Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 2

Sponsored Links

0?2?

 

 

Related Articles

Kusan rabi da rabi take karatun,fiye da rabin hankalinta ya ta’allaqa ne akan wayarta,wadda ba komai take kalla ba sai wasu numbers wanda ke rubuce da sunan MAMA NA,ta kallesu yafi sau shurin masaki,ta kwatanta kira fiye da irgen yatsun hannunta saidai ta kasa hakan,ba wani abu bane ya jawo haka ba illa tsoro da fargabar abinda kiran zai biyo baya,taji ance bata ji dadi ba,tana so ta kirata ta mata sannu da jiki,saidai bata da wannan damar,ba qaramin qunar baqin wake take ba duk sanda tayi jarumtar kiranta,wanda hakan daga qarshe baya haifar mata da d’a mai idanu.

“Qawata sarkin sammako” taji an ambata ta gefanta,wayar ta rufe ya dago kai fuskarta qunshe da murmushi tana duban Aliya dake sauke jakarta daga kafada kana ta yiwa kanta mazauni kusa da ayshan itama tana murmushi
“To ya za’ayi” ayshan ta maida mata amsa tana gyara zamanta
“Hala yauma uwar masu gidan zata fito da wuri ne kika kwaso qafa kika biyota?” A maimakon ta bata masa murmushi ayshan ta saki,tasan halin rigima sarai irin na Aliya.

‘Yar tsama suke qwarai da asma’u,basa hada hanya da ita,saboda banbancin halaye qwarai dake tsakaninsu,bugu da qari tana jin haushin yadda take mu’amalantar ayshan wadda ta zame mata qawa kuma aminiya a dui fadin makarantar,sosai Aliya keson aysha sabo managartan halayenta,nutsuwa haquri gami da kunya,uwa uba ayshan na daya daga cikin daliban da sukayi fice a duk fadin department dinsu,kai bama iya tsangayar tasu kadai ba a duka makarantar ma.

Kai Aliya ta kada cikin takaici,saidai ayshan bata bata damar cewa komai ba ta tareta
“Kinso yau ki makara qawata,ya akai haka?”
“Hmmm,wlh yau mama ta tsaidani sai dana hadawa ya khalil breakfast,Allah ne ya soni na masa sharp sharp na fece,da Allah ne kadai ya san makarar da zanyi” duka tana zancan ne sanda take ciro handout dinta daga jaka,kafin su sake cewa komai lacturer din ya shigo ajin.

Qarfe uku na rana ta kammala duk abinda zatayi cikin makarantar,hakan ya sanya ta tattara komai nata ta fito don ta qarasa inda zata samu asma’u,saidai koda taje wayam taga wurin babu alamun motarta,hakan ke nuna bata cikin makarantar,bata wani damu ba ta soma takawa da qafa don zuwa bakin get din makarantar don ta sami abun hawa,don yau Aliya ta rigata tafiya gida,ita ta tsaya ta dudduba wasu karatuttuka.

Jin qarar mota a bayanta ya sanyata sake rabewa don bawa motar damar wucewa,a sannan idonsu ya hadu da drivern,asma’u ce,ita da wasu mutum biyu a motar,da alama qawayenta ne,dauke kai asma’un tayi tamkar bata ganta ba,sai tama qarawa motar wuta tayi hanzarin wuce ayshan,sam hakan bai dameta ba,saboda ba yau farau ba,babu abinda asma’un ta tsana nan gidan duniya irin alaqar da zata bayyanar da cewa ayshan jininta ce,gida daya suka fito ko suna da dangantaka,tunda ayshan ta fahimci hakan sai itama take baya baya da duk wata alaqa da zata hadata da asma’u cikin bainar jama’a.

Kai ta jinjina kawai taci gaba da takawa zuwa qofar makaranta,wannan abun na asma’u zata iya cewa bai bata ranta ko kadan,idan ma ya bata din bai wuce digo daya cikin dari ba,a yanzu qyamatar da take fuskanta take kuma bata mamaki ta shafe ko wacce iriyar qyama da qiyayya da dukkan wata halitta zata nuna mata a doron duniya,dukkan wata tsana saidai ta biyo bayan waccar,da wannan tunanin ta tsaida wani dan sahu dake niyyar gifatata ta masa kwatance inda zata ta fada ciki.

Kamar kullum yauma a qalla ya kusa shafe mintuna ashirin yana tsaye yana jiranta,har sai data kaishi ga qosawa ya haye saman babur din da yazo da shi ya zauna,saboda rashin sabo saura kadan babur din ya tuntsira da shi Allah ya taimaka cikin zafin nama yayo gaba ya dawo ya zauna dai dai,mahmoud dake zaune cikin motarsu dake fake a wani layi ya tuntsire da dariya harda duqawa,ba don ba dabanba da ya fito ya masa vedio ya ajjiye saboda tarihi,saidai yana tsoron tashin balli tilas ya zauna cikin motar kamar yadda yayi masa umarni.

Sake duba agogonsa yayi yana qissimawa ranshi mintinan da zai qara wanda matuqar bata fito ba zai qara gaba,a gajiye yake,daga airphort yake ko gida bai isa ba ya sauya kaya ya canza akalar tafiyar tasa zuwa gidansu,bayan ya yiwa daya daga cikin yaranshi waya ya kawo masa babur din,kwanaki goma ya kwashe a qasar da yaje,bai kuma samu damar kiranta ba tunda ya tafi saboda gudun tonuwar asiri,don kada ta tsammaci ya janye hakan ne ya sanyashi tahowa kai tsaye gidansu.

Kamar ko yaushe yauma haka fuskarta take,ta qaraso inda yake saidai a yau waya take amsawa,ganin ta iso gareshi yasa ta bada uzurin zata sake kira ta kashe wayar ta lanqwasheta a hannunta yauma tana sake qare masa kallo a kaikaice
“Allah ya baka kyau na nunawa sa’a,saidai hakan ba zaiyi tasiri a raina ba saboda kana da babban naqasu na rashin hatimin nasara” duka take wannan maganar a ranta,sama sama suka gaisa tamkar baqin juna,shi kansa yana jin wani irin cikin ranshi,duk yadda yaso kawo sabo da shaquwa tsakaninsu zulaihat taqi bashi dama.

Shiru ya ratsa tsakaninsu bayan ya gama iya maganganun da yaga sun kamata,saidai rashin samun gamsashshiyar amsa yasa maganganun nashi basuyu tsaho ba
“Ammm…dama akwai abinda nakeson gaya maka” ta fada tana gyara yafen mayafinta
“Uhmmm…babu damuwa,yi maganarki”
“Cewa nayi don Allah daga yau ina son ka janye daga zuwa wajena da kake….saboda ina da buqatar space”qaramin murmushi ne ya subucewa fuskarsa,abinda yake zato yau zai tabbata kenan
“Amma wani laifi na aikata ne haka” kai ta kada tana dan tabe baki
“Ko daya,kawai na gaji da alaqarmu ne haka…..har yau jiya iyau,kai ba qaruwa ake da kai ba” ta qarashe furucin qarshe can qasan maqoshinta,saidai abinda bata sani ba shine,yana daga cikin jinsin mutanen da Allah ya musu kaifin ji matuqa,murmushi ya kuma saki mai dan sauti,ga mamakinta taji yace
“Shikenan….in sha Allahu daga yau din zan janye….amma” ya fadi yana sanya hannunsa cikin aljihun trouser dinsa,american dollers ya ciro daga aljihun nasa wanda baisan ko na nawa bane,takawa yayi a hankali har ya isa inda take jingune rungume da hannayenta ya soka mata su tsakanin hannayenta yana ci gaba da jifanta da murmushi
“Na gode da lokutanki na baya da kika aramin…..sai wara rana” ya fadi yana juyawa,binsa tayi da kallo galala,duk wata tasha ta tunaninta ta dauke tsaf,har ya isa bakin wata baqar mota wadda bataji sanda ta iso inda suke ba,gidan baya ya bude ya shige kana ya rufe,sai data ga motar ta bar layin nasu sannan hankalinta ya dawo jikinta,tabi dollers din dake liqe a jikinta da kallo,sabbi kar suna fidda wani irin qamshi dake cakude da sassanyan qamshin turarensa da har rana irin ta yau ta rasa gane wanne irin turare yake amfani da shi,cikin sauri kaman wadda aka yiwa allura ta juya cikin hanzarinta shige gidan su,bata tsaya ko ina ba sai parlourn gidansu,inda tabar qawarta barratu na jiranta
“Ya akayi,kin sallami dan anacen naki” maimakon ta amsa mata saita miqa mata dalolin dake hannunta
“Wadannan fa daga ina?” Barratu ta fada tana zakudawa gami da gyara zamanta tare da tattara dukkan hankalinta kan zulaiha,mayafinta ta yage sannan ta zauna hannun kujera tana baiwa barratu labarin abinda ya faru,ta rufe da cewa
“Tsoro na daya barratu,kada ya kasance irin mijin da nake muradi ne na koreshi da kaina,kinga irin motar daya shiga kuwa” ta fada fargabarta na fitowa fili qarara,murmushi barratu ta saki tana karkada kudaden
“Kinga malama….kwantar da hankalinki….tundan yau kin gano haka ai baki makara ba,waskewa zakiyi,ai kiransa zakiyi kawai ki nuna ke bakison kudinsa yazo ya amshi abinsa,ke gwadashi dama kike yi” bata tsaya ta gama jinma qarshen zancan ba ta zaro wayarta cikin hanzari ta soma laluba inda ta jefa lambar tasa,can cikin black list ta ganota,cikin hanzari ta cireta daga black list din sannan ta soma kiransa.

Dai dai lokacin yana lafe a bayan motar suna tafe, mahmoud nata tambayar sa ya akayi a gefe guda kuma yana sheqa masa dariya,qarar wayar ita ta sanyashi bude manyan idanunshi da suke a rufe,waya ce da ita daya keda number,wadda dama dominta ya siya wayar da layin,hannunshi ya kai ya daga wayar ya kara a kunnensa ba tare da yace komai ba
“Ka dawo ka amshi kudinka,ni basu nake so ba,gwadaka dama nake,kuma alamu sun nuna kaci wannan jarrabawar” irin maganganun data ringa jerowa kenan duk a niyyarta nason amintar da shi da gamsar da shi,murmushi kawai ya sake mata wanda ya ratsa kunne da qwaqwalwarta
“Am sorry to say,ida na wuce aji bana maimaita shi…..sai wata rana” ya qarashe fada yana cire wayar daga kunneshi,bai tsaya a nan ba sai daya cire layin ya karyashi gida biyu,ya sauke glass din motar qasa kadan ya watsar ta window sannan ya maidashi yadda yake ya koma jikin kujerar motar ya sake lafewa ba tare daya bi ta kan dariyar mahmoud ba,hannayensa ya saka ya rufe kunnuwansa saboda yadda mahmoud din ya hanashi sakat,daga bisani da yaga baida niyyar barinshi ya huta ya shammaceshi ya kai masa naushi,Allah ya taimakeshi ya kauce yana cewa
“A’ah,karka lahantani,haka kawai bani na kar zomon ba ai,danma ka samu wai ina rakoka,tunda an kasaka ba shikenan ba sai ka sake sabon lale….amma fa ka riqr a ranka,’yammatan zamani indai zaka ci gaba da zuwa musu a haka za’a dade ana kasaka” dariya ce ta subucewa khalipha ba tare saya shirya ba,suka dan dara tare da mahmoud din,shi kansa lamarin na bashi mamaki gamibda daure masa kai,karo na uku?,karo na uku duk tafiyar ta kasance iri guda?,sai yaushe?,sai yaushe zaiga sauyi,zaya so yaga wannan rana qwarai.

 

 

*mrs muhammad ce*??
*_HUGUMA_*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button