Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 35

Sponsored Links

35

Kusan tunda suka taho ita da shi fuskarta ke a cunkushe,ba don komai ba sai don batasan abinda zata je ta tarar ba a gidan,sam bata wani sha’awar zuwa gidansu hamid din,duk da cewa tunda sukai aure bata taba zuwa ba sai yau daya matsanta mata sai taje,saboda zaiyi tafiya ne shima,gaba daya haushin duk wata tafiya tashi take,a yanzu baya cikakken sati daya a gida,bashi wancan gari bashi wannan,bata isa tayi qorafi ba yanzu zai hauta da gorin yana yawon neman abinda ta aureshi ne saboda shi.

A harabar gidan ya tsaida motar sannan ya kasheta,fitowa yayi hakan ya sanya itama dole ta fito tabi bayanshi tana hade fuska har suka isa falon gidan.

Related Articles

Qannenshi ne zaune gaban t.v suna kallo,maza biyu mata biyu sune wadanda suka rage ba’a aurar ba,mahaifiyarsu na tsakiyarsu,kowanne yaci uban asma’u a girman kai da tabara,hakan ya sanya yayansun kawai suka yiwa sannu da zuwa kowa yaci gaba da sabgarsa,babu abinda uwar tace musu don ko ita bata nuna tasan tare suke da ita ba.

Tana rakabe gefe suna ta hirarsu a qalla wajen minti talatin sannan hamid yajiyo
“Au hajiga ga tare fa muke da ita” gilashin fuskarta tadan saukar kadan ta kalli asma’un sosai sannan ta jashi sama
“Na ganta….sai yau taga damar zuwa?,koda yake ai ba yau muka fara ganinta fuskarta sananniya ce” ta fadi hakan da manufa biyu,don sanda hamid din ke neman aurenta bini bini zai kwasheta suje gidansu,saidai babban abinda ya daurewa asma’un ganin yadda dukkaninsu suka sauya,kaf dinsu ba haka suke mata ba a baya kafin ta auri dan uwansu,hakanan suja sha yata sukaci hitarsu suka godewa Allah,ko ruwa ba wanda ya kalleta da shi,sai daga qarshe ne da hamid din ya cewa qanwarsa ta bashi ruwa ta hado da asma’un,saboda tsabar baqinciki da bacin rai ko kallon ruwan bata yi ba har suka tafi.

Cikin mota ta dinga fushi da kumbure kumbure,saidai ko kallo bata isheshi ba bare ya nuna yasan tana yi ba,har daga qarshe data gaji ta tanka
“Amma dama kawoni gidanku kayi don a cimin fuska?” Wani juyowa yayi ya dubeta ya watsar kafin ya bata amsa
“Kamar yaya?”
“Baka ga abinda akayimin ba kenan?”
“To su kike su tashi suyita rawa suna tsalle sunga halittar da basu taba ganin irinta ba,ni da Allah banason fitina kinji ko?” Nan sa’insa ta kaure a tsakaninsu,bata yi shuru ba har sai data ga yana da niyyar kai mata mangari,koda suka je gida a fusace ta fita daga motar ta buga mishi qofar motar
“Kiyi a hankali,don wallahi idan kika sake kika yimin barna taki zan siyar na gyara” ya fada cikin daga murya yadda zata iya jiyowa.

????????????????

Kwanaki biyar ya rage su soma lacture ta shirya tsaf don tafiya makaranta,duk wani abu daya dace babu wanda ba’a siya mata ba,siyayya irin ta ‘ya’yan gata,itadai kallon komai take kamar almara,kaya kaman wadda zata shekara a can,hatta da ruwan sha khalipha bai bari ba sai daya siya mata,wani abun ma har kunyar kanta da kanta take ji duk da yadda anni ke bata qwarin gwiwa,sai take jin kamar ta zame musu wani kaya ta hadasu da hidimarta.

Tana tsaye a falon sashen nasu sagale da jakarta wadda ta zuba qananun abubuwa irin namu na mata,sai take jin kewa ta soma shigarta,jikinta ya danyi sanyi kamar zata wani garin ta barsu,a haka khalipha ya fito ya taddata,atm card ya miqa mata yana kafeta da idanunshi,a sanyaye ta amsa tana son jin qarin bayani
“Duk sanda kike da buqatar wani abu ki cire kudi ki saya,naki ne accnt dinki ne,sati mai zuwa idan Allah ya kaimu da rai da lafiya nima zanyi tafiya,zanbar qasar na tsahon shekara biyu” saita daga kai tana kallonshi,hakanan zuciyarta ta raurawa,sosai take jin ba dadi,kaman cewa yayi idan ya tafi bazai dawo ba,ganin sun hada ido kaman yadda suka saba sai kowa ya kau da kanshi
“Zan dinga zuwa a duk sanda na samu chance Ya fadi kamar ya karanci abinda yake zuciyarta,kunya ce taji tana neman kamata,kardai ace ya fahimci abinda take saqawa a ranta,saita sunkuyar da kai
“Allah ya bada abinda za’a je nema,ubangiji yayi jagora ya kade dukkan abinqi”
“Ameen kema haka” ya fada a taqaice,kasancewar tun jiya yayi mata duk jan hankalin daya kamata,iya gajeran lafazinsa kawai yayi mata dadi a rai
“Na gode” ta furta a sanyaye.

Qwalla ce fal idanunta sanda suke sallama da anni,har mus’ab ya dinga sheqa musu dariya abinsa,khalipha kam falo ya koma yayi zamanshi abunsa,kewarsu take tun kafin tabar gidan,haka suka rakota har bakin mota,inda haidar zai kaita.

Rufe motar tayi ta daga kai a hankalin,take idanunta suka shiga cikin nashi,yana tsaye bakin window din da take zaune hannunsa harde a aqirji,shima ita yake kallo,sai qwallar da take tattalin kar ta zubo ta silalo saman fuskarta,sakin hannayen nashi yayi ya bar side dinta ya koma mazaunin driver,duqawa yayi ta window din motar dai dai saitin haidar,batasan me ya gaya mishi ba na tsahon minti daya kafin ya miqe yana cewa
“Allah ya tsare hanya,a kula da hanya”
“In sha Allahu yaya” haidar ya fada yana tasar motar,yana nan tsaye hannyensa goye a bayansa har motar tasu ta fice daga gidan.

Kadan kadan taci gaba da fidda qwalla tana qoqarin sharewa,haidar baice mata komai ba har sai da sukayi tafiya ta kusan minti goma sannan ya dan saki dariya
“Nikam kukan nan bansan na meye ba?,anya kukan rabuwa da anni ne bana rabuwa da yayanmu bane?” Dan harararshi tayi tana fidda qaramin murmushi,daga bisani tayi qoqarin controlling hawayenta,saidai duk da haka zuciyarta babu dadi,wayarshi ya zaro ya kira khaliphan,da alama shi ya bashi umarnin yin hakan,miqa mata wayar kawai haidar yayi yana murmushi,hannu ta sanya ta karba gami da karawa a kunnenta ba tare da tace komai ba
“Kina kuka kaman wata baby?,kinason dagawa mutane hankali,ko baki shirya ba adawo dake?” Girgiza kai tayi kama tana gabansa sannan tace
“A’ah”
“Allah ya bada sa’a” ya fada cikin low tune
“Amin na gode”
“Bashi wayar” saita waiwaya ta miqawa haidar dake boye dariyar da batsan ta meye ba,magana sukayi da bata wuce ta minti daya ba ya katse wayar yana ‘yar mita
“Sai wani jaddadawa yake nayi tuqi a hankali waishi me mata,muma dai mun kusa in sha Allahu mu fara hura hanci muma” daroya ma haidar din ya bata,ita ta sani kawai dai yana jaddadawar ne saboda dan uwanshi,amma ita yaushe takai nan,haka haidar ya dinga janta da hira har ta dan saki jiki,yana bata labarin makarantar da yake can suka fara yi shi da mus’ab kafin daga bisani khalipha ya fitar da su waje.

Ajiyar zuciya ya saki yana maida wayar aljihunsa,baisan me yasha kanshi da kukanta ba harya buqaci jin yata kasance,hakanan kawai yaji yana da buqatar jin haka,sai ya sake sauke wata ajiyar zuciyar yana duban wami littafinta data dauko ta manta dashi saman kujera.

Awa guda suka isa a haka donsu tsaya cin abinci a wani gidan cin abinci dake hanya,itakam aysha har sannan babu abinda taci saboda dama can abincin safen ba damunta yayi ba,haidar na tare da ita har aka gama shigar mata da kayanta,kulawa ta musamman ta samu daga ma’aikatan dake kula da hostel din,bata san me yasa ba,saidai tuni khalipha ya gama sallamar kowa a cikinsu,hakan yasa suke ankare da zuwan ta,saidai komai ya zama normal ya tabbatar babu wani abu da zata sake buqata kaman yadda yayanshi ya umarceshi sannan yayi mata sallama,sanda zai tafin ma dai kamar zata bishi,hakanan dai ta daure ta juya zuwa ta koma hostel din.

Su uku ne a dakin,saidai sanda taje mutum biyun sun gama shirya kayansu basa nan,da alama ma ba ranar su sukazo ba,kasancewarta ita daya a dakin ya bata dama itama ta zauna ta jera komai nata a muhallinsa yadda take da buqata,koda ta gama an kusa sallar la’asar,sai kawai ta kunna gas ta dora jallop din sphaghetti sannan ta shiga bandakin dake manne da dakin ta dauro alwala.

A cooler ta aje abincin bayan ta gama,ta bude barander dake bayan dakinsu ta wanke komai ta tsaftaceshi,bata jin yunwa sai kewar gida dake damunta,tana gefan gadonta tana qarewa dakin nasu kallo,komai neat gwanin sha’awa,fata kawai take Allah yasa musulmai ne,masu halin qwarai,sai ta kasa zaman dakin,ta zari hijabinta ta zura ta lalubi muqullin dakin tanufi qofa tana duba wayarta,aliya takeson kira,yau kwana uku basu samu sunyi waya ba,kowa yana busy.

Qofar da aka turo saura qiris ta daki goshinta,da sauri taja baya tana duban mai shigowar,matashiyar budurwa ce wadda duka duka shekarunta basufi na ayshan ba,doguwa ce bata da jiki,kalarta choculet ce mai daukan ido da sheqi,tana da doguwar fuska da jerarrun fararen haqoranta,idanu ta zaro tana fadin
“Ah sorry sister….sannu Allah yasa ban bigeki ba” murmushi aliyan tayi,yanayin yadda take magana kawai ya isa ya gaya maka tana da surutu
“Babu komai,baki sameni ba”
“Alhmdlh….kece ragowar room partner dinmu da baki qaraso ba ko?” Ta fadi fuskarta qunshe da murmushi wanda ke nuna haka yanayinta yake,kai aysha ta gyada
“Eh”
“Thank god…amma naji dadi….ni sunana halimatu abdullahi musa,amma anfi kirana da hanan,daga hotoro nake,saidai iyayena duka na zaune a abuja,kefa?”
“Sunana aysha umar modibbo”
“Fulani girl?” Hanan ta tambayeta tana dage gira,dariya aysha tayi,yadda hanan din bata da wahalar sabo yake bata mamaki,kai ta gyada mata again
“Kice na shirya,na kusa koyon fillanci” tare suka sake sakin dariya gaba dayansu
“Well,na tsaidaki da surutu na ko,naga kamar fita zaki da alama uzuri gareki” komawa ayshan tayi da baya ta nemi wajan zama,don zuwa yanzu kuma bata da wani sauran dalilin fita
“A’ah,zaman shuru ne dama yamin yawa nace bari na dan fita naga yanayin hostel din”
“No more loniless tunda na dawo” ta fadi still tana murmushi gami da zube jakunkunan dake hannunta
“Naje na amshi saqo ne daga wajen uncle dina….ga wata azababbiyar yunwa da nikeji…nace ma ya tausayan ya sayan wani abu amma yaqi” ta fada tana kwabe fuska,dariya aysha tayi tana nuna mata cooler din data zu a abinci
“Ga abinci can saiki diba kici” ido ya fiddo
“Kai amma kin taimakeni wallahi,dama maman hunaifa nake saka ran idan ta rigani dawowa na samu daga wajenta,to itama kinga shuru” ta qarasa fada tana bude abincin,qamshin ya daki fuskarta saita lumshe ido
“Tun kafin naci ma nasan zatayi dadi wallahi,sauko muci”
“Kaman a qoshe fa nake”
“Ba wani nan,saidai idan nima bakiso naci ne” jin haka ya sanya aysha ta sauko,hanan ta zuba musu tare suka soma ci tana ci gaba da jan aysha da hira,itadai kallonta kawai aysha take,tana mamakin saurin sakewa irin na hanan,bata da baqunta sam,saidai ta lura tana da kirki matuqa,tana da hankali tsafta sannan uwa uba da ganinta yar qwalisa ce wato gayu,da haka suka gama cin abincin,suna tsaka da wanke hannunsu aka sake turo qofar dakin nasu,wata matashiya ce ta sake shigowa,shigowarta ya sanya hanan yin dif,da aysha suka gaisa sannan ta dubu hanan
“Kin dawo amma koki sanar min?”
“Babu buqatar hakan tunda gashi yanzu kin ganni” hanan ta fada tana miqewa ta bude bandakinsu ta shiga,ta dade matashiyar a tsaye hanan bata fito ba,hakan shi ya tilasta mata tafiya,sai data tafi sannan hanan ta fito tana jan tsaki gami da mita,ita dai aysha naji bata ce komai ba hakanan bata tambayi dalili ba,saboda ba dabi’arta bace.

Hanan na idar da sallah aka sake knocking,wata matar ce ta sake shigowa,fara ce itama qal da ita,ba siririya bace haka bamai qiba ba,tana sanye da doguwar rigar material da mayafinta,a qalla zata girmewa su aysha da shekara hudu haka,hannunta rungume da yarinya wadda bata wuce shekara daya ba,sai jakar mata data ratayo,bayanta security ne mata dauke da jakankuna manya guda biyu,da sauri hanan ta miqe tana fadin
“Oyoyo hunaifa” ta karbe yarinyar daga hannun mamata,murmushi matar take idanunta na kan aysha
“Sannu da zuwa” ayshan ta fada itama tana murmushi
“Yauwa sannunkj,baquwa muka samu ne hanan?” Waiwayawa tayi tana duban aysha cikin murmushi
“Cikon abokiyar zamanmu ne”
“Ma sha Allah,da fatan kinzo lafiya” ta fada fana zama gefan gadonta
“Lafiya alhmdlh” ta bata amsa tana karbar hunaifa daga hannun hanan,karon farko yarinyar ta shiga ranta,tayi kyau cikin overoll pink da hula
“Ummm su mmn hunaifa,daga cewa yanzu yanzu zaki dawo sai kuma yanzu aka ganki,kodai baban hunaifa ne ya riqeki?” Dariya ta danyi tana sake hayewa gadon sosai
“Kedai bari kawai,shima yau zai wuce abuja sai dana tsaya na kintsa shi tukunna” ta fadi tana dariya,itama dariya hanan takeyi
“Kinsan yanzun zamani ya canza,idan baki iya tsayawa kin kame mijinki da kyau ba kina can kin sau baki wata zata kame miki shi,koba haka ba qanwata?” Ta qarasa fadi tana duban aysha,murmushi kawai tayi ta gyada kanta,a hankali ta furta
“Haka ne”dariya hanan ta kuma sawa
“Eh lallai wlh kam da gaskiyarki wallahi maman hunaifa,nifa iya zaman kwana hudu da mukayi dake ba qaramin qaruwa nayi ba,wannan idan na tashi aure gidanki zanzo na tare”
“Muna miki maraba,amma ki taho da glass din sawa idonki,donmu gidanmu duk baqon da zaizo saiya shirya” ihun dariya hanan ta saki yayin da aysha ke kallonsu tana murmushi,abun ya qayatar da ita sosai,haka suka jima suna hira abinsu cikin dakin,daga bisani maman hunaifa wadda asalin sunanta shine raihana tayi qorafin yunwa,saurin da takeyi ya hanata tsaiwa taci,cooler din aysha hanan ta tura mata,dubanta mmn hunaifa tayi
“A ina kika samu abinci?,kekam nasan ba abinda kika tsana irin girki bare nace ke ke kikayi”

Dariya hanan tayi tana cire hijabin sallarta ta maida rolling dinta
“Baquwarmu ce wlh da qoqari,nima zuwa nayi na tadda ta dafa”
“Sannu fa,na gode” maman hunaifa ta fada tana duban aysha,wadda tayi shuru tana mamakin hanan da akace ba abinda ga tsana irin girki,itakam sam bata ga abin wahala ko abin gudu a girki ba,sun jima suna hira a tsakaninsu,duk gaba dayansu ‘yan hira ne,idan ka dauke aysha da wani abun saidai tayi murmushi kawai,hakanan yanayinsu taji yayi mata,kuma bisa dukkan alamu zataji dadin zama da su,har wajen takwas na dare suna hirarsu kowa na baiwa dan uwansa labarin dan abinda ya shafi rayuwarsa wanda ya kamata dan uwansa ya sani,itadai aysha nata surutun kadan ne,abun da ya tashi hirar tasu kiran wayar hanan da akayi ta haye gado ta barsu a nan,daga bisani itama maman hunaifa bayan ta gama lallaba hunaifa tayi bacci ta sungumi tata wayar ta haye gado,sai ya zamana aysha ce kawai ta rage,itama saita haye nata gadon ba don tana da abunyi ba,likimo tayi tana juya wayarta gami da tunanin wanda zata kira,daga bisani sai ta gwada wayar aliya,a kashe ta taddata,tilas ta sauya akalar kiran nata zuwa ga layin anni,bugu uku ta daga,muryarta cike da fara’a take cewa
“Yanzu bada jimawa ba muka gama maganarki ni dasu haidar a wajen cin abinci,yau gidan duk sai ya yoye babu dadi,khalipha ya wuce shima zai fara tsayawa a legos,rahama ta tafi gida” murmushi mai sauti ta fitar tana jin kewarsu
“Nima nan ba dadi”murmushin itama anni tayi cikin jin dadi
“To ya za’ayi,ba yadda banyi dashi ya barmin diyata a kusa ba yace min can yafi”dariya tayi
” zan saba ai anni in sha Allahu”
“To Allah ya taimaka yayi jagora,Allah ya hadaki da mutanen zama na qwarai”
“Amin anni na gode Allah ya qara girma” yan mintuna suka qara akan layi wanda yawanci tana tambayar annin jikinta da yadda tayi da ‘yan abubuwan da aysha ta dauke mata,tace wani haka ta lallaba tayi wani ta haqura,da yake ba komai takeson masu aiki suyi mata ba,daga qarshe sukayi sallama da annin,bayan ta dan ja hankalinta kan ta kula da mutuncinta,wanda kusan dai duk kaman tana taya khaliphanta ne kishinta.

??????????????

Tsaki taja bayan ta gama zazzage ragowar madarar data rage a kwalin ta wurgar da kwalin gefe tana masifa da mita a ranta,idan akace mata haka zatayi rayuwa da hamid koda mafarki tayi zata qaryata mafarkin,wannan tafiyar da zaiyi babu abinda bai bar mata ba,ya dan rage maqon nashi kadan wanda ada bai wani dameta sosai ba saboda tana da kudinta a accnt,duk abinda take buqata shi take tabawa ta siya abinta,to wancan satin da sukayi waya da daddy yayi mata fada kan ta rage kashe kudi,ya duba accnt nata yaga kudinta sun soma yin qasa sosai,har yana cewa zai sama mata business ta dinga yi,don baison almubazzaranci da rashin adani,ya kawo mata misali da aysha wanda hakan ya qona ranta sosai,ya gaya mata har yanzu babu abinda ta cira a accnt din daya bude musu,tunawa tayi da daya accnt din nata data bude tun tana gida,bayan ta tare ta bawa a hamid ajiyar atm din,kudin cikin accnt din duk kayan aysha ne da take karbewa wanda tasha alwashin sun daina hada komai iri daya take baiwa mommy ta saka a kayanta ta saida saita karbi kudin,ciki harda wannan sabuwar motar tata da daddy ya siya musu iri daya.

Murmushi ta saki tana ayyanawa a ranta yau ga ranar plan dinta nan,a nutse ta soya qwai guda biyu daya rage mata da sauran kayan cikin data baiwa mai gadi ya kaiwa matarsa ta dafa mata ta dumamashi,don mai aikinta tunda hamid yayi tafiya itama ta tafi,shi yace mata ta tafi tunda shima baya nan,amfanin zamanta idan yana nan tunda asma’un bata iya komai ba,tunda baya nan tayi tafiyarta ita asma’un tasan ya zatayi da kanta,ya gaya mata cewar zai cire kudin aikin kwanakin bazai bata ba,tana ji tana gani ta tafin,ba irin bacin ran da asma’un batayi ba,qarshe mummy ta kira ta yiwa qorafi tana kuka,baqinciki ya hana mummyn magana,itakam har ta soma gajiya da jin matsaloli,ba ranarvAllah da zata fito ta fadi bata ji matsala daga asma’u ba sai dai daikun ranaku,wai dama haka auren masu kudin yake ne ko kuwa?,a’ah ta baiwa kanta amsa,koda wasa aysha bata taba kiranta tayi koda tarin da zai nuna cewa akwai wani abu dake faruwa ba tare da ita mara kyau,hakanan ita karan kanta shaida ce cewa bata taba wani kuka da daddy ba,hakanan mummy ke turo mata lantana ta wuni,itama daga bisani data gaji da wahala da ayyukan asma’un da basa qarewa ta tsiri ciwon qarya,dole aka sarara mata.

A nutse ta gama cin abincinta tana jin nishadi zata ciro kudinta ta kashe sabgar gabanta,don dama tun wancan satin ta rasa ya zatayi,za’ayi bikin daya daga cikin qawayensu,kuma kowacce idan bikinta ya tashi gudun mawa ake bata ta qasaita,samanta ta koma ta fesa wanka bayan ta shirya ta soma duba dakinta don dakin hamid din bai barinsa a bude,ko kasuwa zai fita saiya garqame abinsa ga tagi da muqullinsa bare wannan tafiya ta satittika,cikin sa’a kuwa ta gano atm din,ba bata lokaci ko jiran neman izini ta saka mayafinta ta fice daga gidan.

Sau uku tana tada motar taqi tashi,saidaga bisani ta lura ashe mai ne babu,haka ta sauka ta bada dari biyar aka siyo mata a bakin titi wajen ‘yan bututu ta zuba ta tashi motar ta fice.

Ta samu layi sosai a ATM din,babu yadda ta iya haka tayita jira saboda taga mafadata aka hada a wajen har layi yazo kanta,saidai ga mamakinta sai ake cemata babu kudi a accnt dinta
“A’ah!” Ta fadi cike da madaukakin mamaki,ita tasan kudin ciki ya kusa dubu dari takwas da wani abu,sake maidawa tayi aka sake gaya mata hakan,take gumi ya soma yanko mata
“Hajiya kiyi da jiki da Allah,muna da yawa fa” cewar wani matashi dan ci da zuci dake bayanta
“Ba kudi ba a accnt din nata amma tazo ta wani faka mota tana yiwa mutane qarya tazo cirar kudi” inji wanda yafi kusa da ita ya fadi sanda ta fice daga layin da katin a hannunta,waiwayowa tayi da niyyar sille mishi,saboda tana ganin a girmanta ta girmi ayi mata hakan,saidai yadda idanu sukayi mata yawa yasa tayi hanzarin yin gaba ta fada motarta

Bata tsaya ba saidata isa gida,ta fada saman kujera ranta na quna,tana son tayi kuka tana cijewa,to yaushe wai har hamid ya fidda kudaden nan bata sani ba?,a fusace ta dauko wayarta ta nemi lambobinsa,bugu hudu aka dauka,saidai maimakon muryarsa muryar mace taji,a zabure ta daga wayar tana dubanta sai taga an yanke kiran,sake kiranshi tayi harta katse ba’a daga ba,sai data sake bi sannan aka daga,wannan karon shine
“Wace yar iskar ce ta daga wayarka?”
“Au….shi kika kirani kiji uwata?” Tunani ne ya fado mata,idan ta biyeshi suyita ne zatayi biyu babu,gwara ta fara sanin ina kudadenta suke tukunna
“Atm dina na wajenka,na dauka yau zanyi amfani da shi amma babu komai cikin accnt din”
“Anyi amfani dasu” ya bata amsa kai tsaye
“Kaman yaya hamid?,me kake nufi?” Ta tambayeshi tana gimtse fuska tamkar yana wajen
“Abinda nake nufi nace miki nayi amfani da su”
“Kudin nawa hamid?,wannan wanne irin abu ne daga baka ajiya zaka dauki haqqina kaci?”
“Dakata da Allah malama..” Ya katseta ba tare data gama fadin abinda zata fada din ba
“Gori zakimin kome?,karki gayan maganar banzan,nawa ni na kashe miki a rayuwa,nawa kike cimin yanzu?,to na cinye saiki qwata idan kina da qarfi” yana kaiwa nan ya datse kiran,kuka kawai ta saki saboda tsabar baqinciki da takaici,nan saman kujera ta zube duniya nayi mata qunci,wannan wace iriyar rayuwa ce,me ta yiwa hamid yake saka mata da wannan abubuwa?,haka ta dinga qwalla tana tambayar kanta.

*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*KO KUMA*
07067124863
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button