Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 23

Sponsored Links

23

Tunda suka dawo babu zancan da suke sai na gidan ayshan mommy na ji bata dai tanka komai nata ciki ba,a sannan anty safiyya ta dawo daga kai al’amin asibiti,ganin ta gama da wuri sai ta zarto gida,nan ta taras da su ta kuma ji duk abinda suke fadi din,babu wanda ta cewa uffan sai tayi ma kamar batasan me yake faruwa ba,har suka gama sha’aninsu kowacce ta wuce gidanta suka bar safiyyan a gidan
“Ke yaushe zaki wuce…kowa ya tafi ya barki?”
“Mommy dukansu fa sun riga ni zuwa,kuma ma sai nayi sallar isha’i abban al’amin zaizo mu wuce tare”
“Ai shikenan…” Ta fada tana ci gaba da aikin gabanta.

A nan tayi sallar isha’i taci abinci,bata jima da kammalawa ba daddy ya shigo gidan,mintina goma ta bayar ta kwantar da al’amin sannan ta wuce zuwa falon daddyn.

Related Articles

Yana zaune saman kujera sanye da jallabiya,da alama daga wanka ya fito yayi shirin cin abinci,da murmushi a fuskarshi suke gaisawa,saboda duk cikin yaransa bayan asma’u itace ta biyu a wadanda yake so,itama asma’un don itace auta shi yasa ta rigashi zuwa,tana da halaye irin nashi,sauqin kai da fahimta gami da rashin daukar komai da zafi
“Amma ace tun safe kima gidan nan me mike baki koma gidanki ba safiya?” Murmushi tayi tana dubansa sannan tace
“Magana nakeso nayi da kai ne daddy” ta qarashe maganar yana dan satar kallon mommy,bisa dukkan alamu batason yin maganar tana wajen kenan,ya fahimceta,hakan ya sanya ya dubi mummy dake kici kicin zuba masa abincin darenshi wanda aysha ce ta girka yace
“Jeki hadamin coffe sa’adatu”
“Toh” tace tana aje serving spoon din hannunta ba tare data fahimci komai ba ta miqe ta fice.

Sai data gama fita din daddy ya kalli safiyya
“Ina jinki safiya ya akayi?”
“Daddy…..kasan wanda aysha ta kawo zata aura kuwa baida wani qarfi?…daddy kaman ma dai bazai iya riqeta nake gani”
“Indai zai iya bata ci da sha da suttura da muhallin zama ya kiyaye haqqoqinta da mutuncinta da lafiyarta safiya shi ake bida a aure,amma duk da haka akwai wani abu da larabawa ke cewa khafa’a wato dacewa da juna ta wajen aure,ko musulunci ya yadda da khafaa’ah….nasan halayen yaro kuma na binciki lamarinsa naga yana da ikon da zai iya riqe mace….yana da aiki duk da qarqashin wani yake,na gamsu da bincike na shi yasa na bashi ita” lallai daddy qila akwai abinda bai fahimta ba ko ya shige masa duhu,hakan ya sanya ta sake hada nutsuwarta tace
“Daddy….yaufa aka je ganin gidan da aysha zata zauna daddy…gidan qasa fa?” Shuru yayi yana nazarin maganarta,sai yaji shima bai gamsu data zauna a gidan ba,don idan yayi hakan tamkar baiyi adalci ba
“Gidan qasa safiya?…” Ya sake tambayarta don tabbatarwa
“Eh daddy” shuru ya sake shi da ita ba wanda ya sake cewa wani abu,ajiyar zuciya ya sauke sannan yace
“Da kanta ta kawo yaron tana sonshi bata yadda za’ayi na hanata wanda take so,idan nayi mata haka kaman banyi mata adalci bane,amma shikenan babu komai…ki tashi kije Allah yayi miki albarka….zanga yaron zanyi wani abu akai in sha Allahu”
“Na gode daddy….Allah ya qara girma” ta fada tana miqewa,dai dai sanda mommy ta dawo dauke da coffen,hakan ya sanya daddy ya sake basar da zancan
“Ina abokina ne…ko kin soma barinshi gida shima?” Dariya tayi mummy ta amsa masa
“Yau abokinka ba lafiya,haqori ya sakoshi gaba…yana daki yana bacci”
“Ashsha…Allah ya sawwaqe,a gaida babanshi”
“Zaiji in sha Allahu….mummy ni zan wuce,sai da safe”
“Ki gaida gida da sauran yaran” da haka ta fito daga falon daddyn tana jin dadi har cikin ranta,tana jin kamar ta sauke wani nauyi,sam tana jin bai dace subar aysha ta rayu cikin gidan qasa ba ba adalci bane sam,batasan me yasa duk yadda yarinyar ke da hankali da nutsuwa ba basa gani
“Allah ya kyauta” ta fada tana amsa wayar abban al’amin daya kirata ta fito su tafi.

Yayi mamakin ganin kiran daddy da kanshi kan cewa yana son ganinshi,a ladabce ya amsa mishi,saidai yace ya bashi uzuri zuwa gobe,ya fadi hakanne saboda a ranar yaje abuja za’ dauki hoton yatsunshi zai sauya passport dinsa.

******************

Qarfe biyar na yammaci yana zaune falon daddyn cikin shigar yadi wanda aka fi kira da mamar ruwan bula mai haske,cikin mutunta juna suka gaisa shi da daddyn,ya dan bawa khaliphan space ya kurbi lemo duk da bamai yawa ya sha ba sannan yace
“Malam muhammadu….ya gida ya hidimomi” yana dan shafar kansa yace
“Alhmdlh daddy komai lafiya” zamanshi ya gyara bayan yayi gyaran murya
“Nasan zaka yi mamakin kiran ka da nayi ko”
“Hakane” khalipha ya amsa
“Ba wani abu bane babba yasa na kira ka ba….ammm kasan cewa tun ba yau ba na daukeka kaman matsayin d’a a gareni…to haka yake har yanzu,musamman da zaka auri diya ta…inaso nayi maka kyauta ne kamar yadda mahaifi zai yiwa dansa” ya saurara da maganar yana ciro wasu kudi daga gefan inda yake zaune,rafa ce ta ‘yan dubu dubu guda goma ya aje a gaban khaliphan
“Ga wannan…..ka karba kayi amfani da su….duk wani abu da kasan baka samu ka qarasa ba kayi da sh,ka gaya muhallinku da dan abinda zakuci” can qasan xuciyarsa qina da mutuncin daddyn yake sake gani,tabbas ya kai maqura wajen nuna talaucinsa,hakan kuma bai sanya daddyn kai tsaye yace bazai bashi aure ba,saidai kamar yana son taimaka masa ne a fakaice ba tare daya furta ba,yasan mai yiwuwa labarin gidan aka zo aka bashi…..ko kuma ita ayshan talaucin taga ya mata yawa ta soma kokwanto?,kaman daddy yasan tunanin da yake yace da shi
“Tunanin me kakeyi?….kar kayi shakka ko kokwanton karba…babu wanda yasan na baka wannan kudin ko munyi maganar da kai,daga ni saikai sai Allahn daya haliccemu,karka damu ni na baka ba tambaya kayi ba,kuma har abada qimarka na nan a ido na” boyayyar ajiyat zuciya ya saki sannan yace
“Na gode na gode daddy qwarai da karamcinka na batun yau ba,Allah ya saka maka da mafificin alkhairinsa…amma daddy… Am sorry to say bazan iya karbar wadan nan kudaden ba,zanyi dukkan abinda ya dace iyakacin iyawata da yardar Allah daga iya abinda Allah ya horemin….don Allah kar kace saina karba daddy…” Kai yake gyadawa cike da mamaki da alfahari da wadatar zuci irin ta khaliphan wadda ya santa ba tun yau ba,lallai akwai wadatar zuci mai yawa tattare da shi,hakanan daddyn ya sanya hannu ya janye kudin yana cewa
“Shikenan…Allah ya taimaka yayi jagora….yayi albarka a zamanku”
“Amin ya Allah…na gode daddy” ya fada yana miqewa sukai sallama,yayin da daddy ya bishi da kallo,har ga Allah yaso ace ya karbi kudin ko muhallin da ayshan zata zauna ya gyara musu,saboda yayi yaqinin mutumin da bai karbi kudi ba ko gida ya bashi bazai karba ba,yaso ace ya karbi kudin ma sai yayi dabarar da zai bashi gida kudin yayi wata sabgar da ita,ajiyar zuciya yayi cikin zuciyarsa yana jin bari qurar bikin auren ta lafa dole ya inganta rayuwarsu bazai qyalesu a haka ba.

????????????????

 

Saura sati daya bikin a yadda aka tsara aliya tazo ta tasata a gaba zasu je gidansu za’a soma mata gyaran jiki
“Don Allah sashin ki bar wannan zancan,meye wani gyaran jiki don Allah?….ni kunya ma kike bani wallahi”
“Kya gama jin kunyarki ki miqe mu tafi….”
“Don Allah sashen ki barni….”
“Idan kika sake wata maganar Allah ni dake ne…ki shirya kawai” hakanan ta miqe ta shiga bayi wanka ba don tana so ba.

Tana shiryawa aliya na mata mitar tana maida kanta koma baya,har sai da ayshan ta juyo yana dan bata fuska a shagwabe kaman qaramar yarinya,wanda ta riga data saba kusan dabi’arta haka lokaci zuwa lokaci
“To kuma don Allah sashin ba ya riga ya wuce ba gashi ina shiryawa….”
“Oho dai…ina gaya miki ne donma gobe kar kice zakimin musu….don sati za’ayi ana yi”
“Haba kaman wata kaya”
“Whatever….” Aliya ta fada tana watsa hannu.

Tsaf ta shirya ta saka hijabinta sannan suka fito,ta shiga dakin mummy ta sanar mata
“Saikin dawo” kawai ta fadi ba tare data damu da yaya abun zai gudana ko waye zai biya ba.

Suna harabar gidan zasu fice khalipha ya fito daga wajen daddy,zuba ido aliya tayi taga reaction na kowannensu,wucewa ayshan tayi kamar zatayi da sauri aliya ta damqi hannunta ta tsaidata,dai dai sanda khaliphan ya qaraso wajen,duk da yana dan gaggawa ya wuce saboda ya baro baqi a tahir amma saiya rage saurinsa sanda ya iso wajensu
“Ango kasha qamshi…” Aliya ta fada cikin salom tsokana,ya fahimci tana da sauqin kai da barkwanci,hakan ya sanya yayi murmushi
“Qawar amarya…ina zaku haka?”
“Gyaran jiki….da qyar na jajibo wannan amaryar taka” ta fada tana yima aysha da kanta ke qasa dariya
“Wai haka…?” Ya tambaya yana dan kallonta a fakaice
“Ina yini” ta gaisheshi a maimakon bashi amsa,ya fuskanci tana da hanyoyi da dama da take guntule zance idan bata son tsawaitarsa,shima din yana da abinyi hakan ya sanya ya kawo qarshen tsaiwar tasu
“Gashi kuma yayan naki gurgu ne babu abun hawa da.na kaiku”
“Babu komai ango….zamu qarasa a napep babu nisa daga nan” hannunsa ya sanya cikin aljihun wandonshi ya soma zaro kudi,cikin hanzari ya maidasu bayan ya duba yawansu,Allah yasa basu gani ba

Daya aljihun ya sake saka hannunsa,’yan dari biyar biyar ne hade da ‘yan dari bibbiyu,baisan adadinsu ba,yana son ya qirga nawa ne amma ya kasa kasancewar bai saba hakan ba,miqa musu yayi
“Ga wannan kyayi wani abu da shi…..saidai fa haquri angon bashi da komai talaka ne” dariya aliya tayi ta sanya hannu zata amsa,ta daya bangaren aysha ta riqe hannunta,saidai bata kula da ta amsa din tana cewa
“Ba komai…Allah ya amfana wannan din”
“Amin….” Ya fada yana yabawa nagartar qawancen aliyan da aysha.

Shi ya soma yin gaba,aysha ta dubi aliya
“Me yasa zaki karba aliya….yanzun haka kudinsa fa kenan?” Murmushi ya saki sanda ya jiyo abinda ayshan ke fada,wani lokaci halayyarta na masa kamanceceniya da halayyar hajar….wata halitta mafi soyuwa a garesu da bazasu taba mantawa da ita ba,kusan yanayinsu da halayyarsu na gogayya da juna,da wannan tunani ya qarasa ficewa daga gidan ba tare daya ji qarshen muhawarar tasu ba.

“To meye don na karba din…..ya kamata ko yaya fa yasan zaiyi aure ne,za’a bashi mace kuma budurwa,bawai ya aureki kaman an bashi sadaka ba” kai aysha ta kada ta soma takawa sai aliyan tabi bayanta
“Har kullum aliya bana son ki dinga sani ina jin ni dinma kamar kowa nake bayan ba hakan yake ba”
“Ni kuma na gaji da maimaita miki wannan karatun na kema kamar kowa kike,da dama ma kin fisu a wajen Allah”kanta itama take girgizawa,tausayin aysha na rinjayar zuciyarta,ko sai yaushe zata yarda itama ‘yace kamar kowa?,sai yaushe zata sake tayi rayuwa yadda kowacce mace take?,oho…Allah masani…wannan itace amsar da aliya ta baiwa kanta,haka suka dinga tafiya tamkar kurame.

Ganin ayshan nason motso damuwarta wadda zata iya shafar wuninsu na yau,sai aliya ta qara sauri ta jera da ita tana sako mata zancan makaranta da yadda result dinsu ya kaya,hakan sai ya sanyayar da zuciyar aysha,suka ci gaba da tattaunawa,har ta zabi su taka a qafa tunda wajen ba wani nisa bane can da shi,aliya bata musa ba ta biye mata suka dinga takawa a qasa suna hirarsu
“waccan ‘yar qarunar naga kaman bata wani damu da carry overn data samu ba ta aure take….naji labarin ta samu c.o ko?duk da ba’a gaya min ba don kada nayi sharhi…to sai nayi,zancan duniya kuma bai buya” Aliya ta fada tana qunshe dariyarta,don ita hakan yayi mata dadi,ko banza asma’u zatasan da cewa duk inda kakai ga zama wani a duniya dole kayi lacking wani abu a rayuwarka ko kai waye.

Harararta da aysha tayi yasa ta dauke kanta gefe guda tana dariyarta hankali kwance
“Kai..” Aliya ta fada lokaci daya dariyarta tana daukewa,saita waiwayo ta dubi aysha
“Aysha…..kaman angonki fa na gani hakimce cikin motocin can” ta fada tana nuna mata motoci ukun da suka wuce a jere iri daya,bin motocin tayi da kallo kafin ta maida idonta kan aliya tana murmushi
“Dama kina gulmar wata ba dole idonki ya dinga miki gano miki abinda ba haka ba….mutumin da muka rabu da shi yanzu yanzu a gida”
“Allah seriouse aysha shi na gani…don har mun hada idanu sai naga ya dage glass din motar” wannan karon sai da aysha tayi ‘yar qaramar dariya
“Idan shi kika gani yaushe ya zama haka?…yaushe ya sayi dukkan wadan nan motocin yanzu yanzu kenan daga fitowarsa daga gidanmu ko?,may be shi da oganshi ne,don kusan ko yaushe yana gaya min suna tare” Ja aliya tayi ta tsaya,yanayinta ya koma da gaske take irin yanayin da tasan ayshan zata fahimceta
“Wallahi Allah da gaske nake miki aysha khalipha na gani a cikin motocin can,kuma alamu duka sun nuna cewa ba wani yake ja ba shi ake ja motarshi ce,kayan jikinsa fa ba irin wanda muka ganshi da su bane yanzu” shiru dukka sukayi aliya na kallon aysha cikin tantama,yayin da aysha ta soma shiga tunani gami da shakka,ajiyar zuciya aliya ta saki sannan tace
“Allah aysha tun asali sam khalipha baiyimin kama da wanda ke cikin babu ko yake samu a qarqashin wani ba….kin taba qare masa kallo da kyau kuwa tun daga kanshi har zuwa tafin qafa?” Dariya ce ta kubcewa aysha duk da yanayin fargaba data soma shiga
“Aliya ta yaya zan iya kallon wani namiji haka tun daga kansa zuwa qafa koda kuwa mijina ne?” Idanu aliya ta zaro
“Mijinki?…kina nufin ba zaki iya masa wannan kallon ba….lallai aysha akwai aiki a gabanki” qaramin murmushi ta saka tana kada kai
“Muje don Allah….shi din talaka ne kamata hakan shi ya qara min qwarin gwiwar amincewa zama da shi….ba da sunan miji ba…da sunan yaya dan uwa…’yan uwan da na rasa nake fata wannan karon nayi gam da katar da su kuma managarta,bana jin akwai wani ha’inci ko qarya tsakanina da shi”
“Idan kuma abinda idanuna suka gani gaske ne kinga shikenan…shikenan kaya sun tsinke a gindin kaba” aliya ta fada tana dariya
“U r mad aliya…ba don wannan zan zauna da shi ba…na amince ne saboda naga irina ne shi,kaman yanayin rayuwarmu daya ne…idan kuma har da gasken ne….bazan iya shiga cikinsu ba na zauna,ban masa qarya ba ban boye masa komai nawa ba,ban boye masa wacece ni” dukan kafadarta aliya tayi tace
“Shutup my friend….bana son wannan maganar taki ma…muje don Allah” daga haka suka ci gaba da takawa ba tare da sun sake bi ta kan maganar ba.

Numfashi ya sauke gami da lumshe bayan sun wucewa ganinsu aliya,yana sane ya sha mur ya dauke kai gamida dagr glass din sama don tayi tsammanin cewa bashi bane idanunsa ya bude sannan yace
“Jibril”
“Na’am sir”
“Daga yau bana son a sake saukemin glass din mota qasa idan bani na bada umarni ba”
“Yes sir,in sha Allahu” daga haka motar ta dauki shiru,addu’a yake cikin ranshi Allah yasa basu ganeshi ba,don ba yanzu ya shirya bayyanar komai ba.

????????????????

Biki saura kwanaki uku gidan mommy ya soma cika da jama’a ‘yan uwa da abokan arziqi,kowa zancan bikin asma’u kawai yake,da yawansu ma basusan cewa itama aysha nata auren za’ayi ba,idan sun tambaya ma takan ce a can qauyen iyayenta za’ayi,eh haka ne ayshan take cewa,don itama ta matsu ta wuce qauyen nasu,ko banza naka naka ne.

Cikin kwanakin zuwa gyaran jikin sai ya soma yi mata wahala saboda hidimar baqin dake gidan,awanninta kaso mafi yawa a kitchen take yinsu,duk da itama hakan ya mata dadi don bata ga meye na wani yin gyaran jiki ba,hakan kamar wani rawar kaine a wajenta ko wuce gona da iri,don haka sai take noqewa take fakewa da cewa gidan cike yake da baqi,hakan ya fusata aliya kan zasu maidata ‘yar aikinsu,ta dage kan sai ta tattara kayanta ta dawo gidansu,da qyar ta shawo kanta ta nuna mata ranat juma’a ma zasu wuce takai baki daya tunda asabar ne daurin auren.

Tun ranar laraba aka fara gudanar da bikin,gidan kuwa ya cika ya tumbatsa da ‘yan uwa da hamshaqan qawayen asma’u,tun ranar ta soma shiga ta kece raini,bridal shower suka fara yi sannan sauran events din suka biyo baya,ayshan kam mafi yawan lokaci idan bata tana kitchen ko dakinta,don data je gyaran jikin da aliya ta tilastata take dawowa,yawanci da aliyan suke zuwa,saidai ita bata shigowa gidan tunda aka fata bikin a qofar gida suke rabowa ta koma ta wuce nasu gidan.
[3/6, 9:01 PM] Binta Mustapha: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*

*KO KUMA*
(07067124863)

*DAURIN BOYE*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button