Garkuwa Hausa NovelHausa Novels

Garkuwa 20

Sponsored Links

GARKUWAR FULANI**MEVYASA? ME YAYI ZAFI SHI BA WUTABA? ME RIBARKU A CIKIN FIDDA LITTAFINA WOJE KU WATSASHI WA DUBBAN MUTANE? ME FA’IDAR HAKAN? NIYARKU KO TUNANIN KI, KADA WASU SUZO SU SAYA NE? A ZATONKI DANKU DAN KU ƁATA MIN RAINE? KO KUNA ZATON ZAKU HANANI SAMUN BINDA ALLAH YA RIGADA YA ƘADDARA YA RUBUTA RABO NANE? Nayi matuƙar mamakin al’ummar Annabi, Ni a zatona a iya hasashena, idan mace dan Allah da Manzonsa da darajar iyayen na kai ƙololuwar makurar roƙonda duk musulmi zai yi min al’farmar abinda na roƙa! Sai dai abin tsoro ashe abin ba haka bane, to wannan abun shine kadai ya bani tsoro, lallai kam tabbas muna akiruzzaman. Ai na sani kuma kuma mutanen kirki waɗanda kuka sai littafina da zuciya ɗaya kun sani dole za’a fitar da littafi. Sabida ba kaina farauba kuma ba kaina ƙarauba. Sabida haka kuyi haƙuri, dan Allah kuyi haƙuri, kuyi haƙuri da abinda wasu daga cikinku keyi. Alhamdulillah tunda na’annabi basa ƙare wa, tunda har gobe saya akeyi, wasu suna ganin gana satan a gabansu, amman sai su kauda ido suzo gareni su biya kuɗinsu a sasu a group ina godiya gareku*

Bayan Allah da Manzonsa da darajar iyayen dana haɗa mutane dasu bani da wani tsumi ko dabarar tsira daga sharrin masu zuciyar da basu san girman Allah da Manzonsa da darajar iyayensu ba. Domin duniya gaba ɗaya tana fama da gubar irin waɗannan. Iya tsaro dai kamar na bankuna, to amman me ana samun masuyin kutse a ciki har suyi sata. Manyan kampanunnuka na duniya ma suna fuskantar ɓarayj yan kutse, hakama ƴan Film suke fama da wannan matsalar, to mu ma rubuta suwaye mu da zamu tsira dasu, Roƙona anan dan Allah da Manzonsa abar maimaita mgnar a cikin groups ɗin GARKUWA. Su masu fitarwa dai na fita haƙƙinsu tunda inai musu posting sau biyu a rana kamar yadda na faɗa, su sukaji suka gani suka fitar, to wannan can musu. Ina da mutanen da nake matuƙar ganin kimarsu da darajar su a SPG shiyasa, bazan tanka musuba.

*Fatan al’khairi VIP groups ƴan dari uku ina al’fahari daku, kun bawa maras ɗa kunya, shiyasa tun forko nace Ni kune VIP na, duk da nasan kuma ɗin a cikinku tabbas akwai masu fiddawar, to amman dai naku baya zama illa kamar na SPG. Ina yinku ɗari bisa ɗari.*

Wlh rubutu yafi sauƙi akan mu’amalat da wasu taƙadiran da yake jarabtan marubuta da mgna dasu, ya ilahi ya mujibadda’awati, kai ina jinjina muku marubuta fama da wasu mutanen, wato da a haɗaka mgn da wasu gwara kawai a baka renon shanu garke guda na wuni ɗaya, domin shi dabba yasan abinda ake kira da makiyayinsa, amman wasu mutanen basu san darajar Allah da Manzonsa ba bare iyayensu. Allah ya kyau. Allah ka haɗamu da mutanen kirki.

*Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan layin 09097853276, ko ki turo dubu ɗaya ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276.*

*Zan ƙara roƙo ba domin irinku kangararruba a a sai dan masoyan Allah da Manzonsa, dan Allah kada ku fitarmin da littafina. In kin san kin sayane dan ki fitar min da littafina to dan Allah da Manzonsa kizo kimin mgn ta pc kice kawai GARKUWA bani kuɗina bazan iya saya ban fitarba, wlh Salim alim zan meda miki kuɗinki in biki da godiya, in kuma baki sayaba zaki saya dan ki fiddane dan Allah kada ki saya. Dan Allah in kin rigada kin saya kuma Please turo ac no ɗinki kawai kadama kiyi mgnar kamai a take zan meda miki kuɗinki in cireki in miki godiya🙏🏻*

 

Lamiɗo da Galadima da Sarkin Shaɗi. Bisa alamu wata mgna mai mahimmanci suke tattaunawa.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da kallon Umaymah cikin kulawa yace.
“Khadijah lale da zuwa Masarautar Joɗa.”
Da sauri Umaymah ta ƙarasa gabansu, cikin ladab ta zauna gabanshi tare da duƙar da kai tace.
“Allah rene Barka da dare”.
Kanshi ya jinjina irin na sarakuna kana yace.
“Barka dai Khadijah kinzo lfy, ya Sarki Aliyu?”.
kakan Haroon kenan wanda ya haifi baban shi.
Cikin girmamawa tace. “Yana lfy yace yana gaidaka”.
Kanshi ya jinjina, kana ya ɗan kalli Jabeer dake danne-danne a wayarshi.
Ya hakimce ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.
Jakadiyarsu kuwa tayi shiru a gefe kusa dashi.
Galadima da Sarkin Shaɗi kuwa, murmushi sukeyi suna kallon Jabeer.

Gyaran murya Lamiɗo yayi kana cikin dattaku yaci gaba da cewa.
“Ina amsawa, ya kika samu jikin ɗan naki?”.
Cikin murmushi ta juyo ta kalli Jabeer kai ta rusunar ganin samfa hankalinshi baya kansu cikin yin ƙasa da murya tace.
“Alhamdulillah na samu jiki ya worke!”.
Galadima ne wanda yake ƙanine ga baban Lamiɗo ya amshi zan da cewa.
“To sai ki sanar mishi batun komawa Rugar Bani, dan ramuwa bisa cika ƙaidar..”.
Shiru yayi bai ƙarisaba jin muryar Jabeer yana cewa.
“Ƙa’idar Allah da Manzonsa ne da zai zama dole sai an cika, ba ƙa’idar wani zalumci da tozarcinba”.
Kanshi ya ɗan tanƙwara a wuyanshi.
Kana ya zamo kaɗan ya zauna gaban Umaymah cikin nuna rauninshi yace.
“Ayyah Umaymah kada kice min inje, Please Umaymah ki fahimci wannan abunfa al’adace ba addini ba, kuma abune da kai tsaye zamu iya ce mishi makaruhi in ma bamu haramtashi ba, ya za’ayi inje in sake tuɓe kayan jikina a gaban duniya wai dan in daki wani. Ni bana so.
Ba dai sune suka kainiba, suka kuma ce a dakeni, to dan me zasu buwayeni da sai munje na rama”.
Haɗe fuska Umaymah tayi cikin kafeshi da ido tace.
“Ni bana iya yiwa iyayena musu. Jabeer tabbas na sani al’adace ba addiniba, amman ka sani duk wani abun da zakaga ya faru a duniya to akwai dalilin faruwarshi, kada kace zaka tsananta bincike tabbas lokacin zai baiya mana dalilin.
Bana son gardama kawai kaje Dan ALLAH”.
Hannunshi yasa ya dafe kanshi,
kana yayi shiru Umaymah ta gama dashi da tace dan Allah, ya sani tabbas da a madadinsa Ayyah ɗin da yace forkon mgnar da ya mata da ya rigata cewa Dan Allah da shike nan yasan zatayi shiru.
Shi kuwa Lamiɗo murmushi yayi tare da kallon Umaymah cikin jin daɗi yace.
“Allah ya miki al’barka”.
Da sauri tace.
“Amin ya Allah”.
Galadima kuwa, murmushi yayi tare da jinjina kai.
Jakadiyarsu ma cikin jin daɗin tasirin mgnar Umaymah akan Jabeer take murmushi sabida ta sani.
Shi mutunne mai kaifi ɗaya, in yace eh tofa eh ɗince inko yace a a to a’ance.
Especially baya son duk wani abu da zaici karo da addininshi.
Kanshi ya jinjina Umaymah alamar shikenan idonshi yayi jazir alamun dole akasashi yin abinda baya so.
Kana ya kalli kakarsa dake murmushi tsuke fuskarsa yayi tare da cewa.
“Gimbiya Aminatu muje ki bani gashin da kikayiwa Lamiɗo”.
Cikin dariya Gimbiya Aminatu tace.
“Iye gashinsama zan baka?”.
Da ƙarfi yace.
“Eh shi zaki bani, ai in dukane kam ya iya zille kanshi ya turani.
Shine dan gashinsa zakice iye”.
Murmushi tayi tare da bin bayanshi,
ganin Lamiɗo na mata alamun taje ta bashin.

Nan sukaci gaba da hira, suna tattauna wasu mahimman al’amuran da sirrine garesu iya su biyar.
Wato Lamiɗo, Galadima, Sarkin Shaɗi, Umaymah, Jakadiyarsu.
Bayan su babu wanda suke yarda da sanin sirrin Jabeer.
A hakanma kuma a suɗinma akwai wani sirrin da babu wanda ya sanshi sai Lamiɗo da Umaymah.

Suna zuwa har falonta suka wuce.
Wani kekyawan akoshi mai masifar kyau ta ɗauko mishi.
Ta ajiye a gabanshi.
Inda yake zaune a ƙasa bisa carpet ya naɗe sawunshi.
fork ɗin dake saman fefeyin ya ɗauka.
Daddageggen gaseshen jan namane wanda yaji wuta ya gasu gashin tukunyar ƙasa yayi tiɓis.
Sai wani irin ƙamshi na musamman yakeyi,

A hankali yake sa Fork ɗin yana yagan tattausan tsokokin yana sawa a baki.
Ita kuma tana zaune gefenshi.
Tafashesshen madaran shanu mai ɗan ɗumi ta miƙa mishi a wata ƴar ƙwarya mai kyau.
Taune naman yayi tare da haɗiyewa kana cikin zuba mata ido yace.
“Dole sai na karɓa da hannun nane? Ki ajiye mana.
Da wanne hannun zan amsa tunda inacin abinci dana daman”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Dole sai ka amsa, bazan baka shi a ƙasa”.
Kanshi ya ɗan rausayar tare da cewa.
“Allah ya nuna min ranar da za’a bar.
Wannan tsare-tsaren shamfi na masarautar Joɗa. Komai da ƙaida da yadda ake yinshi”.
Ita dai miƙa mishi ƙwaryar takeyi dole ya ajiye spoon ɗin yasa hannunshi ya amsa.

Nan suma sukaci gaba da hira.
Sai kusan sha ɗaya Umaymah da Jakadiyarsu suna fito.
A nan Gimbiya Aminatu ta ajiyesu suma saida sukaci gashin nata kafin suka tafi.

Kafin su isa Side ɗinsa dai sha biyun dare tayi.

Haka yasa suna isa suka samu ba kowa a falon.

Sai Haroon da suke jiyo muryar sa, a falon Jabeer.

Cikin nitsuwa ya matso kusa da Umaymah a hankali yace.
“Sai da safe Umaymah kiyi bacci ki huta.”
To tace har ta juya zata tafi sukaji Muryar Haroon yana cewa.
“Abba yazo wurinki zaku gaisa bai samekiba, nace mishi kun tafi wurin Lamiɗo yace, to saida safe ya gaidaki da hanya Hajia Mama ma yanzu ta fita, tace Lamiɗo ya riƙe mata ƙanwa”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“To Allah ya bamu al’khairi saida safen”.
Amin Amin suka ce.
Kana shida Haroon suka wuce Side ɗinsa.

It’s kuma Umaymah da Jakadiyarsu suka wuce.
Side ɗin da kullum in dai Umaymah tazo nan take sauƙa.

Suna shiga suka samu, tuni Hibba tayi bacci, wannane ya basu damar tattauna wasu mahimman sirrukansu.

Nisawa Umaymah tayi bayan ta saurari jawaban Jakadiyarsu Jabeer cikin tsantsar tafasar zuciya da tarin baƙin ciki tace.
“Uhummm suyi dai Ni nan ina dai-dai- da ƙugun ko wanne shege da shegiya,
In sha Allahu zasusha mamaki.
Zasuga yadda Ubangiji ke ikonsa, ban cire raina ƴar uwarta zata sake rayuwar enci da salama, da izinin Ubangiji zataga sakayar waɗanda suka cutar da ita da yaranta a gaban idonta.

Cikin zubda hawaye Jakidaya tace.
“In sha Allah, sai farin ciki ya dawo, a sashinta, inata addu’a a kullum a cikin dukkan sallolina, Allah ya kare ahlinta, ya kuma baiya gsky tayi halinta kowa ya gani”.

Amin Amin Umaymah tace tare da share hawayenta.

Washe gari ranar Alhamis. Ta kama yau kwana shida da faruwar gasar Shaɗi, kana gobene za’a koma dan ramuwa,
A goben kuma zai cika kwana goma da kisan gilla da kafurai ƙabulun Ɓachama sukawa Fulanin Rugar Bani.

Misalin ƙarfe sha biyu na safe.
Fadar Sarkin Nuruddeen Bubayero Joɗa, cike take maƙil da tawagarsa kama daga.
Galadima, Waziri, Wambai, Dan buram, Dan iya, Ɗan isa, Ɗan Kade, Sarkin fada, Sarkin yaƙi, Sarkin Dowaki, Sarkin Gabas, Sarkin Kudu, magayaƙi, Jarma uban doma, Makawa Ɗurɓi, Turaki, Da dai sauran members ɗin masarautar baki ɗayansu, an cika anyi maƙil.
Sallama na tsaye can bakin ƙofar shigowa.
Dogari kuma suna tsaye gefen hagu da daman Lamiɗo.
Suna rike da mafici sunayi mushi fifita, ɗanzagi kuma yana gefe,
Kana wasu fadawan duk suna gefen.
Gyaran murya Lamiɗo yayi tare da gyara zaman shi cikin shugarsa ta sarakuna masu al’farma, a hankali yace.
“To da farko dai fatan duk kowa na lfy”.
Da sauri Ɗanzagi yace.
“Sarki ya gaisu yana yi muku fatan alkhaiy”.
Sai ya kuma juyo ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Godiya suke.”
Kanshi ya ɗan jingina da tattausar kujerarsa da masu son gadonta sunfi a ƙirga, cikin ƙasaita yace.
“Kamar dai yadda muka tattauna, kwanakin baya akan sarkin Garin Shikan,
to yanzu zan zantar da hukunci.
Sarkin aike na bada umarni kaje garin Shikan ka karɓo min sandar sarautar Shikan ka kawo min shi, yau ɗin nan.
Kaje da jagorancin Galadima, da Matawalle da Makawa, sai sarkin yaƙi”.
Da sauri duk suka runsunar da kayu kansu tare da cewa.
“An gama”.
Nan take kuwa suka miƙa suka tafi.

A cikin gida kuwa. Tunda asuba da Jabeer da tawagar ahlinshin suka dawo masallaci.
Kai tsaye ɗakin Umaymah ya nufa, suna biye dashi a baya.
Bisa sallaya suka sameta riƙe da al’ƙurani mai girma tana karatu cikin tsananin nitsuwa.

Ganin hakane duk suka fito falo.
Nan Aunty Juwairiyya taja Ummi suka tafi side ɗin ta da Hibba da ƴar aikinta suka shiga kitchen.

Jalal kuwa shine yaje wurin Ya Jafar, don bashi mgni kamar yadda Jabeer ya umarceshi.

Jamil kuwa waya yakeyi da sabuwar budurwarsa da ya samu.
Wacce yake masifar sonta,
Ko yaushe suna liƙe da juna a waya.

Haroon kuwa a falon Jabeer ya zauna yana kallon lbrin CNN.

Shi kuwa Sheykh Jabeer.
A hankali ya wuce ta gaban Haroon.

Gefen gabas ya fuskanta, inda labulaye sukayiwa wurin ƙawanya.
A hankali yasa hannunshin ya yaye labulen.
Wani ƙofa ya buɗe a .
Sai ga wani ɗan siririn corridor.
Shiga yayi, kana ya saki ƙofar ta koma ta mannu da ƙofar sai dai bata rufuba.

A hankali yake taku cikin nitsuwa,
Lips ɗin shi na ɗan motsawa alamun tasbihi yakeyi.
Tafiya mai ɗan tsawo yayi sai gashi ya kuma riski wata ƙofar.
Hannunshi yasa ya murɗa key ɗin ya buɗe, ƙofar.
Sai ga kuma wata ƙofa irin ta ƙarafuna kana dai iya hango woje.
Buɗe wannan ƙofarma yayi.
A hankali ya kutsa kai.

Wani irin sassanyan ajiyan zuciya mai tsawo yaja ya sauƙe a hankali.
Idonshi ya lumshe sabida wani irin sanyi mai masifar daɗi daya ratsa mishi jiki da zuciya.

Wani irin ɗan madaidaicin Garden Park ne mai masifar kyau.da sanyi da tsaruwa.

Daga nan bakin ƙofar daya fito ɗin.
Tayis ne fari tas a malale iya ganinka, sai gefen damanshi da bishiyoyin ayaba masu masifar duhu da sanyi dake jere reras.
Gefen hagunshi kuma bishiyoyi mangoro ne irin yan duƙus-duƙus ɗin nan ke jere,
Reras.
A hankali yake taku yana tafe yana tasbihi.
Yana jin kukan tsuntsaye mai daɗin ji yana ratsashi.

Tafiya kaɗan yayi sai gashi ya baiyana a wani irin wurin mai masifar kyau.
Wasu yan zagayen gini dakalin bulok bibbiyu akayi a ƙalla sunfi hamsin.
A ciki ko wanne zagayen akwai bishiyar dabino. Na gabanta inabi na gaban inabi tuppa, kana sai Yazawa, sai kuma na tsada, daga tsada sai na kanya, sai goruba da na giginya.
Cikin ko wanne zageyen kuma ƙasanshi koriyar ciyawa ce mai sanyi.

Can tsakiyar filin kuma wata iriyar ƙoramace mai masifar sanyi,
Ruwanshi na kwance fari ƙal-ƙal bakin wurin kuma jeren bishiyoyi goibane wanda sukayiwa kwaramar inuwa.

Gaban ƙoramar kuma wasu irin kujerun silver ne masu masifar kyau da sansi a jere a ƙalla sun kai goma zuwa ashirin.

Can gefenshi kaɗan kuma wani shingene aka zagaye da waya.
Shuke-shuken gargajiya akeyi a wurin.

Nan kusa da ƙoramar kuma shingen farar waya akayi a cikin ta wanda akayi ƴan ɗakuna-ɗakuna a cikin.

Tsuntsaye ne a ciki iya ganinka ko wanne da muhalli shin.

Kama daga Tattabaru farare ƙal-ƙal.
Sai kuma tsuntsu carki jajaye masu kyan launi ga kuma kanari da suke blue.

Sai kuma zabbi da suke yawo a ƙasa tako ina.
Can bakin ruwan kuma agwagin ruwa ne sunfi ɗari ƙwa-ƙwa.

Sai kuma zabbin daji.
dangin tsuntsaye dai babu irin wanda babu.

Ido ya zubawa tsuntsaye tamkar mai son yin magana dasu.

A hankali ya sunkuyar da kanshi jin tattausan gashin Ɗawisun Masarautar Joɗa da ya kai shekaru masu tarin yawa.
A hankali ya rusuna tare dasa tafin hannunshi ya shafa dai-dai ƙunɗun Ɗawisun inda wurin yake mai kalar blue mai kyau sabida Sheykh blue ne kalar da yafi so.
A hankali ta fara taku, ta juya mishi baya kana ta ɗaga bindinta sama samɓal har yana iya taɓo geminshi.
Wani irin takun ƙasaita tayi kana ta buɗa fikafikinta ta bazasu, ta fara tafiya a hankali.
Wannan itace suntsuwar da muddin mutun ba jinin Masarautar Joɗa bace, in ka shigo mata gaba gaɗi ba tare da an gabatar mata kai ba, zatayi ta yagune mutun tana caccakarshi.
Amman muddin dai kai jinin Masarautar Joɗa ne, kana shiga zata zo gabanka.
Tayi maka hakan.

Sai dai kuma bayan yin hakan in mutun nada wata zazzafar nasaba a masarautar misali shine sarki maici to in tayi wannan baza fikafikinta takanyi ta zagaya sarki sau bakwai kafin ta tsaya a gabanshi sai sarkin ya umarceta data tafi kafin zata tafi.

To babban abinda ya ƙara jazawa Jabeer matsala a rayuwarsa shine,
Duk sanda yazo gaban tsuntsuwar Ɗawisun nan sai tayi mishi wannan abin da zagaya sau bakwai abinda a tarihin masarautar sarki kawai yakeyiwa abin.

Matsalar abin a gaban Barrister Kamal da kuma Baba Bashiru da Abba sai Lamiɗo ne ta fara yimishi wannan abun.
Tofa ta bakin Baba Basiru ne mgnar ta zaga kunnen mazauna masarautar Joɗa.

Babban tashin hankalin masu son gadar wannan kujerar, shine yadda side ɗin Jabeer ke kusanci da Garden ɗin da take ciki.
Tashin hankalinsu ya ƙara tsananta ne tun randa Suka ga Lamiɗo yasa an buɗawa Jabeer hanyar shiga wurin ta cikin falonshi ba sai ya zagaya yabi hanyar da kowa ke bi ba,
Ya zama shida Lamiɗo sune masu hanya kowa daga falonshi zai shiga wurin.

A hankali Jabeer yayi murmushi tare da kallon yadda tsuntsuwar ta gama zagayashi kana tazo ta tsaya gabanshi tare da baza fikafikinta.
Cikin harcen Larabci yace mata.
“Fatana dai ba bauta min kikeyi ba! Domin babu wani abin bautawa da gsky sai Allah, wanda shine ya halicce ni ya halicceki.
Ni kuma ba kowa bane face halittarsa, sai dai na kasance cikin halittarsa mai girma da karrama fiye da komai, dan shi da kanshi yace.
Walaƙad karramna bani Adam.”
Wani irin juya kai tsuntsuwar tayi kana ta meda fiffigefa ta rufe, kafin ta juya ta nufi wani kekyawan wurin da aka ware mata, inda take tare da yayanta da mijinta.

Juyawa yayi can gefe ya hango wasu yan kyawawan tsuntsaye farare
A bakin ruwan.

Ga tattabarun sun zagaye wurin da sauran tsuntsayen.

A hankali ya zauna a wata kujera mai kamar gado.
Kishinƙiɗa yayi kana ya lumshe idonshi yana maijin yadda sassanyan iskar wurin ke ratsashi.
Karatun al’ƙur’ani ya fara cikin sassanyan murya mai daɗin sauraro.

Umaymah kuwa tunda ta fito, sai ta nufi sashin Hajia Mama, hira sukayi sosai cikin shaƙuwa irin ta yan uwa.

Suna zaune a nan Abba ya shigo.
Tana ganinshi tai murmushi,
shima murmushin yayi tare da cewa.
“Maman yara”.
Cikin sakin fuska tace.
“Na’am Yaya”.
Murmushi mai cike da zafi da ƙuna wanda ya baiyana har kan fuskarshi yayi kana ya zauna gefenta.
Gaisawa sukayi cikin danne ababen dake cin ransu.
Hajia Mama kuwa, tuni sai hawaye take zubdawa.
A hankali Umaymah ta miƙa mata handkin dake hannunta alamun ta share hawayenta.

Bayan ta share hawayenta ne,
Abba ya miƙa tare da cewa.
“Kin gaisa da Mom Imran kuwa? Da Salma”.
Fuska a ɗan haɗe tace.
“A a”.
Miƙewa yayi tare da cewa.
“To muje ku gaisa.”

Binshi tayi a baya suka nufi inda yace ɗin.

A falo suka samu Mom Imaran tana ganin.
Sun shigo tare da Hajia Mama tayi wani irin haɗe fuska, cikin nuna ko in kula tacewa Umaymah.
“Yaushe kikazo?”.
A daƙile tace.
“Jiya”.
Kanta ta ɗan kauda tare da cewa.
“Ya hanya”.
Alhamdulillah tace a taƙaice.
Cikin kufula Hajia Mama tace.
“Mu tafi”.
Miƙewa Umaymah tayi kana Abba ma ya miƙa sashin Amaryarshi Salma ya nufa da ita.

Suna shiga tana jin muryarshi ta fito, da sauri ta nufe shi da nufin zata ruggumeshi da sauri yace.
“Ga Umaymah tazo”.
A take taja birki ta tsaya cikin gyatsine tace.
“Ya kike kinzo lfy, ki gaida mutan gida”.
Cikin wani irin kallo Umaymah tace.
“Uhummmm kema ki gaida mutan gidanku”.
Tana faɗin haka ta juya ta tafi abinta.

Hajia Mama na biye da ita.
Ita kuwa Salma tana ganin fitansu ta ruggume mijinta.

Koda suka koma Side ɗin Hajia Mama bata daɗe a nanba ta nufi sashin Gimbiya Aminatu.

To bata fito nan ɗinba sai shabiyu saura.
Koda ta dawo Haroon da Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya kawai ta samu a falon.
Sai kuma Jalal da Hibba da suke dinning area suna zaune bisa kujerun Dinning table ɗin.
Sun sa plet a tsakiyarsu da kofunan tea a hannunsu, alamun sai yanzu sukeyin breakfast.

Cikin kula Aunty Juwairiyya tacewa Ƙanwar mahaifinta ɗin.
“Umaymah muje kuci abinci rana tayi fa”.
Murmushi tayi tare da son danne ɓacin ranta tace.
“Alhamdulillah Juwairiyya Ni kuma da nakeda Hajia Mama ga Gimbiya Aminatu, ai naci nayi nak.”
Cikin sauri Jakadiyarsu ta e.
“Ga kuma Matar Barrister Kamal ma ta aiko miki abin kari.
Gimbiya Saudatu ma ta aiko miki”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“A ajiye minshi sai anjima, kinga Juwairiyya kada ki shiga kitchen yau kizo mu wuni hira abinmu, abinci tako ina zaizo”.
Cikin sanyi Juwairiyya tace.
“Uhummm Umaymah ke har zaki iya cin abinci waɗanan mutane ai Gimbiya Saudatu ba abin wuya bane tasa mana guba muci duk mu mutu.
Sai dai muci na gidan Barrister”.
Kai Jakadiyarsu ta jinjina alamun eh.

Cikin ɗan ɗaga murya Umaymah tace.
“Haroon!.”
Da sauri ya amsa tare da tahowa inda take.
Gefenta ya zauna tare da cewa.
“Umaymah gani”.
Ba tare da ta kalleshiba tace.
“Ina Jazlaan?”.
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Y shiga Garden”.
Kai ta ɗan jinjina mishi tare da zubawa Jalal ido.
Ita Hibba sai murmushi takeyi shi kuma fuskarshi kamar boss.

A hankali ta miƙa ta nufi falon Jabeer ɗin.

Da sauri ta kalli Haroon tare da cewa.
“Ina zakaje”.
Baki ya ɗan tura tare da cewa.
“Umaymah inda zakije mana”.
Cikin tsokana tace
“Sirri zanyi da ɗan”.
Tana faɗin haka ta juya ta nufi can. Shima Haroon yana biye da ita a baya.

A hankali take taku har ta isa inda yake.
Gefenshi ta zauna tare da zuba mishi ido.
Cikin kula tace.
“Jazlaan”.
Cikim nitsuwa ya buɗe idonshi tare da kallon inda tarin tsuntsayen nan suke,
Lokaci ɗaya idanunshi suka kaɗa sukayi jazir.
lips ɗinshi ya fara motsawa da nufin yin mgna amman ya gagara,
sai wani irin kuka mai ƙarfi da yake son ƙawance mishi daga can ƙasan zuciyarsa.
Hakan yasa lips ɗinshi karkarwa tamkar mai jin sanyi.
Umaymah kuwa. Tuni hawaye sun wonke mata fuskarta tana mai kallon tsuntsayen.

Ganin Haroon yasa tayi mishi alamun ya kawo mata ruwa.
Ba musu ya juya ba tare da yayi mgn ba jim kaɗan ya dawo da goran ruwa da glass cup. Ruwan ya tsiyaya a kofin ya miƙa Umaymah.
Cikin sanyin murya tace.
“Ga ruwan sanyi kasha, nasan zakaji sanyin ƙunan da kakeji a ranka”.
Ta ƙare shi mgnar tana miƙa mishi cup ɗin.
Amsa yayi yayinda gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi alamun tsananin tarin baƙin ciki duniya.

Da kyar ya iya shan rabin kofin.
Nan ta gyara zamanta tare da kamo hannunshi ta fara tausar zuciyarshi kan abinda tasan shine babban matsalarshi.

A garin Bani kuwa zuwa yanzu hankali ƙabilar ɓachama yayi matsifar tashi, tsoro mai tsanani ya rufesu.
Tsoron da yasa da yawansu suka rinƙa guduwa suna koma cikin babban birnin Ɓadamaya,
Wasu kuma su tafi wasu jihohin.
Sabida sun gama tsinkewa da goron gaiyata da fulani keta raɓawa babu dare babu rana birni da ƙauye duk inda suka san fulani na nan sai da suka aika musu goro
Wannan ne yasa mafiya yawan kafuran aran na kare.

Inda hakan ya fusata Habban Ɓacama.
Har ta kaishi ga cewa, duk ba ɓacamen da yasan tsoron fulanine ya sashi guduwa to kada ya kuskura ya sake dawo mishi garinshi garin Shikan.
To wannan abun shiyasa wasu suka fasa guduwa, wasu da basuyi nisaba suka dawo.

To kuma kwatsam sai gashi yau an aiko an karɓin sandar sarautar Shikan dake hannunshi
Wannan abun yasa da yawa mutanen cikin Shikan Maza da mata hausa fulani da Ɓacamawa da sauran ƙabilu suka kuma rinƙa fecewa sabida, suna ganin yanzu dai shi kanshi Sarki Shikan bashi da madafa bashi da ƙarfi tunda an karɓe sandar sarautar shi.

To hakane yasa, ya rinka bin ƙauyuka Especially mutanen Bonon da kewaye ya rinƙa zugasu da ingiza su cewa, nanfa garinsu ne ya zasuyi su gudu kan Fulani.
Kuma ma suda sukeda dodon tsafinsu Bonon ai shi kadai ya ishi fulanin.
Da haka yasa duk ƙabilun Ɓacamawa na ƙauyukan basu guduba.
Sunata shirin faɗa yayinda cikin garin Shikan kuma yayi shal ko ina shiru babu mutane.

Cikin garin Bani kuwa, iya tsoronsu da suka gani a cikin kafuran ya sasu jin daɗi tunda gashi har suna guduwa subar garin da suke musu gadara da gori a kanshi da cika bakin sai sun kori Fulani a garuruwansu.
To tabbas sunada nasara akan fansar da zasu ɗauka, zasu ramane dan nemawa kansu enci.
Sun san iya sau ɗaya in sun nunawa arnatakun nan zasu iya gwabzawa dasu zasu barsu su sarara.

Haka yasa suke jin ƙarfin guiwar yin abun.

Ba’ana kuwa yanata ƙara shirya kanshi, sabida ramuwar gasar da za’ayi.

Ya Salmanu kuwa yanzu ya fara jajir cewa, yana fakewa da jarumtar Jabeer yana gasawa Ba’ana maganganu.

Sosai ya ƙara shigewa Shatu a mako ɗayan nan.
Kuma tana jin daɗin hakan.
Ta sake sosai.
Zuwa yanzu kuma jikin Ummey yayi sauƙi garawau sai dai har yau bata taɓa yin mgna ba ta zama tamkar kurma.

Da dare bayan sallan isha’i,
tana zsune ita da ya Salmanu suna hira cikin nitsuwa tace.
“Ya Salmanu gobene zamuje asibiti mu dubo su Junaidu da sauran marasa lfy dake cikin Genaral Hospital Ɓadawaya, dan naji ƙishin-kishin ɗin wai har yanzu babu likitan daya dubasu.”
Cikin gamsuwa da hakan yace.
“Eh hakan yana da kyau, kuje in sha Allah muma jibi asabar zamuyi gamgami muje, danma goben jumma’a ne da munje tare”.
Sai kuma ya ɗan kalleta tare da cewa.
“Da yaushe zakuje?”.
Cikin sanyi tace.
“Da safe zamuje, in anyi sallan azahar zan dawo, amman Rafi’a zata wuce makaranta”.
yace.
“To ke sai yaushe zaki koma?”.
“Sai Ummey ta ɗan ƙara samun sauƙi. Ni da na so mu kaita asibiti kan batun rashin mgnar tata.
Gyara zaman shi yayi tare da cewa.
“Wannan ba matsala bace, wlh firgici da tsoro ne yasata hakan”.
Haka dai sukaci gaba da hirarsu.

Washe gari ranar jumma’a, misalin karfe sha biyu dai-dai suka fito zasu tafi asibitin.

A bakin lambun garinsu sukayi kiciɓis da Ba’ana nan ya tsaidata dole suka zauna.

A can cikin masarautar Joɗa kuwa,
Lamiɗo, Galadima, Sarkin Shaɗi, da Jabeer ne tafe a hankali suka shiga cikin Garden ɗin nan.
Ta gefen Lamiɗo, suna shiga suka nufi inda katon curin dake wurin shekara da shekaru.
Shi dai Jabeer binsu yakeyi baiyi magana ba,
Koda suka isa wurin zama sukayi dabas a ƙasa.
Dole shima ya zauna, cikin sanyi Lamiɗo yace.
“Assalamu alaikum Jaimi”.
Da mamaki Jabeer ya kalleshi,
Hiraminshi ya gyara tare da cewa.
“To yau kuma”.
Da sauri Galadima yasa hannunshi ya rufe mishi bakinshi.
Hannunshi yasa ya janye hannun Galadima tare da cewa.
“Yo ai ba sai ka rufe min bakiba, in kace nayi shiruma zanyi, sai dai ina naga abin saɓon Allah ko tsireni za’ayi sai na faɗa”.
Dafe kai Galadima yayi tare da tsuke fuskarsa.
Ganin haka ya taɓe baki tare da ɗaga kafaɗunshi ya ɗan buɗasu alamar, ban damuba.

Sarkin Shaɗi kuwa bai kallesu bama.

Wani irin zabura Jabeer yayi cikin tsananin firgici da kaɗuwa lokacin da yaga wani irin h ….!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button