Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 8

Sponsored Links

0?8?

 

Kebantaccen waje ne da yake ganawa da muhimman mutanensa,wanda a siffa yafi kama da lambu.

Related Articles

Waje ne mai kyau daya qawatu da shuke shuke da kujeru irin na kaba,daga gefe guda wani magangarar ruwa akayi mai kama da qorama,zakayi zaton ba cikin companyn yake ba saboda yadda aka tsarashi,kallo daya zaka ma wajen ka fuskanci dan qaramin taro aka gama yi a wajen,saboda yadda grass carfet din wajen ya baci da robobin kayan ci da na sha,khalipha na tsaye cikin mutanen wanda baqi ne daga qasar waje wanda zasuyi hadin gwiwa wajen bude wani kamfani,da sauri daya daga cikin yaranshi wanda ke riqe da wayoyinshi ya matso inda yake tsaye,ya tsaya daga bayanshi kadan cikin girmamawa
“Sir,ana kiranka” hannunshi kawai ya miqa ya amshi wayar yana ci gaba da magana da mr james,vivo dinsa ce yasan mai kiran koda bai duba ba,amma duk da haka saiya duba screen din,khadija ce kamar yadda ya zata,bai samu damar daga wayar ba har sai da suka kammala maganarsu da su mr james sukayi sallama da su suka shiga motocinsu suka fice daga companyn baki daya.

Da sauri daya daga cikin yaran ya sake matsowa da niyyar amsar wayar ya adana ta,daga masa hannu khalipha yayi sanda ya danna kiran khadija sannan yaja baya jikin wasu flowers da aka yiwa ado mai kyau
“Muhammad…ni kake qin dagawa waya?” Abinda ta soma fada kenan,kadan ya cije lips dinsa kana yace
“Afwa….ina wani uzuri ne….mun tashi lafiya?”sai data ja iska kafin ta amsa masa
“Lafiya lau…..ya ake ciki ne wai?,gaskiya jiran fa yayi yawa…har yau kana nufin kudin basu samu ba?” Danne bacin ranshi yayi cikin dakiya yace yana kada kai tare da tabbatarwa kansa itama khadijan ta fadi,bata kai labari ba,bata kuma cinye jarabawar ba
“Su naketa qoqarin hadawa basu samu ba….dubu goma ce kawai ta samu” can qasa yaji ta ja tsaki tana qunquni sannan tace
“Ka kawon dubu goman na toshe wata kafar,da babu gwara babu dadi”
“To shikenan”
“Kar ka wuce qarfe hudu saboda inason in fita”
“To babu damuwa” qit ta kashe wayar,ya cirata daga kunne yana kallonta gami da kada kai,har yau dai jiya iyau,dukkansu kaman tare aka haifesu tsabar kamanceceniyar hali,ya talaka yake wanda baida komai kafin ya samu macen aure a wannan zamanin?,ya talaka mara abun hannunsa yake kafin ya samu soyayyar gaskiya?,da wannan maganar zucin ya miqawa jibril wayar,ya amsa yana miqo masa daya daga cikin kebantattun wayoyin nashi wanda kira yake ta shigowa tun dazun,bai bashi bane ganin wata wayar yake amsawa,karba yayi ya kara a kunnesa kana ya soma takawa yana barin wajen,yana fita ma’aikata suka shigo suka soma kintsa wajen da kawar da duk wata dauda ko shara komai qanqantarta.

?????

Kusan jiran da ya saba yi mata na yau ya wuce na ko yaushe,bai damu sosai ba saboda maganar da yake cikin waya tun dazun ta dauke masa hankali,ya jima tsaye qofar gidan sanye da wani yadi mai sauqin kudi wanda aka yiwa dinkin riga iya gwiwarsa da gajeran hannu,irin yadikan nan ne da ake saidawa kan farashi mai sauqi,duk da haka yadin ya masa kyau saboda baiwar qira da Allah yayi masa,daga takalmin qafarsa har zuwa hularsa masu qaramin kudi ne duka baqaqe,mota uku ce ta masa rakiya saidai yau sun shigo har cikin layin,amma suna tsaye bayanshi qofar wani gida wanda a qalla daga gidan zuwa gidansu khadijan gidaje hudu ne a tsakanisu,waya ya daga ya kirata
“Gani nan” ta fada sannan ta kashe tana jan tsaki
“Kaman wani kudin arziqi ya kawo min,sai kyau iya kyau amma babu abokan tafiya,wannan da kyan da yake da shi da shine kudin shi kuma mummuna da da sauqi,kyau ba kudi ai wahala ce tunda ba dashi zaku rayu ba,ba kuma kyan zaka loqa a goshi kayi yawo da shi ba” ta fadi ita kadai tana mita sanda take gyara yafen mayafinta.

Babu wata cikakkar fara’a a fuskarta haka ta iso
“Mun yini lafiya”
“Lafiya lau ya mutanen gidan”
“Suna lafiya…..” Ta amsa ciki ciki
“Ina saqon?” Ta buqata kai tsaye saboda tana tantamar idan ka ya kawo din
“Gasu nan” ya fada hannayensa na harde a qirjinsa ba tare da ya motsa ba yana karantar yanayinta lamarin na sake bashi tsoro da mamaki,sai ya cire hannunsa daya ya saka cikin aljihun wandonshi,ganin haka ya sanyata tadan saki ranta sannan tace
“Ok….mu shiga daga ciki mana” ta fada tana duban qofar gidan sannan ta maido idanunta kanshi,kafadunsa ya daga duka biyun yana ci gaba da qoqarin zaro kudin,ba tare daya dubeta ba yace
“Ba sai na shiga ba,abinda kika fi buqata na kawo miki kawai muyi sallama na wuce” bata fahimci komai ba haka bata ce komai ba,saboda hankalinta dukka yana kan kudin daya ciro a aljihunsa,wanda kai tsaye bata ce ga adadinsu ba,bandir bandir ne sababbi kar a miqe na ‘yan dubu dubu guda biyar,sai ‘yan dari biyar biyar kuma daban,wadan can ya maida aljihunsa ya irga ‘yan dari biyar biyar din dubu goma ya miqa mata yana kallonta
“Lissafa kiga sun kai?” Amshewa tayi,cike da zumudi qasan ranta tare da fatan samun qari ta lissafa cikin qwarewa sannan tace
“Sun cika” sai ya kada kai ya sake ciro wadancan bandiran yana dubanta yace
“Nawa kika ce kina buqata a baya?” Farrrr tayi da ido dadi na ratsata,addu’arta ta karbu cikin zumudin daya kasa boyuwa tace
“40k kawai nake buqata,ina zaton zata isheni komai da komai” sai ya miqa mata dukkan kudaden hannun nasa yace
“Zaki iya gane nawa ne nan ko?” Cikin zumudi bakinta a washe tace
“Yes,duk bandir daya dubu dari ce,duka wannan five hundred thousand kenan”kai ya gyada hannayensa soke cikin aljihunsa,ya dan shaqi iska sannan yace
“ki riqe duka na baki” idanunta ta waro baki daya tana jujjiya kudin cikin rudewa tace
“Kai muhammad please da gaske kake?,dama ka samu kudin kake ta min wasa da hankali haka,oh my god sweetheart na gode na gode,dama ni na sani ba zaka barni naji kunya ba,dama ashe wasa kake min”
“Eh….gwadaki nake…..kuma kinyi failing….baki ci wannan jarabawar ba khadija,kin fadi warwas har abada” sai kuma ta dan saurara daga murnar da take tana dubansa cikin mamakin kalamanshi
“Kamar yaya wacce iriyar jarabawa?”murmushi ya fidda mai kyau wanda ya sake fitar da kyan surarshi,sai taga yau taga yafi kullum yi mata kyau,ya zaro wayarsa yana dannawa wadda khadijan ta bita da kallo,idan bata manta ba wancan satin ta taba tambayar kudin wayar taji tafi qarfin kanta,don har saurayinta ta tamnaya ya siya mata ita a sannan yace bata da hankali,ashe ba qananun kudi ta baro masa ba, cikin burgewa take bin wayar da ido,idanunsa na kan screen din wayar yace
“Kudi kike so khadija bani ba,kudi sunfi miki soyayyata,sune gaba da komao a wajenki….gasu nan na baki su a madadina…as from today ki saka a ranki baki taba sanin wani mai suna muhammad ba a rayuwarki ko mai kama da shi,kisawa ranki kamar a mafarki alaqarmu ta taba wanzuwa…..” Ya qarashe maganar yana kashe wayar tare da maidata aljihunsa fuskarsa qunshe da murmushi wanda take cakude da mamaki,haushi al’ajabi da takaicin halayyar ‘yammatan yau,yayin data saki baki kawai tana binsa da kallo saboda lissafinta dake neman dagulewa lokaci guda.

Kunya da tsoron rasashi a sanda ta fahimci wayeshi suka dabaibayeta,tsoron subucewarsa daga hannunta a sanda ta gane cewa type dinta ne shi suka cikata,cikin qoqarin kare kai ta bude baki da niyyar bawa kanta kariya,saidai isowar motocinsa wajen yasa ta kasa furta komai,a gabanta ilyas daya daga cikin yaranshi ya bude masa bayan motar ya shige ba tare da ya sake koda waiwayarta ba,tana kallo suka janye motocin suka fice daga layin suka barta tsaye riqe da rafas din kudi.

Har suka bace daga layin tana tsaye tana bin kyawawan baqaqen motocin da kallo mamaki ya daskarar da ita,da gaske wannan shine ainihin muhammad ba wanda ta sani ba?,shin mafarki take ko gixo idanunta ke mata,saita maida idanunta kan kudin tana jujjuyasu tare da qare musu kallo,qwaqwalwarta a daure take tamau,ta rasa me zata aiwatar,takai hancinta ta shanshanasu,wani irin lallausan qamshi suke fitarwa irin mai kwantar da zuciya,take nadama da dana sani suka lullubeta,ya akayi ta kasa boye zalamarta?,ya akayi ta kasa gane cewa muhammad ba qaramin mutum bane?,iya motoci kawai data gani na biye da shi da kyautar daya mata a yanzu sun isa bata amsar cewa shi din wani ne,shi din isashshe ne,sam bata jin zata iya haqura da shi,asarace da ba zata iya jurewa ba,samun irinsu muhammad a wannan zamanin tamkar gudun yada qanin wani ne ga ‘ya mace,mai rabo ke samu,zata san yadda zata lallabashi ta dawo da shi cikin rayuwarta,tabbas sai ya zama mallakinta cikon burin rayuwarta kenan,jiki a salube ta juya ta shige gidan tana gyara riqon kudin a hannunta zuciyarta cike da zulumi da fargabar kada ta rasa muhammad daga rayuwarta.

 

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*

*DAURIN BOYE*

 

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button