Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 41

Sponsored Links

41

Qarfe goma na safe suna tsaye harabar farfajiyar gidan,motoci hudu ne kowacce da drivernta suna jiran fitowar boss khalipha,daga ciki aysha ce tsaye zaune gaban anni riqe da kofin kunu mai dumi da qosai wanda tunda safe su atika suka shiga kitchen sukayishi da umarnin annin,ta tsare ayshan tana sha
“Maza ki shanye wannan na haunnunki,ayi tafiya ciki babu komai,zaki biyema wancan mai tsarin da abincin safe sai hantsi ya dubi ludayi” ta fadi tana duban ayshan cikin so qauna da tausayi,tana mata fatan wannan karon sauran matsalarta ta kawo qarshe,tana mata fata yau ta kasance cikin farinciki,ta tabbata batasan inda zasu ba da tuni zuwa yanzu hankalinta na a tashe ne,murmushi ayshan tayi ta dire cup din hannunta wanda ta tilastawa kanta ta shanye din kodom farincikin anni
“Yauwa koke fa” anni ta fada tana jin dadin yadda ta cika cikinta
“Na gode anni” ta fada kanta a qasa,tana qoqarin danne raunin xuciyarta,haka kawai umminta ta fado mata,kulawar data samu wajen anni a iya dan zaman da sukayi da ita bata taba ganin kwatankwacinta ba daga wajen umminta,ta lura sa sauyawar fuskar ayshan,batason ta fuskanci komai ko yanayinta ya sauya tun yanzu

hakan ya sanya tayi nufin bagarar da zancan
“Ayshatu sarkin godiya” murmushi suka saki a tare,sai shuru yadan ratsa falon,cikin haka takun takalman khalipha suka soma ratso falon,a hankali ta daga kai da niyyar satar kallonshi caraf ya kamata,tayi qoqarin dauke idonta daga kanshi amma kamar ya riqeta ne da wani mayen qarfe,yayi wani mugun kyau cikin suits kamar yadda suka zama sune kusan rabi da rabin rabin shigarsa,komai nashi daban yake cikin gayu tsafta da nutsuwa,da qyar ta qwaci ganinta ta dauke kanta.

Related Articles

Gaisawa sukayi da anni ya dora da tambayar lafiyarta,suna tsaka da haka rahama ta shigo parlour din dauke da kofunan tangaran biyu a hannunta qananu
“Ya khalipha ga coffe” ta fada cikin salo tana miqa mishi bayan ta zauna dab da aysha tana sin tantance rigar dake jikin ayshan,ayshan ce ta amsa takai hancinta ta shanshana,saita yamutsa fuska kadan tana dubanshi
“Zaka sha ne?” Tayi tambayar tana dan takure fuska da hancinta,saiya kashe mata idonshi daya sannan ya mata nuni da a’a,hakan ba qaramin dadi ya yiwa aysha ba,saita waiwaya tana duban rahama
“Sorry anty rahama,ya qoshi” ts fada qasa qasa ta yadda anni bata ankare ma da abinda ke faruwan ba,ba qaramin shaqa rahaman tayi ba,uwa uba kiranta anti da ayshan tayi,eh ta girmeta don sa’ar khaliphan ce,amma babu abinda ta tsana a duniya irin a qara mata shekaru ko a bayyana shekarun nata a duniya,mamaki take cikin ranta na yadda ayshan keyi a ayanzu,kishinta fiye dana baya ya cika ranta,bata taba tsammamin yarinyat xata iya canzawa haka lokaci guda ba kuma cikin qanqanin lokaci ba tare data cimma burinta ba.

Anni da khalipha na gaba aysha na baya ita da rahama data shirya wai zasu sauketa a asibiti tana son taga likita,tsaf ta karanci rahaman amma ta qyaleta don tasan meta taka,tunda tasan rahaman bata taba yarda ta fita ba mota ba,kuma koda motar ma ita tafi ganewa tayi driving da kanta,daga valcony anni ta tsaya tana musu Allah ta kiyaye ta koma ciki abinta su kuma sukayo gaba.

Da sauri daya daga cikin yaran ya budewa khalipha bayan daya daga cikin motocin ya shige,aysha ce ta rufa masa baya tana shiga ta rufe qofar bayan ta dage glashin sashen datake wanda shi kadaine a sauke,sun glass din dake hannunta ta manna a fuskarta wanda ya qarawa shigar tata armashi da kwarjini,ya kuma fitar da kyanta qwarai,ta fuske kaman batasan me ake ba,shi kuwa driver ganin khaliphan da aysha sun shigo sai ya tada mota ya soma reverse don fita daga harabar gidan,mamaki fal zuciyar khalipha yake dubanta,tana ji a jikinta yana kallonta amma saita fuske taqi duban sashen da yake

Yadda ta tsume taci magani saiya fito da dan qaramin bakinta wanda ya qara mata kyau sosai,sai yaji hakan datayi ta burgeshi,murmushi yayi a boye yana kada kai,daga jiya zuwa yau duk acting dinta jinsa yake tamkar da gaske take har cikin jikinsa

Baisan me yasa yake yawan jin baqin lamura a kanta ba wanda baida tabbacin meye su,qarar wayarta ita ta sanyata janyo jakarta dake gefe ta bude ta ciro wayar tata,aliya ke kiranta,murmushi ta saki har kumatunta na lotsawa ta latsa cikin farinciki ta kara a kunneta,cikin yanayi na sabo da shaquwa suka soma gaisawa,duk abinda take idanunshi a kanta yana karantar yanayinta,kaf tsayin rayuwarsa bai damu da wata mace ba bare ya tsaya karantarta ba baya ga anninsa,sai yanzu gashi ya dora hankalinsa kacokam kan ayshan,idanunsa ya janye ya lumshesu ganin wayar tasu bata qare bace yana jin sautin muryarta cikin kunnensa gaba ratsa kowacce gaba ta jikinsa
“Ya salam” ya ambata qasa qasa yana jan earpiece dinsa ya cusa a kunnensa dan ya daina jin muryarta ko ya samu sassauci kan yadda tsigar jikinsa ke tashi.

Har suka isa airphort basu gama wayar ba,saida motar ta tsaya sannan sukai sallama da aliys kan zata kirata.

A tsorace take taka matattakalar jirgin,karo na farko a rayuwarta data tana shigowa airphort ma baki daya balle ta doshi jirgi,yana daga gefanta ya lura da tsoron dake tattare da ita,a hankali ya matsa gefanta ya zura hannunshi daga gefan kafadarta ya jinginata da tashi kafadar,juyowa tayi suka hada idanu,saiya mata nuni da qwayar idanunshi da wasu ma’aurata dake gabansu hannunsu cikin na juna,sai ta sako ajiyar zuciya tana shaqar qamshin turarensa da har yau ta rasa wanne iri ne,haka koda wasa bata taba jin mai irin qamshin ba.

Sosai ya matse hannunsa cikin nata sanda jirgin ke shirin tashi,ruf ta rufe idanunta tana karanto addu’ar hawa abin hawa,wanda hakan ya qara mata nutsuwa,saida komai ya daidaita sannan ta sauke numfashi ta bude idanunta a hankali sai cikin na khalipha,girarshi ya daga mata alamar tambaya,saita girgiza kai tana sake maida idanunta ta lumshe.

Qarfe sha daya na safe suka sauka a legos abinka da tafiyar jirgi,wasu motoci ne guda hudu iri daya sak masu dauke da wani tambari da bata lura dana meye ba suke tsaye suna jiran isowarsu,daya daga cikin motocin aka budewa khalipha ya shiga aysha tabi bayansa,daga bisani motar ta gyara tsaiwa ta fice daga airphort din sauran na biye da su,dukka hankalinta nakan titunan da suke wucewa,karon farko data taba barin jihar kano zuwa wata jaha ta daban wadda bata taba zuwa ba,saidai taji sunanta kawai a baki,sosai garin ya burgeta,yanayin weather dinsu irin wadda takesoce,don a sannan suna samun saukar ruwan sama,duk da bai kankama ba amma hakan ya sake qawata yanayin garin da iska mai dadi da sanyi.

Joygate hotel and suites suka sauka wanda ke lateef salami street don yafi kusa da airphort,a harabar hotel din duka sauran suka dakata shi da ita ne kawai suka shiga ciki,executive suite yayi booking dama tun daga gida,shi ya bude qofar yana kan gaba tana binsa a baya har cikin dakin,cikin yan mintina qalilan aka shigo da abinci da sauran abinda mutum zai buqata
“Ki huta nan da two to three hours zan dawo ki shirya kafin nan zamu fita”
“Ohk” ta fada tana gyada kai
“Akwai damuwa?” Ya tambayeta manyan idanunshi a kanta,kai ta kada alamun a’ah sai ya juya ya fice yana ja mata qofar idanunshi a kanta.

Dakin tabi da kallo yayi mata kyau sosai kaman ba cikin hotel ba,gefan gadon ta samu ta zauna tana tunanin me sukazoyi lagos?,har yau bata san dalilin tafiyar tasu ba

Wayarta ta ciro ta kira anni ta sanar mata sun iso,sannan ta duba taga da saura kafin lokacin sallar azahar ya shiga,sai kawai ta kunna tv din dake dakin ta sauya tasha zuwa arewa.

Qarfe daya da rabi na rana tayi sallah,sannan ta bude abincin da aka kawo mata taci,sai daya dan fada mata sannan ta shiga bandakin dakin ta sake wanka ta fito ta shirya cikin wani material mai azabar kyau da tsada mint green cotton ne amma mai dan qarfi,ta nannade gashinta tayi daurin nan da ake a gaban goshi wanda gashinta data yiwa parking ta kama jelarsa ta kitsa ya zama jela daya ya fito ta qasan daurin,sarqa da dan kunne da kuma abin hannun da tayi amfani dasu duka set ne sirara masu ruwan gold,ba qaramin kyau tayi ba fuskarta tayi fresh sosai,gogewar da fatarta ta sakeyi ita kanta yana mata kyau,dai data tsaya gaban mudubi ta tabbatar komai yayi sannan ta koma saman kujerar.

Tana shirin xama akayi knocking qofar,saita fasa zaman ta isa bakin qofar ta murda muqullin ta bude gami da ja baya,khalipha ne ya shigo hannunshi riqe da top din suit dinshi daya hannun kuwa wayoyinsa ne,kana kallonshi ko ba’a gaya maka ba kasan a gajiye yake,da kallo ya bita cikin nutsuwa yake qarewa adonta kallonta,ba qaramin burgeshi adon nata yayi ba,sai yaga kaman canza ta akayi daga fitarsa zuwa dawowarsa,yana son qaryata hakan amma zuciyarsa taqi karba
“Sannu da zuwa” ta fada cikin sanyinta tana mamakin yadda yau ya ware ido yake kallonta kai tsaye
“Yauwa” ya fada yana zama saman kujea gami da cire takalmi da safar qafarshi,tana daga gefe tana wasa da yatsunta saboda yadda kallonshi ya mata nauyi yayin da shi kuma yake ci gaba da satar kallonta,shuru ya ratsa dakin,sai daya rage kayan jikinsa sannan ya tambayeta me suka kawo mata,tashi tayi ta dauko masa ta bude mishi
“Zubamin” yw fada yana kallon lallenta da kamar kullum turashi ake,nan tayi serving dinsa yaci sannan shima ya shiga wanka.

Tana tsaka da kallon maimacin wani indian hausa a tauraruwa t.v ya bude qofar bandakin ya fito lullube da towel a jikinsa,ya daura wani duk da mai yalwa ne amma duka singalalin qafarsa a waje yake,dauke kanta tayi da sauri tana jin wani feeling cikin ranta,ya jima kafin daga bisani qamshin turarensa ya game dakin,wanda ya haifar mata da kasala,ta lumshe idanuwanta tana jin motsinsa cikin dakin,bata bude ba har sai data tabbatar daya gama shiryawa
“Mu wuce ko?” Ya fada yana sanya takalma a qafarsa sabanin wadanda ya cire daxun,sai a sannan ta bude idanunta,yayi kyau cikin dinkin kufta,batasan me yasa idan ya saka manyan kaya ba saiya koma mata kamar wani saraki,cikin mutuwar jiki da kasala ta miqe ta soma nannadawa jikinta laffaya,ta cikin mirrow yake kallonta,duk wani motsi idan tayi shape dinta ne ke fita,irin shape da daidaikun mata Allah ya yiwa baiwa dashi,ajiyar zuciya ya kuma saki can qasa,baisan me yake damunshi ba sam,baisan me yasa baya iya controlling idanunshi ba a kanta

Tare suka jero har zuwa bakin motocin dake fake a wajen,ga mamakinta da kanshi ya bude mata gidan gaba,saita daga kai ta kalleshi suka hada ido,kafeta da ido yayi yana mata nuni da hannunshi kan ta shiga,a hankali ta zura jikinta kafin ya sanya qafafunta ya maida murfin motar ya rufe sannan ya zagaya,sai taga ya shiga sashen driver ga mamakinta ya sanya muqulli ya tada motar da alama da kanshi zaiyu driving,dubanshi take da mamaki saiya waiwayo caraf suka hada ido,girarshi ya dage mata
“Me naci ban baki ba?,karki cinyeni mana wannan kallo haka tun daxun?” Kunya taji saita kauda kai tans yunqurin danne murmushin daya subuce mata,cikin salon kare kai tace
“Da wanne idon kasan ina kallonka,ni me zan kalla” yanq tada motar ya bata amsa
“Abubuwa da yawa mana”
“Kamar?” Ta tambayeshi tana murmushi fuskarta na kallon window din motar ta yadda bazai iya ganin fsukarta ba
“Idan kin isa juyo ki kalleni saina baki amsa” tilas murmushin dake kan fuskarta ya subuce saidai bata yarda sautinsa ya fita ba
“Kidai rage kallona karki je ki soma sona,bayan ni kuma na riga dana siyar” dan dakewa tayi jin abinda yace,saboda ita batayi qorafin yawan kallonta da yakeyi ba shine shi xaiyi mata qorafi,shuru ne yaci gaba da ratsawa a motar,baka jin komai sai tashin qarar ac,da kuma anguwanni da suketa wucewa.

Sun danyi nisa kadan taji yayi gyaran murya
“Ayishah” ya kirata sunanta wanda salon yadda sautin lafuzan ya fita tilas kowace ke ki juyo ki kalleshi,sunan yayi dadi da matuqar tsaruwa a bakinsa,saidai tayi mamakin yadda ya iya kiran sunan kai tsaye duk da sunan anninsa ne
“Duka wani dan adam da kika gani a arayuwarshi daya cimma nasara yana da nashi tarin qalubalen daya taba fuskanta,hakanan babu wani mutum daya a rayuwa da yau zaice bashi da wata damuwa ko matsala koda kuwa ya wadata da komai bai rasa lalura hakane?” Kai ta gyada tana yarda da kowanne lafazi dake fita daga bakinsa
“Hakane” ta furta cikin sanyi gabanta na faduwa,don batasan meye abu na gaba da zai fito daga bakinsa
“Dukkan nasara tana tare da qalubale,hakanan idan kanason cimma nasara saika jajirce kayi tafitar ruwa da duk wani qalubale da zaka fuskanta,ka dauki wannan qalubalen tamkar wani mataki ko tsani ne da zai maka jagora izuwa cimma nasararka”kai ta sake gyadawa tana jiran jin ko xaice wani abu,saidai babu abinda ya sake cewa har suka isa wata anguwa,saiya rage gudun motar tashi ya soma ga garawa cikin layin wanda baida kwalta,unguwar nada kyau dai dai misali,hakanan gine ginenta a tsare suke ba wani cunkuso ko hayaniya mai yawa wanda bata zaci haka ba,ta dauka yadda takeji ana cewa cunkus dakin tsumma ta zaci ko inama haka yake,saidata gama qarewa unguwar kallo har qofar gidan da suka tsaya sannan ta waiwayo ta dubeshi,ashe ita yake kallo shima,bayansa na jingine da sit din da yake zaune,sake kiran sunanta yayi karo na biyu wanda sai dayasa tsigar jikinta zubawa
“duk duniya mahaifiya qwaya tak Allah yake halittarma dan adam saboda muhimmancinta,ina da yaqinin duk wani da zaki samu a rayuwa ba zaki taba samun cikakken kwanciyar hankali nutsuwa da walwala ba matuqar kina tuna alaqar dake tsakaninki da mahaifiyarki,gidan mahaifyarki na kawoki,inaso ki samo soyayyar mahaifiyarki da kanki ba tare da kowa ya shiga tsakani ba….inason inga iya jarumtarki da kuma adadin yawan yanda kike sonta” tuni qwalla ta soma wanke mata fuska,tsoro da fargaba gami da rauni keson shigarta,saidai kalaman da khalipha yaci gaba dayi su suke son tsaida zuciyarta qyam waje guda su bata qwarin gwiwa
“Banason na sake ganin qwalla a fuskarki,aiki zakiyi tuquru saboda ki samawa kanki da zucuyarki salama” ya fada yana miqa mata handkherchief dinsa,amsa tayi sai kawai ta dorashi saman fuskarta ya manne a fuskar yana tsotse sabbin hawayen dake fitowa,yayin da qamshin dake tashi jikin handkherchief din ya dinga sanyaya mata zuciyarta,daga bisani ta zare handkherchief din,daidai lokacin da wasu yara dake sanye da kayan makaranta ke yunqurin shiga gidan da yace ya kawota din
“Basmah” ayshan ta furta tana dubansu,ganinsa yakai inda yaga tana kalla,saiya sauke glass din motar da sauri,cikin muryarshi mai taushi cike da nutsuwa yakirata
“Basmah” waiwayowa tayi tana dubanshi alamun baqunta da rashin sanin fuskarshi,takowa ta dinga yi bakin motar,sanda ta iso gab da window din motar idanunta ya fada kan na aysha,ihu ta saki tana zagayowa bangarenta,itama aysha balle murfin motar tayi da sauri ta fito suka rungume juna
“Anty indo!,wayyo anty indo kece?!,ummi ce tace kizo?” Kai ta kada tana shirin zubda wata qwallar
“Ba ita bace basma tsoron shiga nakeji” riqe hannunta tayi qyam
“Zo muje anty indo ni zan tayaki bawa ummi haquri,tunda kikazo har garinmu zata haqura,dama kinsan gidanmu anty indo?” Waiwayawa tayi ta dubi khalioha suka hada ido dashi,da ido ya bata qwarin gwiwa yana jijjiga mata kai tare dayi mata sign na tayi addu’a,gyada kai tayi ta soma takawa tana bin basmah dake faman jan hannunta tare da zuba mata surutu da tambayoyi kala kala,sai da suka isa bakin qofar gidan ta lura da sauran yaran,duka sun girma,suka zuba mata ido alamin sun ganeta amma ba wanda ya iya cewa komai saida basmah tace
“Anty indonmu ce fa,ku gaisheta” kaman a tsorace suke haka suka gaidata sannan suka bude dan madaidaicin gate din gidan suka saka kai ciko,yayin da khalipha ya fito daga cikin motar ya rufe,ya haye daman booth din motar ya tasa gidan a gaba bayan ya harde hannayensa a qirjinsa yana zaman jiran tsammani.

*mrs muhammad ce*
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button