Hausa NovelsTayi Min Kankanta Hausa Novel

Tayi Min kankanta 19

Sponsored Links

19*

 

Cikin tsananin firgita jameel ya juyo yana kallon Hammad,kamin yayi wani abu hammad ya cakumoshi ya bugasa da jikin bango,ya fara kai masa duka yana fadin.

Related Articles

“macuci azzalumi,Allah ya toni asirinka,dama kaine ka haike mata,shine yanzu kazagayo zaka ɗora,kabani mamaki”yaci gaba da kai masa duka.

Tsananin mamaki ne yasa jameel kasa furta komai,yakuma kasa kwace kansa a hannun hammad ɗin.

Zahra cikin zafin nama tayi kanshi tana faɗin”yaya me yayi maka ka ƙyaleshi,ina ruwanka dashi,”tana jan rigar hammad ɗin.

A fusace ya juyo kamar mayunwacin zaki ya kife ta da wani wawan mari,take yanke tasaki fitsari,sakamakom taurarin da ta gani na gilmawa a idonta.

“munafuka,ke har kina da bakin magana,shiyasa kika ƙi faɗin wanda ya maidake garejin ashe wannan munafukinne,to wlh ba agidana zakuyi bariki ba sede awani gidan”

Jameel tunda hammad ya koma kan zahra ya zame jikinshi ya fice agidan ko ganin gabanshi bayayi sabida tsananin ɓacin rai.

Hammad rasa abunyi yayi kawai shigewa cikin gidan yayi ya barta kwance agurin tana kuka.

A falo ya zauna yana huci kamar zaki.
Jiki asanyaye zahra ta miƙe ta nufi cikin falon,yana ganinta ya ɗauke kai.
Durƙusawa tayi agabanshi tana kuka,cikin kukan tace”jameel ba fasiƙi bane yaya,hasalima hannuna be taɓa riƙewa ba se yau,shima nice nayi kuskuren rungumeshi,nasan shine agarinmu falgore,inda ya nemi taimakon girko abinci sabida wani abokinsa dake fama da cutar ulcer,na rabu da jameel ne ranar da ƴan taadda suka zo garinmi suka kashemin innata,inda na haɗu da abokin jameel ɗin sojan me ulcer daya keta mutuncina ana ruwan sama acikim wata bukka dana shiga domin ceto rayuwata,har baƙin mugun yace min jameel ɗin ya mutu,Allah ya isa tsakanina da kai soja me ulcer bazan taɓa yafe maka ba mugu azzalumi,baƙin kare wanda baze shiga aljannah ba”ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka.

Hammad wanda yayi tsit kamar ruwa yacishi,jin abinda zahra ke faɗi,wasu hawayene masu zafi suka zubo afuskarsa,zuciyarshi ce tai masa nauyi,da ƙyar yace.

“kina nufin kece ƴarfillo?”

“Nice yaya,hala ya baka labari na”

Wata ajiyar zuciya yaja sannan ya yanke jiki ya faɗi agurin ba numfashi,wani farin kumfa na fitowa abakinsa kamar yasha guba.

A gigice zahra tayi kanshi tana kiran sunansa tana girgizashi amma ina ko motsi baya yi.

Da gudu tayi gurin me gadi,ta kirashi koda yazo yaga halin dayake ciki,wayarshi ya ciro ya kira daddy kasancewar yana da numbarshi,baa jima ba,daddy ya iso da tawagarsa hankali atashe aka ɗauki hammad zuwa asibiti rai a hannun Allah zahra se kuka takeyi kamar ranta ze fita,dan gani take hammad dinta ya mutu.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button