Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 43

Sponsored Links

43

Soyayya suke gudanarwa mai kyau da tsafta,ya karbo ruqayya daga hannun ‘yan uwanta ya dawo ma da anni ita,hakan ya yiwa anni da bata da kowa dadi,saitake kallon ruqayya a matsayin ‘yar uwa,suna zamansu lafiya,yayin da daga gefe guda ‘yan uwan sa’id nacin dunduniyarshi duk da cewa shine komai nasu,cinsu,shansu,suturarsu,karatun yaransu,kuka da lafiyarsu da sauransu duk yana wuyanshi,haihuwar farko anni ta haifi muhammad khalipha,nan fa hankulansu suka sake tashi saboda suna ganin sun rasa damarsu,tunda har ya haifi da namiji tasu ta qare,suna ji suna gani suka haqura,suka ci gaba da tatsarshi da tatsar dukiyarshi ta hanyoyi daban daban,yaki halal yaki haram,haihuwa ta biyu anni ta samu mace,ruqayya nata murna ta samu ‘yar uwa amma ana yayeta ta rasu,a haihuwa ta uku ma sai aka sake samun namiji haka ta hudu,sai ata biyar Allah ya kawo hajar…….,har a sannan daga dangin anni ba wanda ya nemeta,ita kuwa kullum zancansu na cikin bakinta,saidai tasan bata isa ta matsa kusa da inda suke ba saboda sun mata sharadi tun farko.

Dukkan wani qauna tattali da soyayya tamu tana kan hajar mu duka baki dayanmu,kasancewarta auta kuma mace a cikinmu,hatta da anni na qaunar hajar,yarinyar hallayyarta daban take,tana da haquri,sanyin hali shuru shuru da rashin surutu tun tana qaramarta,tana da biyayya bata da rashin kunya sam.

Related Articles

Hajar nada shekara goma aka aurar da anty ruqayya,mijinta ma’aikacin gwamnatin tarayya ne,tu a alokaci. Gwamnati na tura ma’aikatanta qarin karatu qasashen waje aka turashi ya dauki ruqayya suka tafi,wata hudu da tafiyarsu babban tashin hankali ya samu iyalin muhammad sa’id mai goro,Allah ya daukeshi sakamakon jinya da yayi wadda batagi ta wata guda ba,tashin hankalin da matarsa da iyalansa suka shiga a sannan bazaiyiwu baki ya musaltashi ba,da qyar aka samu kan iyalin nasa saboda kowa a cikinsu a dimauce yake,ruqayya batasan da wannan ba sam saboda a lokacin wayar tafi da gidanka bata yawaita ba ba’asan number ko layin da za’a sami mijinta a sanar masa ba.

Ba yadda bawa ya iya da hukuncin Allah,haka daga bisani suka haqura suka dauki dangana.

Kwana uku kacal ‘yan uwan alhj sa’id suka soma zirya kan dukiyarsa da abinda ya bari,yau suce a bada muqullin kaza,gobe suce meye password na safe dinshi,jibi suce a bada muqullin mota,gata suce ina takaddun kaza,a lokacin anni da kallo kawai take binsu,kasancewar har yau batayi normal ba,saboda mutuwar tayi mata duka bana wasa ba,alhj sa’id shine gatanta uwa kuma uba a gareta,ko mutuwar iyayenta bata shiga wannan yanayin ba saboda a sannan bata da wani shekaru duka duka bata wuce shekara uku a duniya ba,haka suka dinga karbar abubuwa d’ai d’ai da d’ai d’ai ba tare data ce musu komai ba,uwa uba bata da kowa bare yace zai tsaya mata,khalipha da yake shine babba a sannan bazai wuce shekara goma sha shida ba,duk da haka yaso tasowa da nuna rashin amincewarsa kan abinda ke faruwa,to amma qarancin shekaru da kuma duk sanda ya doshi anni da maganar maimakon ta bashi hadin kai sai kawai ta saka kuka,tana ganin kamar ta dukiya kawai suke bayan wanda suka rasa yafi dukiyar da duk abinda ke cikinta,hakan yasa ya janye ba mataimaki babu mai qwarara masa gwiwa.

Kafin kace meye wannan sun kwashe duk wata kadara daya mallaka,suka debo kauyoyin bogi da sunan duk dukiyar alhj sa’id banki sun karbe saboda bashin daya cicci kafin barinsa duniya,abinda ya rage musu kawai shine gidan da suke ciki sai motar hawanshi guda biyu,wanda shima easa muqullin akayi,muqullan kuma khalipha ne ya kwashe ya boye sanda suka haukace da nemansu,basu da tsayyaye gakan ya sanya dole suka haqura da qaryar da suka yanka musu,ko a sannan khalipha sai daya qaryatasu ya kuma yi maganganu son ransa saboda yasan duk abinda suka fada qarya be,basu ji kunya ko nauyin idon mahaifiyarsa ba,basuji tausayin maraicinsa ba suka mishi duka suna zqginsa kan bashibda mutunci baisan darajar na gaba dashi ba,yarin dasu kansu sun shaida sanda mahaifinsa nada rai ko kallon banza basa iya masa,bawai don wani abu ba A’ah,duk sharrinka da hassadarka idan kaga iyalan sa’id kasan sun samu tarbiyya fiye da duk wani yaro dake cikin danginsu,basu fara ji a jikinsu ba saida kowa ya watse ya kama gabanshi,aka barsu saisu yasu,suka soma cin abinda tayi saura daga kudin hannunsu da kuma store din gidan,don ko daya alhj sa’id ya gatanta anni bai barinta ta saida komai(kira a garemu mata,kada gata da dadin da miji yake baki yasa ki rungume hannunki kiqi sana’a komai qanqantarta,saboda ba wanda yasan ya rayuwa zata kaya mishi,ko babu talauci akwai mutuwa akwai tsufa).

Zara bata barin dami,sannu a hankali komai nasu ya tasamma qarewa,a nan anni ta shiga tsantsar tashin hankali,yaranta basu saba da wahalar rayuwa ba cikin qaramin lokaci saiga talauci na bayya a jikinsu,makaranta aka korosu ganin anci tearm biyu ba kudin makaranta ba dalilinsa suka koma zaman gida,duk wanda tasan suna huldar arziqi da maigidanta ta nemi taimakonsa amma kowa ya janye hannunshi yaqi tabuka komai,masu ragowar imanin ciki ne zasu taimaka daya biyu suma saisu watsar(irin rayuwar da muke ciki kenan a yanzu,kaci arziqin mutum amma bayan qasa ta rufe idonshi kana kallo iyalinsa su shiga halin ni ‘yasu ba damuwarka bane,bamusan cewa kukan maraya cikin al’umma musifa da bala’i bane a cikinmu,kina ko kana katanga daya da maraya zai iya kwana baici abinci ba amma ke washegari kina da sauran da zaki zubar a bola,bamusan tashin hankalin dake jiran duk mutumin da zai kwana a qoshe maqocinsa ya kwana da yunwa ba koda kuwa ba marayu bane,ta yaya zamu rabu da ganin musifu da bala’i a rayuwarmu d’aya nabin d’aya?,ga cin dukiyar maraya data zama ruwan dare,Allah S W T yana fada cikin qur’aninsa mai girma , *_wadan nan da suke cin dukiyar maraya da zalunci haqiqa suna cin wuta ne a cikinsu,da sanju zasu shiga wutar sa’ira_* ,bama dukiyar maraya ba kawai,hatta da haqqin wani idan kaci ranar gobe qiyama duk abinda kaci din haka zaka zo dashi a kafadarka gaban zatin Allah komai girmansa komai qanqantarsa saika dauko shi,gaban mutane da aljannu qwari da dabbobi,tun daga zamanin annabi adamu har zuwa zamanin annabi muhammadu a gaban idanunsu za’a maka hisabi,Allah da kanshi yace *_haqiqa ubangiji baya zalunci dai dai da qwayar zarra_*
Allah ya shiryemu yasa mu gyara dabi’unmu,ya rabamu da cin haram da cin haqqin daba namu ba Allahumma amin.)

 

Duk wani fadi tashi ba kalar wanda bata runguma saboda farincikin ‘ya’yanta da walwalarsu,Duk wannan abun yasan tana yine saboda farincikinsu,tun quruciya yaro ne mai son iyaye da son faranta musu,shi yace ta daina saida komai nata,zai fita yaga yadda zaiyi ya dinga sama musu abinda zasuci din,sam ta hana shi tace bata amince ba,abata haquraba anni sai data qarar da duk wani abu nata mai daraja.

Abu na gaba daya kunno musu kai shine yawan hauro musu gida da aka shiga yi,ga zaton masu haurowar tarin dukiyar da alhj sa’id ya tafi ya bari tana narke a gidan,wannan abun shi ya tsoratasu,musamman anni da take tsoron mutuncinta dana diyarta hajar,hakan ya sanya suka tattara kayansu sukayi balaguro zuwa gidan babban wansu alhj sa’id din wato saminu,wanda dukansu tare suka rabe dukiyar a tsakaninsu.

Sanda suka je matar gidan damai gidan dukansu basa nan,sanin su waye a wajen masu gidan ya sanya mai aikin ta saukesu sauka mai kyau,saidai tana mamakin suturar dake jikinsu,anan suka zauna sukaci suka sha cimar da suka jima rabonsu da ita.

Kafin wani lokaci hajar ta lafe jikin anni bacci ya dauketa saboda sanyin acn dake busowa,wanda rabonta dashi ta jima,a haka matar gidan damai gidan suka dawo tare da alama taren suka fito,tun shigowar saratu ta soma binsu da kallon banza kamar taga kashi,matar da ada kamar zata yiwa ummi sujjada,shima mai gidan abinda ya soma ce musu shine
“Kai yaya?,ya akayi ne mu kukazo yi” da qyar ya amsa gaisuwarmu,ummi tayi masa bayanin abinda ke tafe damu
“A gaskiya gidana babu wajen zamanku,saidai kuyi haquri aisha kuje koda gidan hamza wataqila shi yana da daki spare,ni yarana ma so nake kowa nayi masa nashi dakin daban,saidai ga wannan kwa sayi abinci don wataqila harda yunwa ma ta saku shirya wannan qaryar” ya fada yana ciro dari biyar ya miqa musu,mus’ab zai karba zuciya ta ciyo khalipha ya tankwabe hannunshi kudin ya fadi qafar alhjin,saiya daga kai ya kalleshi,dama neman qofa yake,nan yahau zage zage da tsine tsine,yana kwashewa khalipha albarka,ya kuma yi musu wuta wuta kan su fice masa daga gida bazai iya zama da mara tarbiyya ba,haka suka debi kayansu ‘ya’yanshi na wajen suna sake turasu da sauran kayansu haka suka bar gidan.

Daga nan gidan qaramin cikinsu suka nufa,hakanan yana dan qananun maganganu ya karbesu
“Yanzu kaji ana tuno da tsohon zance,kawai don an siya maka gida kuma sai ayita bibiyarka” daki daya can falle a bayan gidan ya basu,dole khalipha ke kwana a waje sauran su kwana a ciki.

Kwata kwata zamane da babu dadi ko ‘yanci ko ba’a gayawa masu karatu ba,raini da wulaqanci daga wajen masu gidan da ‘ya’yansu kawai ya isa ya sawa zuciya baqinciki da bacin rai,sam basa qaunarsu,rashin tarbiyya qarara da izgili,har anni basu bari ba,abinda ya dinga qona zuciyar khalipha kenan,sau tari yakan yunqura zai dauki hukuncinsu anni ta dakatar dashi,abinci sai anga dama ake basu shi,ba ruwan mai gidan da sutura man shafawa da sabulun wankinsu,hakan ya qarawa khalipha himma,kullum ta Allah saiya fita,duk aikin halak da yasan zai sama mishi kudin da zasu dan kashe buqatar data taso musu komai qaqancin aikin koda kwasar kashi ce zaiyi ta,suna zaune ne kawai akan lalura,wannan shine gidansu amal,mahaifiyar amal macace mai shegen kissa da kutungwila,tun kan wannan lokacin haka take tun zamanin da duniya keyi dasu tafi kowa shishshige,amma a yanzun yadda take saika rantse da Allah Batasan ummi ba,mus’ab da hajar kuwa basu isa su sake ba dayake sune qanana a sannan,karma hajar taji labari,haka suke zaune sam babu wani dadi takowanne bangare sai haquri kawai,suna rayuwa babu makaranta bare suturar kirki,saidai duk tsiya ba zaka samesu cikin qazanta ba,zaka samesu fes dasu,hakanan annin ta tsaya tsayin daka wajen yi musu karatun addini dana boko iya wanda Allah ya hore mata,a haka suka rufa shekara a gidan da qyar.

Qarshen zamansu a gidan kuwa ya faru ne sanadiyyar dukan hajar da amal tayi,anni ta jata tana mata nasiha tare da nuna mata hajar qanwarta ce,abinka da sun samu daurin gindi sai kawai ta zunduma ihu,yarinya qarama a lokacin da ba zata wuce wasu shekaru ba ta zabgawa anni Allah ya isa,khalipha na wajen zuciya ta ciyoshi,dama dannewa kawai yake ya jima yana jin ciwon abinda sujewa annin,mari ya zabgeta dashi mai shiga jiki,gigitaccen ihu ta saki wanda ya sanya har mahaifiyarta dake sashensu sai data jiyo,a gigice ta fito tana neman amal din,sai kuwa suka ci karo a hanya,ta daga hannunta dake dafe da fuskarta saiga shatin yatsun khalipha kwance a kai rudu rudu,ashariya ta dannan ta finciki hannun amal din suka koma sashen su annin bayan ta gama tambayar amal ba’asin abinda ya faru,dai dai lokacin da annin ta balbaleshi da fada kan marin amal din da yayi kamar zata ari baki
“Wato kuna zaune a gidan ubanta kuna cin arizqinsa shine zaku taru ku kashemin diya ko?,to wallahi bazaiyuwu ba,saidai ku fita ku bar gidan nan matuqar haka zaku dinga yiwa yaraba,kowa ya kasa zama daku mu mun haqura mun zauna daku shine zaku takurawa rayuwarmu”da sauri anni ta bude baki zata bata haquri khalipha ya tsaida annin cikin bacin rai
“banga dalilin da zaki bada haquri ba anni kiyi shuru kawai da bakinki,duk abinda yaran nan sukeyi a gidan nan a idonki mama ake amma kin taba tsawarmusu?”
“Iyyee,ni xaka zaga khalipha,to zageni,zageni…..dama ana fadar halinka ashe da gaskene,to zamanku ya qare a gidan nan wlh” ana cikin haka mai gidan ya dawo,mama na ganinsa ta saki kuka qarya da gaskiya ta soma shirya masa,nan ya hau ya zauna daram,dama mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki,nan ya dinga lailayo ashar kai kace khaliphan ba danshi bane,kai kace bai sanshi ba basu taba hada alaqa dashi ba,bai taba cin wani abu na arziqin mahaifinsa ba,hasalima ba zaka ce gadonsu na wajensu sun lamushe shi ba,a sanda yake wannan tada jijiyar wuyar tuni khalipha ya gana hada musu kayansu tsaf,haka ya dauki wasu aliyu da mus’ab suka dauki wasu suka fice daga gidan,har bakin qofa ya musu rakiya yana jifansu da muggan kalamai kala kala,wadanda suka sanya anni zubda qwalla,yayin da khalipha idanunsa suka kada sukayi jawuri saboda bacin rai,zuciyarshi ce kawai ke tafasa,ji yake kaman ya koma ya rufeshi da duka,saidai yasan koda yaso hakan anni ba zata taba barinsa ba.

A bakin layi anni ta sake yanke shawarar suje gidan habibu,sam bayaso yayi musu da ita,hakan ya sanya baice mata komai ba suka kama hanya a qafa,duk da nisan dake tsakanin gidajen haka suka taka har gidan,tun daga yanayin yadda matar gidan ta tarbesu farkon zuwan gidan nasu sukasan cewa akwai babbar matsala,tunda khalipha yaga yadda yaran gidan ke sangarta yasan tafiyarsu ba zata taba dai dai ba,tunda suka je aka zubesu a falo ba wanda yabinta kansu,har aka gama girkin rana a gabansu yaran suka baje suka ci abinsu ba wanda ya basu koda loma daya,a sannan hajar ta soma yatsina fuska tana radawa anni cewa yunwa takeji,haquri annanin ta bata saboda tasan cewa da zarar khalipha yaji ba zaman lafiya saiya samo ya bata,wata iriyar qauna da shaquwa ce tsakaninsa da ita fiye da sauran ‘yan uwanta,tun tana yi a boye har khalipha ya fuskanci abinda ke faruwa,tunawa yayi duk cikinsu babu wanda aka yiwa iyaka da abincin gidansu a sanda suke dashi idan sunzo,daga babba har yaro idan yaje kanshi tsaye yake wucewa ya zabi kalar abinda yakeso a dafa masa,sai kawai ya nufi kitchen din gidan da kanshi,yarinyar gidan ya taras (zeenart a sannan)da mai aiki tana dafa mata indomie,ya tambayi mai aikin abinci,budar bakin yarinyar sai cewa tayi
“Ba za’a bayar ba makwadaita kwadayayyu” ta fada tana murguda baki,zuciya ta tasowa khalipha yayi yunqurin danneta sabida fadan anni daya fado masa,sai ya zari plate kawai ya bude tukunya ya zubo abincin ya fito,aikuwa ta biyoshi tana ihun barawo,umma ga barawon abinci bawai kuna don batasan khaliphan ba,kawai tsabar rashin tarbiyya ce.

Mai gidan da tunda sukazo akace musu yana barci bayan sunsan tabbas yaji zuwansu shi ya sauko daga samanshi yana tambayar zeenart din ya akayi
“Alhaji zuwa yayi har kitchen ya diba mana abinci” hannu yasa ya wafci abincin yana rufe khaliphan da fada
“Wannan wanne irin sakarcin banza ne da wofi,saboda tsabar rashin tarbiyya har takai ka dauki abinda ba naka ba ba’a baka ba?,to ni wannan iskancin ba’a gidana ba” haquri anni ta soma bashi khalipha na kallo zuciyarsa na tafasa,sai daya mula don kanshi yana hura hanci yasa aka basu daki,abinci ko yace saidai su jira na dare,saboda bacin rai khalipha wuni yayi a waje bai zauna agidan ba,ba laifi wunin da yayi a waje yayi masa rana,don neman kudi yayi sosai,bai dawo ba sai bayan sallar isha’i,ya shigo gidan a matuqar gajiye,cikin tausayawa anni ke dubanshi,qwalla ce ta cika mata idanu amma saota maida saboda tasan yanzun hankalinsa zai tashi,tuna tsantsar gata da suka samu daga mahaifinsu take,amma yau rana daya rayuwa ta juya musu baya cikin qiftawa da bismillah,dubansu yayi daua bayan daya,ya tambayi kowa lafiya ko suka amsa masa da eh,awara ya ciro mai zafi ya miqawa kowa tashi,saidai ta ‘yar lelen tashi hajar daban take,ya qara mata da goba irin manyan nan da yaga tana yawanso,ba qaramin dadi suka jiba kuwa,anni ta dauko wani ragowar abinci cikin kwano ta tura gabanshi
“Ga naka abincin nan kaci mu munci namu,hala ma fushi kake damu tunda ka fita baka dawo ba sai yanzu” murmushin yaqe yayi yana amsawa da annin da a’ah,tunda ya kalli abincin yasan cewa ba qoshi sukayi ba,saboda haka ya juye tashi awarar akai yace kowa ya matso yasa hannu suci abincin yafi albarka.

Da murmushi anni ke dubansu sanda suke cin abincin,ta dago wayon khalipha,zuciyarta cike da tausayinsu da kyakkyawar addu’a da kuma fata da data dinga binshi dashi,ta tabbatar cewa Allah ya bata jarumin d’a,daya tamkar da dubu.
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button