Daurin Boye 22
22
Ta kowanne bangare daya shafi asma’u hidima ake tuquru ta bikin autar mummyn,babu wata rana da zata fito ta fadi ba’a tsara wani abu dangane da shirin bikinta ba, tamkar mummyn zata aurar da yara uku haka take ji.
Tun saura sati hudu bikin mai gyaran amare ke zuwa gidan,takanas mummy ta biyata kudin sati hudun take zuwa take gyara asma’un,cikin qanqanin lokaci kuwa ta sake wani kyau,fatarta tayi fes kyanta ya sake fitowa,duk wannan hidimar da ake dai dai da sau daya ba’a taba karar tsoma aysha a ciki ba,itama kuma duka bai cikin lissafinta,don sam tasama ranta aurenta ba irin nasu asma’u bane,irinta yaran gata su ya cancanci suyi irin wannan hidimar.
Kullum ta kwanta fatanta da burinta daya Allah yasa umminta tazo bikinta…Allah yasa a wannan karon umminta ta kulata…Allah yasa umminta zata rungumeta wannan karon a jikinta taji duminta kamar sauran yara,zuciyarta takanyi fari tayi haske a duk sanda wani sashe na zuciyarta ya bata qwarin gwiwar koya hasaso mata kanta kwance a cinyar ummin tata suna hira.
Tun biki saura sati uku aka je ganin gidan,gidan asma’u aka soma zuwa,itadai aysha ba’a gayyaceta ba saboda haka bata je ba,bata ma da sha’awar zuwa,don kullum sake jan jikinta take da gujewa duk wani abu da zai iya zama laifi,ta dai zauna gida tayi abincin baqi,sanda suka dawo nan falo suka baje suna hirar irin gidan alfarma da hamid ya ginawa asma’un,itakam tana tsakiyarsu tana hura hanci farinciki kamar ya kasheta,dama tasan duk wanda yaje yaga ginin sai ya yaba kafin ma akai gayi mata jere,don kusan lokaci lokaci yana daukarta suna zuwa ganin ginin abinda baiyi ba tayi magana a rushe a sake maida mata yadda takeso da haka aka kammala ginin,wanda kafin a gama din ba qaramin hasara aka dinga yi ba saboda an rushe gurare da dama an sauya da wasu plan din.
Kwana biyu tsakani mummy ta sameta a kitchen a sannan tana hadawa daddy abincin dare kamar yadda take lokaci lokaci akai akai musamman idan ‘yar mulkin ta sakar mata mara ranar babu abinda ta sakata dafawa
“Ya kamata ki yiwa wancan yaron magana me yake da suna?….za’a je aga inda zaku zauna saboda asan yanayin kayan gadon da za’a siya,kada a siya kuma azo ayi asara,suyi yawa ko suqi shiga”
“Toh mummy” ta fada kawai,ita batasan ma ya ake cewa ba,batasan ta yadda zata gaya masa wai za’a je ganin waje ba.
Har washe gari bata yi yunqurin yin komai ba,bai kuma zoba don yakan dauki lokaci kafin yazo din,a daren kwana na uku da maganar mummy ta sake tuntubarta a sannan asma’u na wajen
“Ke idan zaki masa magana ki masa,idan baki iyawa ni ina da lambarsa sai na kirashi na shaida masa” cewar asma’u kanta tsaye,ganin bata kulata ba ta sake cewa
“Abinda dai kike gudu duk tsiya sai anje an gano”bar mata wajen tayi,don ita duka bata da lokacin ire iren wadan nan.
Tana tsaka da goge kayan sawarta data wanke dazun wayarta ta dauki tsuwwa,a sannan yana zaune cikin valcony dinsa sanye da farar t.shirt qal mai qaramin hannu da farin trouser,aiki yake cikin system dinsa idonshi ya kai kan wayarta data bashi,sai a sannan ya tuna ma da abinda ya faru,rabonshi kuma da ita tun ranar,ko ya kira yayi pretending kan vivonsa daya baro a hannunta baiyi ba,hakan yasa shi yanke shawarar kiranta,wannan karon da layinsa da yake amfani da shi ya kira ba layin daya ware ba,cikin sanyin nan nata tayi sallama,idanunsa ya dan lumshe kadan sannan ya budesu,karon faro daya soma kiranta a waya tunda suke tare,amsa sallamar tata yayi sannan shuru ya biyo baya dukkansu
“Baki gane dawa kike magana ba kenan?” Ya tambaya a sake,murmushi ta saki kadan,sai daya kuma magana ta gane waye
“Na gane mana” ta fada cikin sanyi
“To waye?” Dan shuru tayi kadan sannan tace
“Yaya ne”
“Kin yarda kin bani matsayin yayan kenan?” Murmushi kawai ta saki,don harga Allah kallon yayanta take masa,bai damu da amsarta ba ya dora da
“Kira nayi na baki haquri kan rashin kawo lefe….kayanne har yau basu gama haduwa ba…kiyi haquri inaga sai bayan an daura aure za’a kawo ko a aje miki can gidan da zaki zauna”
“Babu komai…babu wata damuwa….ni dama ban saka hada lefe ba” ta amsa masa a nutse
“Au…haka ake auren budurwa…ko da yake ni yaya nake…amma duk da haka ai miji nake a idon duniya ko?,xan qoqarta nayi miki dai dai qarfina in sha Allahu bazai gagara ba”
“Ba damuwa…yanzun ma mummy ce….” Sai kuma ta kasa qarasawa,hakanan take jin nauyin fadi,biron hannunsa ya aje ya miqe qafafunsa yana shafa kansa da hannu guda
Haka nan yake jin dadin sautin ta
“Uhmmm….mummy ce meye?,Allah yasa ba wani matsalar bace ta faru” kai ta girgiza kaman yana wajen
“A’ah….wai zasuga gida ne”
“Ya salam…toh” ya furta kaman da gaske ya dan rude din,duk sai taji babu dadi….tana kallon kaman zai taimaki rayuwarta ne shi kuma gashi ana son qureshi da sanyashi cikin takura da matsala duk don saboda ita
“Babu damuwa…..kamar ranar yaushe suka ce zasu je?”
“Ban sani ba nima….kawai dai yau kwananta uku da gaya min”
“Is ok….shikenan….zuwa anjima ko gobe zan kiraki na gaya miki ranar da zasu zo din”
“Tohm…” Ta fada cikin sanyinta da ya sakashi lumshe ido,haka kawai yakeson yanayin muryarta kamar ta yara saboda zaqinta.
Yana katse layin ya soma lalubar wata number da ya tanadeta saboda irin wannan ranar,yana kira babu jinkiri aka daga,bayan sun gaisa ya bashi umarnin sama masa gida tare da gaya masa irin yanayin gidan da yakeso,unguwannin ya lissafa masa ya zabi daya daga ciki,daga bisani sukai sallama ya aje wayar yaci gaba da aikinsa yana murmushi,shi kansa idan ya tuna yadda plan dinsa ke tafiya dariya yake baiwa kansa…bai zaci abun zaiyi tsaho har haka ba,haka kawai yaji sha’awar ci gaba da yi,har zuwa yau kuma baiga komai tattare da ayshan na raini ko qyama ba,duk da cewa bashi da yaqini ko tabbas itama a kanta,bai sani ba ko yanayin rayuwarta ne yasa ta zame masa hakan,amma koma meye saura qiris komai yazo qarshe…kuma lokaci zai nuna.
Sai daya kammala komai yazo kwanciya sannan ya tura mata texs din cewa gobe ko jibi idan sun shirya suyi masa magana yazo ya rakasu,ya kashe wayar tasa ya soma addu’ar bacci,yana cikin shafawa wayarshi wadda ita kadai ta rage bai kashe ba ta soma haske,ramla ce ke kiransa,sharewa yayi yaci gaba da abinda yake,saidai har ya gama din bata daina kiran ba,tilas ya sakashi dagawar ya kara a kunnensa.
Ajiyar zuciya ta saki kafin tace komai,don har ta fidda ran zai daga,khalipha na wahalar da rayuwarta….bata taba tsammanin zata masa irin wannan soyayyar ba da bata bari abinda ya faru ya faru a baya ba
“Ya khalipha….”
“Yaya akayi?” Ya tambayeta ba tare daya amsa ba,harga Allah taba takura masa fiye da kowa a cikinsu,baya son mace mai naci sam
“Kayi haquri don Allah,laifin wani fa baya shafar na wani a rayuwa…ina sonka ya khalipha ka sani ina tsananin sonka….please ka bani dama mu zama abu daya….mu shimfida rayuwa mai kyau da inganci”
“Kiyi haquri bacci nake ji,idan na tashi i will call you back” katse layin yayi ya kashe wayar baki daya sannan ya kwanta,saidai maimakon bacci yazo sai rayuwar da suka tabayi a gidansu ramlat din wasu shekaru can baya suka dinga dawo masa daki daki,cikin lokaci qanqanin idanunsa suka kada,yana kwance rigingine hannayensa harde a qirjinsa sai ya canza yanayin kwanciyar tasa zuwa hannun damanshi yana ta’awizi don kore shaidan daci gaba da tunzurashi da tuna masa abinda ya riga ya shige,a hankali temper din nashi ta dinga sauka,gajiyar ranar ta lullubeshi,nutsatstsen bacci ya sauka a idanunshi.
Saidai bai jima da fara baccin ba yayi mafarkin aysha na kuka….kuka take sosai ba tare da tace wani abu ba,abinda ya sake tashinsa kenan,alwala yaje ya daura ya tada sallah yana jujjuya mafarkin cikin ranshi,tabbas akwai abinda yake damunta haka zuciyarshi ta bashi,tausayinta sosai yake yana jin tamkar qanwarshi,da wannan bacci yayi awon gaba da shi.
????????????????
Tunda aysha tace za’a je ganin gida asma’u ta hana kanta tsaye ta hana kanta zaune,motsi kadan sai tace zasuje suga mansion house din aysha,har sai da mummy ta gaji da ji ta kwabeta.
Ranar da za’a din itace tayi driving dinsu,su anty halima ne…anty kubra,sai anty lubabatu,sai inna laraba,anty safiyya ce kawai bata samu zuwa ba saboda al’amin data kai asibiti ranar baya jin dadi,babu wani danginta ko daya,babu wani da zata kirashi nata qwaya daya,haka tanaji tana gani asma’u ta sanyawa motar key suka fice bayan ta saki waqa cike da nishadi.
Da kashi yaso zuwa,da kansa yaso ya musu rakiyar,saidai kuma a ranar yana da baqi da zasu zauna meeting da su,tilas ya wakilta daya daga cikin manyan yaranshi ya musu jagora,qaramar camera ya bashi wadda ya jonata da system dinsa,ta yadda zai dinga ganin duk abinda yake faruwa har su dawo.
Misalin qarfe uku da mintina suka shiga unguwar,tun daga farkon layin asma’u ke tabe baki tana fadin
“Tab…” Unguwa ce data tara marasa shi qwarai,kusan babu wani gida qwaya daya da zaka nuna wanda zai alamta maka akwai maiqo ko dukiya a gidan,wasu daga cikin gidajen ma qofar buhu ce daure ko labule a jikinta.
Qofar wani gidan qasa dan rakiyar ta tsaya,hakan ya sanya asma’u itama tayi parking,sannan suja fiffito gaba dayansu suna qarewa unguwar kallo cike da qyama kafin daga bisani su maida idonsu kan gidan da dan rakiyar ke kici kicin budewa.
Ginin qasa ne wanda yasha shafen sumunti da makuba,qofar katako irin ta da ta katako sosai maqale da katangar gida wanda ke nuna ta nan zaka shiga zuwa ainihin gidan,kallo daya zaka yiwa gidan kasan cewa ba sabon gini bane,kowanne idanunsa kan gidan suka isa bakin qofar,asma’u ce ta dubi dan rakiyar
“Kaga malam basai kayi wahalar saka muqulli ka bude wannan rubabbiyar qofar ba,da qafa ma budeta zamuyi” ta qarasa fada tana daga qafarta ta daki qofar,qasa da qura suka biyo qofar suka yo kanta,hakan ya sanya tayi saurin ja da baya,ita kanta mamaki take cikin zuciyarta,sam batayi tsammanin talaucin yaron oga yakai har haka bama,wani bacin rai ya sake lullubeta da haushinsa,yasan haka yake har ya zubda mata ajinta ta jera da shi?,ta hada muhallin zama da shi,lallai iya zaman da yasa tayi da shi ba qaramar cutarta ma yayi ba,batasan mutane nawa ne da suka santa suka kuma sanshi suka gansu tare ba,ta tabbata wasu sun mata dariya.
Da qyar ya iya samu qofar ta bude ya tura kai ciki suka biyo bayanshi,tsukakke kuma dogon soro suka fara taraswa mai dauke da rufin azara irin ta da,idan kaci gaba da jumurin cusa kai zuwa cikin gidan kuwa,tsakar gida ne mai fadi da yalwa wanda aka yiwa daben qasa,duqurqushin bandaki jere kusa da kitchen,sai dakuna manya falle biyu
“Ummm….indo ba’a manta gida ba” cewar anty halima,daga kai kawai inna laraba tayi ta kalleta ta dauke kanta….wato shi dan qauye ba mutum ba?…tana da yaqinin harga Allah daddy baisan duka wainar da ake toyawa ba,duk da cewa bata gidan amma tana katarin riskar wasu abubuwan,ta yaya aysha yarinyar da tayi jami’a take zaune cikin birni shekara da shekaru zatayi aure cikin wannan gidan ta kuma zauna a ciki?,ta ina zata iya taimakawa rayuwarta ta fidda ta?
“Hhhhhh,ai tazo inda ya dace da ita” cewar asma’u tana yarfa hannu tare da takawa cikin gidan tana qare masa kallo.
Ba abinda dan rakiyar yace saboda ba’a umarceshi da cewa komai ba,kuma ya tabbatar duk abinda ke wakana boss din sa yana ji kuma yana gani,bai furta komai din ba har suka gama isgilancinsu suka gama suka tako zasu fita ya rufa musu baya,yana maida muqullin zai rufe asma’u ta dubeshi
“Kana wahalar da kanka ne kawai….banda abinka wai meye abun qwaqumawa wannan kangon kwado kayita wani rufeshi,da ka barshi ma a bude don baida maraba da kango” kallo daya yayi mata ya maida kansa yana ci gaba da ruge gidan,ranshi fal da mamakin me ya hada boss da wannan gidan me zaiyi da shi?,sannan kuma meye gaminsa da wadan nan matan?,ko da ya gama rufe gidan tuni sun hau kwalta sunyi gaba abinsu.
Cikin motar ma zancan gidan sukeyi,kowa na tofa albarkacin bakinsa,anty lubabatu ce tace
“Anya ko asma’u wannan plan din baiyi worst ba….talaucin mutumin nan fa kamar yayi yawa” dan tsaki ta ja saboda sakuwarta ce
“Kinjiki kema da wani irin zance….to daga ina ita din ta fito?….ina cewa irin wannan gidan anan taci ta sha,banda ma tsaurin ido irin na talaka daga an riqeka a waje sai kace lallai sai kayi rayuwa irin tasu?,kuma wa ya hanata musanta zancan tun yana farkonshi…wai ita saliha a dole baiwar Allah…..munafuka inaga ma kyanshi ta gani ta kasa cewa bata sonshi….so ni banga wani worst ba da yayi,ungulu ce kawai zata koma gidanta na tsamiya” tabe baki anty halima tayi,sai a sannan tayi magana
“Lubabatu a yadda yarinyar nan take gani tana da kyau idan ta auri wani kan mage ne zai waye,uban kowa ma neman taka shi zatayi,irinsun nan ki gansu haka haka ba qananun ‘yan iska bane idan suka samu waje…Allah ne kadai yasan manufar jaki da bai bashi qaho ba….daddy nema haka kawai ba dangin dangiro kaje ka jajubo yarinyar mutane….ta gama abinda ya kawotan ma maimakon ka maidata a’ah ka daukama ranka saika aurar da ita….bayan ko uwarta bata ta tata saikai” ta qarashe maganar da tsaki
“Shi yasa nakesonki anty halima….kinfi kowa fahimta”
“Mu ai da yake jakai ne ko?” Lubabatu ta fada tana hararta,dariya tayi tana cewa
“Bance ba”.
Nannuyar ajiyar zuciya ya saki ya soma latsa system din bayan ya gama gani da jin duk abinda ya gudana tun daga qofar gidan shigarsu ciki zuwa barinsu unguwar,tunani ne cikin qwaqwalwarsa kala daban daban,mamakin baqar zuciya da mugunta irin ta wasu mutanen,buri da fatan jefaka a rana koda baka takawa kowa komai ba,aysha dai aysha ba’a son ci gabanta a rayuwa kwata kwata?,shikam wanne irin gata zaiyi mata daya dace da ita wanda zai bada mamaki ya girgiza zukatan maqiya
[1/14, 1:37 PM] Om Muhammadiyya: Mamakin abinda aysha tayi wanda ya tsarewa asma’u a rai yake,me tayi mata mai zafi da taketa yunqurin daqile duk wani ci gabanta,wacce irin macace asma’un?,bama ita kadai ba,hatta da ‘yan uwanta ya fuskanci haka suke,ta ina suka gado wannan halayya?,wato da da gaske shi din haka yake zasu fi kowa farincikin dawwamarta cikin wahala kenan?.
Kusan wunin ranar baki daya abinda ke masa kai kawo kenan a zuciya,har sanda yake zaune gaban anni yake cin abinci abunda ke tsinkulinsa kenan
“Muhammadu lafiya dai?gajiya ko kuma aikin?” Dan murmushi yayi sannan a nutse ya bata labarin dukkan abinda ya faru,kai take jinjinawa cike da mamaki da.nazari
“Muhammadu yarinyar nan tana buqatar wani ginshiqi da zai tallafeta….inama ace kana mata soyayya mai qarfi wadda zata zame mata jigo?….saidai duk da haka ina jin qaunar zama da ita…sai nake jin kamar a maida daurin auren gobe ka dauketa daga cikinsu,me yasa mutane zuciyoyinmu suke ciki da kishi qyashi da hassada?…Allah ka shiryamu ka gyara mana zukatanmu”ta furta cikin sanyin jiki
“amin ya Allah….amin”
_kuyi haquri da wannan don Allah_
*mrs muhammad*??
[3/6, 9:01 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*
*DB*