.

Nasan zakayi mamakin ummina ko?,kace ina mahaifanta?,su basu isa su gaya mata taji ba?,mahaifinta Allah yayi masa rasuwa,tunkan rasuwarsa kuma mahaifiyarta ta rasu don itama ita kadai ta haifa,ta taso a hannun matar ubanta,duk yadda dangin mamanta dake jahar kaduna sukaso daukarta tun a lokacin babanta yaqi,haka suka haqura suka bar masa ita,itama ta danci wuya hannun matar ubanta,saidai ba wata mai yawa bace kasancewarta mai baki,tana iya qwatar kanta,kuma bata barin ta kwana bata yadda a danne ta ba,hakan kusan shi ya ceceta.

Inna kulu matar babanta macace mai azabar son abun duniya,ko yaya zaka bata to kaine mai daraja da mutunci,tana iya take gaskiya saboda kudi ko abun duniya,tana ganin dai dai indai kana miqa mata sai ta gaza gaya maka ko gyara maka haka rayuwarta kenan,dalili daya sanya sanda mahaifiyata ta soma girma tana amfanarta ya sanya bata iya yi mata gyara ko gaya mata gaskiya,saboda ko bayan rasuwar baaba taci gaba da zama a gidansu ne ba gidan wanda ta koma,cikin makusantan ummi da wanda ya isa da ita dama wanda bai isa ba ba wanda baisa baki ba kan abinda take gwadamin wanda ni bansan mafari ba,saidai duk wanda ya mata maganar tamkar ya kawo qarshen alaqarsa ne da ita,tun ana yi har aka gaji aka zuba mata idanu.

Ina cikin wannan halin labarin yin auren ummina ya sameni,na tsinceshi ne ina daga kurkukun da aka sakani,zaman da matan gidanmu keyi qasan bishiya na kisan dabe daga safiya zuwa yammaci,an baje kolin maganar kowa na tofa albarkacin bakinsa,a nan naji cewa a legos zata zauna,ta samu mijin ne cikin dangin mamarta dake birni,kusan duk wanda zai bude baki yayi magana a kai ba alkhairi zai fada ba,sai mugun abu yarfe da sharri,duk da cewa na danji kishin wani da zata aura bayan ga baba na amma na mata murna jin zata samu ci gaba ne,duk da bata damu da rayuwata ba,haka aka sha biki cikin garin na kece raini da tsone idon ‘yan adawa,yako tsone din,don zama na musamman akayi cikin gidan har na kwanaki biyu ana tattauna abinda aka gani wajen bikin da abinda ya faru,don faccalolinta banda inna talle da tata adawar ta bilhaqqi ce ba wadda bata je ba bata kuma riqo tsarabar gidan bikin ba,ina daga daki ina jiyo qarar motocin da suka zo suka dauki ummina tabar garin takai zuwa legos,a sannan kamar nayi tsuntsuwa naje na taresu na ganta koda ba zata min magana ba,koda zata dakeni,koda zata tsinemin din kamar yadda tace,don ban sani ba shin zan sake ganinta ko mun rabu kenan?,a haka ina hawaye har na daina jiyo sautin motocin.

Tun daga ranar ban sake ganin ummi na ba sai idan tazo garin ganin gida,duk sanda ko zata zo din zan saki jiki na jima a soron gidan baba ina kallonta,koda kuwa waye ya aikeni,ko aiken waye a hannuna,a sannan duka sa’anni na suna gidan aurensu,a masu shekaruna ni kadai na rage cikin gidan.

Wani zubin kuma hanyar da take bi nake zuwa na zauna,ina sane nake fitowa wai yadda zata ganni ko ta manta da ni ne,sau tari idan muka hada ido harara take cilla min ko taja min qwafa,ta rage duka na,don wani bin har tazo ta tafi ba zaka ga ta dakeni ba,hakan kuma ina zaton baya rasa nasaba da girma da taga na fara,saidai ban isheta kallo ba,ko muhalli kuma bata yarda mu hadanikam kallonta kawai nake yadda ta canza lokaci daya tayi kyau,a yadda naji mutanen gidanmu na gulmar mijinta yana da shi,tana kuma jin dadi fiye da gidanmu data bari nesa ba kusa ba.

A haka rayuwa taci gaba da garamin,ga girma na fara yi,a lokacinne na samu mutum daya yake kulani saboda qazanta ta da rashin gyara wato dan ladi,babu mutumin dana tsana a rayuwata sama da shi,saboda tantirin dan iska ne,haka nan cikakken dan shaye shaye,babu nau’in abun mayen da baya sha kaf cikar fadin garinmu an sanshi,a hakan kuma ‘yan gidanmu tayani murna suke an samu mai sona,idan dan ladi zai shekara bina da yimin magana bazan kulashi ba saboda haushinsa nake ji,a haka dai bai haqura ba yake bibiyata,duk da shima wani lokaci idan ya gaji yaba min maganganu yake
“Dalla can donma na rufa miki asiri nace zan aureki?,waye ma ya taba cewa yana sonki?,aibu fal tattare dake,uwarki ma data kawoki duniya gudunki take amma ni na bugi qirji nace ina sonki,banza mara rabo,kuma wallahi saina aureki inga ta tsiya” iren iren wadan nan kalaman yake jifa na da shi koda a hanya muka hadu gaban mutane,bama irin ranar da yake a cakensa.

A haka ummi na tayi haihuwar farko ta haifi mace,duk sanda tazo garin saina aika yara a zuwan qawarta ke aikowa a bani yarinyar ta dade a waje na,ina son yarinyar ina qaunarta sosai,inajin kamar ota kadai nake da ita a duniya,hakan ya sanya basma ta saba da ni ta shaqu da ni,sam ummi bata farga da hakan ba sai da basma ta soma wayo ta fara yawaita yi mata zancena,a nan naga tashin hankali,tayimin duka ta kuna koran gargadi mai qarfi babu ni babu ita,itama basman bata qyaleta ba,saidai ko gezau bamuyi ba,duka kuwa muna shanshi bama ya kamar sanda basman ta sake wayo,take debo kayan bayarwa cikin na mamanta da nata take kawo min,ranar dukanmu ta hada ta daka ta kuma jefoni waje tare da aikawa gidanmu ayimin gargadin zuwa gidansu tunda ba gidanmu bane,haka inna yelwa ta dinga bala’i da masifa,shikenan duk sanda tazo gari bani ba sake fita har sai tabar garin.

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKO SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*DB*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button