Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 40

Sponsored Links

40

 

Tunda suka doshi sashen anni suke jiyo muryar rahama,hira suke da mus’ab amma kamar musu musu haka,anni na gefe bata sa musu baki ba tana sabgar gabanta,suna shiga ta bisu da idanu,idonta kan litattafan dake rungume hannun khalipha,duk wata walwalarta ta bace tsaf kunnuwanta da idanunta dukka suna kansu,idanu suka hada da aysha ta daga mata gira bayan ta sakar mata murmushi,ta mata sign na toya kika gani? Da idanunta,saita dauke idonta ta basar tamkar bata gani ba,saidai har yanzu kunnuwanta na wajen
“Gobe zamubi jirgin qarfe biyu anni in sha Allahu”
“To Allah ya bada sa’a,Allah ya nuna mana goben”
“Amin” ya fada cikin hikima yana karantar yadda hankalin rahama ya raja’a a kansu,littafi daya ya zaro cikin wadanda suke hannunshi ya dan buga ma ayshan kadan
“Wuce muje ki qarasa aikinki” kunya ce ta kamata,amma ya riga yayi warning dinta tun jiya,idan ma bata bishin ba zaiyi abinda yafi haka ne gaban annin kamar yadda yace mata,dole ta miqe,ya tasata a gaba suka fice.

Related Articles

Zube litattafan yayi saman kujera sannan ya harde hannunsa a qirji,ya zuba mata ido kaman yadda ya saba,baisan me yasa idanuwanshi suke qawatuwa da kallonta ba,amma har yanzun yaqi yarda da hakan dari bisa dari
“Ki sauya wasu kayan kafin mu sake fita” ya fadi yana sauke hannayenshi,kayan jikinta ta kalla,duka duka nata wuce awa daya da sanyasu ba,saboda ta riga data dauki corse wajen maman hunaifa,ba zaka taba rasata cikin tsafta da qamshi ba ko daga bacci ta tashi bare da ranar Allah,ya fahimci me take nufi tsaf,sai ya soma takowa zuwa gabanta wanda bata ankara da shi ba sai daya zo gab da ita,cikin hanzari tayi niyyar ja baya saiyayi caraf ya riqo hannunta,idanunshi cikin nata yace
“Kwalliyarki tayi kyau,qamshinki yana tashi zuwa ko ina,kawai inason ta darsa a ranta cewa akwai dalili na sauyin kayan da kikayi daga shigowarmu na awanni biyu kacal” wayyo,ji tayi kamar qasa ta tsage ta shige,gashi yaci gaba da kallonta ne bayan ya gama maganarshi ba tare daya sakar mata hannu ba,fatanta daya ya sakar mata hannun saidai yaqi
“Ko baki ji ba?” Ya fada yana murza yatsunta wanda hakan ya haifar mata da wani yanayi cikin jikinta da nashi gaba daya,gaba daya jikinsa ya amsa shi yasa ta samu damar zare hannunta saboda kasalar data saukar masa
“Naji….toh” ta fada da sauri tana zamewa ta nemi wajen zama,sai ya juya kawai shima ya wuce cikin bedroom.

Yatsun nata take lanqwasa idanuwanta na a rufe,tana son tantance wane baqon yanayi ne haka take ji cikin jikinta sa zuciyarta,idanu da fuskar khalipha na mata yawo cikin tunaninta,yaba kwalliyarta zuwa qamshinta da yayi sai take jin kanta na kumbura,baqin kalamaine a duniyarta,sai take jin kamar hira ce irin ta tsakanin masoyi da masoyi,murmushi ya qwace mata tana hasaso gata ita da khaliphan kamar yadda take ganin hanan da saddiq,kamar wadda aka tashi a barci ta gargadi kanta,saidai ire iren wannan tunanin ya kasa barin kwanyarta,a haka ya cinye duk awoyinta har ta soma jiyo kiran sallar magariba sannan ta miqe ta zauna sosai tana tattara nutsuwarta waje daya.

Sanda ya fita sallah ita kuma ta shiga ta shirya hadi da dauro alwala,taga shigar da hayi na qananun kayan marron and black,tana sane ta gidda wata gown maras nauyi saidai tana da duhun kala wadda take guda biyu ta ciki marron mai dogon hannu tana hade sarqar wuya saita sama baqa armless,tayi rolling da maroon vail,kwalliya kadan tayi ta gogawa tausasan lips dinta lipstick marron,hakan sai ya sake fidda kyanta ya kuma fitar da shape din qaramin bakinta,dan siririn abun hannu mai guda daya da zobe ta sanya a hannunta sannan ta yiwa kanta ruwan turaruka masu sanyin qamshi,ba qaramin kyau shigar tayi mata,kafin ta gama sallar magariba taji shigowarsa,bata fita ba saboda tasan sai sunyi isha’i zasu shiga,ana idar da sallar isha’i kuwa ta fito daga dakin.

Yana tsaye gaban t.v batasan me yake dubawa ba,yadan bawa qofar fitowa daga dakin baya,takun takalminta duk da plate ne ya sanyashi juyowa,baisan ya akayi ya tsinci kanshi da kallonta ba,wannan karon muraran ko alamun kunya bare ya waske babu
“Hi….na shirya”,aje remote din hannunshi yayi ya nuna mata hanya da hannunshi alamun tayi gaba,ko sau daya bai dauke idonshi daga kanta ba sanda take takawa,kamar wadda ake busawa sarewa haka take takawa,gab da zasu shiga sashen taji an riqo hannunta ta baya ya janyota baya,saura kadan ta fada qirjinsa,ta daga kai tana dubanshi,qwayar idanunsu suka hadu da juna,saiya saukar da idanunshi zuwa kan dan qaramin bakinta daya qawatu da jambaki ya qara masa taushi,yatsanshi ya saka ya lakaci jambakin yana ci gaba da duban fuskarta
“Kinsan yadda jambaki ke miki kyau kuwa?,Allah yasa bakya sakawa a makaranta”abinda yakeosn fadi mata kenam don iya gaskiyarsa kenan,saidai kuma baiso ta fassara maganar da wata siga ta daban,a daidai lokacin rahama dake zaune ta cikin falon tana hangosu,ranta yayi qololuwar baci,tana ji a yau saita nunawa aysha iyakarta,sai ta miqe tsam kawai ta isa saman teburin,wanda tun dazu mus’ab ke mata magana tazo bata taso ba,don yau anni ba zata samu saukowa ba saboda ciwon da qafarta ke dan mata.

Dauke kanta aysha tayi tana jin wani nauyi na ratsata,shima saiya basar yaci gaba da riqon hannunta har zuwa cikin falon.

“Ina anni?” Khalipha ya soma tambaya sanda suke tsaye shida ayshan bayan sun gama gaidashi
“Tana sama qafartace tadan matsa mata”
“Ohk bari mu ganta” ya fada yana danyin gaba aysha zata bishi mus’ab din ya sake cewa
“Ammm….yaya,tace idan kunzo ku fara cin abinci tukunna” yasan ta fadi haka ne saboda tasan halin kowanne cikinsu
“Anty ko wata fita ta musamman zakuyi da yaya?” Haidar ya fada yana murmushi yana duban aysha,itama sai tayi murmushin tana cewa
“Me ka gani?”
“Wannan kyau haka?”khalipha dake zuba ruwa a cup yana daga tsaye ba tare daya zauna ba ya daga kai ya dubi haidar din,haka kawai yaji wani iri,itakam ayshan bata lura da haka ba tayi murmushi
“Bana son zolaya haidar”
“Allah ko,ga guri ki zauna dama inason muyi wata magana dake” ya fada yana nuna mata kujerar dake daura dashi,duk da cewa akwao empty chair guda daya a tsakaninsu
“Zauna nan” khalipha ya fada a kausashe yana ja mata kujerar da yake tsaye a bayanta,yanajin wani irin ba dadi cikin ranshi wanda baisan dalili ba,bai ankara ba sai da yaga suna kallonshi shida rahama,don mus’ab ya duqufa danna waya wanda bai wuce charting yake ba,yayin da amal ta maida hankali wajen zuba lemo tana sha wanda idan ka qare mata kallo hankalinta ba wajen yake ba itama,sai data zauna shima yaja ta kusa da ita ya zauna
“Amal,zuba min abincin” ya fada a dake,dubanta takai ga amal din,sai taga fuskarta ta washe ba kamar dazu ba,ta aje cup din hannunta ta miqe tsaye tana dauko platw wamda yake daga gaban ayshan,haka kawai taji haushi ya kamata,me kenan me yake nufi,raini yakeso yaja mata ko kuwa,dafe hannun amal tayi suka hada idanu,saita sakar mata murmushi
“Yi zamanki,shi ala dole yau bazanyi komai ba,bayan ya sani idan ina kusa dashi lokacina duka nashi ne” ba amal kawai amsar ta taba ba,hatta da rahama dake gefe taba karantar kowa d’ai d’ai dashi kanshi uban gayyar daya tsokani abun,wanda shi kansa baisan me yasa yayi hakan ba,yasan dai baiji dadin yabawar da haidar ya yima adonta ba
“Love is….”sauri mus’ab yayi,yayi yayi gum da bakinsa daga sunutar bakin dayaso yi,saiya soma zungurar haidar yana masa gulma,
“uhmmm…kya fadi gaskiya idan ma kishi kika ji,tunda dai shi ita yace ta zuba mishin ko?” Rahama ta fadi tana qarashewa da dariya duk da cewa dariyar bawai har cikin ranta ita kenan ba da biyu ta fadi hakan
“Babu damuwa idan ma kishin ne,ai na isa ne” itama ta maida.mata rai kwance kai kace wasa take mata,sai taja plate dinta rahaman ta soma juya abincin tana cewa
“Namiji dai mijin mace hudu ne”
“Is enought….kici abincinki kawai” yace da rahama,sai ya dubi aysha
“bani abinci naci” ya fada yana zubawa aysha ido,shi kadai ya gano bacin rai kwance a fuskarta a bayan murmushin dake kan fuskarta,fushin na meye?,abinda bai taba gani tattare da ita ba?,miqewa rahama tayi tabar abincin nata ta sauka daga wajen ta fuce daga falon ma baki daya,tsit wajen yayi,cikin nutsuwa ta zuba mishi komai ta tura gabanshi sannan ta samu waje ta zauna bayan ta zuba kunun gyada cikin cup wanda anni aka yiwa shi tasha ta rage mata saboda kusan ita da annin sunfison cima daya,haidar da mus’ab ne suka miqe a tare suka bar gun cin abincin suma
“Wannan sanya idon na rahama ya soma yawa,ya kamata yah khalipha ya dauki.mataki fa” haidar ya fada cikin jin haushi
“Idont know why suka addabi mutane ma,kowacce ya zauna gidansu ta kasa” mus’ab ya amsa yana jan tsaki.

daga idonta tayi ta dubi amal,sai taga tana satar kallonsu,yau duka sai tayi maganin masu shegen sa ido,sai ta dire cup din hannunta ta janyo plate din dake gaban khaliphan ta amshe cokalin hannunshi ta debo lomar abincin
“Uhummm” ta fada tana gyada kanta,cikin mamaki yake kallonta saita bude mata dukkan idanunta wanda hakan yasa suka sake girma suka fito sosai
“Karbi mana,kacemin dazun kana jin yunwa” ta fada a shagwabe wanda hakan ya taba zuciyarshi sosai,murmushi ya sakar mata idanunshi cikin nata,tana jin nauyinsu sosai a kanta amma ta dake
“Dont bother pls,zanci da kaina,banaso ki wahala” ya furta cikin wani irin salo da ya kusa tarwatsa zuciyar amal wanda ya tilastata barin wajen da hanzari,yayi tasiri mai girma cikin zuciyar aysha daya sanya jikinta yin laushi,sakar masa tayi ganin amal tabar wajen,cikin sauri ya kamo hannunta ya riqe gam cikin nashi
“Baki isa ba saikin qarasa abinda kikayi niyya,kinsan akwai ‘yan sa ido dake shige da fice ko?” Haka dole ya hanata tashi daga wajen duk da taqi yarda ta bashin,saiya ci gaba daci da kanshi jifa jifa idanunshi a kanta,yana mamakin me yakeson sauyashi daga ainihin halayyarsa haka.

Ita ta soma gaba taje ta gaida anni,bata tsaya jiranshi ba ta wuce,hakanan yau takejin haushin amal da rahama gaba daya wanda batabtaba jin hakan ba kamar yau.

Tunda wuri tayi shirin kwanciya saboda tafiyar da yace mata zasuyi gobe wanda batasan ta mece ba,ko cikin gida bata qara shiga ba,kuma dama bata da sha’awar shiga din,don ta tsani kallon qwaqwqwafi da rahaman ke mata,ta dinga binsu da kallo ita da khaliphan kaman wanda ke zaman dadiro,tsako taja saboda tuna hakan da tayi,ya kamata ta yiwa tufkar hanci,koma meye fa khalipha ya biya sadakinta no need a samu wasu mutane da zasu dinga sanya musu idanu,tayi kyau cikin red night gown ta lullube kanta da farin mayafi,saika rantse ba shigar bacci tayi ba sabida yadda kayan sukayi mata kyau,qaramar jakarta ta bude ta zuba kayanta kala biyu da duk wani abu da zata buqata,duk da batasan adadin kwanaki ko kwana nawa zasuyi ba,ta hada komai tsaf,saita ciri tashi jakar mai kyau ta buda kayanshi shima ta zabi kala biyu ta shirya masa komai da komai a ciki,sai data kammala duk wata sabga tata sannan ta dauki system dinta da haidar ya siya musu su biyu shi da ita kala daya ta fito parlour,tana son kallon wani film da ta taba ganin tallanshi ta baiwa haidar ya mata downlod dinsa.

Saman doguwar kujera ta miqe abinta ta dora system din saman cinyarta ta kunnata,saida komai ya daidaita ta lalubo film din ta soma kalla,sosai hankalinta ta tafi kan film din dalili daya sanya bataji takun shigowarsa ba,ya hangi bayanta,saiya wuce bedroom din.

Tsayawa yayi yana kallon kayan data shirya din,komai a tsare daga gani kasan tasan me takeyi,a qa’idarshi bai tafiya da kaya idan tafiya ta sameshi amma wannan karon sai yaji bazai iya ignoring ba,maida jakar yayi ya zuge yana murmushi sannan ya sake dawowa falon.

A hankali ya taka ya tsaya a bayanta hannayenshi harde kamar yadda al’adar tsaiwarshi take,ya zubawa screen din system din ido yana kallon abinda take kallo daya dauke mata hankali haka,murmushi take saki lokaci lokaci saboda yadda film din ya tafi da ita,soyayya ce ake bugata sosai,ta tuna sanda hanan ke bata labarin film din,a sannan kallon shirme takewa hanan din da batawa kai lokaci,wani irin feeling naso da qauna taji yana shiha zuciyarta,yadda jaruman ciki ke tafi da soyayyarsu mai ratsa zuciyar masoya ce.

Miqa tayi tana ware hannayenta gami da fidda murmushi daga fuskarta sanda aka gama wani sin wanda hakan yasa ta dunguri khalipha dake tsaye a bayanta shima yana tayata kallon ba tare data sani ba,da hanzari ta waiwayo suka hada idanu,yadda ta ganshi a tsaye tasan ya jima a wajen,gabanta ya fadi kunya ta kamata,yanzu haka duk yaga yadda take appreciating film din,Allah ya rufa mata asiri ba wani film din banza take kalla ba,waskewa tayi tana tsaida film din tana son rufr system din,hannayensa ya saki yana zagayowa inda take,shi kansa film din yaji yana taba wani sashe na zuciyarsa,zai iya cewa tun wancan lokacin daya shude zuciyarsa ke a rufe,bai taba bada qofa ga wata ba bare yaji me ake ji koya dan dana irin abinda masu soyayya ke dan danawa,hannayensa yasa zai gyara qafafunta dake miqe don ya samu wajen zama,santala santalan qaurinta yabi da kallo wanda,cikin sauri ta tanqwashe qafarta tana dan hade rai,baice komai ba ya sanya hannunshi ya ya dauki system din ya janyo qaramin tebur gabansu ya aje samanta ya dannan play film din yaci gaba dayi,ji take ba zata iya zama su kalli film din tare ba,duk da bana badala bane amma soyayya ciki mai zafi ce akwai kunya,tana jin nauyinsa sosai saboda haka ta miqe da sauri,caraf ya kama tsintsiyar hannunta ya janyota baya wanda hakan yasa ta koma da baya ta zquna ba tare data shirya ba,har zaman datayi yafi na dazu kawo kusanci a tsakaninsu
“Zauna ki kalla abinki,ni tayaki kawai zanyi” ba yadda ta iya saboda yadda ya dabibayeta da idanunsa ta zauna din,tun tana a takure harta dan saki kadan fim din yaci gaba da garawa,ji tayi ba zata iya daurewa ba abun ya mata nauyi da yawa aka,ga zamanshi a gefanta dake qara raurawa zuciyarta,haka kawai zuciyarta taji kamar zata narke,saita rarumi system din ta soma yunqurin kasheta gaba days,a hankali ya dora hannunshi saman nata,dagowa tayi tana kallon qwayar idanunshi karo na farko,wani irin kallo yake binta dashi kamar wanda ke jin bacci,manyan idanunshi nan sun rusuna sun rage girma,wani abu taji yabtsirga mata saita soma yunqurin zame hannunta ta gudu tabar masa system din ma gaba daya amma yaqi bata space din yin hakan
“Kinsan me?” Ya fada cikin sanyi da taushi
“Indai kaga mutum na yawan kallon fina finan soyayya to aure yakeso” idanunta ta zare tana dubanshi,aure kaman yaya?,me yake nufi xai fassarata?
“Yaushe kika soma kalla humairaaa?” Ya kira sunanta da wani irin tune wanda ya qarawa zuciyarta bugu,saita kasa daurewa taci gaba da yunqurin zame hannunta amma duka a banza,tafin hannunshinya saka cikin nata yana murzawa a hankali yana ji cikin jikinsa kamar zai fita da control dinsa amma ya kasa tsaida kanshi,shi kansa baisan me yakeji haka cikin jiki da zuciyarsa ba
“Uhmm…tell me mana”
“Pls ya khalipha…ka sakarmin hannu” ta fada a narke kaman mai shirin sakin kuka,saidai kasalar daya saukar mata ya sanyata fidda sautin cikin wannan yanayin.

Sautin kidan da wayarshi ya dauka shiya dawo dashi,ya zame hannunshi daga nata a hankali ya soma laluben wayar,hakan ya bata damar miqewa ta fice daga falon zuwa dako cikin gudu gudu sauri sauri,binta yayi da kallo ta koma kamar qaramin yaron da aka biyo yakeson ya cimma mamanshi ya buya bayanta,mahmoud ne ke kiransa,sallama yayi bayan ya daga wayar
“Kana ina miscal kusan uku?”
“Da yaushe kenan?”
“Yanzu mana wannan ne kira na hudu dana yi maka fa” cikin mamaki ya daga wayar daga kunnenshi ya kalli screen din,tabbas ga alamun miscal nan ya nuna amma saiya dake
“To nidai banji ba”
“Kacemin kawai kana angonci,tunda ka dawo ba wanda yaji motsinka daga company” kalmar angoncin ita ta sashi sakin sihirtaccen murmushi,yana son yayi nazqri akanta amma surutun mahmoud ya hana,hakanan ya biye mishi suka tattauna maganganun dq zqsu tattauna,daga qarshe ya buqaci ko zai shigo company
“A’ah fa,gobe zanje legos”
“Kayi me a can?”
“Nida humairaaa ne”
“Honeymoon?” Ya tambaya cikin shaqiyanci
“Laifi ne?”
“Ko kadan na wajena,amma legos inaga ta muku kadan fa,ka manta tsohon tuzuru ne kai daya ga ‘yammata kala kala?” Ya fadi cikin tsokana,dariya taso kubce masa ya danne abarsa,shi sam baima kai can inda mahmoud din yakai ba ko kadan a ransa
“Kaga sai da safe”
“A miqamin gaisuwa” bai saurareshi ba ya yanke kiran abinsa yana murmushi,yana juya maganar da sukayi da mahmoud,haka ya dinga juya maganar cikin ransa kamar dai tana so tayi masa tasiri,a nutse ya janyo system din tata zai kashe mata,babban hoton haidar ne aka screen din,cikin shigar qananun kaya,yayi kyau sosai suna diban kaman dashi qwarai fiye da mus’ab,haka kota fannin halayya,saiya tsaya yana duban hoton,tsaki ua danja,sai ya juya bayan system yaga irin ta haidar dince sak,tsaki yadanja wanda baisan dalilinsa ba,kasheta yayi ya hada da charger din ya nufi study room dinshi da ita ya ajeta a can.

Tunda ta shiga dakin take kwance rub da ciki saman gado a side din da yake kaman nata ne nan take kwanciya shi kuma daya side din tun sanda ya tasota daga falo ta dawo ciki,a hankali komai ke dawo mata cikin qwalqwalwarta,wani yanayi da batasan na neye ba yana bin jiki jini da zuciyarta,ta jima a haka kafin ta gyara kwanciyarta ta juyar da fuskarta daya sashen,hoton fuskar khalipha ta soma yi mata yawo,manyan idanunshi masu kyau da haske,kwantancen sajen fuskarshi daya zagaye haba zuwa qasan hancinsa,dogon hancinsa mai dan tudu kadan,pink din labbansa suma masu tudu kadan,cikakken gashin gira daya sake qawata fuskarshi da zara zaran eyelashes,fararen haqora,saita cure waje daya tana jin kunya na kamata,cusa kanta tayi cikin filo tana tuhunar kanta me ya kaita fasalta siffar da namiji idan ba rashin ta ido ba,murmushi ya qwace mata tana sake cusa kanta tsakanin filalluka,ita daya kamar wadda za’a kama.
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button