Daurin Boye 34
_NO. 34_*
……….Fuska ta kuma ha?ewa tana janye idanunta daga cikin nasa, ta fara takowa a hankali zuwa inda suke da nufin kama Ahmad su tafi. Amaan kam sam yakasa ?auke manyan idanunsa a kanta, sai binta da kallo yake ?asa-?asa da mamakin ina zata je? Sam ya kula bata da tsoro yarinyar nan.
Mayen ?amshin turarenta ne ya fargar dashi kusancin da suka samu, ya sauke wata ?oyayyar ajiyar zuciya yana kuma tamke fuska.
Ko kallon inda yake Ummukulsoom ba tai ba, ta kamo hannun Ahmad dake la?e a bayansa zata jawoshi, shima saiya ri?e ?ayan hannun Ahmad ?in.
Kallan kallo suka sakema juna kowa fuska babu ?igon walwa, har ?asan zuciya Ummu haushinsa takeji.
“Zamu wuce”. Ta fa?a a kausashe.
Banza yay mata kamar bai jiba, saida ya sha?i iska ya fesar sannan yace, “Dani na kawo ki?”.
?in tankawa tai itama, ta ja hannun Ahmad kawai.
Ahmad da yake tirjewa yace, “Aunty ni kibarni zan zauna a wajen big daddy”.
Hannu ta ?aga tamkar zata makesa, harda cije baki. Ahmad daya tsorata ya ?ankame hannun Yaa Amaan sosai.
Ba ?aramin dariya abin yabama Amaan ba, amma saiya fuske ya ha?iye abarsa yana kafeta ta idanunsa, ”Miyasa kika fasa? Ki dakesa mana”.
Baki ta murgu?a masa tana wani wulkita idanu da ka?an ya rage ta wulkice da zuciyar sa, dan gaba ?aya ?ofofin gashin jikinsa sai da suka bu?e, ya ha?iye yawu da sauri yana janye idanunsa a kanta.
Ita kam bama tasan yanaiba, sai ?o?arin ?aukar Ahmad ?inma da take hannu biyu.
Sam bazai iya jurewa kusancinsu ba, dan haka ya sakar matashi kawai, amma sai Ahmad ya fasa kukan shifa anan zai zauna.
Bata saurari kukansa ba ta fice abinta.
Idanunsa ya lumshe tareda kai hannu ya shafi girarsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, lallai indai wannan shine so to sam bai masa adalciba, dan shikam bazai juraba. Gaba ?ayama jiyay aikin nasa ya fita kansa, dan haka ya tattare kayan ya koma ciki.
Ummukulsoom kam tana fitowa taci karo da Bily a ?ofar gidan sunan ita da wani saurayi.
Cikin mamaki tace, “Bestie daga ina haka?”.
Tsaki Ummu tayi tana dire Ahmad da har yanzu yake kuka a ?asa, “Ki bari kawai Bestie, wai dan wula?anci fa Ahmad ya kama kaimu wannan gidan a matsayin gidan sunan”.
Bily ta ?an waro idanu waje tana dariya, “Amma Ahmad ALLAH ya shiryeka, gidan Yaa Amaan ?inne ya zama gidan su Sulaiman?”.
“Ai ki barni dashi, yau ba sai gobe ba sai na zanesa, da wani kansa tun na haihuwa”.
Sosai saurayin da ke tare da Bily yake dariya, shi mamaki ma take bashi, ta dage ita a dole fa?a takeyi, amma kuma muryarta na fitane a nutse kuma cikin amo mai da?i.
Sam Ummu ko kallonsa bata yiba itakam tai gaba ta bar wajen, Bily ma dai sai da ta dara, tana binta da kallo, dan ita tunda taji ala?ar dake tsakanin Ummukulsoom da Yaa Amaan tasan sun dace, fatanta kuma komai ya zama normal ta koma ?akinta.
???????????
Sosai Suhailat ke bincike akan Baseeru, ba dare babu rana, ta haka ne ta samu ganawa da abokansa su Abdul, da yake duk sunsan da zancen rabuwarta da Baseeru basuyi mamakin komaiba, sai dai canjawar da tai musu.
Itama sun canja mata ?warai da gaske, dan gaba ?ayansu sunyi aure zuwa yanzu.
Najeeb ne ya fara fa?in, “Mudai a bayan rabuwarku mukejin ?ishin-?inshi akan aure yayi, badai mu tabbatar ba dan sam ya?i yarda mu ha?u dashi, sai bayan aurensa da ?ar gwamnan katsina ta yanzune mukabi diddiginsa har mukasan ashema bayan ya auri Lubnar da muka ta?a ganinsu tare sannan kina amarya amma yace mana ?awarkice ya kuma auren wata yarinya Fannah, a tare ma ya sakesu da Lubna lokacin aurensa da Meenal ?in”.
Mamaki ya kuma danne Suhailat, lallai lamarin Basiru ya gawurta, amma ta ?auki alwashin nuna masa *WUTSIYAR RA?UMI TAI NESA DA ?ASA*.
“To yanzu ta yaya kuke ganin zamu sami Lubna da Fannah?”.
Abdul yace, “Lubna dai samunta zaifi sau?i, tunda mahaifinta ba ?oyayyen mutum baneba, Fannah ?ince dai matsalar”.
“Hakane, amma inhar mun ha?u da Lubna itama Fannahr zamu sameta insha ALLAH”.
A tare sukace hakane.
*Washe gari*
A washe garin ranar Suhailat tai shirinta na alfarma ta doshi kanon dabo, batasha wata wahalar samun gidansu Lubna da aka bata address ba, hakama bata sha wahala ba wajen masu gadin gidan, kasancewar tace ita?in ?awar Lubna ce. Tai kuma sa’a Lubna na gida bata fita ko inaba.
Tana tsaye jikin motarta Lubna ta fito tare da mai bama fulawar gidan ruwa da yaje ya sanar mata, kallan kallo kawai sukema juna, dan babu wanda yasan wani a cikinsu, sai dai kasantuwarsu wayayyu duk sai suka basar wajen yima juna murmushi.
Suhailat tace, “Sorry dear, ba?uwa babu sanarwa, baki kuma sannni ba”.
Murmushi itama Lubna tayi mata, “Babu damuwa, koma dai minene mu shiga daga ciki”.
“Thanks”. Suhailat ta fa?a a hankali.
Tunda suka shigo gidan Suhailat ke jinjina tsarinsa, dama tasan ai Basiru bazai ta?a aurar macen da babu manda a gidansu ba, dan shi kaska ne ra?u mai jini.
Sai da aka gama ajiye mata kayan motsa baki sannan Lubna ta zauna suka sake gaisawa, Suhailat da ke shan lemo ta kalli Lubna da fararen idanunta, “Nasan zakiyi mamakin ganina, gashi baki sanniba, Sunana Suhailat, tun daga kd nayo takakkiya zuwa gareki. Ta sanadin ala?ar da wani banza ya ha?amune nazo nan”.
“Wake nan?” lubna ta tambaya tana tsare Suhailat da idanu.
Murmushi Suhailat tayi na takaici, kafin ta ajiye kofin hannunta tana gyara zama, tace,
“Ba kowa bane face Basiru”.
Tuni murmushin dake kan fuskar Lubna ya gushe gaba ?aya, ta yunkura zata mi?e Suhailat ta dakatar da ita ta hanyar fa?in,
“Ni ya cancanta na fara irin wannan fushin Lubna, amma dana zauna nai tunani sai naga bazai amfaneni da komaiba, domin kuwa zan ?are rayuwatane inayinsa batare da wanda nakeyi dan shiba ya sani balle yasan na tsanesa, zuwa yanzu ba zuciyar fushi bace a ?irjina Lubna, ta ?aukar fansace, wannan dalilinne yasani zuwa gareki domin mu ha?a hannu wajen maida murtanin bashin gaba. Badan Basiru zai gagareni bane ba, sai dan nasan irin tabon daya barmin kema shine ya barmiki, kenan ya dace mu ha?a ?arfi da ?arfe wajen tabbatar masa da mata ba hularsa bace da zai ?auka a sanda yaso yakuma aje a lokacin da yaso, amma in babu ra’ayin hakan a tare dake karki damu zan koma, na ida cikar burina, na gode da tarbar mutunci da kikaimin sosai, sai gani na biyu…….”
“Indai wannan shine burinki nima shine nawa, dan nayi al?awarin sai Baseeru ya ?wankwa?i madarar ba?inciki fiye da wadda ya bani na ?an?ana, na tsani cin amana, hakama yaudara”. Lubna ce mai maganar a fusace.
hakan ya saka Suhailat dakatawa daga shirin fitar da takeyi, ta juyo gaba ?ayanta tana kallon Lubna fuskarta shinfi?e da murmushi, ?aramin ?an yatsanta ta mi?a mata, Lubna ta tako har gabanta suka ?ulla tareda sakarma juna murmushi.
Komawa sukai suka sake dasa hiran basiru da rayuwar da kowa tayi dashi, anan ma Lubna ke sanarma Suhailat ta haihu da Basiru ita, yarinyar tana nan Amal.
Sosai Suhailat ta tausayama Lubna da yarinyar kanta da batai dacen mahaifiba.
Sun yanke hukuncin yanda zasu samo Fannah itama, dan daga baya bayan rabuwar Lubna dashi itama takejin ya auri Fannah, a tarema ya sakesu.
???????????
Tunda ta fito daga lecture ta hangesa tsaye jikin motarsa, sai dai ta yauma ba irin ta shekaran jiya bace, sanye yake cikin suit kalar sararin samaniya, ?ya?ykyawane ajin farko, sannan ?an gayu, yau kwanaki hu?u kenan daya fara bibiyarta, sai dai sam taki saurarensa, amma bawan ALLAH ya?i yin zuciya.
Ta ?an sauke numfashi tareda cigaba da takowa inda yake, dan yau taji a ranta zata sauraresa taji da wacce yazo shikuma.
Sanye take cikin atanfa ruwan fauda siket da riga, sai hijjab ?inta da ka?an ya wuce cinyarta mai hannu shikuma ruwan madara, tayi ?yau sosai dukda kamar kullum babu kwalliya a fuskarta.
Tunda ta dososhi murmushi ya fa?a?u akan fuskarsa, yarinyar ta ha?u ta ko ina, kallo ?aya ta wuce da dukkan tunaninsa, gata da jan aji, dan itace mace ta farko a rayuwarsa da zaice yanata bi tana yarfashi amma yakasa yin fushi……
“Assalamu alaika” zazza?ar muryarta ta ranga?a masa sallama.
Eyeglasess ?in fuskarsa ya zare yana murmushi, “Wa’alaikissalam gimbiyar mata, Wannan juma’a tazo min da babban alkairi, ga farin wata gab da ni yana haska min hanya”.
Basarwa Ummukulsoom tai tamkar bata fahimcesaba, sai ma cewa da tai, “Wai kai bakayin zuciyane?”.
“Zuciya kuma Babie? Ai akanki ki ?auka banida zuciya irinta fushi”.
Murmushi Ummukulsoom tayi ba tare da ta shirya ba, ta ?auke kanta gefe kawai tana fa?in, “Nifa bana zama inuwa ?aya da maza”.
“Babie aini kece inuwa ta, dan ALLAH a tausaya mini abarni na shiga daga ciki, zafin rana na gasani, sanyin kuma da ya kasance ba na inuwarkiba cutarwace a gareni, aji dani ra?ar ?ankara tana neman daskarar da jinina”.
?an kallonsa tayi kafin ta ?auke idanunta, “Zan duba naga idan ka cancanta”.
“Yeeees!” yafa?a yana dunkule hannusa.
Hakan sai ya bama Ummukulsoom dariya, tai murmushi mai kayatarwa da har ya bayyana jerarrun ha?oranta farare tas.
Duk yanda taso ?in binsa saida ya kalameta da da?in baki ta amince ta shiga motarsa.
Suna tafiya yana janta da hira game da kanta, a ta?aice taita bashi amsa, yayinda shikuma yake sanar da ita wanene shi kai tsaye.
A gate ?in farko tace ya ajiyeta, dan tasan baza’a barsa ya shiga Barrack ?inba.
Fitowa yay da kansa ya bu?e mata ta fito, harda wani ?an sunkuya mata irin na girmamawa, hakan ya sata sakin ?ar siririyar dariya……
Cak numfashin Amaan dake tsaye a ?ofar gate ?in ya nemi ?aukewa, tsaye suke shida Attahir da wani abokinsu a wajen, da alama wani abun sukeyi, Attahir ne kawai sanye da complet Uniform a jikinsa da ?ayan abokin nasu, Amaan kuwa wandonne kawai sai dark green ?in t-shert data kamashi sosai.
Attahir da yaga Amaan ya tsirama waje ?aya ido fuskarsa na kuma tsukewa sai abin ya bashi mamaki, dan haka ya kalli inda ya ke kallo shima.
Ummukulsoom ya gani tsaye da ?ya?y?yawan saurayi tana zabga murmushi waya a hannunta tana dannawa, yayinda saurayin shima yake murmushin hakoransa waje yana kallonta, ta mika masa wayar dake tabbatar da tasace, da alama Number ?inta ta saka masa.
Attahir ya janye idanunsa daga kansu ya maido kan Amaan da Abokinsu ke tambayar lafiya?, sai dai sam da alama hankalinsa bama ya wajensa.
Ta?asa Attahir yayi, ya lumshe idanunsa ya bu?e batare da ya kalli Attahir ?inba, zuciyarsa wani irin zallo take tamkar zata fito waje, ga kansa yay masa wani irin masifaffen nauyi, sam baya fahimtar jawabin abokin nasu.
Sarai Ummukulsoom taga su Amaan tun lokacin da zata fito a motar Umar, hakan ne yasata biye masa dan ganin yanda gaba ?aya hankalin Amaan ya dawo kansu, saboda ta sake ?ular dashi harda ?agama Umar hannu da zai tada motar, bata bar wajenba sai da taga motarsa ta hau titi sannan ta saita kanta ta tako a hankali cikin nutsuwarta zuwa gate ?in.
Sai da tazo saitinsu sannan ta kalli inda suke, da Amaan ta fara ha?a ido, amma tsabar wula?anci sai catai “yaya Attahir barka da yammaci”.
Murmushi Attahir yayi yana amsata da fa?in “Yauwa autan Ummi, an dawo lafiya?”.
“Lafiya lau yayana”. Ta fa?a tana yin gaba abinta tareda watsama Amaan harara, Abokinsu kuwa yabar wajen tunkan ta ?araso.
Ko motsi Amaan kasa yi yayi, dan tabbas ba’a ta?a masa irin wannan rainin ba da Ummukulsoom ta masa yau, shi bama wannanba, Ubanwaye wanda ya sauketa a mota? Dolene ya takama wannan yarinyar birki, inba hakaba wlhy zataja yayta karya ?a?an mutane a gabanta….
Yanda yake fidda numfashi da sauri-sauri ya saka Attahir kallonsa, fushi da tsantsar fusata ya hanga a cikin ?wayar idanunsa, “Ajiwa lafiya kuwa?”.
?in takama Attahir yayi, saima yabar wajen gaba ?aya.
Attahir yay ?ar dariya yana girgiza kansa, zuwa yanzu kam yagama yarda Ajiwa yagane Ummukulsoom, tsabar miskilanci ne ya hanasa nuna hakan………..???
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU??._
*?AURIN ?OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ?ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ?AYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RA?UMI..!* (Bilyn Abdull)
????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
*_?an Niger kuma_*
_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*
*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*
_TA NUMBER;_
*+22795166177*
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????