Daurin Boye 36
36
Cikin sati uku kacal ta soma gane kan abubuwa na cikin makarantar,yanayin rayuwar da banbancin muhalli,yanayin jama’a kala kala,banbancin halaye dabi’u jinsi da kuma yare.
Ta fannin abokan kwananta kuwa sai sam.barka,dukkansu mutanen kirki ne kamar yadda take addu’a Allah ya hadata dana gari,hanan matashiya ce wadda zasuyi shekaru daya,haifaffiyar kano saidai iyayenta na zaune akano saboda yanayin aikin gwamnati da babu inda baya kai mutum,’yar gata ce sosai kasancewarta ita daya ce mace cikin yaran da mamanta ta haifa,tana da ilimi nutsuwa da kamun kai,tana da surutu,sauqin kai da saurin sabo da jama’a,batason muce mara kamun kai mara tambayi ko kintsi,yanayin rayuwa da take cikin mutane da suke a waye,uwa uba gata bata rasa komai ba saita zama ‘yar ado ‘yar kwalliya,hanan badai wayewa da gogewa ba,baya ga tsafta taba da son kwalliya da qyale qyale na mata,duk wanda ya santa a haka ya santa,hanan nada saurayinta Abubakar saddiq wanda aka riga akayi musu baiko da shi aka saka musu rana,shekara guda,wato shekara mai zuwa kenan,suna matuqar son juna irin soyayyar nan mai tsafta.
Sai ruqayya ummu hunaifa,matar aure ce wadda aqalla ta basu shekara hudu ko uku,saidai tana da sauqin kai faran faran da son jama’a,macace wadda itama ‘yar gayu ce mai zaman kanta,wanda gayunta ya nuna har a jikinta,shekararta uku da aure yanzu haka tana da yarinya ‘yar shekara daya,suna zaune a farawa saidai mijinta na aiki a abujane shima,duk weekend yana dawowa gida yayi da iyalinsa,mijinta nada hali don a revenue yake aiki,ruqayya nada ilimin xama da dan adan da experience na rayuwa mai yawa,sakamakon dan yawace yawace na qasashe da sukayi ada da mijints ibrahim,da kuma tashi da tayi a hannun kakarta,tun zuwan aysha taji jininsu ya hadu,kamar yadda Allah ya hada jininsu da hanan,wannan kenan.
????????????????
Dakin babu kowa sai ita kadai,ita kadai dince ta dawo saboda hanan da mmn hunaifa duka suna aji,sakamakon banbancin course da suke dashi,kowacce akwai abinda take karanta,rana ake qwalawa sosai,shi yasa tana shigowa ta sauya kaya zuwa doguwar riga mai yankakken hannu,ta nade tulin gashinta daya soma damunta da dankwalin rigar,sannan ta shiga bandaki ta daura alwala ko zata ji sanyi,duk da tana fashin salla,saman gadonta ta dawo tayi rubda ciki,dai dai nan kiran aliya ya shigo mata,ba bata lokaci ta daga don dama kwana biyu basuyi wata doguwar hira ba karatu ya soma sa kowa gaba.
Sun kuwa jima suna hirarsu daga bisani sukayi sallama ta yanke ta kira anni suka gaisa,daga anni ta nemi mero sai gwaggo asabe,wanda daga bisani ta tuqe kan lambar umminta,ta jima tana kallon lambar kamar ta kira haka zuciyarta ke raya mata,tayi kewarta qwarai,tana son jin muryarta koda fada zata yi mata,tana son jin motsinta ko yaya ne,qwalla ce ta cika mata idanu,saidai tayi iya yibta ta maidata jin an turo qofar dakin.
Hanan ce,kallo daya zaka yi mata ka tabbatar a jikace take,haka ne kuwa don litatafan ta watsar a qasa
“Wayyo eesha yunwa” dariya aysha tayi tana saukowa daga saman gadonta
“Aikuwa kin daki gurbi,don yau ban dora komai ba na zaci tun yau zaku tafi gida weekend” ciki ta kama tana yamutsa fuska
“Ki taimako don Allah” dariya tayi ta soma yunqurin kunna gas
“Saikin dan qara haquri” saman katifar ta ta koma ta kwanta tana yar mitar data baiwa aysha dariya,tana tsaka da jajjage maman hunaifa ta shigo dakin,ita daya ce don tun wancan satin tabat hunaifa a gidansu bata dawo da ita ba,ba irin mitar dasu aysha basuyi ba
“Ke kike biye mata aysha,barta don Allah yau tasha yunwarta,saison abincin amma bazata iya tsayawa ta dafa ba” ta fada tana hararar hanan
“Haba surukata(haka take tsokanarta tunda qanin maman hunaifan ya ganta yace yana so),idana gaban nazir ishaaq dinne ma haka zaki fada?”
“Eh mana tunda ke son jiki gareki”
“Karki damu zan koya fa ai aysha zata koya min” ta fada tana miqewa zaune
“Ko ba zaki koyamin ba naga kina bata rai?” Sosai ta baiwa aysha dariya,zama da hanan akwai dadi amma idan baka iya ba saikuyita fada,bata ma kalleta ba bare ta gane hakan da har zatayi mata sharhi
“Zanfi kowa murnar ki koya din,saboda sanwa adon macace”
“Gaya mata dai” cewar mmn hunaifa,haka suka dinga zolayar juna suna hirarrakinsu,har aysha ta gama musu jallop din couse couse data ji kifi suka hadu suka ci.
Qarfe hudu hanan ta fito a wanka,tana saka doguwar rigarta ta dubi aysha
“Ko zaki rakani,naga tunda kika zo baki taba zagayawa ko yaushe daga daki sai aji”
“Ina zaki je” mmn hunaifa ta tambayeta
“Kinsan jibi weekend,ga lallen hannu na ya fita,kaina tun last month rabonsa da retourching zan leqa ayimin”
“Nima fa lallen nakeso wlh,abban hunaifa zai biyo jibi mu wuce gida”
“Za’aci amarci kenan?” Hanan ta fada tana kashe ido cikin son tsokano ruqayya,dariya ta bata ta riga ta saba da halinta
“Allah ya shiryeki hanan,ko kunyata bakiji” ta fada tana shiryawa itama
“Ki shirya muje ko?” Ta sake cewa aysha wadda ke kwance tana duba handout,sauketa tayi daga fuskarta tadan yatsina fuska
“Kuje kawai,nikam ban sha’awa,kaina ma kuma a wanke yake” baya hanan taja tana dubanta
“Nimam aysha mamaki kike bani,kekam kaman ba budurwa ba?,duk wani qyale qyale na mata babu ke a ciki,ko dan saurayi haka ban taba ganinki da shi ba?,to tashi yaukam ko kallo saikinje kinyi” ba yadda ta iya da jarabar hanan,hakanan ta miqe ta daura alwala ta sake shafa mai powder da man lebe ta zizara kwalli,har ta dauki hijabinta zata dora saman rigar jikinta tace bata isa ba,bazata jawo a rainasu ba waje zasu je na masu aji,hakanan ta maida ta ciro doguwar riga tayi rolling da mayafinta,plate shoes ta saka da jakarshi,sai wani agogo dan siriri da yazo a cikin jakar
“Ma sha Allah” mmn hunaifa tace
“Da ina da wani qanin bayan ishaaq da nayi masa kamu wallahi” hakanan taji gabanta ya fadi,saita tuna khalipha,tunda ya tafi basu yi waya ba gashi sunci qarfin semester farko,dariya tayi kawai ta basar da zancan suka fito daga dakin,duk cikinsu babu wanda yasan komai game da rayuwarta,ba wanda yasan tana da aure,har yau kuma batayi maganar da kowa ba cikinsu,kallon budurwa duk suke mata,anni ce babarta,haidar qaninta.
Tunda suka fito duk wanda suka gamu da su saisun kalleta,ta rasa kallon na meye,har hakan ya soma damunta yasa ta fara tsarguwa ko tayi wani abu ba dai dai ba,don yawanci idan zata fita lacture shigar hijabi takeyi wani lokaci harda niqab,jefi jefi hanan ko mmn hunaifa kan tsaya su gaisa da wasu wasu kuma su wuce,mamaki take ya akayi sukasan jama’a haka?,sai da suka fito gate din makaranta suka samu abun hawa suka wuce.
Babban waje ne wanda idan aka ce mata akwaishi a wudil zata qaryata hakan,gurin suna gyaran gashi da jan lalle da baqi,hakanan akwai turarukan jiki dana kaya masu kyau da zabar qamshi,kana shiga wajen ma zakasan eh lallai akwai turare a wajen,hanan aka soma yiwa gyaran kai aka sa mata lalle sai mmn hunaifa,daga bisani hanan din da taimakon mmn hunaifan suka tubure sai an saka mata,hakan ba yadda ta iya ta ware kanta aka soma gyara mata
“La haula fi shi’atillah,ba banza ba bakison gyaran kai,muda bamu da mai yawa muke damuwa dama da shi” inji hanan gana zaro ido,itakam murmushi kawai tayi,sai take jinta a takure kaman tana waje,bayan an gama itama aka saka mata lallen,amma.ja tace tana so,iya yatsun hannu da qafa,data cire kuwa saiga yatsun nata shar da su,lallen yayi marroon a farar fatarta,itakanta sai daya bata sha’awa,don ta manta when last da tayi qunshi irin haka.
Sai magariba suka gama,hanan ta siya turarukan kayan dana jiki leda biyu,da gawayi irin mai saurin kamawar nan ta biya suka wuce,suna zuwa daki ta miqawa aysha daya
“Nima a gun mmn hunaifa na soma gani,yana da kyau idan ya kama jikinki” godiya tayi mata bayan ta amsa din,don tana jin qamshinsa a kayanta yana da dadi sosai,a ranar ita kanta taji dadin yadda kanta yayi kyau,hakan bayan ta gama sallar tayita kallon yatsunta har hanan ta lura ta dinga yi mata tsiya.
Tun daga sannan zuwan itama ya zame mata jiki,ko basu je ba data fita ita zata je a sake mata,cikin lokaci kadan saiga ayshan ta soma koyar wasu abubuwa irin na matan da suke da aji daga wajen hanan da mmn hunaifa,yanayin zamantakewarsu da samari da kuma mijinta,idan suna wani abun kallonsu kawai take,ruqayya badai iya tarairayar miji da shagwabashi ba,hakanan hanan da nata saurayin,wani lokaci ita kunya ma take ji sukuwa ko a jikinsu,har gori suke mata kan tayi zuciya tayi saurayi
“Na aurar dake keda hanan na huta lokaci daya” cewar anty ruqayya,sai abun ya soma burgeta,ta dinga jin inama itace su,ta dinga ji inama zata samu wanda zai nuna mata zallar kulawa kamar ibrahim din mmn hunaifa shida mmn hunaifar,ko hanan ita da saddiq dinta,da alama soyayya zaqi gareta,tana son dandana nau’in wannan soyayyar baya gata sauran mutane gama gari data sameta a yanzu,takan jima tana wannan tunanina ranta.
Cikin taimakon Allah suka gama semester daya har suka soma nisa cikin ta biyun,a sannan ayshan ta samu qarin wayewa da budewar ido,komanta ya soma sauyawa saboda gogayya da mu’amala da mutane iri daban daban,shuru shurunta ya ragu duk da cewar har yanzu akwai wannan kunyar da kamun kan,saidai yanayin ado da kwalliya,qyale qyale,iya magana da sauransu duka akwai sauyi tattare da hakan.
A wani zuwa da tayi weekend anni ta mata maganar zuwa gida,itakanta tana son hakan,don tunda tabar gidan a qalla yanzu watanni kusan bakwai zuwanta daya gidan,babu musu ta shirya,kwalliya tayi sosai abinta,dama gashi ta soma zama expert a wannan bangaren,kwalliya mai sanyi da aji da nuna asalin gayu,ba hauka ba hayaniya,haidar shi zai kaita kaman yadda suka saba yawanci idan zata fita ko zata koma makaranta shi yake kaita.
Ana magariba suka isa gidan,ya sauketa shi ya wuce masallaci don yayi sallah,da sallama ta shiga falon,mutum biyun dake tsaye a falon aka rasa mai amsata,sai mummy ce tayi qarfin halin amsawa tana cewa cikin borin kunya
“Indo ce…maraba” sai ta dubi asma’u wadda ke tsaye,inda tasan aysha ce babu abinda zai tsaidata har tazo suyi tozali da juna,uwa uba kuma ga cartoon na kifi da nama da lantana ke fito mata da su wanda zata tafi dasu gida,don dama tuni hamid ya shafe wannan babin,yace abinci shine dole aci,wadan nan sai idan ta kama aci din,ita kuma bata iya jurewa sam,tunda ta saba a gidansu ko yaushe cikin ci suke,uwa uba kuma bata saba laluba abu taji babu ba
“Bari usama su gama sallah sai ya kaiki,wannan ciki da kwadayi yake gashinan saikiyita ci ai tunda na gidanki baya burgeki,banda abun hamid ma da ya barmiki motarki basai ya wani sauya miki sabuwa ba,dududu motar watan ta nawa ma…” Mummy ta waske don kar suji kunya wajen ayshan,ta wannan bangaren sai asma’un taji dadin waskewar da mummyn tayi,hakan ya sanyata ta dan saki jiki kadan,ta koma daya daga cikin kujerun ta zauna .
Aysha baiwar Allah ita sam bata ma fahimci komai ba,hakanan bata kawo wani abu cikin ranta ba banda ma mummyn tayi magana,fuskarta a sake ta soma gaida asma’un,amsawa tayi tana dage kai kaman dai yadda take mata a baya,saidai duk da hakan bai hanata satar kallon ayshan ba,mamaki da fargaba suna mamayarta,sauyin data soma gani tattare da ayshan,saita kwatanta da kanta,babu komai tattare da ita sai uban koma baya data fara cimmata,tana shirin yi qarkon kifi daga ruwa tana shirin komawa wuta,ba ita kadai ba,ita kanta mummyn a ankare take,saita kasa daina kallon ayshan,komai nata ya sauya,hatta da yanayin maganarta
“Anty asma’u ina yaya hamid?” Aysha ta tambaya bawai da wata manufa ba,da manufa daya,duk sai asma’un ta tsargu,tana ganin kaman ayshan tasan wani abu dake faruwa da ita
“Hamid dan albarka yana nan….baha qasar ne ma,yana dubai,dazu suka gama waya wai ya aiko a dauki motarta ya auno mata wata shine kika jini ina fadan almubazzarancin da yake,bayan ba komai motar tayi ba” biyayyar ajiyar zuciya asma’un ta saki,tasan inda don ta itace masifa zata hau ayshan dashi,wanda qila garin masifar ta tona asirin kanta bata ma sani ba
“Allah sarki….an gode Allah ya qara arziqi”
“Amin amin dai…..ke kuma daga aure miji ya kwashi jiki ya tafi cyprus har yau babu shi ba labarinsa,ya bazamaki makaranta kema kamar karatu aka kawo duniya,don yana ganin hadin asma’u ne ai bai kamata ya wulaqanta ki haka ba ko?,kema saikace ba mace ba,komai sai an miki ko an kwatanta miki?” Sallamar daddy ita ta katse wannan dogon sharhin na mummy,ganinsa ya sanya asma’u miqewa,hankalinsa na kan aysha,cikin walwala yake mata maraba bakinsa a bude,itama zamowa tayo cikin qauna da kulawa ta soma gaidashi,ya amsa cikin kulawa yana tambayarta mutanen gidan da karatunta tace komai lafiya
“Khalipha ana can dai karatu da business ya riqeshi,ai ma sha Allah har yau halayensa dana sanshi da su suna nan,kusan kullum sai ya kirani mun gaisa” kanta ta duqar tana murmushi,cikin ranta tana tambayar kanta me yasa yana neman kowa amma banda ita
“Au baki tafi ba?” Daddy Ya tambayi asma’u dake yana dubanta
“Eh usaman bai shigo ba”wayarshi ya ciro yana lalubar lambar usaman yana cewa
“Ai ya kamata ki koma haka,sha’anin zaman aure sai haquri,kowacce mace da tata jarrabawar”
“Haka yake fa,kowa da tashi,ga ayshan nan ita tunda ya ajeta bai sake dawowa ba,gwara ke yakan dawo gida,kuma dama haka masu kasuwanci a qasashen waje suke,kinganta aysha wai tana qorafi kan hamid ya fiye fita waje” murmushi kawai tayi,tasan mummyn ta jina da sanin wace ita,hakanan yanzu da wayewa da karantar mutane ta cikata saita sake yiwa halayyar mummyn fashin baqi ta sake karantarta sosai
“Neman halak yake,saiki qara haquri,wani ma wannan damar yake nema bai samu ba” sai kuma mummyn tayi shuru tana sin yiwa maganar fassara,tana jin kamar ayshan da biyu ta fadi haka,hankalin daddy bai kansu sai daya gama wayarshi
“Yana waje usaman” ya furta yana ciro kudi daga aljihunsa ya miqa mata
“Aci gaba da haquri,kinji dai me na gaya miki dazun ko?”
“Eh daddy na gode”
“To madalla,zan aiko alqasim ne idan kayan sunzo ya kawo miki,zama babu sana’a babu kyau,Allah ya wuce gaba”
“Amin daddy” ta fadi tana addu’a cikin ranta karya furta wata kalmar da zata sa aysha ta gane komai,haka sukai sallama aysha na mata ta gaida gida,da qyar ta amsa tana jin kishi da qyashin ayshan cikin ranta,batasan me yasa kamar ta fita sa’a ba a rayuwa,miqewa.mummy tayi ta bita bayan ta saka an kwashe mata kayan an bita da su ta barta ita da daddy a falon suna hira,hira suke sosai abinsu gwanin sha’awa,yana jin dadin yanayin daya ga ayshan,yasan cewa da ikon Allah ta sake samun ci gaba ne a rayuwarta,a duk sanda ya tuna yadda ya daukota daga qauye su saiyaji tausayinta,ya kuma sake binta da addu’ar ci gaba da samun dacewa a rayywarta,nan haidar ya samesu,shima ya shiga hirar tasu,sun jima kafin daga bisani suyi haramar tafiya,sai a sannan ta kuma ganin mummy,ta danqa musu tsarabar data yi musu daddy ya amsa yana murna bawai don baifi qarfin abun ba,a’ah,saidon yadda kyauta take da girma da kima koma kafi qafin abinda aka yi maka kyautar da shi,yayin da mummy ta karba kadaran kadaham,duk da cikin ranta tayi farinciki,don wata sarqa ce fashion sabuwar shigowa mai tsadar gaske,ko ita bata kai ga siyanta ba har yanzu,anni ce kuma ta bata tace ta bata a zuwan ita ta saya matan,da biyu kuma tayi hakan tasan saqon zaije yadda ya kamata har cikin jiki da zuciyar mummy,ya kuma je din.
????????????????
Washe gari da safe suna breakfast anni ta dubi aysha
“Ni kuwa ayshatu jiya zuwa shekaran jiya kunyi magana da khalipha?” Daga kai tayi ta dubeta gabanta na faduwa,tunda ya tafi baifi sau biyu daya ya kirata,batasan me zata ce mata ba,bata so tayi wata magana kuma batasan me khaliphan yace da anni ba karta warware masa,saita gyada kai kawai
“ke kika sakarma khalipha har haka kenan ya jima bai waiwayo gida ba?”gabanta ne ya fadi,sai tayi qoqarin tattara nutsuwarta,ta hade hannayenta waje guda bayan ta aje spoon din hannunta
“Tunda ya zauna anni akwai uzuri,idan baida wani uzuri na tabbatar bazai zauna har haka ba,zai zo da zarar ya samu dama in sha Allahu,aci gaba dai dayi masa addu’a” sosai kalamanta da amsar data bata ta kwanta mata a rai,sake shiga ranta tayi,tana yaba nutsuwa hankali da kuma haqurinta,wanda hatta yaran ‘yan uwanta da dangin mahaifinsu khalipha masu zuwa dama wadanda basa zuwa bata ga masu hankali da nutsuwarta ba
“In sha Allahu aishatu,Allah yayi muku albarka” duka suka amsa da amin.
Bayan ta kammala ita ta soma tashi,saboda yau takeson ta yiwa anni gyaran dakinta kamar yadda ta saba duk sanda tazo weekend din qarshen wata,abun na damun amal sosai,amma ba yadda ta iya,kuma ita din ba iya yi zata yiba,hakan ya sanya duk weekend ita kuma take tafiya wajen mamanta har sai ayshan ta koma makaranta.
Haidar ne ya sauke ajiyar zuciya yana duban anni
“Anni….nifa ya khalipha bana ganin yana kiran anty…anya ko da gaske ne abinda ta gaya miki kidai bincika”
“Na sani haidar,ina sane na tambaya din,babu wani cikinku da zai layancemin wani abu,na san halayen kowannenku dai dai gwargwado,amma zan sake tambayarta don na tabbatar din”
“Nikam anni kimin addu’a Allah ya bani matar aure kaman takwararki” haidar ya sake fada yana dan murmushi,itama murmushi tayi tana dubanshi
“Aysha tana da nagarta aliyu,nagarta mai yawa,tana da tarbiyya wadda dai daikun yara a yanzu keda irinta,duk da tarbiyyarta daga indallahi ce,ina maka fatan samun mace kamanta”
“Allah amin” ya amsa yana daga hannu,bata rai mus’ab yayi
“Nifa anni?”
“Kaima haka auta” ta fadi tana murmushi gami da shafa kanshi,sai ya saki dariya yana jin dadin annin ta mishi haka gaban aliyu don yaji haushi fadansu na sako da sako,saidai wannan karon dauke kai yayi kaman bai gani ba.
_Ya Allah ka karemu daga sharrin mutum da aljan_????
*mrs muhammad ce*??
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha: