Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 42

Sponsored Links

42

Ko ina na ‘yar harabar gidan har zuwa cikin gidan fes yake,tasan za’a rina saboda tana da labarin yadda ummin nata keda matuqar tsafta,don har gorin tsaftar tata take mata abun dariya,donsu a wajensu gani suke tamkar wani iyayi ne kawai na naja’atu,ko tana son nuna cewa tafi kowa,ba zata zauna tayi rayuwa yadda tazo ta tars da sauran matan gidan nayi ba.

Ci gaba tayi da binsu har zuwa cikin falon gidan,falo ne mai dan yalwa wanda yake shima tsaf,sai qamshin girki dake fitowa daga kitchen din dake cikin falon
“Ummi!” Basma ta qwala mata kira sanda yaran kowannensun ya nemi wajen zama yana cire takalmansa da kayan makarantar dake jikinsu
“Ban hanaki wannan iskancin ba basma?,shekara goma sha biyar idan baki hankali ba bansan sai yaushe ba” muryar ummin dake kitchen ta ratso falon,sai aysha taso tanemi nutsuwarta ta rasa,tsoro da fargaba suka cikata
“Ummi kinyi baquwa ne fa?”
“Tohm,su zauna ina zuwa”ta fada daga kitchen din
“Ki xauna anty indo” basma ta fada tana nuna mata kujera,murmushin qarfin hali aysha tayi kawai,fiye da rabin hankalinta nakan kitchen din,haka ta dosana ta zauna gefan kujerar tana rarraba ido a falon,kitcheb basma ta shiga ta dauko mata ruwa da lemo,tana tajanta da hira saidai itasam aysha hankalinta ba’a jikinta yake ba.

Shudewar kusan minti goma sannan ta jiyo takun fitowa daga kitchen din,ummince ta bayyana cikin dinkin riga da zani na atamfa,kanta daure da dankwalin kayan wanda sokashi kawai tayi,miqewa tsaye zumbur aysha tayi idanunta akan ummin,zuciyarta kamar zata fito saboda tsabar bugawar da take
“Basma ina…..” Maganar ummin ta maqale sakamakon hada idanu da sukayi da aysha,kallon kallo sukayi na tsahon mintina biyu,tuni hawaye ya cika idanun aysha,bata isa ta tsaidasu ba a irin wannan yanayin saboda haka ta barsu suka soma zuba,juyawa ummin tayi zata koma kitchen,cikin muryar kuka rauni da kuma karyewar zuciya ayshan ta soma magana kuka na rirriqe wasu kalmomin nata
“Karki koma don girman Allah ummi,karki sake juyamin baya ummi,ki tausayamin ki dubi ‘yarki,ina sonki ummi bani da kamarki duk duniya,ina da buqatarki,inason in rayu dake,ina buqatar kulawar uwa,inason inji duminta a jikina kamar yadda kowanne yaro kejin haka” bata waiwayo ba sai taci gaba da takawa zata wuce kitchen din,da gudu aysha ta zube jakar hannunta ta bi bayantq,kafin takai ga shigewa kitchen din aysha ta cafki hannunta ta baya ta riqe gam,saita sulale ta duqa kan gwiwarta
“idan kika barni wa kika barwa ni ummi?”
“Ummi me anty indo tayi miki ke wai haka da bakya sonta,kome tayi miki ummi ta dade fa tana baki haquri yaci ki haqura,ki kalla fa kiga irin kukan da take…”
“Rufemin baki basma,uban ya baki damar sanya bakinki kan wannan maganar,har yaushe aka haifeki da kika isa saka bakinki!” Ummin ta fada cikin wata murya dake cike da fushi cakude da rauni daga boye a can qasanta
“Idan kina son salama a rayuwarki ki tashi ki tattara kibar gidan nan,bama gidan ba garin gaba daya nakeso ki bari” ta fadi still har yanzu ayshan na bayanta bata bari taga fuskarta ba,ta sabule hannunta ta shige kitchen din gami da rufe kanta a ciki.

Kuka sosai aysha ta saki har yana fidda sauti sosai ta duqe a wajen
“Don Allah ummi don Allah” shine abinda take iya fadi kenan,cikin bacin rai basma ta tako inda ayshan take tana qoqarin dagota
“Yi haquri anty indo ki tashi,kiyi tafiyarki anty indo tunda har bata sonki karki sake nemanta,tashi ki tafi Allah yaga zuciyarki” da sauri ummi data hada kanta da qofar wanda ita bata fito ba ita bata koma ciki ba ta daga kanta,cikin hanzari ta bude qofar kitchen din ta isa gabansu,hannun basma ta fincika sannan ta zabga mata mari,janta tayi har zuwa dakinsu ta turata ciki ta rufesu ita da basman baki daya,kasa tashi aysha tayi kuka take bilhaqqi,ta kusa a qalla minti goma sannan ta iya miqewa da qyar tana jin jiri na daukarta ta lalubi hanyar fita.

Tunda ya kafawa gidan ido bai dauke idanunshi ba,cikin jikinsa yake jin akwai matsala,da hanzari ya duro daga saman motar sanda ta fito daga gidan ya nufeta,kama hannayenta yayi jin yadda jikinta ke rawa sai ya hadata da qirjinsa ya lullubeta da dukka hannayensa yanajin yadda take nishin kuka bugun zuciyarta na sake yawa,a qalla minti biyar sukayi a haka sannan yaci gaba da takawa da ita a hankali zuwa bakin motar,gidan baya ya bude ya sakata shima ya shiga,har a sannan kuka take sosai,gorar ruwa mai sanyi ya dauko da handkherchief sannan ya sake komawa bayan gab da ita ya zauna yana fuskantarta yana kallon yadda takr kuka kaman babu gobe,ranshi ya soma baci,tausayinta ya sake ninka nada cikin ranshi,ko ba’a gaya masa ba yasan amsar data biyo baya,tsahon shekaru har yau bata haqura ba?,tsahon wannan zamanin har yau jiya iyau?
“La’ilaha ilallah,Allahumma la sahla illa ma ja’altahu sahla,wa’anta taj’alil hazna iza shi’ita sahla” ya dinga fada cikin taushin murya da sanyi,a hankali itama ta kama suka dinga maimaitawa tare,sannu sannu kukan nata ya ragu,hawayen ya soma daukewa,sai ya bude gorar ruwan ya miqa mata,bata musa ba ta karba tasha,saidai ba wani abu dataji ya ragu na quncin da take ji,ta kusa minti goma tana zuqar ruwan da kadan da kadan,don da qyar yake wuce mata,daga bisani ta miqa masa robar,yasa hannu zai amsa yaji alamun jikinta ya dauki dumi,goshinta ya dafa dai yaji jijiyoyin kanta suna harbawa,hakan kan ya dauki zafi
“Zazzabi kike ji?” Ya tambayeta cikin tausayawa
“Kaina…ke ciwo”
“Ya salam” ya fada yana qarasa hade gap din dake tsakaninsu,wanda hakan ya bata damar jingina sosai da kafadarshi.

Wayarshi ya ciro cikin aljihun wandonsa ya kira wata lamba,ba’a wuce minti goma ba wani matashi ya iso,cikin wani yare da aysha ke kyautata zaton yarbanci ne sukayi magana da khalipha cikin girmamawa,ya shiga ya tads motar suka bar unguwar.

Lokaci lokaci yakan dora hannunshi saman goshinta yaji ya dumi jikinta yake,jin zazzabin na sake hawa yayi masa magana ya juya dasu xuwa asibiti,kafin ko suje asibitin har ta soma rawar dari.

Aminity aka basu bayan ‘yan gwaje gwaje da likitan ya sanya aka yi mata aka sanya mata qarin ruwa sannan ya buqaci ganin khalipha,cikin murmushi likitan ya yiwa khalipha barka da zuwa sannan sukayi musabaha da juna
“Madam na cikin damuwa qwarai,gaskiya tana buqatar kulawa,tana buqatar abinda zai kwantar mata da hankali ya debe mata kewa….yanzu zamu dan riqeta haka zuwa ko nan da gobe ne idan muka ga yanayin jikin nata zaku iya tafiyama a yau”jinjina kai khalipha yayi sannan ya yiwa likitan godiya ya fita daga office din.

A hankali ya tura qofar dakin idanunsa akanta da take kwance saman gadon barin hannun damanta wanda hakan shi yasa fuskarta ke fuskantar bakin qofa,bacci take sosai wanda hakan baya rasa nasaba da ruwa da alluran dake cikin ruwan dake shiga jikinta,kanta babu mayafi sai dankwalin dake daure a kanta wanda shima ya zame ya bayyanar da rabin gashin kanta,har ya qaraso wajen batasan me ake ba,kujera yaja gaban gadon saitin kanta ya zauna.

Tayi wani fayau tayi kyau,haskenta ya sake fitowa sakamakon kukan data sha daya sanya fuskarta ta sake yin jaa,dan qaramin bakinta na tsuke hakanan girarta a tattare take alamun ba dadin baccin take ji ba,tausayinta ne ya dinga ratsashi,ya shiga tunani kan maganganun da likita ya gaya mishi,ta jima a rayuwarta cikin damuwa dole hakan yayi affecting lafiyarta,ya dade zaune gabanta yana tunanin abubuwan daya dace yayi,har sai da lokacin sallar la’asar yayi sannan ya daura alwala ya fita can masallacin daya gani gefan asibitin don bada farali.

Har ya dawo baccin take,sai ya sake komawa gurbin daya tashi ya zauna,yanayin kwanciyarta yaga ya sauya cikin dabara ya gyara mata gami da lullubeta zuwa qugunta,kallonta yaci gaba dayi tausayinta na ratsashi,a hankali ya laluba hannunta dayan wanda ba qarin ruwa ya sanya tafin hannunshi cikin nata,tasowarta tun daga quruciya,irin gwagwarmayar data fuskanta cikin rayuwata har zuwa yau,wani rauni zuciyarshi keson yi,dauko tashi rayuwar a baya yayi ya soma hadata data aysha,sai yaga ta wani fanni rayuwarsu na kamanceceniya,yanayin gwagwarmayar da fadi tashi,qalubale mai tarin yawa,a hankali zucuyarsa yaji tana gaya masa cikin nutsuwa da yanayi mai ratsa jiki,wataqila rayuwarsu tayi kamanceceniya ne saboda sun dace da juna,wataqila Allah ya shigo da kowa cikin rayuwar d’ayanshi saboda dacewar hakan,ba shakka babu wani abu yanzu dazai goge mata dukka wani tabo na rayuwarta idan ba soyayya ba,saidai ta yaya zai sanyata ta soshi?tana buqatar soyayya lallai ba shakka Allah ya aikosu ne cikin rayuwar junansu saboda kowanne nada buqatar dan uwanshi,cikin zaren tunaninsa har baisan sanda ya matse hannunta cikin nashi ba
“Ayshaaahh” ya furta cikin wani irin sanyi.

Tamkar cikin mafarki taji muryar na kiranta,muryar da bazaiyuwu ta mance da itaba tsahon rayuwarta,sai taji kamar umarni yake mata ta bude idonta,a hankali cikin bacci take bude idanun nata,fuskarshi ta soma gani zaune dirshan a gabanta,saita soma zaton cikin mafarki ne,saboda haka ta bude bakinta daya mata nauyi
“Ya khalipha taqi saurarona,taqi ta kalleni,bata sona,ummi bata sona waye zai soni?” Matsowa da fuskarshi yayi gab da tata har suna musayar numfashi,cikin muryar da babu maijin amonta koda mutum na cikin dakin yace da ita
“Ni muhammad khalipha,ni zan soki aysha idan kin yarda” shuru tayi tana tunanin idanu biyu ne ko a farke,yanayin yadda numfashinsa mai cakude da qamshin turarensa ke bugun fuskarta yasa ta tabbatar a farke take,nauyin maganarsa yasa ta lumshe ido kaman wadda ta koma.bacci,saidai ba haka bane,abu biyu ke mata kara kaina,lafuxansa da haduwarta da ummi yau wanda lamarin kecin jiki da zuciyarta,ci gaba yayi da duban fuskarta dayau tayi masa kyau muraran fiye da kowanne lokaci,ya gane ba bacci ta koma ba amma ba aqalla yana jin bari ya bata space sai yaja da baya ya jingina jikinsa da kujerar da yake kai.

Batasan awa nawa ta kwashe a haka ba,itadai taji shigowar likita,bata ankara ba ta ji hannunshi saman kanta yana kiran sunanta,idanunta ta runtse gam,saiya duqa saitin kunnenta
“Taimaka ki tashi likita ya shigo” hannunta ya kama ba yadda ta iya ta miqe ta zauna sosai da taimakonsa,saiyaqi matsawa saidaya gyara mata dankwalinta ya lullubata shi kaman mayafi.

‘Yan tambayoyi likitan yayi mata ya sake gwada ta sannan ya dubi khalipha,cikin harshen yarbanci sukai magana wanda bata ji komai suke cewa ba,daga bisani likitan ya juya ya fita,kujerar tasa ya sake komawa ya matso da ita dab da aysha har qafarshi na gogar tata,yayi qoqarin su hada idanu amma taqi yarda da hakan,baisan me yasa take da matsananciyar kunya irin haka ba
“Yanzu me zakici?” Kai ta kada
“Babu komai”
“Bazaiyiwu ba” ya fada yana danna wayarshi,kira yayi na mintina sannan ya kashe
“Humaira” ya kira sunanta a tausashe,
“Humaira” ya sake kiran sunan nata duka tana jinsa,kasa dagowa tayi ta dubeshi sai amsawa da tayi kawai
“Dubana nakeso kiyi” shi baisan me kusancinsu haka ke haifar mata ba,baisan me take ji idan ya kira sunanta ba,yana shirin sake cewa wani abu akayi knocking qofar ya tashi ya bude ya amshi saqon ya dawo ya zauna inda ya tashi.

Saman cinyarta ya aje ledar da aka kawo,ya fidda duk abinda ke ciki ya shirya sannan yace mata bayan ya debo abincin cikin cokali
“Uhmm,bismilah”
“Na…..”
“Shhhhshh….” Ya fada yana dora yatsanshi akan lebansa
“Banason kice komai just open ur mouth” hakanan ta bude bakinta ya dunga bata abincin a hankali har suka kammala,shi ya taimaka mata tayi alwala tayi sallah sannan yace mata
“Zamu iya komawa gida?” Kai ta gyada don itadinma bason zaman asibitin take ba,cikin mintuna qalilan drivern ya iso,tana rungume jikinshi har suka isa hotel din da suka sauka.

????????????????

Shuru falon saika dauka babu kowa a ciki,dukka yaran baki dayansu jikinsu a sanyaye suke,abincin da suka saba zama suci tare koda yaushe yau ba wanda yaci na kirki,hasalima basma da mai bi mata yusrah har yanzu suna zaune wajen amma babu wanda yaci abincin a cikinsu,tunda take dasu irin hakan bata taba faruwa tsakaninsu ba,tasan kuma bai rasa nasaba da ganin basma ba cikinbwalwala ba ya shafi duka sauran,saboda suna da hadin kai tsakaninsu yaran gaba daya,sharesu tayi itama tanata qoqarin ganin tayi al’amuranta kamar yadda ta saba,saidai kuma hakan taci tura,don itama juya abincin kawai take ba tare data ci komai ba,shurun ne ya isheta sai ta daga kai cikin hade fuska
“Kai abba,hadim ku dauki abincinku kuci”kai suka girgixa a tare
“mun qoshi ummi”
“Ku dauki abincinku kuci nace!” Ta sake maimaita musu cikin tsawa da qaraji,wanda ya sanya babu shiri suka ja kwanon abincin gabansu suka soma kaiwa baki kamar basaso
“Yusra basma,zoki zuba abinci kuci” ta fada tana tsareta da ido,Dole yusra taja itama plate din ta soma ci kamar dole,yayin da basma ta tashi daga falon da gudu ta shige daki tana sakin kuka,ta jima tana tausayin anty indo,tun batasan ciwon kanta ba har zuwa yanzu,da kallo ummi ta bita,cikin zuciyarta takewa inna yelwa Allah ya isa,har zuwa yanzu bata daina ganin illar matar da sharrinta ba har ya zuwa yanzu?,saita danne abinda ke taso mata ta zubawa yarn ido dake cin abinci kamar dole,a haka babansu yayi sallama,dukkaninsu suka miqe suka taryeshi,saidai ba yadda suka saba ba,tunda yaga hakan yasan lallai akwai abinda ya faru,ko kuma ta tuna da ayshan ne kamar yadda aka saba,zama yayi saman kujera bayan yaran sun koma sun zauna ya tambaya yana dubam fuskarsu daya bayan daya
“Me ya faru?” Sai suka soma kallon kallo aka rasa mai bada amsa,yusrah ce tayi qarfin halin cewa
“Anty indo ce tazo gidan nan dazu ita da mijinta” zumbur ummi ta miqe tabar falon,saiya bita da kallo har ta shige dakinsu,sake duban yarab yayi yana sake tambayarsu,yusrah ta kwashe komai ta gaya masa,ya jima yana nazari kafin daga bisani yace
“Shikenan kuci abincinku,kar wanda yasa damuwa a ranshi,zanje naga umminku” ya fadi yana miqewa suka amsa da to abba gaba dayansu.

*************************

Zaune take saman kujerar dake cikin dakin hotel din wadda ke daura da gadon baccinsu,tana sanye cikin kayan bacci masu kyau da kauri kanta yana da mayafi,tana nade saman kujerar idanunka kan t.v da suke hasko wani wasa,saidai kusan fiye da rabin hankalinta ya karkata ne kan tunanin abinda ya faru da ita dazun da safe tsakanina da umminta,shawarar da basma ta bata tana mata yawo cikin qwaqwalwarta,khalipha ne yayi clapping hannunshi gaban fuskarta wanda ya dawo da ita daga tunanin data tafi,yana tsaye a kanta yana dubanta
“Kin saba alqawarinmu,kin manta?” Dan siririn murmushi ya subuce daga lebanta,sam ta mance da maganar daya gaya mata kafin ya shiga wanka,saita maxe kawai,yanayin yadda ta basar din saiya burgeshi,ta tsuke dan bakinta waje guda ba tare data sani bama,agogo ya kalla yaci ace sun kwanta bacci saboda haka ya qarasa ya kashe kayan kallon yana fadin
“Time for sleep” maimakon ta tashi ta hau gado saita gyara zamanta a saman kujerar alamar anan take shirin kwana,dubarta yayi sai baice komai ba yaci gaba da shirin kwanciya barci,sai daya kammala komai zuwa sannan tana zaune idanunta nakan system dinshi daya kunne ya aje a wajen zaiyi aiki,tanata nuno hotunan dake cikinta daya bayan daya,takawa yayi ya kashe qwan dakin ya kunna mara haske,a nutse ya qarasa gaban kujerar ya zauna gab da ita har kafadunsu na gogar juna,ta jishi sarai amma sai taqi nuna hakan,tadanja wani littafi dake gefan system din din bataso ya fuskanci kamar tunani taci gaba dayi,system din yaja gabanshu yana dauke idanunshi daga kanta ya soma aikinsa,wanda galibi na office ne wanda ya kamata ace a matsayinsa na shugaba ya dubasu da kanshi.

Idanunta nakan littafin tana bin pages bayan pages tana dubawa,duk rubutun dake cikin littafin yana dauke da kwanan wata da time kowanne rubutu,duk layi daya data karanta mamaki ne yake kamata,bata fahimtar komai saidai rubutun kamar yana bada labari ne kan wani abu daya faru lokaci zuwa wani lokacin,buron hannunshi ya aje ya jingina da kujerar da yake kai gami da hade hannayenshi waje guda,ya lura da yadda ya shiga rudu kadan da mamaki,zuwa yanxu yana ganin ba wani boye boye tsakaninsu,ya kamata tasan su su wayesu duk da bata taba tambayarshi ba,tamkar ma bata damu ta sani ba
“Wanene khalipha?” Ya furta cikin sanyi yana ci gaba da kafeta da idanunsa,da hanzari ta daga kai suka hada idanu,sai taji tambayar tazo mata a banbarakwai,abinda ta jima tana tambayar kanta da kanta kenan,abinda ta jima tana son sani,saidai koda wasa bata taba gigin tambayarsa ko wani nasa ba,saboda tana ganin a matsayin wadda kamar alfarma akayi mata karanta baikai tsaikon ta tambaya din ba,sake dubanshi tayi wannan karon idanunshi nakan biron hannunshi dake jan wasu layuka saman farar takardar dake gabanshi

“Kowanne dan adam yana tare da nashi qalubalen a rayuwa,karki zaci ko tsammaci ke daya kike fadawa matsala ko kika fada,dukkan tsanani yana tare da sauqi haka ubangiji ya fada cikin qur’aninsa” sai yayi shuru yaba ajiyar numfashi,tunaninsa ya luluqa ya koma can baya wasu shekaru da suka shude.

*_muhammad khalipha_*

“Cikakken sunan mahaifinsa shine muhammad sa’id mai goro,haifaffen garin kano dan kasuwa wanda ya shahara da sana’ar saida goro a fadin qasar nan,kusan ya gaji sana’ar ne daga wajen mahaifinsa,wanda yake da mata biyu,uwargidansa ita ta haifa masa yara maza guda biyar ta shidan autarsu mace anty ruqayya,idris shine babba,hamza,habibu,munzali,sai saminu,matarshi ta biyu har ta koma ga Allah yaronta daya wato mahaifina muhammad sa’id,a sannan dukkansu suna ganin babu wani abu da mutum xai iya xama cikin sana’ar saida goro sai duka suka qita,mahaifinsa shiya karbeta hannun biyu ba tare da rainata ba,hakan ya yiwa kakana dadi saboda dama duk cikin yaran sa’id halinshi daban,sai Allah ya sanya yafi qaunarshi,dalili kenan daya saka ya dinga fuskantar qiyayyar ‘yan ubanci mai zafi,sai ya tashi a kyare a tsangwame,gashi kome za’ayi masa mahaifiyarsa khadijah da ake kiranta kubra bata daga kai kotace wani abu saboda mutum ce mai tsabar haquri,haka rayuwarshi ta kasance a tsakanin ‘yan uwansa,babu wata qauna sai tsabar yan ubanci da nuna banbanci,ruqayya wadda ita ta kasance qanwa gareshi kuma me binsa ita kadai take sonshi,a irin haka Allah ya yiwa mahaifin nasu rasuwa,mahaifin khalipha da innarshi suna gani akayi rabon gadon rashin gaskiya,saidai innarshi bata ce komai ba kamar yadda shima baice ba,suka rungumi abinda aka raba aka basu,sa’id bai zauna ba ya koma kasuwa,wajen abokan arziqi da sukayi zaman lafiya da mahaifinshi masu irin sana’arshi,sanin halayensa na gaskiya da amana,hankali da nutsuwa yasa suka karbeshi yaci gaba da sana’a a qarqashinsu,wato babu maraya sai rago,hakanan babu nakasashshe sai kasashshe,kyau da samartakar sa’id ko daya basu sanya masa girman kai ba ya kama sana’arsa ka’in da na’in,hakan kuwa yayi matuqar taimakawa don nasu raba abincin ci ko suturar sanyawa ba,yayin da a bangaren su hamza kuwa komai ya tsaya cak,rigima ta dinga tashi tsakaninsu,kowa yana ganin shi ya cancanci a baiwa gadonshi dana ‘yan uwanshi ya juya,kowa yaja ya kafe kan ra’ayinsa,tilas aka sake gutsuraws kowa aka miqa masa nasa kason,inda mahaifiyarsu daga qarshe ta karbi nata itama dana ruqayya ‘yarta,saiyw zamana komai nasu ya soma lalacewa saboda hadin kai,kowa ya tasamma cinye dukiyarsa ba tare da yasan ina tayi ba,hakanan suka dinga fada tsakaninsu kamar zasu yaqi junansu,a haka rayuwa taci gaba da garawa kowanne bangare.

Cikin shekarun da suka biyo baya Allah ya sanyawa dukiyar sa’id da innarshi albarka,yayi kudi mai ban mamaki,yasha fada cewa gaskiya da riqon amana sune ginshiqi kuma matakin nasararsa,sai abu na farko tsoron Allah da kuma bin iyaye,kuma haka yake,duk wani dan adam dake neman cimma wata nasara a rayuwarshi to yayi riqo da wadan nan matakan da taimakon ubangiji zaikai inda yasa gaba.

Zuwa sannan dukka yayyenshi sunyi aurensu,saiya zama babu da talauci ta saukar musu,ci da iyalin na neman ya gagaresu,ruqayya da suke ruqo dalilin mutuwar mahaifiyarsu saita soma passing passing daga hannun wannan zuwa na wancan,a nan ne suka soma rabowa wajenshi,kowa ya soma kwantar dakai dayi masa biyayya kamar zasu kwanta mishi,innar sa’id ita ta umarceshi da kada ya fasa taimakawa kowa a cikinsu ko bayan ranta,to shima mai sauqin raine da haquri,saboda haka sai ya zama shine lalurar duka gidajen nan gida biyar,yayin da sukaci gaba da nuna mishi soyayya da qauna ba don Allah ba,ko sau daya bai taba kawo komai a ran shi mara kyau game dasu ba,haka yaci ga ada taimaka musu har Allah ya kawo rasuwar innarshi,abinda bai sani ba shine a bayan idanunshi murna suka dinga yi da faruwar hakan,suna ganin abu mafi sauqi shine su aikashi lahira su cinye gadonshi,tunda a yanzu baida wani wanda zaici gadonshi tunda ba aure gareshi ba.

Zakaran da Allah ya nufa da cara,suna can suna nasu shirin a sanda Allah ya hada soyayyar sa’id da aishatu buzuwa daga niger,Allah shi yakai sa’id garin ta silar kasuwancinsa suka hadu da ita,soyayya suke da juna tuquru da gaske a lokacin da ayshan tuni yayanta kuma mariqinta ya bada ita ga wani dan uwansu,sam tama mance da wannan batun don bashi takeso ba,ba tsoro ta aika sa’id gaban yayan nata ya gabatar da kansa a wajensa,yayi mamakin yadda aysha ta manta da batun da sukayi da ita,amma ya kauda wannan yayi masa bayanin cewa an bayar da ita,aysha ta sakawa ranta sai sa’id yayan nata ya dage sai wanda ya zaba mata,duk da bata taba fito na fitodashi kan lamarin ba amma duk wanda ya santa yana kallonta yasan tana cikin damuwa,abinci na mata wuyar ci,da yaga dai da gaske take saiya amshi neman aurenta da sa’id yake,amma bisa sharadin idan ta tafi dadi ko wuya karya dawo musu da ita,tace ta amince da hakan,saboda dukka wata nagarta da mace ke nema wajwn mijin aure sa’id nada ita,wanda ko kwatan haka bata gani ba daga wajen wanda yayan nata ya zaba mata ba,duk da yake dan uwanta amma tasan yana da raunin nagarta,akan wannan sharadin akayi aurensu,ya daukota daga nijer zuwa nigeria,yayi mata dukkan wani gata,ya riqe anni da kyau cikin qauna da soyayya da kuma kulawa da juna,itama ta riqeshi da irin biyayyar nan da akasan matan aure nada dashi.
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button