Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 45

Sponsored Links

45

Haka khalipha yaje masallacin unguwar ya fada,aka hadu aka yiwa hajar sallah aka kaita gidanta na gaskiya,sai a sannan anni tayi kuka,irin kukan da tunda suka shiga wannan halin bata taba yarda tayi gaban yaranta ba saboda karta karya musu gwiwa,daya daga cikin aninda ya hadarwa khalipha kenan ciwon kanshi ya tashi,yayi jinya sosai,Allah ya taqaita musu wahala ya warke ba tare da an dauki dogon lokaci ba.

A wannan karon anni bata yarda ta sake zama haka ba,domin tana tsoron faruwar abinda ya faru a baya,sana’a ta kama wanda duka dai bai wuce wankau ba,abinka da bata saba duk,sanda tayin sai hannunta sun kumbura suyita ciwo,amma gobe haka zata sake yin wani,tun suna kumbura har suka daina,daga bisani ta samu aikatau na shara da wanke wanke a wani gida dake bayansu,aikine mai shegen yawa,duk randa taje ta dawo zaiyi wuya bata kwana sa zazzabi ba sabida yawan aikin da take tilliqa,gashi dama tunda hajar ta rasu bata qara lafiya ba,khalipha shi ya hanata zuwa saboda yanayin lafiyarta,haka ta haqura taci gaba da wankau da sauran sana’o’in hannu.

Related Articles

To tunda hajar ta mutu anni batayi cikakkiyar lafiya ba,sannu sannu sai ciwo itama ya kwantar da ita,hankalin khalipha yayi mugun tashi tamkar zai zauce,yana ganin kamar zasu rasa annin ne kamar yadda suka rasa hajar dinsu,suka shiga sintirin asibiti duk da basu dako sisi,hawan jini ne yayi mata mummunan kamu ya haifar mata da matsalar qoda,wanda tana buqatar ayi mata aiki,wanda indai akayi mata akan lokaci shikenan zata warke sumul kamar bata taba yiba,amma matuqar aka jinkirta tofa la shakka ciwon zai girmama ne ya zame mata wani abu na daban.

Shawara ta qarshe da khalipha ya yankewa kanshi shine su saida gidan da suke ciki abiya maqudan kudaden aikin,tunda yana da yaqinin idan ba hakan sukayi ba saidai annin ta mutu ta barsu kamar yadda hajar tayi.

Akan hanyarsa ta zuwa neman dillalan da zasu sayi gidansu ne ya tsinci jakar kudin daddy har ya zama sila na biyan kudin aikin anni,zuwan ibrahim kuwa da ‘yan sanda kawu idris yaji labarin saida gidan ne,so yayi ya qullawa khalipha sharrin da za’a kaishi birsin,shi kuma ya samu damar saida gidan ya kora anni daga ciki.

Bayan samun lafiyar anni khalipha bai fasa saida gidan ba bisa shawarar anni,saboda babban abinda hankalinta ya karkatu akai shine ya samu ya koma karatu,saboda shine gatan duk wani dan adam,Allah ya taimakeshi sukayi masa tayi mai kyau suka karbi kudin,qaramin gida suka sami wanda daki daya ne ciki da falo da bandaki,sai dan mitsitsin tsakar gida suka siya,sai wani dakin a soro,sauran kudin kuwa suka cire wanda zasu fara sana’a dashi sannan ya musu duk wani kai kawon makaranta a ciki,gaba dayansu makarantun gwamnati suka koma,cikin qanqanin lokaci al’amuran suka soma dan daidaita,tunda a qalla suna da abincin da zasuci susha,sun dan sauya suturu ga makaranta sun koma islamiyya da boko,sannan anni na sana’o’inta sosao wanda Allah ya dubi maraicinsu ya soma sawa abun albarka.

Zuwan khalipha makarantar cikin qanqanin lokaci yayi suna yayi fice,sakamakon tarin baiwa da basirar da Allah ya bashi,bugu da qari kuma ya samu background mai kyau don makarantar da yayi a baya duka ba qananun makarantu bane,qoqarinsa har ya wuce tunani,sai aka kaishi ss3 kawai,don sunce da akwai ajin gaba dahaka ma can zasu kaishi.

Bayan ya kammala secondry dinsa yana zaune gida suna qulla yadda zaici gaba da karatunsa katsam saiga kira daga makarantar daya gama,khaliphan yazo ya samu schoolarship,abinda bai taba zata ba ko tsammani koda cikin mafarkinsa,cikin makarantun gwamnati tasa aka bata dalibai bibbiyu masu hazaqa,ba bata lokaci akayi dukkan abinda ya dace khaliphan ya daga yabar qasar.

Koda yaje din sai ya zama dalibi na daban,karatu babu kama hannun yaro,bai zauna acan ba saboda neman kudi daya shiga jikinsa,ya dinga karbar duk aikin daya shigo hannunsa matuqat bai kauce hanya ba yanayi yana turowa annin da kudin,duk da cewa basu da wata matsala a yanzu ta rashin ci sha ko sutura,har wanke wanke khalipha da dafa coffe yayi a gidajen abinci nacan.

Cikin haka wani mai kudi ya saka gasar zane a can qasar,zai gina companynsa yana buqatar a zana masa yadda zai kasance,khalipha nada tarin baiwa ta wannan fannin,kamar wasa ya dawo daga aikin da yake a wani restaurant yaga takardar tallar,bai taba zaton zaici ba ganin yawan mutanen da suka shiga gasar,sai gashi yazo na daya,ya rabauta kuwa da tarin kudade masu dimbin yawa da bai taba mafarkin samunsu ba.

Yana can anni ta hadashi da ruqayya a wayar daya siyawa annin ya aiko mata da ita wadda sai a lokacin Allah yayi dawowarta gida ita da mai gidan nata da yaranta data haifa guda biyu,tayi kuka tayi kuka,tayi baqinciki tayi takaici,tayi Allah wadarao da ‘yan uwanta,tayi kewar sa’id da alhinin mutuwarshi kamar ta hadiyi zuciya itama
“Allah sarki yayana makwafin mahaifina,ina can ina jin dadin rayuwa ashe kai ka jima kwance cikin qasa,ubangiji ya gafarta mala,halinka na gari ya bika,Allah yaci gaba da kulama da iyalinka kar ya barsu su tozarta har abada” taso haduwa da khalipha amma Allah baiyi ba harta koma qasar,saidai lambar waya da sukayi musaya ita dashi suke gaisawa,ta tafi tana kewarsu bayan tayi musu alkhairi mai.yawa,cikin ‘yan uwanta ba wanda ta waiwaya,haka suka di.ga mata zarya suna zaton samun abun duniya daga gareta,saidai yadda tazo da abinta haka ta koma dashi,abinda sukayiwa zuri’ar sa’id bata jin zata iya baiwa kowa komai nata.

Da wannan kudin ne khalipha ya gina rayuwarshi,ya gina mahaifiyarsa,ya gina ‘yan uwanshi,Allah ya albarkacesu ya bude company nashi na kanshi,duk da kamfaninsa bai fasa hulda da wasu kamfanunuwan da yasan sunfi nashi suna ba,bai raina duk wanda ya nemeshi,kafin wani lokaci Allah ya sanyawa dukiyarshi albarka,rayuwarsu tayi kyau,suka manta da duk wata wahala ta rayuwa,fili ya siya mai azabar girma,ya ginawa anni gida na gani a fada,saboda yayi alqawarin dukkan wata wahala data sha a rayuwarta saiya mantar da ita,bazaiyiwu dan adam ya manta sharri ko alkhairi ba,amma tabbas anni ta manta da wata wahala ta rayuwa data sha a baya,haidar da mus’ab kuwa dukkansu saida suka zabi makarantar da sukeso a duk qasar da sukeson yin karatu,ya wadatasu da duk wani abun buqata na rayuwa.

Abu daya ne anni ke fama da khalipha akai danginta na niger,kamar yadda ya gaya mata ne har yau yaqi sakin jiki dasu,duk yadda suke nuna musu qauna da kulawa,yana jin cewa suma suna da tasu gudunmawar da suka bada wajen tabarbarewar rayuwarsu da halin da suka fada,saboda watsar da anni da sukayi da duk lamuranta tunda suka aurar da ita tamkar ba jininsu bace ita,dole daga bisani don babu yadda ya iya ya sauko suke gaisawa da su.

Rahama jikar wannan yayan annin ce,wanda kusan lokaci daya akayi aurensu da anni da babarta,kusan sa’anni suke da khalipha,tunda taga hoton khalipha take mayatar sonshi,saidai shi ko kadan bai taba sonta ba,asali ma cikin dangin nasa baya jin zai iya aurar wata.

Cikin shekara biyu suka zama tamkar basu ba,saika rantse cewa basu taba dadanar zafin talauci ba,Allah ya sanya albarka mai yawa cikin rayuwarsu,ya duba zuciyarsu basu nufin sharri ga kowa,hakanan basu zalunci kowa ba,har lokacin basu manta da hajar ba,shuru shurunta,haqurinta,kawaicinta da yanayin kyawawan dabi’un da take dasu,hakanne ya sanya khalipha ya gina masallatai da.islamiyyu rijiyoyi da borehole borehole duka da sunanta kan Allah yakai mata ladan,hakanan bai manta da mahaifinsa ba,shima yayi gine ginen masallatan juma’a dana kamsusu salawati sadaqatul jariya a gareshi (a nan dan jan hankalin da zanyi ga wadanda Allah yayiwa iyayensu rasuwa kafin suyi arziqi,idan arxiqi yazo musu daga baya suyi qoqarin yin wani abu da Allah zai dinga kaiwa iyayen nasu ladan,koda baka da arziqin gini ko qur’anai ka siya kakai masallaci duk wanda ya karanta Allah zai kai ladan cikin mixanin mamacin,koda qur’ani daya ne,koda rijiya daya ce,koda borehole daya ne,Allah ya jiqan iyayenmu wadanda suka rigamu gidan gaskiya,wadanda ke raye kuma ya qara musu lafiya da nisan kwana mai amfani)

Lokaci guda sunan khalipha ya soma fantsama cikin al’umma,ya soma shuhura tauraruwarsa ta fara haskawa,duk wani mai kudi so yake ya qulla alaqa dashi,duk wani dan kasuwa so yake yayi hurdar kasuwanci dashi,a sannan ne su kawu hamza hankalinsu yadawo kansu,wanda tun bayan rasuwar hajar basu sake ganin gilmawar wani daga cikin iyalin sa’id ba,hakan babu wanda ya nemesu ko ya tambayi ba’asi,ko yabi dalilin shurunsu,sabgar gabansu sukaci gaba dayi,dare daya suka tashi sukaji an fara ambatar sunan khaliphan cikin jaridu gidajen t.v dana redio,nan fa kowa ya kade babbar rigarsa,kowa ya kade tsohon zumunci da suka bunne suna alfahari da dansu ne,suka bazama zuwa gidan khaliphan donsu sabunta kusancin dake tsakaninsu.

Duk wanda yaje gidan a cikinsu saiya jima a qofar gidan yana qarewa gidan kallo cike da mamaki da tambayar kanshi ya akayi khaliphan yayi kudi?,ba shakka ya taka sahun mahaifinsa,babu ko kokwanto arziqi ajininsu yake kenan?,duk cikinsu ba wanda baiyi wannan tunanin ba.

Da fari sanda suka soma zuwa anni qin saurar kowa daga cikinsu tayi,saboda dukkansu ba wanda abinda sukayi musu bai tsaya mata a rai ba,kwantar da kai ban haquri da magiya gami da zirya haka suka dinga yi,daga bisani ita da kanta taga meye riba idan ma ta riqesun?,kafin ita dubu nawa aka yiwa irin haka yau ina suke?,haka ta haqura ta yafe musun.

Duk abin nan da ake khalipha bai qasar yayi tafiya,sanda ya dawo ya taras da abinda ke faruwa ba qaramin tashin hankali yaso yi ba anni ta dakatar dashi,a qarshe ranat bai iya kwana a gidan ba,saboda ganinsu da yayi ba abinda yake tuna masa sai halin da suka jefasu a baya,ba abinda yake tuna masa sai hajar dinsu,ba qaramin daga anni tasha da khalipha ba kafin ya sassauto,duk da haka bai qaunar haduwa dasu kada ma kawu idris yaji labari,domin shi ya sani yanda basu so mahaifinsu ba,basu sosu sanda suna cikin halin ha’ula’i ba,basuso su sanoda duba maraicinsu ba to babu yadda za’ayi a yanzu su sosu fisabilillahi saidon wata manufa.

Ai kuwa ganin sun samu afuwa sai kowa ya soma yunqurin yadda zai samu fada mai girma a wajen,abu na farko da suka soma fafutuka akai shine cusawa khalipha ‘ya’yansu ko Allah zaisa ya kamu da soyayyar wata daga ciki ya aura,duk abinda suke kallon takunsu kawai yake,yasan manufar kowa a cikinsu,abun ya sake baiwa khalipha tsoro da mamaki yadda kowa ya koma yana haba haba dashi mahaifiyarsa da ‘yan uwansa,kowa so yake ace na hannun daman khalipha ne,kowa ‘yarshi yakeso ya bashi,hakanan suma yaran kowacce burinta yace yana sonta,kama daga ‘yammatan danginsu dama wadanda bana danginsu ba,kowacce zalamarta ta fito muraran,abinda ya sake tsoratar dashi kenan,yana tsoron ya dauko wadda zata soshi ba don Allah ba,wadda zata zama silar rabuwar kawunanshi shida ‘yan uwanshi,wadda zata hana ‘yan uwanshi su mori wahalar da suka sha,ta cire duk wata qauna da shaquwa a tsakaninsu,ta cutar masa da mahaifiyarsa shima qarshe ta cutar dashi,dalili kenan daya sanyashi bin hanyar daya bi domin gwajin samun soyayya ta domin Allah.

Qatutuwar ajiyar zuciya khalipha ya sauke yana ci gaba da jan layukan da zuwa yanzu sun qaru kan takardar babu adadi,aysha dake jingine jikin kujera idanunta alumshe hawaye na ratsowa saita rasa abinda zata ce,tsakanin ita dasu khalipha batasan wanda yafi wani fuskantar qalubale matsatsi da wahalar rayuwa ba,batasan wanda yafi wani fuskantar qalubale ba,wacce iriyar rayuwa muke ciki a yanzu?,me yasa zuciyoyinmu babu kyau?,me yasa muka watsar da zumunci muka wulaqanta shi?,muke jin jininmu ahalinmu?,muka fifita mai dukiya akan mara shi?,ashe haka shima ya fuskanci rayuwa?,ashe haka suka sha fama da gwagwarmaya?,zuciyarta karyewa tayi baya ga hawaye sai sautin kukan ya fara fitowa kadan kadan
“Humairahh” ya kira sunanta a tausashe duk da yadda zuciyarsa ke zafi sakamakon tabo wani ciwo da yayi da yake zuciyarsa,saita bude jiqaqqun idanunta akansa ba tare data motsa ba sautin kukanta nason qwacewa,bude mata hannayensa kawai yayi batayi wata wata ba ta isa inda yake ta fada ya maida hannayen nasa ya rufe,kuka sosai ta saki,saiya dinga hadiyar wani abu mai tauri wanda idan ka kalli adam’s apple dinsa dake motsawa sama da qasa zaka fuskanci hakan.

 

*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*ko kuma*
07067124863

[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button