Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 9

Sponsored Links

09

 

A gaggauce ta tsame hannunta daga cikin flour din da take kwabawa ta dauraye hannunta ta goge jikin towel sannan ta fita a kitchen din don amsa kiran da mommy sa’adah keta qwala mataba tare da tayi la’akari da aikin data sanyata take yi ba

Related Articles

Cikin bedroom dinta ta taddata,tana zaune gefan gado,daga daura da ita kayan turarukan wuta ne lodi guda da alama lissafinsu takeyi,yar lelen nata kuma na gaban madubi tana ta shafe shafe da qalqale qalqale,saboda yau fita ce ta musamman zatayi,dinner ake na wata cikin qawayenta na makaranta da take aure,qawaye ne irinta ‘yan ji da kai da daukar duniya da fadi,su kansu kayan da zata sanya a ranar order dinsu aka yi mata bayan an musu dinki na musamman,ba’a maganar jaka da takalmin da zata sanyawa qafafunta na kudade masu yawa.

“Mommy gani” aysha ta furta tana rusunawa gefan mommyn,wayarta ta aje sannan ta dubeta
“Saura me da me ki kammala ne?,qarfe shida na yamma fa zasu soma taron,kuma nasan tana can tana jira”
“Mommy na gama komai da komai,doghnout din ne naga kamar bazai isa ba shine zan dan qara yawanshi”
“Zaikai kamar nan da minti nawa?” Ta tambayeta bayan ta kalli agogo
“Awa daya ko minti hamsin”
“To kiyi sauri ki gama din,saboda ke zan aika ki kai matan”
“To mommy” ta fadi tana miqewa tare da qoqarin ficewa daga dakin
“Idan kin gama ki debi komai kimin packaging,ki hada masa dambun kazar nan da kika ma daddy last week,yau nake xaton hamid zai dawo gobe zai shigo waje na” cewar asma’u dake goga jambaki kan lebanta,wanda ta bada umarni ne kawai ba tare data waiwayo ta dubi wadda ta bawa umarnin ba
“Toh” shine abinda aysha ta fada tana ficewa daga dakin cikin ranta tana fadin autan maza,hamid shine saurayin asma’u data zaba cikin dubban samarin da Allah ya bata a matsayinta na budurwa ‘yar qwalisa wadda har ranta takejin duniya na damawa da ita,me ji da kyau aji ado da gata takowanne fanni,hamid ya yiwa asma´u dari bisa dari,tana jin ya dace da tsarinta ya kuma yi dai dai da ra´ayinta,hamid matashin saurayin dan kasuwa ne maiji da gata da kuma dukiya,mutum ne shi mai shegen son girma,son matsayi da qyamatar mu’amala da duk wani wanda baikaishi arziqi ba,tafiyarsu tazo dai dai da asma’u saboda katarin hali da akayi yazo guda,soyayya ake bugawa sosai,wani irin so asma’u take masa wanda yake baiwa kowa mamaki,irinson da ba’a taba ganinta ta yiwa wani d’a namiji shi ba,saboda ta jima tana jan maza a qasa,tana daga musu kai da hura musu hanci saboda baiwar kyau da Allah ya bata da iya kwalliya,uwa uba gata data samu daga wajen uwa da uba kasancewarta auta a gidansu,saidai tashin farko ta matowa hamid,ya rushe duk wani plan nata ya tafi da zuciyarta,a yanzu haka babu wanda baisan da zaman soyayyarsu ba,haka nan ta tsaidashi a matsayin wanda zata aura,saidai iyaye duka basu shiga ciki ba,saboda tana da plan din sai ta gama degree dinta sannan a soma maganar aurensu,shi dinma hakan ya masa shi yasa komai ke tafiyar musu dai dai,suke kuma gudanar da soyayyarsu hankali kwance.

Sam jinin aysha da hamid zan iya cewa bai hadu bane ko kuma banbancin halayya ya sanya hakan,tsakaninta da shi gaisuwa,sai ko idan yazo ta miqa masa kayan maqulashen da asma’u ke sawa ta hada masa ta kama gabanta,yana da ji da kai girman kai da kuma daga kai da jin shi wani ne,wannan halayyarsa ce a jininsa.

Cikin awa gudan ta kammala komai ciki harda wanka,ta shirya tsaf cikin lace bayan ta nannade jikinta da laffaya wadda ta dace da shigarta,ita ba ma’abociyar son kwalliya bace,hakan ya sanya kaso hamsin na kyawunta ke boyewa idan ba ka mata kyakkyawan kallo ko kyakkyawan sani ba,ita dai barta da qamshi,tana son qamshi,kuma dukkan turaren da take amfani da shi ba mai hayaniya bane,saika matsa kusa da ita zaka dinga jin tashinsa,kuma a hankali,yawanci tafi ta’ammali da turaren kaya haka sai rollon body spray masu kyau da dadi tamkar wata babarbariya.

A parlour ta tadda momy tsaye tana amsa waya,dai dai sanda asma’u ta fito,ba banza ba ta kashe awa guda tana kwalliya,ba qaramin kyau tayi ba,duk wanda ya ganta kuma dole ya sake juyawa ya kalleta,ankon lace din yayi masifar karbarta,uwa uba make up din da tayi
“Hey momy sai na dawo” ta fada tana ficewa cikin hanzari tana kada muqullin mota,itama hannu mommyn ta daga mata cikin dan daga murya take cewa
“Kiyi qoqarin dawowa kafin daddynku ya dawo kinji na gaya miki” daga haka ta maida wayarta taci gaba da yi,hannun kujera aysha ta samu ta zauna idanunta kan film din da ake haskowa a tashar zee world hannayenta rungume a qirjinta tana jiran mommy ta gama wayar ta bata umarnin tafiya,sai data gama din sannan ta dubeta
“Na saka usama ya sanya komai a cikin mota,a motar asma’u zakuje saboda ta fita a tawa,na mata bayanin komai ki gaisheta idan kinje”amsa mata tayi ta miqe ta fice daga falon yayin data bar mommy na zama saman kujera tare da qwalawa daga cikin ‘yan aikinta kira ta kawo mata drinks.

Hajiya laraba qawa ce ta qut da qut ta momy,saidai akwai banbancin halaye tsakaninsu,hajiya laraba macace mai kirki da mutunci qwarai da jan mutane a jiki,faran faran da rashin girman kai duk da arziqin da suke da shi,sanda ta isa da kayan ba qaramin murna ta nuna ba ta bubbuda tana cewa
“Kai ma sha Allah,wannan da gani aikin indo aisha ne ko?” Murmushi aysha tayi cikin jin kunya har fararen haqoranta na bayyana bata ce komai ba
“Sannunki da aiki,lallai hajiya sa’adatu na morar mai girki”
“Yauwa mama” ta amsa mata tana matsa yatsunta
“Gashi dukka su muslima tun shekaran jiya suka gudu gidan bikin suka barni a gidan saini kadai sai ‘yan mazan,maza kuma kinsan ba zama suke ba,gidan babu dadi duk saini daya” ta fada sanda mai aikin mama ke aje mata kayan motsa baki,ruwa kawai ta zuba tasha tana sauraren maman data daga waya tana kiran yaronta,sai data gama wayar take dan jan ayshan da hira,bata da saurin sabo a wasu lokutan amma tayi qoqarin sakewa maman suna dan taba hira.

Sallamar matashin saurayin ce ta katse musu hirar da suke jefi jefi
“Banda abin ahmad kuma saika zauna,kasan amfani za’ayi da kayan,ka hanzarta don Allah ka miqa mata” ta fadi tana miqa masa muqullin mota bayan ta miqe ta nufi dakinta tana cewa
“Bari na baka wadan nan kudin ka kai mata,ni inajin sai wajen gobe zan samu shigowa qafar nan yau ta matsanta min” amsa mata yayi yana gyara zamanshi saman kujerar idanunsa kan aysha wadda ta gaidashi a sanyaye kamar yadda haka yanayinta yake,ya amsa mata yana tambayarta mommy,daga haka falon ya sake daukan shiru har mama ta fito ta sallameshi ya wuce.

Sam hanata tafiya maman tayi har sai data yi sallar isha’i ta kuma tilastata taci abinci,kyautar turare maman tayi mata da agogon hannu mai kyau kafimn su wuce,hannu biyu tasa ta karba tana mata godiya,hakanan aishatu ke burge maman saboda yanayin nutsuwarta da tarbiyyarta.

Suna gab da shiga unguwarsu wayarta ta soma ringing,da mamaki ta cirota daga jakarta tana duba mai kiran,saboda tasan bata da wani mai kiranta a irin wannan lokacin,bama wannan lokacin ba,da wuya ka zauna da ita kaji kira ya shigo wayarta,saboda bata da mai kiran nata bata da wanda ya damu da ita baya ga Aliya a cewarta,idan kaga kiran mommy kona asma’u cikin wayarta to qaruwarsu ce.

Ilai kuwa asma’un ke kiranta,tana shirin sallama saidai bata tsaya ta saurari sallamar ba bare ta amsa ta soma magana,da alamun bacin rai cikin muryarta
“Mommy tace min ta aikeki gidan mommy laraba,ki bar abinda kike ku sameni keda usama a meena event” qit ta kashe wayar daga haka,wayar aysha ta sauke daga kunnenta tana qoqarin maidawa cikin jakarta tace da usama
“Usama meena event center zamu je,kasan wajen?” Dariya ta bashi har ya dan murmusa cikin sautin murmushin nasa yace da ita
“Na sani mana aisha wanne dan kano ne baisan wajen ba….sai irinku kifin rijiya” itama murmusawar tayi,tana ganin meye hadinta da wajen me zata jeyi?,a yadda ma taji Aliya na fadin haduwar wajen tasan ba tsarar shigarta bane
“Amma me zamuyi a wajen?” Usama ya jeho mata tambayar
“Yaya asma’u tace muje,halan daukota zamuyi”
“Amma da motarta ta fita ai,me zamuyi a can”
“Ban sani ba nima usama” ta bashi amsa tana dan dafe kanta tare da maida kanta ga titi,ba ma’abociyar son doguwar magana bace sam,hakan yasa sau tari asma’u kan soketa da kalmar macijin sari ka noqe,taqi yarda har yau cewa a halittarta ne.

Ba wanda ya sake cewa komai har suka isa wajen taron,wajen adana motoci usama yayi parking sannan aysha ta soma kiciniyar kiran asma’u,jifa jifa tana bin wajen da kallo wanda yake da haske saidai ba tarwai ba,amma hakan bazai hanaka ganin yadda hadaddun maxa da mata ke kaikawo a wajen ba cikin ado da qawa.

Kusan sau biyar tana katsewa ba tare da asma’un ta dauka ba,sai ana shidan ta daga,shima kunnuwanta cike da kidan dake tashi daga cikin ainihim rufaffen dakin taron taje tsinto muryar asma’un
“Wai meye ne?” Abinda ta soma cewa kenan
“Muna wajen mun iso” tsaki ta doka
“Bana son qauyanci fa,daga zuwanku sai nabar abinda nake…ku jirani malama” daga haka kashe wayar,itama kashe tata wayar tayi sannan tace
“Ammm…usama tace muyi jiranta”
“To,bari na zaga nima nadan kama ruwa”
“Ba damuwa” ta furta tana bude data din wayarta,cikin qanqanin lokaci ta soma browsing tana duba abubuwa masu amfani dake da alaqa da karatunta.

Jira sukayi na tsahon awa biyu,har a sannan ba asma’u ba dalilinta
“Tayar motar nan kamar tayi faci aishatu,ko zaki fito na sauya wata kafin ta fito?”taji usama na fada saitin window din da take zaune
“Toh ba matsala”ta fadi tana maida wayarta jaka sannan ta bude murfin motar ta fito,idanunta ta sake sanyawa tana qarewa filin kallo,komawa tayi jikin motar ta jingina tana ci gaba da kallon wajen jifa jifa.

Cikin minti goma usama ya gama canza tayar yace ta koma ciki,amma sai tace ya barta anan saboda ta gaji da zaman cikin motar.

A gurguje yake takowa daga bangaren nasa zuwa bangaren anninsa,shigar baqaqen kaya yayi gaba daya har takalminsa hight top sai ratsin ja jifa jifa,agogon hannu yake daurawa hakan yasa sam bai lura da zeenart ba,qiris ya rage suyi gware,da sauri ya ja da baya yana ci gaba da daura agogonsa,yayin da zeenart ke qare masa kallo cike da sha’awa da burgewa,ya mata kyau sosai haka shigarshi ta burgeta matuqa
“ya khalipha badai fita zaka yi ba”murmushi ya saki kadan bayan ya dubeta yana ci gaba da gyara wuyan rigarsa
“Xan dan leqa dinner din wani abokin kasuwanci na”a shagwabe tana dan buga qafa tace
“Kai ya khalipha,amma ka sani already na hada maka dinner yana kan dining ko?”
“Dont mind,bazan jima ba zan dawo”
“Kayi alqawari?” Ta fada tana langabar da kai,murmushi ne ya qwace masa,yaran na bashi mamaki matuqa,wai sun mata baya ne?,ko sani ne basuyi ba saboda qanqantar shekaru?,ko sun sani takewa sukayi
“Nayi” kawai ya fada,binsa tayi suka jera har zuwa bangaren anni.

A parlour suka taddata kamar ko yaushe tana zaune saman kujera sanye da hijabi hannunta riqe da carbi,haka al’adarta take musamman da yake ba’a jima da gama sallar isha’i ba,amal ce zaune gefanta tana shan fruits,idanu suka hada ta sakar masa murmushi,bai iya disgi ba hakan ya sanya ya maida mata ya qarasa gefan anni ya zauna a qasan carfet kamar yadda al’adarsa take idan annin na sama bai zama a sama shima
“Ka fito khalipha”
“Eh anni na fito……ina su haidar ne?”murmushi annin ta saki tana dan tabe baki
“Nan yaci wanka ya fice,yace yaga alama saiya kawomin surukata har gida sannan zaka farka” murmushi ya saki shima yana shafa sumarsa cikin jin kunya,yasan jirwaye annin ke masa me kama da wanka,bai maida amsa ba yace
“Anni zan leqa wajen bikin mus’ab”
“Ikon Allah….lokacin har yayi kenan?”
“Eh wallahi….”
“To Allah ya sanya alkhairi,ka miqa masa saqon taya murnata”
“Zaiji in sha Allah…sai nadawo”
“Allah ya tsare hanya” amsawa yayi da amin sannan ya miqe zai fice,zeenart ce ta rufa masa baya,tsam amal ma ta miqe ta biyosu.

Gab da zasu isa jikin motocin ya jiyo muryar amal na tsaidashi,dakatawa yayi yana dubanta har ta qaraso,bata damu da zeenart dake wajen ba cikin shagwaba tace
“Yaya…amma nace ka kaini shopping kace baka da lokacin fita da dare..kuma….”
“Wannan uzuri ne daya kama dole…later ma fita ko” ya katsi qorafin data soma jerowa
“Yauwa yaya na na gode” ta fada cikin farincikin,tasan cikin ruwan sanyi ta rama abinda zeenart din tayi mata dazu na karbe girkin da ita tayi niyyar yiwa khaliphan.

Har motoci ukun da zasu fitan tare suka bar harabar gidan suna tsaye,sai da suka gama ficewa sannan zeenart taja tsaki tayi gaba zuwa cikin falon cikin gudu gudu sauri sauri,amal ta bita da harara sannan tabi bayanta suka shige ciki.

Ranta a bace ta hau step ta yiwa amarya sallama da niyyar sai gobe,don sam ba yanzu taso barin wajen ba,amma mommy ta katse mata hanzarinta ta kirata kan lallai ta biyo su aysha su dawo gida yanzu yanzu,saboda daddynsu ya dawo yana tambaya ta masa qaryar ta aikesu su duka gidan hajiya laraba.

Cikin takunshi dake nuna baiwar da Allah yayi masa ya hawo mazaunin ango da amaryan don ya shigo a makare,mus’ab din kuma yaqi karbar uzurinsa ya kafe lallai sai ya qaraso nan ya bada uzurinsa wajen amarya.

Sakkowa take a hankali saboda yanayin tsinin takalmin dake qafarta,dab da zasu gota juna idanunsa ya sauka a kanta,yanayin hade ranta abu na farko daya soma jan hankalinsa,tafiyar nutsuwa da adonta,da hanzari ya qarasa wajen ango suka gaisa sannan ya juya yace masa yana zuwa.

Ita kadai ke sakin tsaki jifa jifa saboda komawarta gida da bataso ba,yana biye da ita tare daci gaba da karantarta a haka har suka kusa isa parking space din dake wajen sannan ya qara hanzarinsa har ya cimmata,a bayanta ya tsaya sannan yayi mata sallama,ta dan tsorata hakan yasanya ta waiwayo tana dubanshi,da fari taso gaya masa magana ne saboda yadda ta tsorata,amma tashin farko sai ya mata wani irin kwarjini,kyan fuskarsa ya dakushe tsiwarta,saita sake ajiyar zuciya tana dubanshi tace
“Meye haka malam?,haka kawai ka tsorata mutane” murmushi ya saki cikin sassauta tsare gidansa da ragewa kwarjininsa kaifi
“Kiyi haquri ranki ya dade,banyi zaton zaki tsorata ba”
“Naji…lafiya?”kai ya girgiza
“ba lafiya ba” ido tadan fiddo waje
“Ba lafiya ba kamar yaya?”
“Idan ba zaki damu ba ko zamu matsa daga gefe?”
“Ba buqatar hakan don ni sauri nake,fadi matsalarka”
Cikin nutsuwa ya soma fadi mata sunanshi da abinda ke tafe da shi,kallo ta dinga qare masa tun sanda ya soma maganar har ya gama
“Kai din waye?” Ta furta tana son sanin waye shi din har zuciyarta,shafa kanshi yayi kamar wani mara gaskiya
“Ba kowa bane ni,hasalima qarqashin wani nake,shine ubangidana kuma shi na rako nan wajen” dariya ta saki cikin ranta tana jin haushi da takaici,tana ganin ya gama raina mata wayo,ya kuma fado da ajinta,ta yaya yaron wani zaice yana sonta?,maici a qarqashin wani?,me na sama yaci ballantana na qasa,toko gashin kanshi yake ci ai bata jin zai samu soyayyarta ta sauqi bare yaron wani,abu guda ne zai hanata ci masa mutunci,tsantsar kyau da kwarjinin da yayi mata,sai kawai taja siririn tsaki ta juya ta soma takawa a hankali da niyyar barin wajen

Cike da hanzari da zafin nama ya sake binta,daf da zasu isa inda su aysha ke jiranta ya sake shan gabanta,tsam tayi tana dubansa har ya gama maganarsa,tsiwa takeso ta masa amma ya mata kwarjini,yayi mata tako ina ya hadu,kai tsaye ma zata ce yafi hisham

Kyau kwarjini da cikar zati,namiji ne mai irin kyan da takeso,mai surar da takeso,saidai bai mallaki abinda zai bashi damar shiga jerin masoyanta ba,abu guda tak daya fada yasa taga sam bai dace tayi tarayya da shi ba,wato lafazin uban gidansa ya rako
“Kar ka sake bina pls,ka saurara min” lafazin da aysha ta iya jiyowa sun fito daga bakin asma’u kenan,tana iya hangoshi tar ta cikin hasken,a hankali ta janye idanunta daga kansu tana yunqurin komawa cikin motar ganin asma’un ta doso su tun kafin tazo itama ta sauke mata nata kason,tana matuqar mamakin yadda asma’un keda zarrar tsayawa gaban maza tana musu yadda taga dama ba tare da damuwa da shekaru ko darajar koma waye ba.

Garam ta rufe murfin motar ba tare data dubi usama ko aysha ba tace
“Muje” kai tsaye

Ita daya ta dinga mitar biyotan da akayi aysha na jinta bata ce komai ba,tana ganin kamar ya rage mata aji ne daya biyoya ma,kiran wayar hamid ita ta janye hankalinta har suka je gida suna waya,a cikin mota ita dai ta barta ta wuce ciki.

Kan dining ta samu daddy shi da mommy suna cin abincin dare,a nutse ta qarasa,tana shirin gaida daddy mommy tayi caraf cikin salon data saba amfani da shi koda yaushe tace
“Ina kuka tsaya tun la’asar sai yanxun?” Kanta a qasa tace
“Hajiya ce tace sai munci abinci zamu taho”
“Ina ita husnar?”
“Tana mota” ganin tambayoyinta sun qare yasa ta waiwaye bangaren daddyn ta gaidashi cike da ladabi da girmamawa,shima ya amsa mata cikin kulawa,tana shirin miqewa ta wuce asma’u ta shigo,a shagwabe take qarasowa zuwa wajen
“Ke ba zaki ci abinci ba?”mommy sa’adah ta fada ganin ayshan na niyyar wucewa,ga idanun daddy a wajen
“Na qoshi,naci wajen hajiya”har ta soma takawa daddy ya kira sunanta,sai duka hankalinsu ya koma kansu daddyn duk da magana suka soma yi a tsakaninsu,a ladabce ta dawo ta durqusa
“badai wata matsala ko?” Murmushi ta saki dan kadan,to wacce matsala ita din take da bakin cewa tana da ita?,a yanzu bata ganin wata matsala tattare da rayuwarta idan ta kwatanta da rayuwarta ta baya
“Eh daddy babu”
“Kin tabbatar?” Ya sake jaddadawa don har ga Allah yana qaunar yarinyar yana tausayin rayuwarta,sam bata da marsala tunda har yau duk abu irin na sa’adatu bata taba kawo masa qararta ko qorafi a kanta ba,duk da cewa bata taba yabonta ba,amma hakan ya alamta masa bata da wata matsala,yqsan halin matarsa sarai,da tana da damuwa yarinyar tofa duk sanda suka zauna hira ta dinga sakin qorafin akanta kenan,duk da ba zata fito kai tsaye ta kawo masa qararta ba,haka nan nutsuwarta ta daban ce
“Na tabbatar daddy” ta amsa masa muryarta can qasa idanunta na duban tiles din dake shimfide a qasan falon
“To Allah yayi albarka ya kuma yi jagora”
“Ameen daddy na gode,Allah ya saka da alkhairi”
“Ameen” ya amsa cikin jin dadi,miqewa tayi bayan ya sallameta,asma’u na zabga mata harara a fakaice tana ayyana munafuka cikin zuciyarta,yayin da haushi da takaici ya tuqe mommy sa’adatu,saidai sam ba zaka ce haka ba don ko kan fuskarta bata nuna ba,sai abinci da take diba kadan kadan.

A gajiye take liqis,cikin kasala ta dinga warware lafayar jikinta sannan ta shiga bayan gida ta hada ruwa mai zafi tayi wanka,mai ta shafa ta feshi jikinta da turare sannan ta zira rigar bacci doguwar mai taushi da kauri,bacci kawai take buqata tayi,saidai qarar wayarta ta dakatar da ita,ta qarasa ta cire wayar daga chargy tana duba mai kiran,asma’u ce,ta shafa ta kara a kunnenta
“Fito ki daukomin kayan da nace ki ajemin” ta fada da salon muryar data saba yi mata magana,aje wayar tayi ta zira hijabinta ta fice zuwa kitchen.

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*

*DAURIN BOYE*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

HASKE WRITERS ASSO

(Home of expert and perfect writers)

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button