Garkuwa Hausa NovelHausa Novels

Garkuwa 38

Sponsored Links

Da Mamaki kwallo a maƙabarta.
Wato dai haka za a cigaba da gwara kawunan mutanen. Masarautar Joɗa ana mayar da su marasa tunani?”.
Gimbiya Saudatu Ta faɗa tana ya mutsa fuska don ta kasa kallon ƙwayar idon Sheykh.
Banza ya yi da ita duk da ya waiwayo ya kalleta, ya so tanka mata, amman sai ya share yaci gaba da takunshi cikin nitsuwa yana tafe yana tasbihi.
A hankali ya isa falon.

Kanshi ya ɗan juyo ya kalli tsakiyar falon.
Sam bai hango Shatu da Ummi ba dake zaune a falon.
A nitse ya maida kanshi ga inda ya nufa ya juya zai shiga corridor’n da zai sadashi da falonshi. “Ba ka ji me nace bane? Dutse ne kai ko waliy? Wata da watanni a kawo maka mace a ce sai yau ake bada kyautar budurci dan rainin wayo tuntuni kallon hoto kake mata ko me.
Ba ma wannan ba, wanne irin munafurci ne ya sa aka bada kyautar dawakai amarya da ango? Duk yana cikin sahun munafurcin da boye-boyen..”
Cikin tsawa ya dakatar da ita da cewa.
“Bana son shirme fa! Fitar min a gida tunda ba wancan tsohon ne ya gina min shiba”.
Da sauri tace.
“Zan fice ba sai ka koreni ba.”
Ta ƙarashe mgnar cikin tsananin takaicin tsawar da ya yi mata don sai da hantar cikinta ta kaɗa.
A dake ta jujjuya idanuwanta tare da cewa.
“To wai ɗaga Muryar na meye ne? Tambaya fa kawai nayi nake son amsa.
Wannan sarƙar kuma ta mece ce? Ta asalince wacce ta ɓace ɓat ko in ce ta yi ɓatan-dabo, ko kuma wata ce ta dabam aka ƙirƙiro, don nasan waccer dai bata kai labari ba, daga wuyan waccer ts…”
Bai bari ta cigaba ba ya tare ta da muryarsa a nutse cikin iya sarrafa harshe, ya lumshe idonshi kana ya buɗesu a hankali yace.
“Dakata, tsaya kiji.”
Da sauri tace.
“Uhum ina jinka”.
Rausayar da kanshi yayi kana a hankali yace.
“Kyauta ce ta girmamawa, wacce ba kowacce mahaluƙiya ce take katari da irinta ba a cikin Masarautar Joɗa, duk da kyautar ta yi kaɗan a wajen wacce ta cancanci ninkin hakan, bana ji akwai abinda za a iya biyan macen ƙwarai da abun duniya ba ko da kuwa za a bata kujerar masarautar Joda wanda wasu wayayan mazaunan cikinta ke wawasun nema ba. Darajarta da kimar kyautar data bada yafi ƙarfin tukuicin da masararutar Joɗa ke badawa, ita ba irinku bace ta wuce hakan”.

Shiru Ummi tayi tana mai jin kalamanshi tare da yin wani sassanyan murmushi.

Related Articles

Ita kuwa Aysha a hankali ta lumshe idonunta tanajin kalamanshi masu sanyi da sanyaya zuciya.

Gimbiya Saudatu kuwa. Wani irin baƙin ciki ne ya turniƙe ta, da kyar ta iya saita numfashinta cikin karkarwar jiki da rasa abin cewa ta ce, “Wannan wanne irin yabo ne haka har sai ka haɗa da sarautar gidan nan?”
Yanayin ta ya kalla ya yi Murmushi, wanda ya ƙara tunzirata kana a nitse yace.
“Dan na tabbatar miki da ƙimarta da darajarta ne, ina son kuma hakan ya zauna a cikin ƙoƙon ranki har illa masha Allah…”
Cikin takaici tace.
“Wannan kuma ka yi kaɗan ka sani adana shi a raina”
Kallon da yake mata ne ya hana ta ƙarasa zancen, don daga inda take tana iya jiyo sautin hucin da yake, muddin ta ƙara sa maganarta tsab zai iya wanka mata marin da zai sa ta rasa jinta na awanni.
Da hannu ya nuna mata ƙofa alamar ta fice mishi a gida.
Kamar munafuka ta wuce simi-simi tana gunguni.

Juyowa yayi ya nufi cikin, sai kuma ya ɗan juyo ya kalli cikin falon jin alamun akwai mutun a ciki.
Juyowa yayi cikin falo.
Cikin nitsuwa ya kalli Ummi da Shatu.
Da alamun Ummi lallaɓata take taci abinci,
Idonshi ya ɗan lumshe, haka nan yaji wani irin sanyi har cikin ransa yake jin daɗi.

Wani ɗan guntun Murmushi yayi bayan ya kalli fuskar Shatun data ke kwaɓe har da turo baki.
Wayar Ummi ce ta fara suwa juyowa tayi ta ɗan jawo wayar,
tana dubawa taga Umayma cikin farin ciki ta ɗaga, tare da karawa a kunne kana tace.
“Assalamu alaikum, Umaymah Sheykh.”
Cikin tarin jin daɗi Umaymah tace
“Wa alaikassalam Ummin Sheykh ina yaran naki? Ya jikin ɗiyar tawa”!”.
Murmushi Ummi tayi kana tace.
“Alhamdulillah suna lfy, ɗiyarki jiki da sauƙi gatasu ma kusa dani”.
Cikin kula tace.
“Bata wayar”.
To Ummi tace kana ta miƙawa Aysha wayar.
Tare da cewa.
“Ga Umaymah”.
Amsa Aysha ta yi ciken jin sanyi tace.
“Assalamu alaikum Umayma barka da rana.”
Cikin tsananin kulawa Umaymah tace.
“Waalaikumus salam Habibty, sannu Aysha Addana, Allah ya yi miki albarka, Allah ya saka miki da al’khairi, na ji daɗi sosai, in sha Allah al’khairi da haske yanzu zai bayyana, sannu kin ji my dear, ki kula da kanki sosai, ki dinka shiga ruwan dumi akai akai, sannan kada ki yi wasa da kunun nan da Ummi take miki, kin ji ƴata ki yawaita cin gashin naman da zatanayi miki da shan kunun har na tsawon kwana uku kinji ko Aysha.”
Wata azababbiyar kunya ne ta rufeta.
A kunyace tasa ɗayan hannunta ta rufe fuska tana jin inama ƙasa ta tsage ta shige cikinta.
Da ƙyar ta iya ce wa,
“To Umayma.”
Jin Muryarta ya sa Umayma yin dariya don tasan kunyace irin na ƴaƴan Fulani ne yasa ta yin shiru.
Cikin murya mai baiyana jin daɗin da take ciki tace.
“Yauwa Aysha, Allah ya yi miki al’barka.”
Cikin sanyi da jin daɗi tace.
“Amin Umaymah”.
Kana daga nan
Suka yi sallama ta kashe.

Sunkuyar da kanta tayi tare da mikawa Ummi waya, don izuwa yanzu kunya ta gama jiƙeta, kallonta Ummi ta yi tana jin dadi aranta tana kuma addu’ar Allah ya nuna musu ranar da ƙwai zai fasha, don ga alamun nan suna ta tabbata.
Shi kuwa Sheykh ajiyan zuciya mai sanyi ya sauke kana ya juya ya nufi falonshi.

Ummi kuwa Kitchen ta wuce da tray’n a hannunta.

Ita kuwa Aysha Anan falon ta zauna tana tunani kala-kala musamman akan masarautar sam ta kasa gane mata.
A kullum da kalar surƙullen da zai bayyanar mata, ko meye ma’anar zantukan da suke yawan yi wanda bata gane masa ba?.
Dazu tajiyo Gimbiya Saudatau da Sheikh maganganunta sun bata mamaki, lallai akwai wani babban al’amari a cikin gidan nan, wanda da sannu zata fahimci menene wannan abu.
Kuma zata tambayi Ummi wani abu ko zata gaya mata, ko ta samu sauƙin Tsarkakkiyar dakw cinnzuciyarta.
Tana nan zaune har aka kira sallar la’asar ta tashi daƙyar don har yanzun bata jin dadin jikinta.
Bedroom ɗin ta ta wuce.
Kai tsaye Bathroom ta nufa.

Al’wala ta ɗauro don har masallacin masarautar sun tada kabbara.

A hankali take taku sabida har yanzu tanajin jikinta na mata zafin rabuwa da budurci.
Sallaya ta shimfiɗa kana itama ta tada kabbara.

Bayan ta idar da sallah ne,
ta kuma miƙewa a hankali ta fito falo, sabida ta gaji da baccin kwanciya tayi bisa kujera da wayarta a hannunta, tana mgna da Junaidu.

Ummi kuwa tana kitchen.

Murmushi ta ɗanyi jin Junaidun na cewa.
“Dan Allah Adda Shatu kicewa su Bappa su dawo haka nan, zamansu a waccar ƙasar ya isa.
Ina kewar Junainah, Rugar Bani gaba ɗaya muna kewarsu dan Allah su dawo”.
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
“To Junaidu in sha Allah zan gaya musu, su dawo maka da masoyiyarka dan nima nayi kewar Junnu ina kewar Ummey na”.

Ummu dake kitchin ne ta ɗan tsagaita daga motsa naman da take fasawa Aysha
Sabida jiyo sallamar Hajiya Mama da Aunty Zuwairiyya.
Haka yasa ta fito tai musu barka da zuwa kana suka gaisa tare.
Sannan tace su isa Aysha na ciki.

To Juwairiyya tace kana tai gaba Hajia Mama na biye da ita a baya.

Ita kuma Ummi ta koma Kitchen dan kawo musu ruwa.

Ba a jima ba sosai Ummi ta debo drinks ta fito da nufin kai musu.
Sai kuma sukayi kiciɓis a bakin ƙofar falon Ayshan. Sun fito falon Shatu fuskarsu a murtuke, da alamun ransu a ɓace, suka wuce ta.
A hankali ta bisu da ido, tare da tambayarsu.
“Har kun fito ko ruwa baku shaba”.
Dukansu babu wacce ta kulata suka fice.
Ajiyan zuciya ta ja ciki da mamaki, sai kuma ta juya ta nufi falon Ayshan.
Tana gab da shiga falon ta ji sautin muryar Aysha na faɗa da ɗan ɗaga murya take cewa. “Mitssssss munafukan banza masu fuska biyu mugaye masu baƙaƙen zuciya. In sha Allah sai Allah ya toni asirinku!”.
Da sauri Ummi ta ƙaraso gareta tare da ajiye tray’n hannnunta bisa stoll cikin kula tace.
“Lafiya dai Shatu Meya faru?”.
Girgiza kai Shatun ta yi cikin jin haushi ta ce
“Ummi nace bana son su, bana son ganin sun shiga rayuwata, bana son su rinƙa zuwa inda nake saboda na tsani mu’amala da mai fuska biyu.”
Ajiyar zuciya Ummi ta yi tana jujjuya zancen Shatun, da kuma tsananin mamakin takun sakar dake tsakanin Aysha da Hajiya Mama.
Numfashin ta ɗan fesar tare da dafa kafaɗarta kana a hankali tace.
“Shike nan ki yi hakuri yanzu ai sun fita.”
Ƙwafa Aysha ta yi tare da kishingiɗa sosai tana mamakin yanda mutanen gidan suka kasa fahimtar komai tana matuƙar mmkin in ance wai Hajia Mama itace Mamansu Sheykh kuma ita har yau bata yardaba bata kuma jin zata yarda har gaban abadan.

Bayan ta idar da sallar isha har yanzun jikinta ba kwari haka tana jin ciwo a gabanta musamman in ta miƙe tana tattakawa, miƙewa ta yi a ciccije, “Wash Allah na!”.
Ta faɗa haɗe da miƙewar ta fara tafiya tana gwale-gwale kamar ƴar kaciya, kallonta Ummi ta yi tana nazarinta, bayan ta shige ɗaki ta tashi ta bita ɗakin.

A tsaye ta sameta gaban drower’nta.
Juyowa tayi ta kalli Ummin dake matsowa kusa da ita tare da cewa.
“Aysha kin sake shiga ruwan ɗumi kuwa?”.
Kai ta jujjuya mata a hankali tace.
“Ɗazu da yamma dai na shiga”.
Kai Ummi ta jinjina kana tace.
“Yauwa to kije yanzuma ki shiga ruwan ɗumi zakiji sauƙin abin sosai.”
Ya mutsa fuska ta yi irin na mai jin ba daɗi kana cikin sanyi tsce.
“Ummi bana jin daɗi kwata-kwata.”
Kusa da ita ta matso cikkn kula tace.
“Na sani, amma shiga ruwan ɗumin zai tai maka kwarai wajen jin daɗinki, don zaki sake sosai, duk wannan ciwo-ciwon zaki daina ji.” Kwafe fuska ta yi kamar zata yi kuka.
Yanayinta Ummi ta kalla, ta so yin dariya sai dai kuma danne tare da cewa.
“Yi haƙuri kin ji Ayshs, daure kada ki zama raguwa mana.”
“Uhmm”.
kawai tace ta miƙe ta shige cikin bathroom.

Ita kuma Ummi ta wuce kitchen tare da ɗauko haɗaɗɗen kunun gero wanda ake yinsa na musamman kuma shi ake bawa amaren masarautar haɗe da farfesun farararen tattabaru, wanda shi ma wani haɗi ne na sirri mai tsuma mace, da yajin da ake barbaɗawa akan tattabarun wanda yake ƙarawa mace wani ɗanɗano na musamman.

Ita kuwa Aysha ta daɗe cikin ruwan ɗumin tana jin wani irin daɗi na ratsa ta, lumshe ido ta yi, tare da miƙewa tayi wanko fes kana ta fito.

Tana buɗe toilet ɗin ta ji ɗakin na ƙamshin wannan gashin tattabarun da Ummi ta kawo mata su har ɗaki.
A hankali ta matso gefen Ummi dake cewa.
“Yauwa kin fito ko Aysha?”.
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
“Eh Ummi”.

“To yanzu ya kikaji jikin naki?”.
Ummi ta kuma tambayarta.
A kunyace tace.
“Alhamdulillah naji sauƙin”.
Cikin gamsuwa Ummi tace.
“Toh zo ki zauna ga wannan kici duk za su ƙara miki ƙwarin jiki.” Girgiza kai tayi alamar bazata ciba.

“Yi haƙuri ki daure kici.” Ummi ta daɗi mata cikin lallami.
Zama Ummi tayi tare da janyo flask ɗin ta zuba mata mai ɗan yawa.
Kana ta turo mata plate ɗin gabanta, kunu ta tsiyaya mata a cup mai ɗan girma ta miƙa mata tare da cewa.
“Yauwa maza kici zakiji daɗin jikinki”.
A hankali ta gyaɗa mata kai, dan bacci ya fara kashe mata jiki.
Cikin lumshe ido ta fara sawa a bakinta.
Jin wani irin ɗanɗano mai daɗi ya ziyarce harshenta ne yasata, lumshe ido tare da haɗiye tsinkekken yawun bakinta ta cigaba da taunawa tana haɗiyewa tare da korawa da kunun geron.

Ummi kuwa tana ganin ta faraci ne ta wuce ta fita.

Bayan ta gama ta shanye kunun don shi ma ya yi mata daɗi sosai.

Cike da bacci ta ɗaura plate ɗin kan kofin ta turasu gefe kana a kasalance.
Ta wonke hannunta.
hamma mai sanyi tayi kana ta kwanta nan bacci ya yayi awon gaba da ita.

Shi kuwa Sheikh yana dawowa daga sallar isha ɓangarensa ya wuce kai tsaye.
Yana shiga bedroom ɗin sa ya zare al,kyabbarsa tare ta ajiye hirami gefen gadonsa ya zauna, yana ajiyar zuciya tare da lumshe idonsa.
Wayarsa ce ta yi suwa,
Ido ya zubawa wayar yana kallon mai kiran, kamar ba zai ɗaga ba,
Sai kuma dai ya janyota hade da murza screen ɗin wayar.
Da sallama ya amsa. Cikin zolaya Haroon ya ce.
“Barka da dare angon Shatu.”
Wani ɗan guntun Murmushi Sheikh ya yi, haka nan yaji sunan yamishi raɗau yayi masa a kunne a zahiri kuwa ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
“Bana son surutu fa.” Cikin Murmushi shi ma Haroon yace.
“Kasan dai ba ƙarya na yi ba, balle ka fara yi min wa’azi.”
Gyada kansa yayi tare da cewa.
“To ina jinka menene zaka kirani da daren nan?”.
Murmushi nan Haroon ya cigaba da tsokanarshi har ya gaji ya katse kiran.

Dai-dai lokacin kuma ya ya fara jin yunwa haɗe da zazzabi mai zafin gaske wanda ya jisa atake.
A hankali ya miƙe yana jin zazzaɓin tamkar wanda ake ƙarawa tun daga kan yatsansa har zuwa saman kansa, cikin tafiya a hankali ya fito daga bedroom ɗin zazzaɓin na cigaba da fisgarsa da ƙyar ya kai tsaƙiyar falon ya zauna kan kujerun dake falon, a hankali ya kwantar da kansa jikin kujerar yana furzar da numfashi mai zafi, lumshe ido ya yi, saboda ƙugin yunwa da cikinsa ke yi, zaman da ya yi, so yake ya ji dama-dama ya ci abincin ya kwanta, tun yana iya jujjuya jikinsa har ya gagara yin hakan saboda ilahirin gaɓoɓinsa sun amsa da zazzafan zazzaɓin ji yakeyi gaba ɗaya gabban jikinsa kamar allurai ake sokawa mushi, yana nan kwance har wajen ƙarfe ɗaya na dare jikinsa na karkarwa.
Cikin rawan sanyi daƙyar ya lallaɓa ya samu ya shiga bedroom ya kwanta a kan gadon a gicciye, hannunsa na rawar ɗari ya janyo blanket ya rufe dukkan jikinsa, shi kansa yana jiyo hucin numfashinsa da zafi, yana yi yana ɗan nishin azaba ƙadan,
a haka ya samu yayi baccin wahala mai cike da rikitaccen mafarki mara kan gado.

Kiran sallan farko ne ya tashe shi, cikin yanayi wanda bai saba tsintar kansa ciki ba ya miƙe, kasala-kasala gajiya-gajiya, ga mamakinsa zazzaɓin ya sauka, don yana ga ɗumin da jikinsa ya fitar da gumi alamun sauƙan zazzaɓi duk da akwai sanyi ac, addu’a ya yi ya miƙe a hankali ya shige toilet sai da yayi wonka da ruwa mai sanyi sannan yaji jikinsa ya yi masa daɗi.
Da sauri ya fito ya fara shirin zuwa masallacin masarautar don har sun fara kiran assalatu.

Bayan sun idar da sallan acan ya yi zamansa don gabatar da azkar da sauran addu’o’in da yake gabatarwa a dai-dai lokacin, sai da gari ya yi washe sannan ya dawo ya wuce falonsa kai tsaye.

Da hantsi ya fito daga falon. Cikin shigarsa ta yau da kullum.
A nan ya taradda su ita da Ummi suna zaune.
Da alamun Ummi nata lallashinta akan ta yi breakfast ne.

Tsayuwa ya ɗan yi gefensu tare da cewa.
“Ummi yunwa”.
murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Dama yanzu nakeso Aysha taci, sai ta kai maka nakan.”

A hankali ya ɗan yi taku biyu zuwa uku, ya kana ya zauna bisa kujerar dake fuskantar tasu.
Ido ya ɗan zuba mata, tare da jingina kansa jikin kujera.
Cike da wani irin mayataccen shauƙi.

Ita kuwa Aysha yatsun sawunshi ta zubawa ido, tare da shaƙan ƙamshin turaren jikinshi dan tun da ya shigo daddaɗan ƙamshin turarensa ya cika wajen har sai da Aysha ta lumshe ido, Allah ma ya sani tana masifar son ƙamshin turarensa.

Idonshi ya ɗan buɗe tare da ƙanƙancesu kana ya tsira mata su yana kallonta, a nutse sai kuma yayi wani gajeren.
Murmushi cikin nutsuwa da jera kalami yace.
“Me zai sa ace ba za a ci abincin safe ba? bayan kuma shi ya fi kowanne amfani a jikin ɗan adam?”.
Kallon shi ta yi tare da kwaɓe fuska kana ta ɗan tura bakinta tare da fara magana ƙasa-ƙasa can cikin maƙoshinta.
“Dama ba dole kace haka ba, tunda kai ne sanadiyyar ciwon, kuma ba ajikinka yake ba.” Ummi dake gefenta ta jita sarai duk da ba kalmomin duka ta ji ba amma tasan abinda take nufi.

Shi kuwa Sheykh Jabeer lumshe ido ya kumayi tare da sauke sassayan numfashi kana ya buɗe idon ya zubasu kan bakinta.
Kallon bakinta yayi ba tare da ta gama haɗe lips ɗintaba yace.
“Kika ce kin yi yajin cin abinci?”.
Ya faɗa da zolaya duk da ba halinsa ba ne, ba kuma ɗabi’arsa bane.
Shima kanshi bai san ya aka yi zuciyarsa ta raya masa faɗin hakanba.
Lips ɗinsa ya ɗan laso da harshensa lokacin da yaji tana cewa.
“Uhmm ni ba haka na ce ba.”
Gyara zamansa ya yi yana mata wani irin kallo mai cike da fassara, kallon nasa ne ya sa mata mutuwar jiki da kasala, don sai da ta ji wani iri a jikinta sabida wani irin kallone mai tsada da masifar ratsa jiki da zuciya.
Shi kuwa cikin tsareta da idon yace.
“Uhumm to muna jinki Aaaaishhh!”.
Kiran sunanta da yayi da wata siga haka ya sa ta ɗago kai ta zuba mishi ido.
Sai kuma ta kauda kanta da sauri tare da sauƙe numfashi,
kwarjininsa ne ya cika mata ido sai wani Murmushi mai tsada da yake mata.
Cikin narkekkiyar murya tace.
“Cewa na yi na ƙoshi.”
Ta ƙarashe mgnar tana kauda kai aranta tana jinjina kwarjini da haiba irin ta shi.

“Yarinyar goye a ke yiwa dole ta ci abinci fa, ko kema sai Ummin ta goyaki zaki ci? Tunda naga nima mancewa sani takeyi sai ke”.
Dariya Ummi tayi tace. “Idan zata ci sai na goyata”.
Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai ƙasa tana nanata zancensa wai agoyata.
“Yi haƙuri ki ci abincin kin ji.” ta kuma jin muryarsa a bazata.

Janyo flask ɗin yayi gabanta,
flask ɗin ta ɗan kalla tana jujjuya kwayar idanunta, cikin ranta take jin kwarjininsa ke yi mata barazana da ta ji shakkarsa, ban da haka ba zata iya shan da ruwan zafi acikinta ba sabida ɗazu da sassafe Ummi ta sata cin sauran naman ji data ɗumama mata.
Sama-sama a haka ta ci abincin da ɗan yawa duk da bata so cinsa ba.

Tana gamawa Ummi ta kwashe kayan kwanukan, shi kuma Sheikh ya wuce falonsa.

Yana shiga Jamil ya shigo, shi da Juwairiyya, zama suka yi suna hira Ummi ce ta ɗan kalli gefen da Aysha ke zaune tare da cewa.
“Yauwa Aysha tashi ki kaiwa Sheykh abincinsa”.
Cikin sanyi tace.
“Ayyah Ummi bawa Jamil ya kai mishi”.
Sai kuma ta kalli Jamil tare da cewa.
“Jamil ɗauki ka kai mishi”.
Ta ƙare mgnar tana ɓoye ainihin tsoron sake shiga inda yake da takejin.
Murmushi Ummi tayi dan ta ganota, tray’n ta miƙawa Jamil dake cewa.
“Ummi kawo dai in kai dan ke”.
Murmushi sukayi, kana shi kuma ya kai mishi sannan ya fiti.
ba su daɗe ba Yah Ja’afar ya shigo shi ma ya zauna kusa da Jamil nan suka ɗan ci gaba da hirarsu

Haka dai sukayi wunin wannan.
Ranar cikin farin ciki suka yini don anan falon suka ci abinci dukansu.

Da daddare ba yanda Ummi ba ta yi da Shatu ba akan ta kaiwa Sheikh abinci ta ƙi, sai da kanta ta kai masa.
Don Aysha tsoron zuwa ɓangarensa take, saboda har yanzun tana jin jiki.

Washegari ma da safe Ummin ce ta bawa Jamil ya kai masa, don fir Aysha ta ƙi zuwa.

Bayan yayi wanka ya fito, ya shafa mai ya kimtsa cikin wani tattausan yafi boyel mai taushi da kyau, Sky blue ne sai aikin da akayi mishi da farin zare sosai yayi kyau sai ƙamshi yake zubawa.

A haka ya fito falonshi
breakfast ɗinsa Wanda yana kimtsawa ya jiyo muryar Jamil ɗin na ce masa ga breakfast ɗinka Hamma Jabeer.

Zama yayi bisa kujera, yana mai mgnar zuci. “Rabon Aiiish da side ɗinna tun shekaran da safe yau kwana biyu kenan ana na uku rabon data shigo nan”. Murmushi mai yelwa yayi wanda bai san dalilinsa ba.
“Uwar raki da tsoro”.
Ya faɗi a fili lokacin da ya fito babban falon ba kowa a falon haka yasa ya wuce yana girgiza kai ya wuce dan sauri yake Asibitinshi zaije.

Bayan ya shiga asibitin ɗaki ɗaki ya bi duk marasa lafiyan ciki suna gaisawa tare da basu taimako na musamman yana duba lfyarsu wanda dama hakan al’adarsa ce kyautawa marasa lafiya, bayan ya gama da shiga ɗakunan suna binsa da addu’o’in nasara da lfy a rayuwarsa.

Ya wuce office ɗinsa don duba outpatient, lumshe ido yayi bayan ya zauna kan kujerar,
Miƙa ya ɗanyi a hankali tare da yin salati.
Gaba ɗaya yanayi shi ya sauya.
Tun jiya yake jinsa cikin wani irin matsi.
Yau kuma tunda gari ya waye yake jin wani abu na fusgarsa a hankali yake dannewa zamansa waje ɗaya ya ji abun na ƙoƙarin son bijire masa, patient ne ya shigo, ya duba sa cikin kulawa tare da ɗaukan dukkan bayanansa ya rubuta masa magani ya fice, kwantar da kansa yayi jikin kujerar haɗe da lumshe idunsa da suka ƙanƙance saboda wani irin feelings yake ji na bin sassan jikinsa a haka ya duba dukkan patient ɗin sai gab da magriba ya bar asibitin saboda hadari da ya fara haɗuwa alamar za a yi ruwan sama.

Direct masarautar Joɗa wuce.
Yana shiga cikin masarautar kai tsaye Masallaci ya wuce don yana shiga cikin farfajiyar gidan aka kira salla.

Bai fito daga masallacin ba, sai da aka yi sallan isha’i sannan ya fito ya nufi gida.

Sosai yake jin wani irin masifeffen feelings mai shegen fitina yana bibiyar sasan jikinsa gaba ɗaya, a haka ya shigo falon, su Jalal na biye dashi a baya.

Ba a falon Ummi na ɗalinta hakama Aysha.

Wuce Side ɗinsa yayi.

Su kuwa su Jalal abincindu suka ɗauka suka tafi Side ɗinsu sabida jin yayyafi ya fara sauka tare da wata iriyar sassayar iska mai sanyi daɗi mai ratsa jiki.

A Dinning area ya nufa.
cikin kasala da gajiya da yunwa ya zauna.
Abinci ya ɗan zuba kana ya fara ci yana mai matse cinyoyinsa yana mgnar zuci.
“To shi wannan me yake buƙata ne da zai hanani zaman lfy, ina dalilin da zakayi ta tashi tsaye, uwar me kakeso kayi”.
Sai kuma ya ɗan sha ruwan sanyi tare daci gaba da mgnar zuci.
“To ita wannan uwar tsoron ma ni rabon da ita kwana biyu, na lura tsoron zuwa nan ɗin ma takeyi.”
Mitssssss ya ɗan ja dogon tsaki tare da tafin hannunshi ya dafe kanshi.
Yau gaba daya sha’awarta ta cika shi don har sai da ya ji Jabeer ɗinshi tana harbawa da cekiyar neman aminiyarta.

A hankali ya miƙe ya bar wurin.
A kasalance sabida ua fara jin zazzaɓin nan na ƙoƙarin da yanzu kullum yake kwana dashi yana bin jikinsa, da sauri ya nemo paracetamol yasha.

Sai dai abin mamaki ba abinda yayi masa don ji yayi kamar ma ƙara ciwon aka yi jingina ya yi da kujerar yana sakin ajiyar zuciya tare da tambayar kansa meyasa ne? Meke damuna?”.
Yau dare na huɗu kenan Kullum da zazzaɓi yake kwana a jikinsa, asuban fari yayi lfy, sai kuma wani daren. cikin sanyi yace.
“Ya zama dole inyiwa kaina medical checkup”.
Don zazzaɓin na da zafin gaske, saboda ya fara jin ya yi loosing appatite, da ƙyar ya samu ya yi bacci don abubuwan sun haɗun masa goma da ashirin ga zazzaɓi ga azabebben Feelings mai fitinarwa.

Tun asuba ya tashi bayan zazzaɓin ya sauka, cike da kuzari da kuma tarin Feelings ya shirya ya wuce masallaci yana danne kanshi.

Yau yini akayi zurr ana tsuga ruwa kamar da bakin kwarya sai gab magriba ya ɗauke.
zuwa dare garin yayi luffff gwanin sha’awa sai iska mai sanyi da ɗan karen daɗi dake kaɗawa tare da ƙamshin ƙasa, yanayin garin yayi daɗi ko ina lib gwanin ban sha’awa da birgewa.

Bai shigo ba sai bayan sallar isha’i, kai tsaye side ɗinsa ya shige yana jinjina yau kwanansa uku rabon da ya sa Shatu cikin idonsa gaba ɗaya ta mai da shi dodo ta ƙi yarda su haɗu, ko abinci ne sai dai Ummi ko Jamil su kawo masa ga tsananin jarababbiyar sha’awarta da take fusgarsa yau kwana biyu, da ƙyar ya iya cin abincin yana jin alamomin bayyanar nataccen zazzaɓin da yake duk dare wanda baya jin magani ya kuma rasa meye sanadinsa ga kuma wannan mayataccen Feelings dake hanashi nitsuwa.

Zubawa sarautar Allah ido ya yi, yana jira yaga wai ko zata zo kuwa saboda yau kwana nawa rabon da su haɗu.

Wuce su da ya yi a falo suna hira ya kuma ce Ummi ta bata zam-zam ta kawo mishi yasa ya yi tunanin ko zata zo.

Shiru-shiru har goma da rabi hakan yasa ya miƙe ya fito falon ya tarar da su suna hira ita da Ummin, jikinsa sanyaye alamun zazzaɓin ya kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi zam-zam ɗinfa”.
Juyowa Ummi tayi cikin kula tace.
“Aysha baki kai bane?”.
Kanta a sunkuye tace.
“Na kai mana yana kan Dinning table ɗin ka na ajiye”.
Juyowa yayi ya ɗan zuba mata ido,
sai kuma ya jinjina kai ya juya ya koma cikin falonsa .
yana lallaɓa kansa don sha’awarta na ta fusgarsa musamman sautin dariyarta da ya ji tana yi, sai da Jabeer ɗinsa ta harba da masifar ƙarfi.

Ƙarfe sha daya da minti goma ya kara komawa falon ya tarar da su har da Jamil da Jalal, da Ummin suna hira sosai, haushi ya kama shi, haka nan yaji sun nashi haushi, kamar ya rufesu da duka.
Don dariyar da suke yi cikin hirar ya sa ya ɗan tunzira yana jin kamar ma da shi suke, hakan yasa ya fito da sauri cikin faɗa yace.
“Jamil meye ya hanaka bacci ka zo ka tasa mutane a gaba da surutu kamar lalataccen Radio?”.
Gyada kai Jamil ya yi tare da cewa.
“Eh yanzu zan tafi, Ummi ce ta faɗa mana mana, in munci dai zamu tafi.”
Sai kuma yayi magana ƙasa-ƙasa.
“Yau kuma waya taɓo Sheykh alaramma akarmakallu, Hamma Jabeer naga masifa da fushi yakeji.”
Bai ji mai ya ce ba, amma yaga dukansu sun kuma yin dariya ƙasa-ƙasa a hankali, miƙewa Jamil ya miƙe tare cewa.
“Asha bacci lafiya Sheikh Hamma Jabeer”.
Ya wuce ba tare da Sheikh ɗin ya sake magana ba, don shi ma daki ya koma, saboda yaga Ummin ita ko motsi bata yi ba daga inda take a zaune shima Jalal moƙewa yayi yabi bayan Jamil dake fita yana dariya.

Suna fita Aysha ta ɗan juyo, ta fuskanci Ummi da kyau kana da gyara zamanta.
Numfashin ta ɗan fidda a hankali, sannan ta juya kanta ta ɗan kalli corridor’n shiga falon Sheykh.
Ummi kuwa ido ta zuba mata ganin yadda take waige-waige da alamun mgna mai mahimmanci takeson suyi.
Cikin nitsuwa da yin ƙasa da murya tace.
“Ayyah Ummi dan Allah zan tambayeki wani abun dake damuna, dan Allah Ummi ki gaya min gskyr meke faruwa a masarautar Joɗa”.
Woni dogon numfashi Ummi ta sauƙe tare da cewa.
“In sha Allahu zan gaya miki gskyar da na sani a masarautar Joɗa, sai dai ina sirrine shi bazan faɗa miki sittin wasuba”.
Cikin sanyi ta ƙara matsowa gaban Ummi kai ta ronƙofar bisa kafaɗunta kana cikin sanyi tace.
“Ummi koda sirrin Yah Sheykh ne baza ki gaya minba?”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“To ai shi sirrinsa naki ne?”.
Cikin jin kunya da daɗi tace.
“To dan Allah Ummi wai me Yah Sheykh yayiwa Gimbiya Saudatu ne? Meyasa bata sonshi? Meyasa su Bappa Nasiru basa sonshi? Meyasa baya shiri da Mom Imaran? Waye Gimbiya Samira amaryar Abba”.

Dogon numfashi Ummi ta fesar tare da gyara zamanta ta ɗan jingina bayanta da jikin kujera, cikin sanyi tace.
“Tambayoyin ai duka amsarsu ɗaya ne!”.
Da sauri tace.
“To Ummi gaya min sai muje tambaya ta biyu?”.

Fuskantar Aysha tayi da kyau kana a hankali tace.
“Kwanakin baya can munyi makami ciyar wannan hirar.
Babu wani abu da Sheykh yayiwa kowa na masarautar Joɗa, domin wannan ƙiyayyar da suke nuna mishi ta samu asaline tun yana yaro”.

Da sauri Aysha tace.
“To tun yana yaro kuma haka kawai kenan suka tsaneshi?”.
Kai Ummi ta jujjuya mata tare da cewa.
“A a ƙiyayyar da dalilin zaɓin tambarine”.
Cike da kaɗuwa Aysha tace.
“Menene zaɓin tambarin?”.
Cikin yin ƙasa da murya Ummi tace.
“Bisa al’adar masarautun gargajiya na Hausa Fulani, dole har kwanan gobe suna da al’adu ko wacce masarauta da al’adarta, sai dai mafiya yawan masarautun al’adar tambarin ɗaya ce.
In kinji ance tambari wani kayan kiɗane da babu shi a ko ina sai gijen manyan masarautu. A bisa al’adar masarautar Joɗa bawai sarkine ke ko mutanen gari kance wane ne zai gaji sarauta ko wanene zaiyi mikinba. Duk ranar bikin salla ana fito da kakaki da al’gaita mabusar masarauta da kuma tambari a ajiye a tsakiyar faɗa, gaban sarki. Kana duk ƴaƴan sarki da jikokinsa da makusantasa maza, zasu hallara a fada, inda kowa zaije gaban sarki ya gaishesa, to muddin akwai nasibin gadar sarauta, a jikin mutun kana isa gaban sarki, kakaki da al’gaita nan zasu fara bisa kansu da kansu.
In kuma kaine zaka gaji mulki daga hannun shi wannan sarkin na wannan lokaci to tambarin masarautar zaiyi ta kaɗa kanshi da kashi,. Duk sanda ka isa kusa dashi, in ka wuce zai bari in ka dawo zaici gaba da yi.
Wannan al’adace tun ta zamanin jahiliya, kuma har yanzu wasu masarautun sunayi, to Amman masarautar Joɗa tun a kan Sheykh aka bar wannan al’adar tun yanada shekara uku a duniya, da akaje fada gaisuwar salla da yazo gaban Lamiɗo sai tambari yayi ta kaɗa kanshi kana kakaki da al’gaita sukayi ta busa kansu.
Tofa wannan shine musabbabin ƙiyayyar da yake fuskanta har ya shafi mahaifiyarshi mahaifinshi yayanshi da ƙannenshi, sabida duk mutanen masarauta sun gani a gabansu abin ya faru”.
Ɗan tsagaitawa tayi kana a hankali tace.
“Kinji amsar tambayoyinka duka”.
Da sauri Ummi ta kalli Aysha jin ta jefo mata tammayar.
“Ummi Waye Mamansu Yah Sheykh ina Mamansu Yah Sheykh meya sameta”.
Jikin sauri Ummi ta miƙe tare da cewa.
“Hajia Mama ce”.
Da sauri Aysha tace.
“Kiyi haƙuri Ummi ki gaya min gsky”.
Juyawa Ummi tayi ta nufi falonsu tare da cewa.
“Je ki tambayi mijinki shi yafi cancanta ki tambaya bani ba”.
Tana faɗin haka ta wuce ɗakinta.

Jiki a mace Aysha ta miƙa ta nufi ɗakinta cikin tsananin gaskata tunaninta na ba Hajia Mamace mahaifiyarsu Yah Sheykh ba.

Kai tsaye Bathroom ta shige,
Brosh tayi sannan tayi wonka da ruwan ɗumi sosai, kana tayi al’wala.

Tana fitowa ta shafa mai tare da shefe jikinta da humranta mai ɗan karen sanyi da daɗin shaƙa.

Wata tattausar rigar bacci wacce iya karta cinya ta saka tare da pant ɗinta da hularta, rigar pink guava color cr mak taushi.

A hankali tayi hamma tare da salati, ba tare daya kashe wutan ɗakinba ta juya ta hau kan gadonta ta kwanta ta bawa kofar shigowa tasa hannunta zata jawo blanket kenan taji wayarta na ringing da sauri tasa hannu ta ɗauka ganin Rafi’a ce, haka yasa bata rufe jikin nataba.
Murmushi Rafi’a tayi tare da cewa.
“Ina son kiranki Ina jin tsoro kada oga yana kusa”.
Ido ta ɗan lumshe tare da cewa.
“To baya kusa, muyi hirarmu”.
Cikin shaƙuwarsu Rafi’a tace.
“A a kai ba wata hira zamuyi ba, zan dai gaya miki cewa, gwamnatin tarayya ta nemi malaman jami’o’i da su zauna wata ƙil zasu sasanta mu koma makaranta”.
Cikin jin daɗi tace.
“Kai Alhamdulillah Allah yasa a sasanta nima gobe zan kira Umaymah in gaya mata”.

Cikin sauri Rafi’a tace.
“Allah ya kaimu, Ni saida safe tashi ki tafi wurin mijinki”.
Da sauri tace.
“Ke da Allah baya nanne tsaya muyi hirarmu”.
Cikin wasa Rafi’a tace.
“To da sauƙi tsoro nake kar in shiga lokacin sa ai”.
Dariya tayi kana sukaci gaba da hira.

Shi kuwa Yah Sheykh ya kasa zaune ya kasa tsaye, yanzu karo na biyu kenan ya shiga Bathroom ya watsa ruwan sanyi.
Sabida a zatonshi ko har yanzu suna falo da Ummi sabida ya leƙa ɗazu ya gansu duk da baijin me suke cewaba.

Yana watsa ruwan ya fito jikinsa ya ɗan tsane kana ya shafa OudKareem dake cikin saman dreesing mirror’n.
Wasu riga da wondo masu taushi red color and white
yasa wondon iya guiwa ne rigar kuma mai guntun hannune sai dai tana da hula rigar.
sa hular yayi a kanshi, kana ya feffesa turaren.

A hankali ya ya kuma fitowa ganin sun hada ido da Ummi wacce lokacin ne ta miƙa zata tafi.
da sauri ya ɗan wayance ya koma falo yana jin kasala, da sha’awa, zama ya yi kan kujera, ya jingina da ita tare da lumshe ido, hancinsa na zuko masa ƙamshin ƙasa mai daɗi, kunnensa na jiyo sautin kukan tsuntsaye mai daɗi, yanayin ya ƙara sakar masa da jiki kasala mai ƙarfi ta rufeshi wannen yasa bai sake leƙawaba, har suka watse, har yaje tai wonka.

Ido a lumsh miƙe da sauri.
Ƙarfe ɗaya na dare dai-dai agogon wayarshi ta nuna mishi.
Hannunshi na hagu yasa ya damƙi kan Jabeer ɗin sa daketa harbawa, da miƙewa tsaye.
“Hehyyyyyy”. Ya fidda wani wani dogon sauti tare da komawa zaune yana taune lips ɗinsa ido ya zubawa Jabeer ɗin nasa data miƙe tayi sama ba alamun sassauci.
Don izuwa yanzu ya fara jin mararsa ta yi nauyi, cikin tafiya da sassarfa, ya fito falon wani dogon ajiyan zuciya ya sauƙe ganin basa nan kuma ko ina shiru alamun sunayi bacci.
Da sauri yaje ya rufe kofar babban falon tare da addu’a, kana ya kashe duk kayan wutan falon, ya wuce falon Aysha.
A hankali yake taku wai sabida kada Ummi ta jishi.
Saɗab-saɗab yake ɗaya ƙafafushi.
Har ya isa kofar bedroom ɗin Aysha, hannunshi yasa a hankali ya murɗa handil ɗin, ajiyan zuciya ya kuma sauƙewa jin ɗakin a buɗe ne.
Ga kuma wani masifeffen ƙamshi daya shaƙa.
Ƙamshin turaren da take amfani da shi idan zata kwanta, ƙamshin ya kara hautsuna masa tunani.
Can ya hangota bisa gadon, tana riƙe da waya ta bawa kofar shigowa baya,
sai dariya takeyi, sam bataji motsin buɗe ƙofar ba bare shigowarsa.

Cibiyoyin ta ya zubawa ido sabida a bayyane suke a fili.
Dogon numfashi yana tare da ƙarasawa kusa da ita a hankali, ya hau bisa gadon tare dasa hannun sa ya rug……

 

 

By
*GARKUWAR FULANI*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button