Garkuwa Hausa NovelHausa Novels

Garkuwa 25

Sponsored Links

*GARKUWAR FULANI*”Kamar tsoffin karnuka”. Cikin fusata Gimbiya Saudatu ta miƙe tsaye tare da nufo inda yake.
Shi kuwa kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Kinyiwa kanki Garkuwa da kika tashi daga kan kujerata”.
A hatsale tace.
“Wai kai a zatonka tsoronka nake jine ko meye?”.
Da sauri ya jujjuya mata kai tare da tsuke fuskarsa alamun baison sautin amon muryanta da take ɗaga mishi, a daƙile yace.
“A a, na isa inyi zaton tsorona kikeji. Ke da bakinji tsoron Allah’n daya halicce ki bama, ina zakiji tsoron wani bawa nashi, ai masu tattausan zuciya suke tsoro”.
Hannu Baba Nasiru ya ɗago da alamun zai kifeshi da mari.
Ba zato yaji ya kama hannunshi, kana ya ɗan juyo fuskarshi gareshi, cikin sakekkiyar murya yace.
“Wai ku meyasa bakwa gane, yare da harshenmu na bani adam ne? Meyasa kukafi son Yaren dabobbin marasa hankali, a zatonka ka kai matsayin da zaka ɗago hannunka ka mari fuskanta?”.
A hatsale ya fuzge hannunshi tare da cewa.
“Da uwarka kakeyi, kasan wacece dabbar ai!. Ɗan hegiya mai jajayen kunnuw..!”.
Shiru yayi bai ƙarisa mgnarba ganin wani irin kallo da Jabeer ke mishi, ido cikin ido.
Kana ya ɗaga hannunshi na dama, yana ɗan buga bayan tafin hannun damanshi cikin tafin hannunshi na hagu.
Still idonshi na kan fuskar ƙanin Mahaifinshi, miƙar da tafin hannunshi yayi, tare da mishi alamun datsa a cikin tafin hannunshi, kana cikin danne fushinsa, dan baya son su gane abinda ke masifar ci mishi rai, sai dai duk danniyarsa ya rigada, sun gane babu abinda ya tsana a duniya sama da azagar mishi mahaifiyarshi bare a suffantata da ƙaddararta, da binta da kalaman bita da ƙulli.
Baba Basiru ne, yayi wani irin dariyar mugunta kana ya ɗan matsa baya kaɗan cikin izza yace.
“Datse mana wuya zakayi, dan a zagi waccar munafukar da Allah ya nuna mata ishara tun a duniya”.
Murmushi mai rauni yayi kana yace.
“Mahaukaciyar tsohuwar ku ko! Eh na gane lallai kam, batunka haka yake”.
Cikin fiffiƙewa suka fara kumfar baki ina dalilin zaicewa uwarsu mahaukaciyar tsohuwa”.
Daga nesa za’a iya jiyosu.
Shi kuwa ko Aunty Juwairiyya dake Dinning area bata jiyo abinda yake faɗa.
Domin cikin nitsuwarsa yake zaro musu, duk amsar mgnar da sukayi mishi tunma kafin harshensu ya huta.
Gimbiya Saudatu kuwa, a masifance tace.
“Ai asirinku zai tonu nan bada dadewa ba, munafukar kakar takace, tayiwa mahaifiyarsu asiri ta haukatata dan baƙin kishi irin nata”.
Murmushi yayi ganin yadda ƙannnen mahaifinshi keta ihu uwa karnuka.
Allah ya sani lamarinsu yana bashi mmki har yau ya rasa me yayi musu mai zafi a duniya da suke gaza danne tsanarshi a aransu.
Me Mahaifiyarshi tayi musu da suke masifar tsanarta?.
Kanshi ya juya ya kalli Umaymah daketa murmushi mai cike da jin daɗin yadda yake komai a nitse.
Juyawa yayi zai nufi gefen hanyan falonshi.
Sai kuma ya ɗan tsaya ganin Gimbiya Saudatu tasha gabanshi.
Cikin danne shakkarsa tace.
“A haka zaku ƙare. Komai na muna furci, anje anyi aure a muna furce a ɓoye, sannan an kawota yau kwana uku kenan an kasa fito da ita a nunawa mutane ita, dan masifar rashin gsky.
Ko dai cikin shegene da ita yasa kuke ɓoyeta.”
Da sauri Umaymah ta ƙara so inda suke, cikin tsuke fuska tace.
“A kanki shege zai samu, in sha Allah bazai samu a tsatson yar uwata ba, kin kuma yi gaggawa, da yake dama aikin shaiɗan ne dole zakiyi ta aikatashi.
Ki koma ki wanke idonki zai kawo miki Amaryarshi matarshi kuma uwar ƴaƴan shi, har Side ɗin ki, cikin falonki, har gaban ki.
Kinaji zai gabatar mata ke da munanan ɗabi’unki dan tasan irin zaman da zatayi dake”.
Laminu ne yace.
“Ke kuma waya kasa dake, ki bari ƴan gida suyi mg…!”.
Wani irin tsalle yayi ya koma baya, jin marin da Jalal wanda yanzu ya shigo ya kifa mishi ta bayanshi.
Da sauri Baba Nasiru da Baba Basiru suka juyo kan Jalal, alamun wai zasu dakeshi.
Karkata kai yayi ya kallesu da gefen ido.
Kana a hankali yasa hannunshin ya ɗaga rigarshi, wata ƴar madai-daiciyar bindiga AK 47 ya zaro a ƙugunshi .
Wani irin wawan birki sukaja, tare da cewa.
“Eh lallai babu shakka masarautar Joɗa ta raini tantirin ɗan ta’adda bindiga, wato abin har yakai ka matakin riƙe bindiga”.
Kanshi ya tankwashe tare dasa bakin bindigar yana sosai tattausan sajenshi irin na Hamma Jabeer ɗin shi.
Kana da bakin bindigar ya nuna musu hanyar fita.
Ai a jere suka juya suna fita.
Gimbiya Saudatu na cewa.
“Duk wanda yaci tuwo dani, tabbas miya zaisha.
Amaryar munafurcin a fito da ita mu ganta in an taki gsky”.
Laminu ne ya amshi zancen da cewa.
“Menene ma abin gani a Bororiyar daji”.
Da haka dai suka fita.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin kallo na tuhuma, da tarin mamaki yakeyiwa Jalal.
Bindiga a hannunshi, shi kuwa Jalal ganin yadda duk suka zubawa bindigar idone yasashi.
Meda ita cikin rigarsa.
Kana ya juya da sauri ya nufi hanyar fita.
Jabeer bai ce mishi komaiba.
Yana ganin ya fitane shi kuma ya juya, ya nufi falonshi.
Bedroom ya wuce, a hankali ya zauna bakin gado,
tare dasa hannunshi yana buɗa bakin al’kyabbar jikinshin sai kuma yasa hannu shi na dama ya dafe kanshi, kalmar amarya mata ya maimaita a fili.
Wani irin rumtse idanunshi yayi da ƙarfi Allah ya sani shi yama mance, batun wannan jagulellen auren da akayi kamar na wasan yara.
kanshi ya ɗago a hankali ya kalli Umaymah dake shigowa da sallama a bakinta.
Gefenshi tazo ta zauna bisa bedside drower’n tana fuskantarshi.
hannunshi yasa, ya fara cire hiramin kanshi.
ita kuwa Umaymah cikin hikima tace.
“Idan mutun yana yi maka fatan ci baya to kayi mishi nuni da nasarorin rayuwarka, ban cika son takura maka akan baka umarnin yin abubuwan da baka soba, to amman bani da zaɓi akan duk wata al’ada ta masarautar Joɗa, da cikin masarautarmu ne, tabbas inada damar hana wani abun da saka wani abun.”
Cikin rauni ya kalleta da idonshi da sukayi jazir a hankali yace.
“Me Mahaifiyata tayi musu mai zafi da suka sata a gaba ita da ah’linta.
Duk abinda sukeyi Mata bata kulasu, bare ta kai ga ramawa, tana haƙuri akan komai, haka yasa suke zaton tsoronsu takeji.
Ita kullum yanayi musu uzuri.
su kuma kullum fatansu su cutar da ita har dai suka samu nasarar cutar da rayuwarta sannan muma basu barmu ba.
Ni na gaji da zama cikin masarautar Joɗa, zan bar musu garin gaba ɗaya”.
Sauƙe numfashin tayi tare da cewa.
“Basu da nasara a rayuwarsu.
Nasara ɗaya ce garesu kuma sun yi ta.
Ta ƙare musu”.
Sai kuma ta ɗan kalleshi cikin sanyi tace.
“Jazlaan!”. A hankali ya amsa mata.
Fuska ta ɗan raunata kana a hankali tace.
“Yau kwanan matarka uku a gidan nan!”.
Da sauri ya kauda fuskarshi a kanta wani irin haɗe fuska yayi tare da taune lip ɗin shi na ƙasa ta ciki.
Shi ya mance da wannan batun yana rayuwarshi hankali konce. Wannan kariyar matar Gimbiya Saudatu tazo ta tono zancen.
Ita kuwa Umaymah a hankali taci gaba da cewa.
“Baka gantaba! Baka nemeta ba! Baka san halin da take cikiba! Baka nunata wa ah’linku ta masarautar Joɗa, a matsayin ta, na matarka.
Lamiɗo yayi mgna har ya turo Umminka taxo ta sanar maka, sai tace bata so ɓacin ranka. Abbanka yace shi bazai ce maka komaiba, sabida babu abinda baka saniba kan al’adar masarauta.
Yace kada wanda yayi maka mgna akan matarka sabida.
kai ba jahili bane, duk ka fimu sanin haƙƙin mace akan mijinta. Yace kunya tashi kake son yi a idon mutane!”.
Kanshi ya fara jujjuyawa a hankali yace.
“Me kukeso inyi! Umaymah ya kuke son inyi? Bazan iya juya kaina in dawo yadda kukeso bafa, daga yadda Allah ya halicce ni”.
Cikin hikima da sanyi tace.
“Ka shirya gobe, ka gabatar da matarka ga ƴan uwanka da iyayenka”.
Hannunshi biyu yasa ya dafe kanshi.
Tare da rufe idonshi, sabida sarawar da yaji kanshi nayi.
sai kuma ya ɗan kalli Umaymah jin tana shessheƙan kuka.
Cikin sanyi yace.
“To!”.
Murmushi tayi tare da shafa kanshi kana ta juya ta fita da sauri.

Kai tsaye sashin Gimbiya Aminatu ta wuce, ta sanar mata yadda sukayi da ɗan nata.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, a hankali ya miƙe al’kyabbar jikinshi ya zare, kana ya nufi bathroom da jallabiyar.

Yana shiga ya zare jallabiyar da snglet ɗin. Kana ya shiga wurin wonkan.
Ruwan sanyi ya sakarwa kanshi.
sabida sarawar da kanshi keyi,
tun ihun dasu Baba Basiru sukayi mishi a kanshi.
Ga kuma wani sabon zance na zagaye idanun mayu da kulullukan masu konciyar ɗaukan rai na masarautarsu.
A ƙalla yayi mituna biyar ruwan sanyin na zubo mishi a tsakiyar kai, kafin ya fara sauƙe ajiyan zuciya alamun kan ya fara lafawa.
Al’wala yayi kana ya fito.
A nan drower’n glass dake bathroom ɗin nashi ya kimtsa kanshi cikin wasu datsastsen yadi mai masifar kyau Super Nour, Noble blue mai ɗan karen kyau, tattausan yadine mara nauyi, kana yanada ɗan shara-shara kaɗan, riga da wonɗo ne dai-dai jikinshi rigar half jomfa ne wanda aka watsa mishi aiki da da baƙin surfani.
in ka tsura mishi ido sosai zaka iya hango shatin snglet and white boxes jikinshi.
Wani Oud mai daɗin gaske ya fesa.
Kana ya fito.

Baƙar fula ya kafa a kanshi wanda ya bawa tattausan gashin kanshi damar baiyana ta gefe da gefen kanshi da kuma ƙeyanshi.

Fararen kyawawan Ƙafafunshi, ya zura cikin. Wasu tattausan takalma baƙi.
Sai kuma yasa hannu ya ɗauki carbinshi.
Agogon dake liƙe saman mirror ya kalla,
Lokacin sallan la’asar yayi, dan haka dole babu baccin tsakanin azahar da la’asar ɗin da ya dawo yi.

A masallaci ya samu su Haroon da Jamil.

Bayan anyi sallan ne kowa ya kama sabgogin gabanshi.
Shi Jabeer komawa gida yayi.
Ya saka garen kayan jikinshin kana.
Ya fito, Ummi ya samu tsaye a tsakiyar falon, cikin kula tace.
“Zaka fitane?”. Kai ya gyaɗa mata alamar eh.
ba tare da damuwar rashin bata amsarba tace.
“Da yan rakiya ko kai ɗaya?”.
Yana gyara zaman hular kanshi yace.
“Ni kaɗai. Zanje gidan Malama Abubakar ne!”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ka gaida minshi”.
“In sha Allah zaiji. Umaymah fa?”.
Gane abinda yake nufine yasata cewa.
“Tana can sashin Gimbiya Aminatu, wurin ɗiyarta Amarya Aysha”.
Kanshi ya ɗan sunkuyar ba tare da yace mata komai ba,
ya fita.
Malam Abubakar shine, malamin da ya fara ɗiga mishi harafin Ba”un a allon shi, wato Be a fillance, Basinmi’arra a hausance ko?.
A wurin shi yayi sauƙan forko, sai dai zuwa yanzu, shi Jabeer shike ƙara wa Malam Abubakar sani, akan Nahawu da Tajwid sabida shi da karatun zaure yayi.

Umaymah kuwa, ita da kanta ta sanarwa Lamiɗo cewa, gobe Sheykh zai gabatar da amaryarshi.

Haka yasa, ta fara shirya Aysha, shiri na musamman.
Cikin Hadiman Juwairiyya ɗaya daga cikinsu.
Mai suna saratu, itace Umaymah tasa ta yarfawa Aysha zanen lalle mai ɗan karen kyau.
Kana Ummi da kanta ta wonke mata kai sabida ita keyiwa Juwairiyya ma.
Sosai ta fito ras.
Ita kuwa Shatu duk abinda sukeyi Mata.
Tunanin Hibba al’hinin da tun randa tazo bata kuma ganinta ba.
tana son ta tambayesu ta rasa ta ina zata fara, dole dai haka ta haƙura tai shiru.

Washe gari ranar talata. Da hantsi, ko ina na sashin Gimbiya Aminatu sai ƙashi yakeyi, sabida shiri da kimtsa amarya.
Umaymah da kanta take kimtsata, wani irin dakekken wagambarine mai matukar kyau Royal blue, tasaka doguwar rigace. Tayi cib-cib da jikinta.
wani irin ɗauri ɗan kwali Aunty Juwairiyya ta murza mata a kanta, irin mai stpes ɗin nan.
Kana sai wata farar al’kyabbar masarauta fara ƙal mai kolliyar zaren aiki da ulunta Royal blue.
da surkin Golding color mai sheƙi.
Wasu fararen takalma masu ratsin Sky blue ne a kekyawan kafarta da yasha jan lalle, takalman basu cika tsini da tuduba, sai dai kuma ba dab da ƙasa bane.
Tayi kyau iya kyau, sai ƙamshi da sheƙi take zubawa.
Umaymah ce ta kama hannunta har zuwa falon Lamiɗo, wanda bai rigaya ya fita fadaba.

Gefen Gimbiya Aminatu ta ajiyeta, kana tace.
“Bari inje inzo da Angon.”
Murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
“To kuyi sauri dai”.
To tace kana ta fita.

A can sashin Sheykh Jabeer, kuwa.
Da alamun wonka ya fito, a nitse yake kimtsawa, cikin wani fitinenne yadi mai taushin gaske.
yadin Royal blue ne mai masifar kyau.
rigar half jomfa yar tsukekkiya,
tsaki ya ɗan ja lokacin daya gama dai-dai-ta zaman rigar a jikinshi sabida tayi kib-kib a jikinshi har kamar ta ɗan matseshi.
Wondon kuma irin mai iya kuibin sawune, irin sakun wondunan ahlul sunna.
a hankali ya iso gaban drower’n da hulunanshi da hirami da baƙin abun saman hiramin ke jere a ciki.
Har yasa hannunshi bisa wani farin hula, sai kuma ya sunkuya ya ɗan kalli. Kanshi.
Fuskarshi ya ɗan tsuke, sai kuma ya ɗan juyo jin muryar Haroon yana cewa.
“Wow masha Allah, gsky kayi kyau, Please ka fita haka mana, ka ganka ɗan saurayi mai jini a jika, amman in kasa al’kyabbar nan, sai kwarjininka yayi yawa yaseen.
Ni kaina sai inji ina shakkarka,”.
Kai ya ɗan shafa kana yasa hannunshi ya zaro hiraminshi fari da baƙin zagayen.
ɗaya marfin drower’n ya buɗe tare da zaro wata dakekkiyar al’kyabbar fara mai ratsin blue na zaren aiki gaba da bayanshi.
Gaban gado ya dawo yana warware al’kyabbar tare da cewa Haroon.
“In na fita a haka ai ji zanyi kamar babu tufafi a jikina, sabida sunyi min kaɗan.”
Ya ƙarishe mgnar yana zura al’kyabbar a jikinshi.
Masha Allah, Haroon yace.
Kana ya matsoshi yana tayashi gyara zaman al’kyabbar yana cewa.
“Duk shigar da kayi tana maka kyau, in na ganka ba al’kyabbar sai inga kamar kafi kyau.
In kuma kasa al’kyabbar sai inga kafi kyau”.
Baice dashi komaiba yaci gaba da gyara sakun hiraminshi,
saida ya gama dai-dai-ta hiramin sai ya juya ya nufi, wannan drower’n da hulunanshi ke jere a steps biyu na sama.
Biyu na ƙasan kuma jerin takalmanshi ne.

Fararen takalma masu taushi ya saka ƙirar Gucci,
Zara-zaran yatsunshi sarari sabida ba sau ciki bane ba kuma half cover bane.
turare ya fesa, tare da sa hannunshin ya shafa sajenshi.
Kana ya kalli Haroon daketa ɗaukar shi hoto.
Cikin tura baki Haroon yace.
“Na bari, nasan yanzu zakayi ƙorafi, yanzu ina zakaje?”.
Yana fita yace.
“Valli Hospital, akwai yaron da zan duba aikin da akayi mishi”.
Bayanshi ya biyo tare da cewa.
“To sai ka dawo”.
Ni zamuje wurin Budurwar Jamil taga babban yayanshi.
Wani kallo ya mushi tare da cewa.
“Allah ya shiryeka babban kobo”.
Dariya Haroon yayi tare da cewa.
“Eh naji na yarda, zanje yaro ya samu matsala da ita tanata wahal dashi ba dole inje in dai-dai-ta musu matsalar ba”.
Juyowa yayi jin abinda Haroon yace cikin sakin gajeren murmushi yace.
“Uhumm yaushe ka zama luwali, bani da lbri, to kai taka matsalarma yaushe ka warware ta, kun iya cikamu da zancen ku ƴan soyayya ne, kuma bakuma san yadda ake soyayya da magance matsalolin ta da tattalinta gudun ta lalaceba”.
Wani irin dariya mai sauti Haroon yayi tare sara mishi.
Da sauri ya juya, da nufin tafiya,
sai kuma yaga Umaymah na tsaye a gabanshi.
Hannunta tasa ta kamo nashi tare da janshi suka fara tafiya.
Cikin sanyi yace.
“Oh Umaymah ina zamuje?”.
Haroon kuwa baki ya taɓe tare da cewa.
“Wlh gobe zan koma in sha Allah, komai sai an nunawa mana ƴan ubanci”.
Dariya Umaymah tayi tare da cewa.
“Allah kiyaye hanya”.
Da sauri yace.
“To na fasa tafiya”.
Suna gab da fitane yace.
“Umaymah sakeni karmu fita a haka”.
Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
“To taho”.
To yace mata kana yabi bayanta.

Suna tafiya cikin ƴar faffaɗan hanyar da bishiyoyin namijin gwanda yayi musu ƙawanya,
shiyasa wurin yayi sanyi.

A hankali ya kalleta lokacin da suka iso.
Bakin ƙofar Gimbiya Aminatu.
tare da cewa.
“Umaymah me zanyi a ciki?”.
Hannunta tasa ta kamo nashi.
Kawai ta kutsa kai ciki. Dole ya bita a baya.
Yana saka ƙafarsa cikin falon yaji zuciyarshi ta buga,
da ƙarfi, lokaci ɗaya ta fara harbawa da sauri-sauri.
Cikin sanyi yace.
“Umaymah barni a nan”.
Bata kulashi ba taci gaba da janshi tayi har bakin ƙofar falon Lamiɗo.
wani irin rumtse idanunshi yayi yin yadda zuciyarshi ke barazar fashewa.
Da sallama a bakinta, suka shiga.
Yayinda Lamiɗo da Abbanshi suka amsa mata.
Cikin wani irin azabebben bugun da zuciyarshi keyi, yasa ƙafarshi cikin falon.
yayinda Umaymah ke riƙe da hannunshi tana mishi jagora har zuwa gaban Lamiɗo da Galadima da Abbanshi da kuma Malaminshi Malam Abubakar.
Kana ta tsaya dashi kusa da Aysha tare da rusunawa.
Yayinda shi kuma cikin fargabar yadda ƙirjinshi keyi ya rusa a hankali ya zauna bisa tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a wurin.
Dib, dab, dib, dab, dib, dab. Haka zuciyarshi keyi.
yayinda itama Aysha da bai lura da ita Bama haka zuciyarta keyi,
sabida jin an mutun ya zauna kusa da ita.

A hankali ya lumshe idonshi, sabida bugawar da zuciyoyinsu keyi a tare yasa, ƙarfin nashi bugun ya ɗan ragu kaɗan.

Cikin nitsuwa ya kalli Abbanshi kanshi a sunkuye yace.
“Barka da safiya Abba”.
Cikin kula yace.
“Barka dai”.
Sai ya kuma kalli Malamin nashi cikin kamala yace.
“Allah hokke sabbugo, Malam Barka da zuwa ya gida?”.
Cikin nitsuwa Dattijan yayi murmushi tare da cewa.
“Alhamdulillah Sheykh Jabeer ya hidima”.
Alhamdulillah yace, kana ya kalli Lamiɗo da Galadima.
sai kuma ya kauda kanshi.
murmushi Galadima yayi tare da cewa.
“Mu bazaka gaishemu ba kenan?”.
Ɗan tsuke fuskarsa yayi tare da cewa.
“Gaggawa dai aikin shaiɗan ne”.
Murmushi Lamiɗo yayi sabida ya fahimci duk abinda zasuyi,
sai ya cisu gyara ta kuma fuskar gsky.
Galadima ne yace.
“To ni bari in gaisheka Ina kwana”.
Kanshi ya jinina mishi tare da cewa.
“Kayiwa kanka tanadin lada ashirin, a madadin kaɗan da zaka samu in ni na ɗaga maka gaisuwar.
Lfyta lau Alhamdulillah.”
Ya ƙarishe mgnar da amsa gaisuwar.
Dariya sukayi kana, ya kalli Lamiɗo a daƙile yace.
“Ina sauri dan inada aikin yi, menene kasa aka jawoni nan”.
Ya ƙarishe mgnar a hankali yadda Abbanshi da Malaminshi bazasu jiba.
Kana ya ɗan muskuta ya matsa gefe yayi nesa da Aysha sabida wani tsalle da yakeji zuciyarshi nayi, a madadin bugun da takeyi kafin ya zauna kusa da ita.
Cikin zuba musu ido.
Lamiɗo yayi murmushi sabida sunyi masifar dacewa da juna, shigarsu da ta zamo iri ɗaya tayi matuƙar yi musu kyau.
Cikin wasa irin na kaka da jika yace.
“Ga amaryar taka baku gaisaba, ku gaisa sai ka kaita kuje ka gabatar da ita”.
Fuskarshi a haɗe yace.
“Hakan addinine ko al’ada?”.
Da sauri Galadima yace.
“Al’adace kuma sai kayi ta”.
Ta gefen ido ya kalli Galadima tare da cewa.
“Da ba Galadima za’a bakaba, da sarkin raya al’adu za’a baka”.
Shiru yayi jin Abbanshi na cewa.
“Allah ya bamu nisan kwana, kaima watan watarana a gabanka yaranka zasuyi min haka Muhammad”.
Cikin yin ƙasa da kai cikin girmamawa da karrama mgnar mahaifin nashi yace.
“Sun isa! Suyi maka haka in barsu”.
Murmushi Malam Abubakar yayi tare da cewa.
“Kamar yadda ka isaba”.
Shiru yayi gane manufarsu.
Jin duk sunyi shiru ne, yasashi ɗago kai ya kallesu.
Suma shi suka zubawa ido, da sauri yayi ƙasa da kanshi.
Ita kuwa Aysha shiru tayi tamkar ruwa ya cinyeta, tanajin yadda suke musayan kalamai. Sai dai bata fahimtarsu domin, tuno nata ahlin.

Gyaran muryan da Abbansa yayine yasashi ɗago kai ya kalleshi.

Cikin bada umarni Abba ya nuna mishi Aysha tare da cewa.
“Kama hannunta kuje, ka gabatar da ita, ka fara daga sashin ƙannen Lamiɗo, sai na Mamanku, daga nan kuje wurin Gimbiya Saudatu,
dama sauran matansu Babanku Nasiru”.
Bisa dole yace.
“To kana ya yunƙa ya miƙa,
da sauri Umaymah ta miƙe tazo ta miƙar da Aysha.
kana ta kamo hannunta ta miƙa mishi alamun ya riƙe hannunta.
Cikin tsuke fuskarsa da kwaɓeta tamkar zai ɗaura hannunshi a ka ya kurma ihu.
Ya zuba mata ido. Muryar Abbanshi ce ta katse tsayuwar da yayi kamar an dashi.
“Riƙe hannunta ku je”. A hankali ya ware tafin hannunshi da Umaymah ta kamo
kana lokacin guda yaji zuciyarshi tana tsalle da harbawa, kamar dai tana mararin wani abu.
Hannun Aysha Umaymah tasa mishi cikin nashi tare da meda yatsunshi ta rumtsesu.
Dam-daradam-dam haka zuciyarshi tayi wani masifeffen bugun mai kama da na aradu kana tafara wani irin tsalle.
Ita kuwa Aysha, wani irin tsuma jikinta ya fara lokacin da taji tattausan yatsun hannunshi da fatar tafin hannunshi ya rumtse nata.
Hannun wani irin masifeffen tsoro da kunyane suka diro mata, a lokaci guda.
Shi kuwa Sheykh wani irin asirtace kuma ɓoyeyyen dogon ajiyan zuciya ya sauƙe mai sanyi, jin gaba ɗaya zuciyarshi ta koma ta nitsu tabar wannan tsinkewar da bugawar da tsalle tayi lib a cikin ƙirjinsa.
Jin muryar Jakadiya ne yasa, Sheykh Jabeer, yin ƙarfin halin ɗaga ƙafarshi ta dama.
Jin ya ɗan yi gabane yasa itama, ta ɗaga ƙafarta ta hagu, sai hakan ya bada wata dama ta musamman, ya zama suna ɗaga ƙafafuwan su, a tare kana suna taku a jere.
Sai dai shi ɗin ya ɗan kereta kaɗan.

“Masha Allah. Tabarakallah,”. Sune kalaman da Umaymah ke Maimaitawa, lokacin da take biye dasu a baya.

Lamiɗo da kanshi da Galadima sunga wani irin dacewa na musamman a tsakin Muhammad Jabeer da Aysha.
Abba kuwa murmushi yakeyi mai baiyana jin daɗi.
Malam kuwa, Addu’o’in yaketa jero musu na fatan al’khairi da zaman lafiya da nitsuwa da samun zuriya ɗayyiba.

A hankali suke taku yayinda kowa zuciyarshi ke bin takun sawunsa,
A haka suka fito babban falon Gimbiya Aminatu nan suka samu Ummi. Tana ganinsu ta miƙe da tsauri tayi gabansu, hadimai hudu cikin na Gimbiya Aminatu kuwa, sukayi bayan Umaymah dake bayansu.

Shi kuwa Sheykh Jabeer suna fitowa yayi wani irin saurin sake hannunta tare da janye nashi,
Sabida shi ji yake tsikar jikinsa na tashi tamkar ya riƙe wutan lantarki ne sabida masifar tsuma da yaki naman jikinsa nayi.
Murmushi Umaymah tayi ganin still dai suna tafiya a jere a jere suna wani irin taku mai ƙayatarwa.

Suna fitowa, suka samu sallama a bakin mashigar wurin.
Nan ya shaida musu, duk sashukan gidajen anje anyi sallama dasu an kuma basu daman shiga.

Tafiya kaɗan sukayi daga sashin Gimbiya Aminatu, ta gefen hagunshi,
suka ɓullo farfajiyar wani babban part,
Jakadiyarsu na gaba suna biye da ita a baya, Umaymah na biye dasu.
A hankali suke taku cikin ƙasaita hadimai da fadawa na mara musu baya.
Suna shiga ciki, suka samuwa wata dattijuwar tsohuwa mai tarin shekaru.
Cikin murmushin da muryar tsufa tace.
“Malamai magada annabawa, lallai yau inada babban baƙo da babbar baƙuwa.”
A hankali suke tafiya har zuwa gabanta, inda take zaune bisa tattausan carpet hadimanta na kewaye da ita.
wanda biyu daga cikinsu, suka tashi da sauri suka kawo ababen motsa baki suka jera a gabansu.

Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya kalli tsohuwar da take matar ga Galadima.
Cikin kula yace.
“Barka da safiya Innano”. Cike da kula tace.
“Barka dai Malam Muhammad, mun samu ƙaruwa ko”.
Kanshi ya gyaɗa mata a hankali haka yasa duk basu ganiba sai ita da yake gabanta.
“Cikin muryar tsufa tace.
“Allah ya sanya al’khairi. Ya baku zaman lafiya. Yasa matarkace iya rai da mutuwa. Ya azurtaku da zuriya ɗayyiba.”
Da Sauri Umaymah ta amsa da Amin Amin hakama sauran baki ɗayansu.
Ita kuwa Shatu, cikin saisaita nitsuwarta ta ɗan kalli tsohuwar tare da cewa.
“Ina kwana”.
Murmushi tayi tare da kai hannunta ta kamo hannun Shatu, tafin hannunta ta buɗe ta zuba musu ido, na yan wasu ɗakiƙu kana tace.
“Lafiya lau, ya baƙu ta?”.
A hankali tace.
“Alhamdulillah”. Jakadiyarsu ce ta ɗan rusuna tare da cewa.
“Mun barki lfy”.
Kai ta gyaɗa kana tayiwa hadimanta umarni su miƙo kyautar da take gadon masarautarsun ce farin gyale ne mai kyau da taushi.
Umaymah ce ta amsa ta miƙa hadiman dake bayanta.

Kana suka miƙe suka fita.

Daga nan sashin wani sashin na kusa dashi suka shiga.
Wanda yake sashin ƙannen Lamiɗo ne.
Saida suka gama da sashukan manyan masarautar.
Kana suka nufi sashin Hajia Mama.
Tuni tasan da zuwansu.
haka yasa ta kimtsa ta tsara komai na tarban surkar tata.
A matsayinta na uwar ango.
Har can cikin bedroom Ummi ta wuce, su kuma suna biye da ita a baya.
Suna shiga suka sameta, zaune bisa kilishi,
Batool na gefenta, wacce son ganin amaryar ne, ya hanata tafiya.
Hadimanta kuma na zagaye da ita.
Suna shigowa ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi.
Cikin tsananin baiyana farin cikin ta, ta nunawa Jabeer kusa da ita.
a hankali suka iso suka zauna gabanta.
Umaymah kuwa gefenta ta zauna.
Ummi ko na bayansu hadiman kuma suna can falo.
Hannunta tasa ta kamo hannun Jabeer.
Cikin fara’a tace.
“Alhamdulillah Muhammad Jabeer, Allah ya sanya al’khairi ya baku zaman lfy”.
To shifa suna ɗaure mishi kai, da tarin addu’o’insu na al’khairi, shi dai ba sonta yakeba ba kuma zama da ita zaiba,
to me zai wahal dashi da zaice Amin Amin.

Umaymah da Jakadiyarsu ne suka amsa da Amin Amin kamar dai yadda sukayi a sauran wuraren.

Batool ce ta kalli Shatu cikin isa tace.
“Amarya ki ɗago kanki mana kinga gaban uwar mijine kike”.
Duk da taji mgnar Batool sai tayi kamar batajiba,
Abubuwan ci da sha dake gabansu ne,
Hajia Mama ta jawo wani ɗan ƙaramin tray da cups biyu ke kanshi.
Gyara zama tayi da kyau, tana murmushi ta kalli Shatu dake mgna a hankali.
“Ina kwana Mama”.
Cikin kula tace.
“Lfy lau ɗiyata ya baƙun ta”.
Alhamdulillah tace, tare da tsurawa madara da zumar da Hajia Mama ta zuba musu cikin kofu nan ido.
a hankali ta ɗan muskuta kaɗan tayi baya, tare da ƙara yin ƙasa da kanta.
ita kuwa Hajia Mama, kofin ta ɗauka ta miƙa mata.
Tare da cewa.
“Gashi ɗiyata amshi kisha.”
Cikin sanyi murya can ƙasa ta girgiza kanta tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
cikin nuna kulawa da so Hajia Mama ta ƙara miƙo mata kofin tare da cewa.
“A a ɗiyata, amshi kisha, wannan al’adace ta masarautar Joɗa, dole in marabceki dashi.”
Kai ta kuma girgiza alamun ya isheta.
da sauri Umaymah ta matso kusa da ita tare da cewa.
“A a Shatu amshi kisha kinji ko?”.
Cike da mamaki ta ɗan kalli Umaymah ta gefen idonta.
jin Umaymah na ƙoƙarin matso da kofin kusa da itane yasa tayi mgna cikin ɗan ɗaga murya tace.
“Bana shan madarar”.
wani irin kallo mai cike da damuwa Hajia Mama tayi mata tare da cewa.
“Subahanallahi, bakya sha, kuma, amai yake sakine? Ƙa’idane da dole kishi”.
Ta ƙarishe mgnar cikin damuwa.
Ita dai Shatu shiru tayi idonta na bisa kofunan madarar.
Ummi ce ta matsota tare da cewa.
“Shatu amshi kisha koda kurɓa ɗaya ne”.
Cikin rawan murya tace.
“Bana sha”.
Jin alamun rawan murya irinta an takura mutum ne, yasa duk sukayi cirko-cirko suna kallon Madarar.
Zuwa can Hajja Mama ta sauƙe wani bahagon ajiyan zuciya, kana ta ɗauki ɗaya kofin ta miƙa Jabeer tare da cewa.
“To gashi kai kam kasha naka”.
Zamanshi ya ɗan gyara tare dasa hannun damansa ya amshi kofin.
Wani irin zaro ido Shatu tayi.
Kallon kofin takeyi tamkar zata maida kwayar idanunta cikin kofin.
duk jikinta tsuma yakeyi, wani irin masifeffen bugawa ƙirjinta yakeyi da ƙarfi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer zaune yake riƙe da kofin, ya fuskanci Hajia Mama da kyau.
Ita kuwa Hajia Mama hannunta tasa ta kamo ɗaya hannun Jabeer da baya riƙe da kofin.
Kana ta miƙowa Shatu hannun alamun ta miƙo mata hannunta.
Ƙara runsunar da kanta tayi tamkar bata gane me take nufiba.
Cikin murmushin Hajia Mama tace.
“Kawo hannunki ko ɗiyata”.
A hankali ta ƙara maida hannunta baya,
dai-dai lokacin kuma Jabeer ya ɗago kofin ya kai saitin bakinshi da niyar zai sha.
cikin hikima ta muskuta ta ƙara matsowa jikinshi da sauri ta ɗago hannunta kamar zata miƙawa Hajia Mama hannun.
sai kuma ta ɗan kaikaice, ta buge c…!

 

Ƙaƙa tsara ƙaƙaTa bugi kofin madarar, ba zato ba tsammani, Jabeer yaji kofin ya tsumbce mishi.
ya faɗi gefenshi.
Tass ya fashe madarar ta kwaranye a ƙasa.
Cikin sauri da tsuƙe fuskarshi ya juyo ya kalleta.
Itama ɗin shi take kallo.
Ido cikin ido sukayi da ita a karo na forko a rayuwarsa duk da yasan sun taɓa haɗuwa.
Kallon kwaɗayye mai irin bakin Junainah, tayi mishi.
Sai kuma ta janye ƙwayar idanunta cikin nashi da sauri.
Sabida wani irin kallon da taga yanayi manata.

Umaymah da Ummi kuwa, kallon junansu sukayi, cikin yanayin son gane ya akayi kofin ya faɗi dan basuga sanda ta ta ɗan buge mishi hannunta.

Hajia Mama kuwa cikin tashin hankali da kiɗima ta kalli Umaymah tare da cewa.
“Akwai matsala, ita batasha, shi nashi ya kwaɓe.”
Sai kuma ta maida dubanta ga Shatu cikin alamun damuwa tace kawo hannunki na dama.”
Still maida hannun nata tayi baya, ba tare da tace komaiba.
Ummi ce ta ɗanyi ƙasa da murya tare da cewa.
“Miƙa mata hannunki ku gaisa”.
Murya can ƙasa tace.
“Yana ciwo”. Ta ƙarishe mgnar da jin haushin kanta da ƙaryar da suka satayi.

Batool ce ta kalleta sama da ƙasa kana cikin gyatsine tace.
“Umaymah ai wannan ba irin matar Sheykh bac.”
Sai kuma ta haɗiye ragowar mgnar dan ganin wani irin kallon daya watsa mata na alamun.
Ki kama kanki da kiran sunana a bakinki.

Wani dogon ajiyan zuciya Hajia Mama ta sauƙe cikin fargaba tace.
“Tashi Kuje ku gaida sauran. Allah yayi muku al’barka ya baku zaman lafiya.
In sha Allah babu komai”.
Kamar jira Shatu takeyi a basu izinin tashi tayi fit ta miƙe.

Da tarin mamaki Umaymah da Ummi suka miƙe, dan abubuwan da suka faru da yanayin Shatu, ya tsaya musu a rai.
Shima Sheykh Jabeer miƙewa,
yayi kana suka jere suka fita.
Sai dai Shatu na ɗan sassarfa.

Cike da mamakin wannan abun suka nufi Side ɗin Gimbiya Saudatu.

A falonta suka sameta tana hakimce bisa kujerar ikonta,
ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana karkaɗa ƙafar cike da izza.

Ummi na gabansu suna bayanta Umaymah na bayansu.
Cikin rusunar da kai Jakadiyarsu ta durƙusa gefenta tare da cewa.
“Barka da safiya Gimbiya Saudatu, ga Sheykh Jabeer ya kawo miki da amaryarsa!”.
Cike da izza ta ɗan kallesu sama da ƙasa, kana ta nuna musu gabanta.
Alamun su zauna, cikin sanyi Shatu ta rusuna tare da sunkuyar da kai ta zauna gabanta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin kallo yayi mata, mai cike da ma’anoni,
gefen ta ya kalla inda wata kujerar ke kusa da tata komansu iri ɗaya.
Taku yayi cike da ƙasaita ya isa gaban kujerar, kana ya juyo ya zauna kan kujerar.
Hakan yasa ya fuskanci Shatu da Umaymah.
zaman ƙasaita da isa yayi.
wani mugun kallo take binshi dashi har ya zauna.
Ita kuwa Shatu kanta a duƙe tana murzam ƴan yatsunta.

Umaymah ce ta ɗan taho zata zauna kusa da ita, a hankali ya jujjuyawa Umaymah kai, alamun. A a kada ta zauna a ƙasa.
gane manufarsa ne, yasa ta zauna bisa kujera.

Shiru kakejin falon, sai takun sawun hadimanta dake kawo ababen motsa baki, suna ajiyewa gaban Shatu.

Suna gama jerawa suka koma can gefen.

Jin shiru-shirun yayi yawane yasa Shatu ɗan ɗago kwayar idanunta, ta kallesu.
A ranta take mgnar zuci.
“Ikon Allah, ohoho ni Shatu wannan wanne irin bahagon gidane, mai cike da sarƙaƙiya da tubkar baƙin zare,
To ko dai ita wannan ɗin kurmace.”
Muryar Gimbiya Saudatu ce ta ƙatse mata tunani ta,
cikin isa da izza ta kalli Sheykh Jabeer, kana ta juyo ta kalli Shatu, murya a daƙike tace.
“Bakiyi sa’an mijiba, yarinya duk da gashi kamar kinada nitsuwa”.
Ido Shatu ta jujjuya cikin hular al’kyabbar jikinta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, ko ta kan mgnar ta bai biba,
sabida ai dama ya tsammaci, hakan
kai ta juyo ta kalli Umaymah cikin ɗagawa tace.
“A buɗe min fuskar amaryar in ganta da kyau, inga wanne irin idone da ita”.
Bata rufe bakintaba taji yana cewa.
“Baza’a buɗe ba!.”
Murmushi Umaymah tayi sabida tsamar Sheykh Jabeer da Gimbiya Saudatu wani lokacin yadda kasan shi ubanta ne, haka yake mata mgna da yanke hukunci kai tsaye a karan kanta ma bare akan abinda ya shafeshi.
ita kuwa Shatu a hankali take juya ƙwayar idanunta, tana kallon sawun Gimbiya Saudatu.
cikin al’kyabbar ta ɗan juya idonta da kyau ta maidasu, kan kyawawan fararen sawun Sheykh, wanda suke tamkar ka taɓa jini yayi yo tsalle ya fito, sabida taushi da laushin fatar
Wanda duk mutun mai zama da al’wala da yawan karatun al’ƙur’ani tafin hannunshi da ƙafarshi sukanyi wani kala mai masifar kyau da ɗaukar hankali koda baƙin mutun ne sai fatar hannunshi dana ƙafarshi sunyi kyau na musamman, hakama kuma fatar jikinshi wannan shine baiyanennen darajar zama da al’wala da yawan ambaton Allah kenan.

Da ƙarfi ta rumtse idanunta tare da buɗe su.
kan babbar yatsar kafarshi ta zubawa ido, sosai da sosai.
wani ɗan zane baƙi mai suffar tafiyar maciji ta gani.
sai dai bata samu ganinshi ras yadda take soba, shiyasa taketa zare ido,
shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya ɗan turo ƙafar damanshi gaba.
Dan ya gyara zaman ɗayan a kanta.
Hakanne ya bawa Shatu damar zubawa yatsun nashi ido, suna nan zara-zara alamun mutum ne mai matsakaici tsawo.
Ras zanen bindin maciciyar nan yake kan babbar yatsarshi.
har zuwa bisa rumfar ƙafar kamar zanen dayis,
cikin tarin mamaki da al’ajabi take bin zanen da idanunta.
har inda igiyar takalminshi ya tsare zanen.
Wani irin sassanyan numfashi ta sauƙe a hankali.
sabida rashin ganin ƙarshen wannan zanen, da kuma inda ya nufa, da kuma ganin ya saman zanen yake.
Hankalinta kab ya tafi ga zanen shiyasa bata jin ta ƙaddamar da Gimbiya Saudatu ke zubawa ba.
Muryar ta taji da ɗan ƙarfi tana cewa.
“Bata da sunane? Ke me sunanki”.
Ta ɗago kai da nufin yin mgna kenan sai kuma tayi shiru.
jin Umaymah na cewa.
“Sai kisa mata naki sunan, ba sai kiji namu ba”.
A gyatsine ta kalli Umaymah kana, ta ɗan matso bakin kujerar,
hannu tasa ta ɗauki tupa cikin jerin ƴaƴan itatuwan da aka jera a gaban Shatu.
miƙa wa Shatu tayi tare da cewa.
“Kici kada ki tafi bakici komaiba,”.
A hankali tace.
“Alhamdulillah!”. Cikin sauri Gimbiya Saudatu tace.
“A ni ba’a zuwa sashina a tafi ba abinda akaci”.
Hannu ta miƙa ta amshi tupan kana ta riƙe shi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer miƙewa tsaye yayi alamun tafiya hakane yasa.
Suma suka miƙa suka fita.

Daga nan kai tsaye Side ɗin.
Baba Nasiru suka nufa.
A falo suka samu matarshi da yaranshi dama shi kanshi.
Bayan sun zaunane.
ya kallesu sama da ƙasa yace.
“Dama baku zauna ba, a hakama na ganku.
ba sai kun zauna ba”.
Cikin sanyi ƴarshi Jamila ta ɗanyi ƙasa da murya tare da cewa.
“Ayyah Baba ka barsu mu gaisa”.
Haɗe fuskarshi yayi sabida yasan irin masifeffen son da Jamila keyiwa Jabeer lokuta da dama, takanyi ta kuka in taji abubuwan da mahaifinta yakeyi mishi.
shi kuwa Sheykh Jabeer tuni ya zauna ya harɗe ƙafa,
Jamila kuwa cikin nitsuwa ta gaidasu kana.
Ta kawo musu abin sha,
Ummanta ku ko kallo Bata ishesuba yadda itama bata lallesu ba.

Haka dai suka fita suka tafi.
gidan Baba Basiru kuwa suna shiga ya tashi ya bar musu wojen.

Daga nan suka shiga gidan Barrister Kamal
Baba Kamal kenan.

Yana ganinsu ya tashi ya ruggume Sheykh tare da cewa.
“Masha Allah, Alhamdulillah yau dai Allah ya nuna min ɗana da matarsa”.
Zama sukayi bayan sun gaisane yayi musu addu’o’in al’khairi.
Daga gidanshi gidan Dr Aliyu sukaje,
wanda yake mutun mai mutunci da kamar Barrister Kamal.
Sosai suka jima a sashinsa,
yayi musu addu’o’in da sanya al’khairi da al’barka.

Daga nan kuma sai Sashin Mom tsakar gidan Abbanshi.
Maman Imran, ba yabo ba fallasa ta amsa musu.
Daga nan wurin Amryar Abbansu sukaje, wanda suka sameshi a can.

Daga nan sukaje gidan Ya Hashim da sauran ƴan bappanunsu.
Gida na ƙarshe dai gidan Aunty Juwairiyya ne, can suka samu Hibba da Ya Jafar.
Bayan sun gaisane,
Umaymah ta ɗan matso kusa da ita cikin sauƙe numfashin gajiya tace.
“Ɗago kanki Shatu kinga nan ƙofar Aunty Juwairiyya ce, ga mijinta shine babban yayan Jabeer, kuma yanada matsalar ƙwoƙolwa.
Yanzu daga nan Side ɗinkin zamu wuce, wanda yana nan kusa da nasun. Sai gefen nakun kuma nasu Jalal ne.”
A hankali ta ɗago kanta ta kalli Ya Jafar, yana riƙe da hannun Jabeer yana karatun shi a hankali.
Cikin sanyi tace.
“Ina kwana yaya!”.
Kafaɗarta Umaymah ta dafa tare da cewa.
“Baya mgnar komai a duniya inba karatuba, sai dai yanajin komai kuma yana gane komai in an gaya mishi amman fa baya mgna kam in ba karatuba.”
Cikin tsananin rauni da tausayawa,
idonta cike da ƙwalla tace.
“Allah sarki, Allah ya bashi lfy”.
Karon forko kenan tunda suko fito dashi taji ya amsa addu’a duk da tarin addu’o’in da akayi ta musu sai yanzu taji yace.
“Amin ya Allah”. Hakama Umaymah da Jakadiyarsu da Hibba sai dai duk ya riga su amsawa.
A hankali take ɗan satan kallonshi a fakaice.

Hibba ce ta janye mata hankali da cewa.
“Aunty Shatu kin gaji kam. muje ki huta, gashi azahar ta kusa ma.”
Ɗan guntun murmushi tayi tare da cewa.
“Uhum”.
Umaymah ce ta miƙe ita da Ummi kana sukace.
Taso mu tafi, yanzu Hibba zata cikaki dan zance.”
Cikin murmushi Aunty Juwairiyya tace.
“Ayyah Umaymah ku bar mana ita mana”.
Ummi ce tace.
“Lokacin sallafa ya ƙara to”.
“Hakane kam”. Juwairiyya tace tare da ɗaukar Foodflaks dake kan dinning table, tabi bayansu tana cewa.
“Hibba ɗauko sauran!”.
To tace kana ta suggumi sauran tabi bayansu.

Nan suka bar Jabeer da Ya Jafar ɗin.

A babban falon suka zauna.
Aunty Juwairiyya da Hibba suka ajiye Foodflaks ɗin bisa Dinning table,
kana suka dawo tsakiyar falon.
Umaymah ce ta miƙe tare da kallon Shatu, tace.
“Taso mushiga ciki, kiga tsarin wurin naku”.
Miƙewa tayi cikin alamun gajiya, domin zagaye masarautar Joɗa babban aikine mai zaman kanshi. Donma su sun saba, ita kuma bafulatanar dajine tafiya baya bamu tsoro.
Bayan Umaymah tabi, ta gefen Dinning area ta ɗan ratsa da ita,
Suka shiga cikin kitchen, juyowa tayi ta kallesu Ita da Hibba,
“Nan shine babban kitchen ɗin ki, dake babban falonki.
Shine wanda in kinada aiki mai yawa, kamar na salla ko azumi, ko zakiyi ki aikawa surakanki.
Hadimai zasu iya shigowa su tayaki.”
cikin fahimta tace.
“Toh”. Hibba ce ta ɗan ƙara so shigowa ciki tare da cewa.
“Kai wanga kitchen badai girmaba, gashi komai a tsare gonin kyau. Kalarsa green and white komai na ciki gwanin kyau”.
Murmushi suka ɗan yi kana, Umaymah ta juya dasu.
Daga nan cikin kitchen ɗin ta gefen dama akwai wata ƙofar da sai ka hau stpes huɗu.
A gefen ƙofarne wani datsetstsen Fridge mai girma yake kwance.
Haurawa sukayi kana Umaymah ta tura ƙofar ta shiga.
Store ne mai zaman kanshi.
akwai komai na buƙatar rayuwa, sai dai ba mai yawa bane.
Shatu ta ɗan kalla tare da cewa.
“Ga kuma store ɗinki. Nan za’a ke aje miki duk wani abun buƙata”.
Kai ta gyaɗa, kana suka fito.
Wata ƙofar daketa hannun hagu ta nuna mata suna buɗe wa suka fito.
Sai gasu bisa wata baranɗa mai girma, kana can ƙasan barandar fulawine da kuma pompona ke jere iya ganinka,
Daga sama kuma igiyoyin shanya ne da a ƙalla sun kai huɗu.
sai saman barandar kuwa, injin wanki ne.
Nan dai ta nuna mata komai na wurin kana suka dawo cikin gida.

Suna shigowa falo. Sheykh na shigowa.
A nitse yake taku, kanshi na sunkuye yana kallon wayarshi da yake lallatsawa.
Umaymah ce ta ɗan bi bayanshi tare da cewa.
“Zo nan Shatu”.
Cikin zuba bayansu ido. Ta ɗan gyaɗa kai, tare da taka sawunta a hankali tabisu.
Hibba kuwa gefen Aunty Juwairiyya ta zauna.
Shi kuwa yana shiga falon nashi, ya juyo ya ɗan kalli Umaymah cikin kwaɓe fuska yace.
“Umaymah, Dan Allah ni bana son ana shigomin da wasu ababen cikin Side na, bare rayuwata, me wancan abun da kika kira zaizo yi anan?”.
Ido ta kafeshi dasu hakane, yasa yayi ƙasa da kanshi.
tare da shigewa bedroom yana cewa.
“Dan Allah iya kar abun can falo”.
Ƙeyanshi Umaymah ta zubawa ido.
“Wato ma wai wancan abun, lallai ma Jazlaan”.
Juyawa tayi ta ɗan leƙo a corridor ta hangota, murmushi tayi tare da cewa.
“Taho mana”.
Kai ta kuma gyaɗawa tare da ƙara saurinta tafiyarta a hankali.

Suna shiga falon, tayi wani irin ɓoyeyyen ajiyan zuciya mai sanyi,
sabida wani irin masifeffen sanyi mai gauraye da ƙamshi mai ɗan karen daɗi da taji ya bugu jiki da zuciyarta.
lumshe idonta tayi, kana ta buɗe su a hankali jin Umaymah na ce mata.
“Nan falonshi ne, namusamman ba kowa ke shigo mishi wurin kai tsaye ba.
dan ko Juwairiyya bata shigo mishi nan, kana akwai ƙannenshi ƴan uba maza da kuma Jalal basa shigo mishi nan.
Jamil kan shiga in baya nan in zai dawo shikeyi mishi shara da gyaran wurin.
Jalal kuwa yakan iya shekara ƙafarshi bata tako nanba.
Sai kuma Ya Jafar ɗin sa, shi kam bashi da hijabi da Side ɗin Jabeer, yakan shiga har cikin Bedroom nashi wani zubin har bathroom.
Sai kuma Haroon da Ibrahim su dama, dan su yasa aka gina sama wai masauƙinsu in sunxo.
To ammanfa in sunzo a ɗakinshi suke ko motsi zasuyi tare zasuyishi.

Sai kuma yayan Hibba, Hibbab shi na hannun damanshi ne.

Dan haka daga yanzu in dai yayi tafiya kece, zakiyi aikin da Jamil keyi”.
A hankali tace “to”.
Haura step ɗin Dinning area ɗin shi dake falon wanda akayiwa ƙawanya da wani irin labule mai masifar kyau.
Labulen ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu kama dana Daimond. wasu farare wasu Sky blue wasu Royal blue. suna da wani irin haske mai wal-wal. Cikinsa kuma.
Wani badaidaicin Dinning table ne mai kujeru shida nan uku nanma uku sai wani fridge ma daidaici. Gefensa show glass ne mai kyau wanda yake ɗauke da cups and plates and spoons and forks Mug. Da dai sauran ƙananan abeben buƙata.
sai woshing hand Baby, dake liƙe a can gefe.

sosai tsaruwan wurin yayi kyau, komai Sky blue and white. Abun sai ya zama kamar a duniyar taurarin yake yadda walwalin ke haska ko ina.
Falon kuma yanada ɗan karen duhu, domin saida Umaymah ta kunna musu wuta.

Bedroom nashi ta nuna mata da yatsa.
“Ga makwancinsa, sai kuma wancan ɗakin shi ba mai kwana a cikin ɗakine na musamman babu mai shiga ciki sai shi ni Lamiɗo Galadima, domin ɗakin aikinshi ne”.
Ita dai da to take bin Umaymah, sabida sanyin falon yana gab da sata kuka.
Allah ya sani bata son sanyi ko kaɗan. Ta kuma lura su kuma mayun sanyi ne.

Falon suka fito. Nan dai suka samu su Hibba nata hira da Ummi.
Side ɗin ta suka nufa.
Cikin kula tace.
“Ga Side ɗinki ga falonki ga kitchen ɗinki.”
Ta ƙarishe mgnar suna shiga kitchen ɗin. A hankali take kallon komai na Kitchen ɗin kalarsa Pink and white. Sosai tsarin wurin yayi kyau.
daga nan Dinning area Suka shiga ta nuna mata kana suka fito falon.
Suka shiga bedroom ɗinta komai ya tsaru.
Kuma komai sabone fil gwanin burgewa.
juyawa Umaymah tayi tare da cewa.
“Wancan ɗakin kuma masauƙi nane in nazo.”
Cikin ɗan murmushi tace.
“Ayyah”. Ƙofar Bathroom Umaymah ta nuna mata tare da cewa.
“Azahar tayi shiga kiyi al’wala kiyi salla sai kizo muyi Lunch”.
to tace kana Umaymah ta juya ta fita.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, yana shiga ya maida ƙofar Bedroom ɗin ya rufe shiyasa Umaymah bata gwada shiga da itaba.

Shi kuwa bathroom ya wuce wonka da al’wala yayi, ya sauya kaya. Kana ya fito cikin shigarsa ta musamman ya nufi. Masallaci.

Koda sukayi salla suka fito.
Falon ganin bata fito bane yasa, Umaymah cewa Hibba.
“Jeki kiramin ɗiyata”. Da sauri Hibba ta juya ta nufi ɗakinta.
Kwance ta sameta bisa sallayar da tayi salla, ta kife kanta cikin hijabin jikin nata,
bisa dukkan alamu kuka takeyi.
jin shigowar Hibba ne yasa tayi saurin share hawayenta,
tare da juyowa,
cikin mamaki Hibba ta zuba mata ido.
A hankali tace.
“Aunty Shatu meya sameki kike kuka”.
Murmushin ƙarfin hali ta ƙaƙalo tare da cewa.
“Kuka kuma Hibba”.
Cikin sauri tace.
“Eh mana gashi idonki yayi ja”.
Miƙewa zaune tayi da kyau cikin sanyi tace.
“No bacci na fara, shiyasa kikaga hakan”.
Kai Hibba ta gyaɗa kana tace.
“To taso mu tafi falo Umaymah tace kizo muyi Lunch”.
Hannu tasa ta ɗan shafa cikinta tare da cewa.
“Kamar na ƙoshi fa”.
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
“Tab ai Wlh taso kawai mu tafi, dan Umsymah bazata barki bakici abinci ba”.
To tace kana ta miƙe ta ninke sallayan. Sabida gajiya ne da bege da kewar yan uwanta ne ya sata kuka da kuma jin yunwar ta mutu a cikinta.

Suna fitowa su Umaymah duk suka miƙa, Dinning area suka nufa.

Bayan duk sun zaunane, Ummi, ta miƙe da nufin saka musu abincin.
Da sauri Aunty Juwairiyya ta miƙe tare da cewa.
“A a Ummi ki huta bari in saka mana”.
Foodflaks ɗin dake kusa da ita ta ture tare da jawo wanda suka shigo dasu.
Ummi ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
“Ya kika ture wancan?”.
Baki ta ɗan taɓe tare da cewa.
“Uhummm wai fa Gimbiya Saudatu ce, ta turowa amarya abinci dan salon munafurci”.
Wani irin kallon ƙasa-ƙasa Shatu tayi mata tare da zuwa abincin data buɗe ido, cikin mgnar zuciya take cewa.
“Uhumm wai zata cewa wata muna fuka, muguwa Itan ko meye sunanta!?”.
Sai kuma ta kalli Umaymah jin tana cewa Juwairiyya.
“Ni zubo min na gidan Hajia Mama naga tuƙeƙƙen tuwone da biyar zogale”.
To Aunty Juwairiyya tace kana ta zuba mata.
da sauri Shatu ta ɗan kalli Umaymah lokacin da aka saka mata mal-malan tuwon farar ɗanyar shinkafa,
tare da miyar a side sup.

Sai kuma ta juyo ta kalli Hibba da Ummi da tuni sun ja plate ɗin da Aunty Juwairiyya ta saka musu. Couscous and vegetables sup, mai ɗan karen kyau da ƙamshi.

Da sauri ta jujjuya kanta lokacin da Aunty Juwairiyya ta turo mata na plate ɗin gabanta, cikin sanyi tace.
“La da baki saminba”. Da mamaki Umaymah tace.
“Sabida me?”. Sunkuyar da kanta tayi tana tunanin.
suma ta yaya zata hanasu cin abincin. jin Ummi ta kuma mata tambayar da Umaymah tayi matane yasa ta ɗan kallesu.
Ta buɗe baki zatayi mgnar kenan.
Sheykh ya shigo da sallama, a bakisa.
kusan a tare, suka amsa masa.
A fakaice ya ɗan kalli Aunty Juwairiyya kana yace.
“Kije ki bawa Ya Jafar mgninshi”.
To tace tare da miƙewa da sauri ta fita.
Ita kuwa Shatu, wata nannauyan ajiyar zuciya ta sauƙe.
Kana tasa hannunta ta ture plate ɗin gaban Umaymah tare da jawo na gaban Ummi da Hibba,
Ido suka zuba mata cike da mamaki.
Ita kuwa cikin sanyi ta kallesu tare da cewa.
“Dan Allah kada kuci wannan abincin.
Kuci wancan ne”.
Jabeer dake ƙoƙarin shigewa falonshi ne, a ranshi yace.
“Uhumm lallai kam wannan abun wato itace ma zata zaɓa musu abinda zasuci”.

Hibba kuwa da sauri tace.
“Aunty Shatu abincin gidan Gimbiya Saudatu fa kike cewa muci.”
Ganin kallon mamaki da tuhuma da Umaymah da Ummi keyi matane yasata yin ƙasa da kanta cikin jin tausayinsu a ranta tace.
“To in bazaku cishiba, Umaymah bari ni in shiga kitchen nida Hibba yanzu zan girka muku duk abinda kukeso”.
Ko inda suke Sheykh Jabeer da yanzu ya fito zai wuce baiba, yacewa Umaymah.
“Zan fita”.
Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
“Allah kiyaye hanya, ya bada Sa’a”.
Amin Amin yace, hakama Ummi tai mishi addu’a.

Ita kuwa Shatu kanta na sunkuye,
Umaymah ce ta ɗan kalleta cikin nazartan yanayin ta, da yin tunani hakafa ɗazuma taƙi shan madarar Barka da shigowa masarautar Joɗa da Hajia Mama ta bata,
ta kuma amshi tuppar da Gimbiya Saudatu ta bata,
yanzu kuma tace kada suci abinci Juwairiyya.
Wannan abun shi yafi komai tsayawa Umaymah a rai.
Yaya daga shigowarta zata kasabto wasu hasashen a ƙwaƙwalensu.

Kai ta jinjina tare da cewa.
“Hibba sa mana abincin Gimbiya Saudatu, muci”.
Jin hajane yasa Shatu jawo Foodflaks ɗin ta fara saka musu.
Ita kuwa Hibba ta kwashe plate ɗin da Juwairiyya tasa musu ta kaisu kitchen.

Nan sukaci abincin kowa da abinda ke ransa.

Ita Shatu bataci na kirki bama.
Sabida ta lura da kallon da Umaymah keyi mata kamar da tuhuma.

Suna gamawa suka tattare wurin ita da Hibba.
tuni su Umaymah kuwa suna falon.

Suna gamawa suka fito falo.
da sauri ta kamo hannun Hibba suka wuce falonta har bedroom ɗinta.

Suna shiga Haroon, Jamil, suka shigo.
Shigarsu ba jimawa Jalal ma ya shigo.
Nan sukayi ta hira.
to ganin yanzu ta shigane yasa Umaymah bata kirata dan tazo taga ƙannen mijin mataba.

Suko. Suna cin abinci suka fita sabida kiran sallan la’asar,
daga nan kuma basu kuma shigowa falonba sai kusa goma na dare kafin nan kuwa tuni Shatu da Hibba sunyi bacci ma.

Washe gari ranar Laraba, da safe.
Aunty Juwairiyya ta shirya musu breakfast kamar yadda ta saba, koda su Umaymah basa nan, abincin Sheykh a sashinta yake duk da ma, yakan iya wata biyar baisa abincin nata a bakinshi ba.
sai dai Ummi Jakadiyarsu ta ɗan dafa mishi irin ababen da yafi so yaci lokuta da dama kuma na rayuwarshi da Lamiɗo yake cin abinci a Side ɗin kakarsa Gimbiya Aminatu shiyasa bai fiye cin wanda ake kawowa sashinsa ba.
Jalal Jamil Ummin suke cin wannan abincin.
To sashin Hajia Mama kullum za’a kawo Side ɗin shi.
Hakama gidan Barrister Kamal da Dr Aliyu yawanci suma sunasa ana kawo mishi.
kana gidan Baba Nasiru ma,
yawanci ana kawowa.
Especially kamar yanzu da su Umaymah ke nan.

To yauma haka abin yake tako ina an kawo musu breakfast, na maraba da zuwan amarya.

Koda suka zauna cin abinci.
Kamar jiya da dare, haka yauma Shatu ta ɗan kalli Aunty Juwairiyya cikin hikima tace.
“Aunty Juwairiyya asaka mana na gidan Gimbiya Aminatu”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Wato kema irin mijin nakine, kuna son girkin Gimbiya, kunsan nata yafi naku na zamani daɗi da lfy”.
Murmushi Shatu tayi cikin jin sanyi da daɗin basu fahimci manufarta ba.

Sun fara ci kenan.
Jalal Jamil suka shigo.

Dama Haroon, Ya Jafar, oga Sheykh Jabeer suna falonshi.
can Ummi ta kai musu nasu karin.

Cikin murmushin Umaymah tace.
“Yauwa Jalal kuzo nan, kuga Aunty Amaryankun.”
Matsowa gefenta Jalal yayi tare da kallon Shatu a fakaice kana yace.
“Uhumm aini na santa, taje ta tasa min ɗan uwa gaba har cikin Office dinshi tana mishi ihu a kai”.
Cikin sauri ta ɗan kalleshi tabbas ta ganeshi ta kuma tunashi Umaymah ta ɗan kalla tare da cewa.
“Sherri ne, Umaymah ni banyi ihuba”.
Murmushi Jamil yayi tare da cewa.
“Eh ai ba ihun kukaba, shi da mijin naki duk bauɗaɗɗun mutanene, da zaran kin ɗan yi musu mgna da murya a sama to cewa sukeyi, wai kayi musu ihu”.
Ya ƙarishe mgnar yana kallon corridor fitowa falonshi.
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
“Ga baki ga tsoro”.
Aunty Juwairiyya ce ta nuna musu wurin zama tare da fara zuba musu abincin.
Ita kuwa Shatu murmushi kawai ta ɗan yi, sai taji hawaye na neman cika mata ido.
Zamansu hakan ya tuna mata yayunta, ko ina suke? Wani hali suke ciki? Ko ya jikin Ummeynta? Ya Junainah keyi da kewarsu.
Ba ya Lado, Babu Ya Gaini, Babu Ya Seyo, babu Ya Giɗi, sannan nima an kawoni nan an cusani cikin wani irin bahagon gida mai wuyar ganewa”.
A hankali tasa tafin hannunta tana share hawayenta cikin hikima.
Ɗan juyowa tayi ta kalli. Umaymah dake cemata.
“Shatu, ga Jalal da Jamil tagwaye ne, sune ƙannen Sheykh Jabeer da suke binshi
yanada wasu ƙannen Affan baya ƙasar.
Sai Imran ɗan amaryar Hajia Mama mom.
sai kuma yayunsu mata, kin san su ai ko? Rumaisa da Rumana”.
A hankali ta gyaɗa kai alamar eh.
Ita kuwa Umaymah su Jalal ta kalla tare da cewa.
“Ga Auntyn ku, matar Hammanku”.
Jamil ne ya ɗan yi dariya tare da cewa.
“Allah ya ɗaiyiba”.
Murmushi sukayi tare da cewa.
“Amin Amin.”

Nan dai sukaci sukasha kana suka dawo falon.

Kamar jiya haka yauma suka wuni.

Umaymah da Ummi na yawan yi mata dukkan bayanin komai na Side ɗinta.

Washe gari ranar. Al’hamis, da yamma taja Hibba suka koma falonta.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Yauwa Hibba sammin wayarki.
Wallahi na nemi tawa har na gaji ban ganiba tun a Side ɗin Gimbiya Aminatu”.
Da sauri Hibba tace.
“Dama kinada wayane? Kuma ya ɓata baki faɗawa Umaymah”.
Da sauri ta jawo hannun Hibba tare da cewa.
“Ina zakije?.”
“Zanje in gayawa Umaymah mana”.
Ta bata amsa tana cire code ɗin wayarta-ta tare da miƙa matashi, da sauri tace.
“A a ki bari ke dai bani aron taki bari in kira Bappa na”.
Ajiye mata wayar tayi bisa cinyarta kana ta wuce ta fita.
Ita kuwa Shatu, da ido ta rakata, jin tana ta rabkawa Umaymah Kira tun kafin ta fita.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare dasa hannun ta ɗauki wayar.

Jujjuya wayar tayi tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗinta.
Number Bappa ta saka, kana kirashi.
tare da kara wayar a kunne mugu ɗaya ana biyu, aka amsa kiran.
Wani irin murmushi tayi jin muryar Junainah tana cewa.
“Bappa! Bappa ga wayarka ana kiranka”.
Da sauri tace.
“Ƙanwaliya”.
Cikin wani irin mamaki da jin daɗin Junainah tace.
“Laaaaah Adda Shatu, kece? Ina kike? Adda Rafi’a tazo jiya wai tana neman wayarki baya shiga, Bappa yace mata ai anyi miki aure, taita kuka tace to ya batun karatunki,
Bappa ma ya nemi number ki baya shiga.
Ina kika ajiye wayar ne to Adda Shatu”.
Cikin sanyi tace.
“Wayar ta ɓata ne Junainah”.
Cikin tura baki tace.
“To mijinki ya saya miki mana”.
Ido ta lumshe tare da cewa.
“Ina Ummey na? Ya jikinta?”.
Cikin sauri tace.
“Ummey tana na Kitchen, yanzu jikinta da sauƙi tana mgna kaɗan-kaɗan, ko ɗazuma itace tace.
“Bappa ya kira mata ke!.”
Cikin tsananin jin daɗi tace.
“Alhamdulillah, kai mata wayar”.
Da sauri ya juya ta nufi kitchen tana cewa.
“Ummey! Ummey ga Adda Shatuna”.
Da sauri Ummey ta fito, ta amshi wayar.
Cikin murya mai cike da sanyi tace.
“Aysha na!”.
“Wasu zafafan hawayene, suka zubo mata,
Cikin rawan murya tace.
“Na’am Ummey na! Ya jikinki?”.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Jiki da sauƙi, Shatu yaushe zaki zo?”.

Bappa da yanzu ya iso daga rakiyar da yayiwa Rafi’a ne, yayi murmushi tare da cewa.
“Bani wayar nan”.
A hankali cikin girmamawa ta miƙa mishi wayar.
Shi kuwa amsa yayi tare da karawa a kunne.
jin muryar bappa yanayi mata sallama ne yasata jin sabbin hawaye masu masifar ɗumi, sabida tausayinshi.
Duk da tsufanshi mugayen ƙabilar ɓachama basu barshiba, sun kashe mishi babban ɗan shi.
Kana sun tafi da uku, sun barshi cikin zulumin suna raye ne ko sun mutu? A ina suke? Me akayi musu? Me sukeyi? Sannan itama data rage anyi mata wani irin bahagon auren da yafi kama da na mulkin mallaka.
Muryarsace ta katse mata mgnar zuci da takeyi da cewa.
“Shatu kina Lfy ko?”.
Murya na rawa tace.
“Lfy lau Bappa, amman bana jin daɗin gidan, ina kewarku, ya jikin Ummey na? Ya lbrinsu su Ya Gaini an samu wani lbrin ko har yanzu shiru? Ya Ba’ana bai muku komai bako? Ya tafi ne ko yana nan?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“To Shatu wacce tamɓaya ɗaya zan amsa miki’.
Tana kuka tace.
“Duka”.
Cikin hikima da jinƙai irin na iyaye yace.
“To sai kinyi shiru kin dena kuka”.
Da sauri tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa.
“Na bari”.
Taku biyu yayi zuwa uku kana yace mata.
“Ba’ana bai mana komaiba! Ya gudu ya bar ƙasar ma baki ɗaya! Jikin Ummey ki da sauƙi sosai! Su ya Giɗi munata addu’a in Sha Allah, in Allah ya yarda zasu baiyana garemu da izinin ubangiji.
Kafuran nan kuma mun rigada mun karya ƙarfi su yanzu bazasu sake samun damar cutar da muba, in Sha Allah munfi ƙarfi su.”
Sai kuma ya ɗan tsagaita jin, tana murmushi mai ɗan sauti alamun jin daɗi,
a hankali yaci gaba da cewa.
“Rafi’a tazo, nayi mata bayanin komai, kuma in ta dawo zata zo, in an barta zata shigo”.
Da sauri tace.
“Zan gayawa Ummi ta sanarwa sarkin ƙofa in tazo a barta ta shigo”.
Cikin danne ainihin tarin ƙunar watsewar gidanshi yace.
“Yauwa to haka zakiyi.
Sannan in sunƙi yarda kada ki damu.
Umarnine gareki, kibi dukkan umarnin mijinki, kiyi mishi biyayya a cikin dukkan lamuranshi nasan bazai saki mugun abuba, kada ki saɓawa umarninshi.
Kada kiyi komai saida amincewarsa.
Ki kasance mai kula da lamuran rayuwarsa kada ki bar wani abun cutarwa tare dashi.
Yanzu shine gatanki. Shine madadin Giɗi, Ganin, Seyo, Lado, ƙannenshi mata ki kallesu tamkar Junainah, mahaifiyarshi ki kalleta kamar Ummeynki, yan uwan mahaifiyarshi ki kallesu kamar yadda kike kallon innarku, yanzu sune ƴan uwanki.
Domin naki basa kusa Ki zama GARKUWAR sa”.
Shiru yayi jin kuka na son kubce mishi.
Ita kuwa tuni hawaye na kwaranya daga cikin manyan idanunta.
Cikin sanyi yace.
“Gobe zamu tafi, lardinmu, zamu koma can na wani lokaci”.
Wani irin tsananin razana da tsoro ta zaro ido tare da cewa.
“Bappa zaku tafi Kardi kuma!? Ni ku barni a nan ba kowa nawa!?”.
Cikin sanyi yace.
“Zamu dawo Shatu. Donke zamu dawo.
Dole muje, in sanarwa iyayen innarku abinda ya faru da ita da yaranta.
In kuma gayawa yan uwana halin da nake ciki a kan ɓatan yayunki, bayan salla zamu dawo. Can zamuyi azumi. Bakiga yanzu a nan ko tinkiya ba’a bar manaba”.
Cikin gamsuwa da zancen Bappa ta ɗan danne shessheƙan kuka tare da cewa.
“Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy. Amman Bappa ku barmin Junainah mana, a kawo min ita mana in samu iƴar uwa kusa dani”.
Cikin tausasamata zuciya yace.
“Kada ki damu, su nan bazasu barki da maraiciba.
Sai mun dawo zan kawo miki Junainah da kaina”.
Kit kiran ya ƙatse sabida kuɗin sun ƙare.
Hibba da tun ɗazu ta shigo tana gefenta ne,
ta ɗan kalleta cikin sanyi tace.
“Aunty Shatu, meyasa kikace bakya jin daɗin zama a gidan nan? Munayi miki wani abune?”.
Cikin zubda hawaye ta jujjuya mata kai.
Hibba bazata fahimci halin da take ciki ba, bazata gane matsalar rayuwarta ba.
Ita kuwa Hibba cikin sanyi tace.
“Aunty Shatu nima ƙanwarki ce, duk abinda zakisa Junainah tayi miki nima kisani zan miki kinji ko”.
Cikin share hawayenta tace.
“To Hibba ngd”.
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
“Yauwa kuma Umaymah ta aika Ya Jamil ya sayo miki sabuwar waya iPhone”.
Cikin sanyi da son tsaida hawayenta tace.
“Ngd”.

Haka yammacin ranar ta yishi a bedroom ɗin ta.
Sai Hibba dake ɗebe mata kewa ne.
Da Umaymah taga basu fito bane itama taje.

Washe Gari yau Jumma’a, kuma yaune ta cika sati ɗaya cib a gida.
Kuma tunda yazo gidan sau uku taga Sheykh Jabeer, tun randa ya wucesu, suna batun abinci bata sake ganinshi ba, koda a gilme ne.
Yanzu ta saba da Umaymah Sosai hakama Ummi
Ita da Hibba kuwa shaƙuwa ta fara ƙarfi a tsakaninsu.
Tana jin Hibba kamar Junainah.
Jamil da Jalal Haroon suna ɗan zama asha hira dasu.
Yau ne kuma Haroon zai tafi Leddi julɓe, sabida yayi masifar kewan Jannart ɗin shi, wacce taƙe ƙanwace ga Aunty Juwairiyya, kuma ƙawance ga Ibrahim.

Ƙarfe ɗaya dai-dai, Sheykh Jabeer, ne tsaye gaban dreesing mirror yana fesa turare bayan ya gama shirin jummarsa tsab.
Yau shigar baƙar Al’kebbar da farar jallabiya yayi.
Yayi wani irin kyau mai cike da sheƙi.
Kusan a tare suka jero da Haroon wanda yake cikin shigar ƙananan kaya.

Su kuwa suna falon suna, zaune.

Jamil da Jalal da Ya Jafar kuwa suna tsaye alamun fitowar Sheykh suke jira.

A hankali Shatu ta ɗan ɗago kanta jin wani irin masifeffen ƙamshi mai daɗin shaƙa.

Da sauri ta janye ƙwayar idanunta,
Sabida idonta da suka faɗa cikin ƙwayar idanunshi.
Wanda shi kuwa Jalal yake kallo ganin wani shegen wondo wai shi crezi ne ko meye ne oho, duk yana ɓuɓɓule har kana iya ganin farar fatar cinyarsa.
ga saɓulellen wonɗo ga kafurin aski.
fuskarshi ya tsuke tare da jan gajeren tsaki wanda shiyasa Jalal juyawa, ya nufi hanyar fita yana cewa.
“To Ni banifa da manyan kayan nan, yanzu bari inje in duba ko inada jallabiya sai in saka a kai zan biyoku daga baya.”
Da ido suka bishi. Haroon da Jamil kuwa murmushi sukayi.
A haka suka fita suka tafi. Har sunje bakin ƙofar fita ba tare da ya juyoba yace.
“Umaymah ku tashi lokacin salla yayi”. Ya ƙarishe mgnar suna fita
To tace.

Kana suma su Ummi suka nufi ɗakinsu.
Aunty Juwairiyya kuma ta wuce Side ɗinta.

Ita kuwa Shatu da Hibba suka tafi ɗalinta.
Hibba ce ta fara shiga tayi al’wala.
Sannan itama Shatu ta shiga.

Tana fitowa daga bathroom ɗin tayi wani irin….!

 

Uhummmmmm tuni mun gama shimfiɗan lbrin GARKUWA yanzu dai muna cikene dumu-dumu .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button