Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 37

Sponsored Links

37

Ta kammala gyaran dakin anni tana shirin fitowa annin ta shigo
“Sannu da aiki ayshatu,Allah yayi ma rayuwarki albarka” sunkui da kai tayi tana murmushi ta amsa da amin,ko yaya annin ta gwada jin dadinta kota yabeta kan wani abu dadi take ji,saboda lafazi ne da bata saba jinsa ba a bakunan al’umma a kanta,cikin karamcin ma da suka yi mata batajin tana da abinda zata saka musu dashi
“Amm…aysha” waiwayowa tayi tana amsawa
“Kikace kuna waya da khalipha?” Kai ta gyada gabanta na faduwa
“Kin tabbata?” Kai ta sake gyadawa kawai ba tare data furta komai ba
“Shikenan jeki,Allah ya dafa mana”
“Amin” ta bata amsa tana ficewa,yayin da annin ta bita da kallo,ta sani cewa samun kaman ya aishan a wannn zamanin abune mai matuqar wahala,sosai take qaunar ayshan tare da fata da kuma addu’ar Allah ya nuna mata wani lokaci da take muradin gani.

Dakinta dake nan sashen anni ta koma tana jujjuya maganar cikin ranta,kaddai ace anni ta dago wani abu ne?,da wannan tunanin ta shiga wanka,bayan ta fito ta shirya,tana son ta debo wasu kayanta daga can sashen khalipha,wanda tunda ya tafi itama ta tafi bata sake leqa sashen ba koda wasa,muqullan ma tunda ta ajesu a locker bata sake bi ta kansu ba,bude locker din tayi ta dauki keys din ta fice zuwa sashen nasu.

Related Articles

Gab da zata shiga wayarta tayi ringing,saita dakata tana dubawa,hanan ce,dariya ta dan saki tasan cewa akwai wata a qasa tunda ta kirata,dagawa tayi da sallama ilai kuwa karadin hanan din ya cika kunnenta,ko gaisawa bata tsaya sunyi ba tace
“Nida saddiq…yace na cikashi da zancan aysha naqi na hadaku ku gaisa,na gaya mishi ba laifi na bane,ke din ce kifin rijiya ce baki zuwa ko ina” dariya aysha tayi
“Bani shi mu gaisa” miqa masan tayi ya amsa suka soma gaisawa,sosai yake da so jama’a kamar hanan din,sun dan taba hira kadan kana daga bisani ya zolayeta kan ta kula mishi da gimbiyarsa,sannan zayazo a raba gardama kan wanda yafi wani son dan uwanshi,shi yace ya fi sonta ita tace shi,da dariya aysha ta katse kiran jin musu na niyyar barkewa tsakanin hanan din da saddiq,tana dariyar abin ta bude sashen ta shiga,abu na farko data soma cin karo da shi daya daga cikin window size na hoton khalipha wanda ya fito tarrr kamar kayi masa magana ya amsa ka,fuskarshi qunshe da murmushi wanda hakan ya sake bayyana kyanshi,gabanta ne yadan fadi,sai taji kaman shine a gabanta yake kallonta,dauke kai tayi taci gaba da shiga sai kuma ta kasa,sake maida kanta tayi zuwa ga hoton,ta soma takawa a hankali zuwa sashen da hoton yake.

Ta jima tsaye gaban hoton tana kallonshi,sai ta sanya hannunta a hankali ta shafi qafafunsa,hakanan tausayinsa taji ya kamata,yabar gida yabar ahalinsa duk saboda ci gaban familynsa,tsahon watanni baiga mahaifiya mafi soyuwa a gareshi ba ko wani dan uwansa,cikin ranta ta soma jera masa addu’ar samun dacewa da nasara a rayuwarsa,ba shakka khalipha wani babban jigo ne a rayuwarta,yana daya daga cikin shika shikan da komai nisan rabuwa komai tsahon lokaci ko zamani bazaiyiwu ta manta da wanzuwarsa ba,iyakacin zamanta a gidan ta shaida jatumtarsa a rayuwa,jarumi ne kuma tsayayye na gaske,zata so taji wani abu daga tarihin rayuwarshi daga bakinsa,ta tabbata akwai gwagwarmaya ba qarama ba,a hankali ta sauke hannunta ta juya,sai hanan da saddiq suka fado mata a rai,murmushi ta saki tana ayyana dadin da soyayya ke da shi,sai ta dinga gwada kanta a matsayinsu,wani tunani ne ya fado mata a rai wanda ya tilastata daga kai ta dubi daya hoton khalipha dake gabanta,wanda yana zaune ne saman wata irin kujera ya dora qafarshi daya kan daya,kai ta girgiza tana gayawa kanta bamai yiwuwa bane,khaliphan?,da hanzarin ta watsar da tunanin ta shiga nazarin sashen,akwai ‘yar qura bamai yawa ba,wanda hakan ke alamta ana shigowa a share lokaci lokaci,sosai ta gayara wajen tsaf,take komai ya koma fes,ta rurruf abubuwan da tasan zasu qara qura ta sake dauraye jikinta ta debi kayan da take buqata tabar sashen.

????????????????

“Wayyo bayana” aysha ta furta bayan ta dago daga durqushen da tayi tana hada kayanta,ajiye littafin hannunta hanan tayi tana dubanta
“Wai karkicemin wannan satin duk sai kin rigamu tafiya gida?da alama ma dai ni kadai zaku bari,don maman hunaifa ma jiya najita tana waya da abban hunaifa abuja zatayi weekend” Sai data samu gefan gadonta ta zauna tana miqe qafarta sannan ta amsa mata
“Wallahi haka kawai wannan karon duk hankalina yayi gida….ki shirya don Allah mu wuce wajen wankin kan nan sai nayi zan wuce”mirginawa hanan tayi daga kwancen da take zuwa daya bangaren
“Wallahi yau kasala nakeji da gajiya…anya zan iya zuwa kuwa?” Harararta ayshan tayi
“Baki isa ba kuwa,ki tashi kawai ki shirya” hakanan hanan ta miqe a kasalance ta shiga wanka ta fito ta shirya suka fice.

Tare suka jero suna ‘yan hirarrakinsu jifa jifa,idan sunga wanda suka sani su tsaya su gaisa wani lokaci har sukan dan taba hira kafin su wuce.

Dab da zasu wuce wata mota hanan ta taba aysha
“Gafa mutumin can,kinga mota zai bude amma ya tsaya satar kallonki”
“Wafa?” Ayshan ta tambaya tana duban hanan
“Waye banda daddy huguma,kinsan Allah gayen ya hadu,a nan makarantar yake geology ya karanta suka riqeshi suka bashi lacturing,da qyar ma idan ba zuwa sabuwar semester ku hadu da shi ba,ki bashi dama kawai aysha wallahi,ya hada komai fa” kallonta ayshan tayi taja tsaki tana kauda kai,gabanta taji yana faduwa
“Kekam hanan kinga dacewar haka?,kinsan wayeshi ne?,pls karki sake wannan maganar” dariya da mamakinta take boyewa,batasan me yasa ayshan ta tsani ayi mata zancan wani ba,ta tsani ace wani na sonta
“Allah ya baki haquri,amma maganar gaskiya karki bari wannan damar ta subuce miki,ina miki sha’awarsa”
“Toh naji” ta fada da alama ta qosa da zancan
“Aysha sai yaushe zaki bawa mutane dama?,waikekam soyayya bata burgeki?,kinsan bakasan dadin rayuwa ba harsai kaso kaima ansoka?,rayuwar da babu soyayya nikam ina tunanin wace iriyar rayuwa kenan?” Hanan ta fada da alamun da gaske take magana,shuru aysha tayi tana saurarenta,saita dinga jujjuya maganar hanan din cikin ranta.

Gab da zasu fice daga makarantar motar saddiq ta sako kai,ja hanan tayi ta tsaya tana dubanshi cikin murmushi sanda yayi parking ya fito
“Wato ba zata kayi niyyar yimin kenan?”murmushi yake yana dubanta
“Tuba nake ranki ya dade,na kasa zama ne kawai naji inason ganinki”
“Yayi kyau,kaman kasan tunaninka nima nake”
“Zuciya daya”
“Ruhi daya” sai suka sanya dariya shi da ita,aysha na gefe tana kallonsu,burgeta suke sosai yadda suke son junansu
“Ranki ya dade” saddiq ya ce da aysha
“Tare da naka..Allah yasa ba zuwa kayi ka hanata rakani ba”
“Ni na isa,ina zuwa?”
“Zamu wankin kaine”
“To bismillah ku shigo nayi rakiya” ba musu suka qarasa jikin motar,hanan ta shiga gaba aysha na baya yaja suka tafi,cikin motarma hirarsu suke,ba komai aysha keji ba,wani lokaci saidai taji dariyarsu har suka isa wajen,cewa yayi zai jirasu,saboda haka tabar hanan cikin motar ita ta shiga aka soma yi mata.

Awa uku aka gama musu komai har lallen,yayi kyau kuwa fiye da ko yaushe ita kanta taga haka,kaman wata amarya haka tayi fes tayi kyau,wannan karon haka tabar gashinta,maimakon daa da ake mata manya kalba guda biyu ko uku,ta saki jelarta kota hadeta da ribbom.

Da suka dawo ma tare ta barsu ta shige hostel din,ta taras maman hunaifa ta dawo harta musu abinci,sallah kawai tayi ta zauna suka ci abincin suna hirarsu har zuwa sanda hanan ta shigo.

????????????????

Qarfe goma drivern gidan anni ya iso
“Toh sai Allah ya kaimu monday kuma”
“Anya ko zako ma dawo monday din kuwa?” Hanan ta fada tana tsokanarta,waiwayowa tayi tana kallontq cikin harara
“Me kika gani?” Dariya tayi
“A’ah babu komai,wannan zumudi haka,kodai kinyi kamu ne?”tsaki ta saki tana dariya
“baki da amsa”
“Idan tayi wari maji” hanan ta fada tana qyalqyalewa da dariya,har bakin mota hanan din ta rakota sukai sallama,don maman hunaifa tun safe ta fita.

Cikin girmamawa dirvern ya fito xai amshi kayan hannunta ta dakatar da shi
“Yi zamanka malam shehu” ba qarami girmansa take gani ba,saboda a qalla ya kusa haifarta,haka shima ba qaramin girmamata yake ba saboda yadda take ganin mutuncinsa,cikin mota suna tafe suna hira jifa jifa,duk da rabin hankalinta na kan dan qaramin littafin dake hannunta,wanda duka lacture din jiya ce.

Da yammaci suka iso gidan,kaman kullum anni na zaune a falo tana kallon africa t.v 3,dukkansu fuskokinsu qunshe da murmushi,anni ta amsa sallamar ayshan
“Lale da ‘yan makaranta”
“Anni sannu da gida” ta fada tana zama qasa kaman yadda al’adarta take yawanci idan annin na zaune kan kujera
“Yauwa ayshatu” gaisawa sukai cikin kewar juna annin na tambayarta hanya da sauran al’amura,daga bisani annin da kanta tace taje ta huta,ba musu kuwa ta wuce dakin ta,wanka tayi tana saman gado zata shafa mai a nan bacci yayi awon gaba da ita,bata farka ba sai la’asar,shi dinma kiran wayar aliya ya tada ta
“Kin dawo kenan”
“Tun azahar ma,wannan satin duka makarantar naji ta isheni gida nakeso”
“Da kyau,ina hanya to ki jireyeni” cikin zumudi ta amsa mata dan sun dan kwan biyu basu hadu da aliyar ba,alwala ta daura ta shafa mai da hoda ta sauya kaya ta tada sallah sannan ta fito falon.

Amal ce kawai zaune a falon da alama bata jima da zuwa ba don har mayafinta na kafadarta,hada ido sukai da aysha,ayshan ta sakar mata murmushi,yayin da gaban amal din ke faduwa,kullum rana ta Allah ayshan sauyawa take kamar wadda ake canzawa,komanta qara kyau da fitowa yake kaman ba ayshan data sani watannin baya da suka shude ba,duk sa cewa ko dacan dinma ayshan a hade take,saidai kanta ya bude sosai fiye da yadda ta santa
“Amal ce?”aysha ta fada tana murmushi
“wallahi” ta amsata a taqaice tana jin kishinta na ratsata,tana satar kallon yadda fatar ayshan tayi kyau,jan lallen yatsunta yayi matuqar zama ado a gareta.
“Kwana da yawa….sau wajen hudu ina zuwa weekend bana samunki”
“Nima makaranta na koma banda cikakken lokacin kaina”
“Ma sha Allah,abu yayi kyau Allah ya taimaka” ta fada cikin fara’a ba tare da ta kawo komai ranta ba ta wuce kitchen.

Atika ta samu a kitchen tana yunqurin hada abincin dare,da fara’a ta tari ayshan
“Habawa,shi yasa tun yau naji gidan ya saki,ashe uwar masu gida ce ta iso” dariya tayi tana zama kan kujerar dake kitchen din
“Baaba atika kina kaini inda banje ba”
“Ai gaskiya ce,na jima banga mutum kamarki ba,Allah ya baki dama kina gida kamar wannan amma baki dauki kanki a bakin komai ba,magana ta Allah ba ganin ido ba halayenki masu kyau ne”idanu ta lumshe,tana qissima inama ace ita da mahaifiyarta ke wannan hirar?,inama ace itace ke yabonta kamar haka?
“Allah ya sanyani na zama mafi alkhairin abinda kuke zato,kuma ina roqon Allah karya kamani da abinda kuke fadi….me zan samu baba banci komai ba”
“Yau dai sinasir na yiwa hajiya,kinsanta da son sinasir,zakici ko a dafa miki wani abun?” Kaita kada
“A’ah baba karki wahal da kanki,kai bawa duk abinda ka samu aici kake,bani sinasir din” murmushi baba atika ta saki ta soma zuba mata,halayyar aysha na burgeta qwarai,kusan tayi gadon anni(kira da jan hankali a gareku masu ‘yan aiki a gida ko gurin aikin da kake da wasu a qarqashinka,abinda ke qarawa mutum girma farinjini da kwarjini shine ka nuna qasqantar da kai dakai da tawali’u a inda ka isa kuma kake da girma ka nuna kai ba mai girma bane dai dai kake da kowa dake wajen,wannan abun na qaramin qara soyayyarka yake a zuciyar na qasa da kai ba,kuma dabi’ace mai kyau,koyi ne da halin ma’aiki,yadda yaje zama cikin sahabbansa kai bakace shine ba banda haiba kwarjini cikar zati da kyan da babu mai yashi da Allah S W T ya bashi,Allah yasa mu dace).

A kitchen din ta cinye abincin tas,tana ci suna hira,muryar Aliya data jiyo a parlour ya sata fitowa,tana zaune suna hira da anni da alama bata jima da shigowa ba,amal na zaune gefensu tana chart saidai rabin hankalinta na kansu,bayan sun gama gaisawar anni ta miqe ta koma samanta ta basu waje,dab da aliya aysha ta zauna tana dala mata duka a cinya
“Autar mama….kinga yadda kika koma me mama ke baki kina cinyewa ke kadai saboda rashin amana koki ragen?” Dariya aliyan ta saki
“Wai don karna tambayeki shine kikai riga malam masallaci,me kuke ci a wudil,koda yake nasan aikin anni ne wannan,wannan ai saikisa angon ya kasa shaidaki idan ya dawo” baki aysha ta rufe da hannunta
“Wallahi sashen masharranciya ce ke”
“Errrrhmm….nikam inason tambayarki dama wanne mai kike amfani da shi yanzu,naga kanki kamar ba haka yake ba sanda kikazo gidan nan” cewar amal bayan tayi gyaran murya,duban jelar gashin ayshan take har tasa aliya ta kalla itama
“Ba wani mai,kawai na samu gidan gyaran gashi mai kyau ne”
“Kuma ma dai abun sa’a ne” aliyan ta fada ba tare data dubi amal ba,tunda aysha taga haka tasan neman magana ne ya motsa da biyu aliyan ta fada,kama hannun aysha tayi
“Muje ciki don Allah kisha labari” miqewa tayi suka wuce dakin ayshan,suna shiga aliyan ta dubeta
“Wai har yanzu wannan ‘yan zaman kisan daben suna zuwa dama?” Baki ayshan ta tabe
“Eh,ina ruwanki dasu?” Dariya ta saki,tasan halin ayshan sarai da rashin son yin zancan wani
“Tabdi,ai wallahi da nice da tuni na saita musu hanya,suna zaune ina da miji kamar khalipha yana giftasu?” Dariya ta bata sosai saboda yadda ta gwada da hannunta,jan hannunta tayi ta zaunar bakin gado
“Ce miki akayi mijina ne,yayana ne” wata harara aliya ta watsa mata taja tsaki
“Kici gaba da fadin haka,kina zaune zw’a farauce miki shi zakice na gaya miki” dariya ce ta subucewa aysha ganin yadda aliyan ta haqiqance bilhaqqi,aliyan zata maida mata amsa ta katseta ta hanyar daga mata hannu
“Yi haquri anty aliya ina zuwa” ta fada tana dariya sannan ta fice ta samo mata abin motsa baki ta dawo
“rannan naje imam wali dubiya….kinsan wa na gani?” Kai aysha ta girgiza tana zubawa aliya lemo sannan ta miqa mata,amsa tayi tana qunshe dariya
“Wai asma’u a third gate tana jiran adaidata sahu,dama tana hawa motar haya a rayuwarta?” Aliya ta qarashe tana bushewa da dariya,kallonta aysha take sosai,labarin bai mata dadi ba saidai bata ma tunanin asma’un ce
“Anya ko sashen?,anty asma’un,kai hamid ma bazai barta ta hau abun hawa na haya ba” ta fada tana girgiza kai
“Wallahi karkiji zancan wasa ita ce,kinsan muna hada ido tayi maza ta dauke kao kaman bata ganni ba,nayi nayi mu hada ido amma taqi” zungurinta aysha tayi
“Kinga kisha lemonki,banson qarya,wai aliya yaushe kika baci da gulma”
“Allah indai gulmar asma’u ce saina kawo miki,don na tabbata itama tana maraba da taki da zata samu wanda zai kai mata,ban taba ganin mugu maqetacin mutum da baison ci gaban kowa ba sai ita” sai data kai nan ta kurbi lemon sannan ta aje
“Kinsan ma Allah labarin da nake ji cikin BUK?,wai reshe ya juye da mujiya,hamid gasata yake”
“Nikam.ban sani ba,Allah ya shiryeki sashen tunda haka kika koma” dariya take sosai,har ga Allah bawai tana jin dadin halin da ake rade radin asma’un na ciki bane,a’ah,sakayya da isharar da Allah ya soma gwada mata ne ta dace da ita,yadda asma’un tayi qaurin suna wajen wulaqanci da yanqwana jama’a a fadin makarantar,hakan ya sanya labarin halin data fada baiyi wuyar isa kunnuwan Al’umma ba,dama ance idan ka shuka alkhairi shi zaka tsinta a gaba,Allah ya bamu ikon aikata mai kyau.

Har akayi sallar magariba basu sani ba saida suka duba agogo sannan suka tashi sukayi,a nan aliya ke bata labarin soyayyar ta da mahmoud yake nema,duk da batasan mahmoud ba bata taba mu’amala da shi ba,amma ance idan kanason sanin waye mutum ka kallo abokinsa sai tayi mata fatan alkhairi ta kuma ji dadi har zuciyarta,har bakin gate ta rakota bayan anni tayi mata kyautar turare suka rabu suna begen juna.

????????????????

Washegari ta tashi da gyaran sashen khalipha kamar yadda ta yiwa kanta alqawari duk asabar din qarshen wata idan tazo zata dinga yi.

Gyara na musamman tayi masa,ta share ko ina fes,tsayawa tayi tana kallon wajen yadda ya dauki qyalli tana maida numfashi,klien take buqata kuma babu sashen,don haka ta maida hijabinta ta kona sashen anni ta samo.

Da sallama ta shiga duk sai suka juyo suka kalleta,mus’ab dake saman dining ya gama cin abincin rana yana saukowa ya qarasa saukowa da dan gudu gudu zuwa wajen anni tun kafin ya qaraso yake cewa
“Suprise,suprise please anni” yana isa kusa da ita ya mata rada sannan yace da haidar
“Zomu tafi” binsu sukayi da kallo,sai da sukazo gab da aysha qasa qasa tace dasu
“Adai qulla alkhairi”
“Babban alkhairi kuwa zaki gani anty” cewar mus’ab,shidai haidar dariya yake suka rankaya suka fice,qarasowa tayi anni tace
“Sannu aysha,aiki dai aiki dai bakya gajiya,ki dakata hakanan ki samu abinci kici kiyi wanka maza” murmushi tayi
“Ai na kusa gamawa anni,klien zan dauka toilet kawai ya rage”
“To Allah yayi albarka,madalla”
“Amin anni” ta fada tana wucewa store don ta dauki klien din,a duk sanda annin ta sanya mata albarka tana jin dadi har cikin ranta,har cikin zuciyarta tana jin wani sanyi,sai taga kamar umminta ce.

Sai data ga komai yayi mata yadda takeso,don karambani har wasu abubuwan ta sauyawa waje sannan ta cire kayanta cikin bedroom ta daura guntun towel ta shiga wanka bayan ta bar duka sashen na fidda qamshin irin turarukan wutar da take siya wasu ta baiwa anni,wasu ta aje wajenta.

Fuskarsa qunshe da murmushi yake takowa zuwa sashen nasa,fes yake jin zuciyarsa,tunda ya shigo gidan fushin daya tsammaci gani wajen anni saiya samu akasin hakan,cike yake da zumudin yin wanka ya koma wajen anninsa kamar yadda ta hanashi zama yace yaje ya watsa ruwa tukun,don na qaramar rana ake ba ranar,sauqinta ma cikin raba yake amma duk da haka shima yana da buqatar watsa ruwan.

Ba wani shakka ko fargaba ta fito daga wankan abinta,ta isa gaban mudubi wanda yake kallon qofa ta baiwa qofar baya,ta zare ribbom din kanta ta tsiyayi mai ta soma shafawa kanta,hade haden mayuka ne wanda suka qarawa kanta kyau baqi da sheqi,ba wani kudi mai yawa ta kashe masa ba amma duk wanda ya kalli kan sai ya tsammaci da wani mai me tsada take amfani,tana shafawar tana rera waqar joeboy ta begining to fall in love jifa jifa,sai data tabbatar ya ratsa ko ina man ta feshe kan da turaren kai ta dauko comb ta soma tajewa.

Daddadan qamshin da falon keyi ya sheqa ya lumshe idanunsa,yasan aikin anni ne ita tasa aka masa wannan gyaran duk da baisan waye yayi ba,tasan yadda yakeson qamshi da tsafta wanda daga gareta ya gada,kyakkyawar jakar hannunsa ya aje saman kujera ya nufi bedroom dinsa,saidai dan motsin da yake jiyowa ciki sai ya bashi mamaki,a hankali ya dora hannunshi saman mabudin qofar ya tura qofar dakin.
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button