Garkuwa Hausa NovelHausa Novels

Garkuwa 7

Sponsored Links

PAGE 7

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

Related Articles

 

*Littafina na kuɗine, turo 1k domin karanta part 1 cikin mako biyu, ko ki turo 300 domin karanta part 1 a kwanaki talatin, da izinin ubangiji. Turosu ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank, Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo min shaidar biyanki ta number da nake whatsapp dashi. 09097853276, in da hali bana son kati, amman in babu dama turo katin ba matsala, domin wani baida damar turowa ta bank ac.*

*Ayyah masuyi mun voice note Dan Allah ku rinƙa ɗaga murya, baku saniba ko inada matsalar kunne bayan na idon. In kinga kinyi min mgn ban amsaba wata ƙl fahimceki bane, ko kuma mgnarki bata da amsa a wurina, kana abubuwa suna min yawa, irin asha hira a chart ɗin nan bazai yiwuba, kuyi haƙuri masoya, yawan maimata min slm ince wslm ayi sama da sau goma yana sa in share mutun tsakani da Allah sabida kamar bashi da abin faɗane so Please na tuba,🙏🏻 a ɓari kada kice ina muku wulaƙanci.*

 

Ido ta zazzaro tare da cewa.
“Hihhhhhhh, ya dahu?”. Kanshi ya rausayar tare daci gaba da ɓare kwan saida ya ɓaresh tas ya fito subul gwannin ban sha’awa, sai turiri yaketayi, Junainah ya miƙa.
“Karɓi kici kiji mana, kwan ya nuna ne Ƙanwaliya”.
Da sauri tasa hannu, zata amsa, cikin sanyi Aysha tace.
“Ke uwar kwaɗayi bazaki ciba”.
Rau-rau tayi da idanu alamun zatayi kuka, shi kuwa Ba’ana fuskarshi ya haɗa tare da kafeta da ido, da sauri tayi ƙasa da kanta, tana mai wasa da ƴan yatsun hannunta, dubanshi ya maida kan Junainah tare da cewa.
“Kici abinki Junainah”. Fuskarshi ya ƙara haɗawa jin Aysha ta kuma cewa.
“Dan Allah Ya Ba’ana kada taci”.
Ba tare daya kalleta ba, tace.
“Kema zakici ai bare ita”. Da sauri ta ɗago kanta tare da girgiza kan tace.
“A a ni kam ngd bazanci abinda ban san da me aka dafashi ba”.
juyowa yayi ya kalli Junainah da tuni ta fara cin kwanta, tana lumshe ido baki cike da kwan tace.
“Ya Ba’ana bari inje cikin gida in kawo mana yaji mai daɗi Addana bata cin kwai saida yaji”.
To yace mata, tuni ta juya tayi cikin gida.

Kallonshi ya maida kan Shatu cikin haɗe fuska yace.
“Mata kina tunanin zan cutar da kene?”.
A hankali ta jujjuya mishi kai alamun a’a, gyara zamanshi, yayi tare da cewa.
“To baki yarda dani bane?”.
A hankali ta buɗi bakinta tace.
“A’a ni dai tsoron abun naji, ka toni rami mai danshi da sanyin yashin damina, ka binne ɗanyen kwai mai sanyi ka fito dashi da zafi a dafe ni kam ina tsoro ban san da wutan me ka dafashiba”.

Fuskarta-ta yayi da kyau kana, ya fara magana.
“Ki yarda dani Mata, bazan taɓa cutar dakeba a rayuwa, duk abinda zakiga inayi, zanyine dan kare lfyarki da kuma baki kariyar. Jikin ki, kici kwannan, babu abinda zai miki”.
A hankali tace,
“Ni bana cin kwai dama, kuma ai shi kariya Allah ke hadashi ga dukkan bayinsa”.
hannu yasa ya amshi robar dakekken yaji da Junainah ta miƙo mishi, wacce yanzu ta dawo wurin.
Wani kwan ya kuma ɓare mata, ya miƙa mata, tanaci tana lumshe ido saida taci biyar, sannan tace.
“Ya Ba’ana na ƙoshi”. Shatu ya ɗan kalla tare da cewa.
“Saura biyar kuma nakine, in kin shiga gida kicishi, sannan kuma akwai wani haɗin maganin da zan kawo miki kiyi amfani dashi. Ni yanzu zan tafi”.
Kai ta gyaɗa mishi alamar to, kana kuma tace.
“Ina zakaje yanzu? Tunda naga lokacin tafiya kiwo dai ya wuce”.
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Zan shiga ƙauyen Bonon ne”.
Da mmki a fuskarta tace.
“Ya Ba’ana me zakayi kuma a ƙauye Bonon garin masafa kafurai ƙabulun Ɓachama”.
Ido ya zuba mata har saida taji tsoronshi a hankali yace.
“Kema watan watarana zakije, ki tuna da kyau Mamata ƙabilar ɓachama ce, ƴar garin Bonon kinga kuwa dole inje can tunda kawuneina ƙannen Mama da yayunta da iyayenta duk suna can”.
Ya ƙarishe mgnar kamsr yaji zafin zancen ta,
ganin hakane yasa a hankali tace.
“Kayi haƙuri”. Kai ya juya mata alamar babu damuwa.

Daga nan ya juya ya tafi, ita kuwa tacewa Junainah su shiga gida.
Suna shiga cikin gidan ta harari Junainah tare da kai mata bugu cikin faɗa tace.
“Hegiya kwaɗayayya maza ki zubar da sauran kwanan jakar yarinya ai sai ya ciyar dake guba tunda kince ke kwaɗayayya ce”.
Ihu Junainah ta kurma tare da cewa.
“Wayyoooooooo Inna kin ganta ko tana cin zalina”. a guje tayi gaba, ita kuwa Shatu tabi bayanta da sassarfa tana cewa.
“Wallahi sai kin zubda ƙoyayen nan”.
A haka suka isa har gaban Ummey da inna da suketa tafasa nonon da aka tatsa a sanyin safiyar yau, wanda a ƙalla ya kai jarka goms sha uku, so masu gidajen fura da nono na cikin Shikan ɗin nema suke saya, dan matan gidan Bappa kab bai lamunce da zuwansu tallan nono ba.

Inna ce tayi saurin kare Junainah dan saura ƙiris ta abka cikin tafasasshen nono da yanzu aka sauƙeshi, cikin tsoro tace.
“Kai ya ilahi ku dai bazaku zauna lfy ba”. Cikin nitsuwa Shatu ta zauna gefen Ummey nan ta labarta musu abinda ya faru da yadda ya dafa kwan ta ƙara da cewa.
“Amman da yake Junainah uwar kwaɗayi ce, a take a gabanshi taci kwai biyar cas tanaci tana lumshe ido”.
Cikin tarin mamaki Inna da Ummey sukayi ta salati tare da tafa hannu, a tare sukace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun, oh wannan yaron anya kuwa mutun ne ba shaiɗan ba?”.
Cikin rau-rau da ido, Shatu tace.
“Ni ina jin tsoronshi, bana sonshi bazan aureshiba, mutumin da komai nashi na tsafine Inna ki cewa Bappa ya rabani dashi mana”.
Cikin alhini, Inna tace.
“Rashin sani yasa Bappanki dama ke kanki kukayi mishi al’ƙawarin shine mijinki duk rintsi, gashi yanzu ya zame mana masifa.
Juyowa sukayi suka kalli Ummey da idonta ya ciki da hawaye a hankali tace.
“Dana sani wlh da ban bar haka ta faru ba”.
Shiru sukayi cirko-cirko a wurin, saida suka jiyo ƙaurin nono na zuba cikin murhune suka dawo haiyacinsu.
Kana suka juya suka ci gaba da aikin su.

A birnin Jalaluddin kuwa ƙarfe tara na safiyar ranar, dai-dai jirginsu Sitti da jikanta Sheykh ya tashi zuwa ƙasa mai tsarki da sauran taro al’ummar Annabi masu zuwa Umrah.

Soyayyar da Sitti keyiwa Sheykh soyayyace mai tarin yawa, wanda ko uwa iya son da zatayiwa ɗanta kenan, tana ji dashi tamkar ranta, wata ƙil hakan baya rasa nasaba da tsananin kamanni da yakeyi da mahaifinta wanda shine baida lfy yanzu kuma shine tsohon Limamin Harami yanada zuriya mai tarin yawa yayansa na cikinsa zalla su arba’in da bakwai.
Bar jikoki da ƙanne da yaran yan uwa, sai dai ya tsufa sosai tun shekaru ashirin da suka gabata ya ɗaura babban ɗanshi wanda yake ƙanin Sitti ne uwa ɗaya uba ɗaya a matsayin shi.
Zuwa yanzu tsotsai tsufa ya kama Sarki Abdulkarim, Hairan wanda yake da shekaru ɗari da biyar a duniya, sai dai sufarsa suface mai tsabta tsuface da ka gani kasan an rainin ƙuruciyarta da tsoron Allah da ibada. Shiyasa babu gigita ko fita haiyaci, yana son diyarsa Sitti kakarsu Sheykh kenan so mai tarin yawa ko dan tayi nesa da shine, wacce ita kuma tun tanada shekaru ashirin da uku, Sarkin Musulmai na ƙasar Kautal na wancan ƙarnin yazo da babban ɗansa, Jalaluddin wanda a nan yaga UmmuKulsum Sitti kenan, ya sota, kuma Allah cikin ikonsa suka dai-dai ta, haka yasa kafin ya koma ma da amaryarshi ya koma dan sitti ta kafe ita dai tana son Bahaushen ga, duk da tasan yanada mata biyu, tace ai a gidansuma bata tashi ta samu mahaifiyarsu ita ɗaya ba.

Tuni ita kam Allah ya mata rasuwa mahaifiyar Sittin kenan, yanzu mahaifinta ne kadai a raye, sai kuma ƙanninta da yake matsayin ɗaya daga cikin manyan limaman harami a yanzu sai sauran zuriyarta da yayu da kannenta.
Kowa na ahlinsu yasan Sheykh domin Sitti tana yawan zuwa dashi tun yana ƙarami, kana tana zuwa da sauran ma baki ɗaya, to shi Jabeer anan ƙasar saudia ya haɗa digiri ɗinshi na forko dana biyu. Shiyasa ya zama duk zuriyar an sanshi farin sani, ga kuma tarin kama da yakeyi da mutanen zuriyar wanda da zaran ka ganshi kasan jininsu ne.

Tafiya mai tsowo sukeyi cikin sararin samaniya suna keta gajumare, a ƙalla tsawon aha huɗu kenan suna tafiya.
Kafin suka sauƙa cikin babban Airport ɗin jidda, wanda yake tamkar zai fashe da jirage, ko wacce ƙasa ta duniya tanada jirginta cikin wannan babban Airport ɗin, tashin jirage da hawa da sauƙansu tamkar babu wani abun hawa a duniya sai jirgi.

Koda suka fito daga jirgin, wani jirgine na musamman suka shiga wanda yake daga fadar Mai Alfarma masarautar garin. Wanda ya turo a tarɓi ƴar uwar abokinshi da mahaifinsu keta begen gani.
A take suka shiga jirgin ya wuce dasu, asalin cikin garin makka, wanda pilot ɗin kuma ɗane ga Umaymah ƙanwar Mamansu Sheykh wato shima jikan Sitti ne ɗan Umaymah sai kuma Jannart wacce ta biyo Haroon Dan tarban kakar tasu wacce ita kuma ƴace ga babban ɗan Sitti wato ƙanwar Juwairiyya ce kuma anan take karatu.

Suna sauƙa a Airport ɗin,
suka fito, a jere, yana gaba yana rike da hannun Sitti tana biye dashi a hankali tana taka step ɗin Jannart kuwa tuni itace a gaba.
Haroon ne wanda yake biye dasu a baya yana kallon yadda kakar tasu ke taka step da kuma yadda ɗan uwan nashi ke rike da hannun ta, murmushi yayi tare da jingina a ƙofar bakin jirgin cikin harshen larabci yace.
“Ko dai zaka goyeta ne ka sauƙar da ita”.
Sheykh bai kulashi ba, har saida suka sauƙo ya gyarawa Sitti tsayuwarta, kana ya miƙawa Jannart hannun Sitti alamun ta rike musu ita. Cikin jin daɗi Jannart ta riko hannunta tare da cewa.
“Ana Uhubbiki ya Sitti”. Cikin jin daɗi da son jikokin nata tace.
“Ana”. Sai kuma suka juyo suna kallon Sheykh dake tsaye cikin shiga ta al’farma shigar salihan bayi, wata dandatsetsiyar al’kyabbace mai masifar kyau ruwan ƙasace al’kyabbar sai surfani da aka sarrafa a jikinshi wanda yake da kalan gold, haka takalmanshi da hiraminshi duk masu ratsin Golding color ne, cikin tsananin jin daɗi Haroon ya fara sauƙowa daga step ɗin, yana kallon ɗan uwan nashi manda suke sa’anni, ruggume juna sukayi, cikin jin daɗi Haroon yace.
“Marhabin da zuwa Al’Sheykh, ya gida?, ina ƙannena? Yaya jikin Ya Jafar? Ya Hajja Mama da kowa da kowa.”
Kwaɓe fuska ya ɗanyi tare da janye jikinshi daga na Haroon cikin sanyinshi yace.
“Duk in kana son ganinsu kaje Nigeria zaka gansu, kana nan kullum sai yawo a jirgi kamar turuwa a daji, duk ƙasashen duniya ka gama zagayesu”.
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
“To ai dama na sani bakinka ɗaya da Umaymah’nka, zan koma ne in sha Allah, zan koma inyiwa ƙasarmu aiki, suma ai suna buƙata na”.
Fuskarshi ya ɗan kauda tare da cewa.
“Da yafi kam”. Juyowa sukayi jin Sitti na cewa.
“Kai Haroon ku taho mu tafi, ka tsareshi da surunka tun daga nan ko?”.
murmushi Haroon yayi kana ya nufi inda take tare da cewa.
“Oyoyo My Sitti”. Kai ta juya tare da cewa.
“Rabu dani ba kaga ɗan uwanka ka shareni ba”.
Ruggumeta yayi ta baya tare da cewa.
“Na isa in share uwar gida ran gida a gidan Sarki Jalaluddin”. Jannart ce tai dariya tare da cewa.
“Sitti karki yadda da daɗin bakinshi”.
Hannunshin yasa ya ɗan dungure kan Jannart tare da cewa.
“Kishi ko dan kinga gani ga uwar gida”.
murmushi Jannart tayi tare da jan hannun Sitti sukayi gaba, shi kuwa Haroon baya ya dawo ya saita da Sheykh suka fara tafiya a jere,
duk wanda yaga salo da tsarin tafiyar Sheykh zai gane cewa jini na sarauta na gudana a jikinshi, zai kuma gane nitsuwa ta addinin musulunci da kamala da haiba na hasken imanin ya game jiki da zuciyarshi.

A haka suka jera suna tafe, suna hira wacce ƙarfinta duk Haroon ke yinta.
Suna tafiya kaɗan.

Nan suka samu wasu irin zafafan tsala-tsalan motoci masu masifar kyau da tsada, suna jere a ƙalla sun kai goma sha biyu, motocine masu azabar kyau da sabunta da sheƙi da kyelli suna jere.
Kana ga kekkyawa fararen larabawa yan uwa da abokai
Da sauri suka rinka ɗan rusunawa suna, gaidasu Sitti da jikokinta, wani cikinsu ne da yake jikin wata dan datsetsiyar mota ƙirar Mercedes Benz maybach Exelero wacce kuɗinta zai kai kimanin $8 million dollars.
Motace mai masifar kyau da tsada, tana da inƙancin da ko bilet baya shigarta. Bisa dukkan alamu kuma sabuwa ce dal.
Direban dake jingine da ita ne yayi maza ya budewa Sitti bayan ta, a hankali suka ƙaraso gaban motar gaba ɗaya ma’akatan sunyi musu ƙawanya, cikin so da ƙaunar jikokin nata, ta yiwa Sheykh nuni daya fara shiga, ba musu kuwa ya shiga, motar, kana itama ta shiga sannan Haroon ya shiga, ya zamana sun sata a tsakiya,
Jannart kuma gaba ta shiga gefen drivern, suna gama shiga aka maida ƙofofin motar aka rufe.
Kana duk sauran hadiman suka shishiga motocin.
Kana suka fara tafiya a jere-a jere, tafiya sukeyi cikin salama da nitsuwa da bin doka da ƙa’idar tuƙi, kai tsaye suka wuce tushen ahlin nasu.

Wanda kafin su zoma, duk labarin zuwansu ya riski al’ummar family, kamar yadda aka saba, haka aka shirya musu tarba ta musamman an gyara sashin na musamman wanda nanne masaukin Sitti asali kuma sashin mahaifiyartace, anan cikin sashin kuma duk ahlinta da zaizo daga ƙasar Kautal nanne masauƙinshi, kuma kullum hadimai da bayin dake kula da wannan wurin suna nan suna tsabtace wurin. Suna isa fadar mai darar Sheikh Aliyu da kanshi ya fito tarbar babbar yayarshi wacce take a madadin uwa a gareshi a yanzu.

A wani falo da yafi dacewa da a kirashi al’jannar duniya, suka haɗu, a hankali Sheykh Aliyu ya ɗaga hannunshi alamun dakatar da ko wanne hadimi, a tare suka rusuna tare da komawa baya gaba ɗaya su.
Da sauri ya karaso gaban Sitti Ruggumeta yayi irin ruggumarsu ta jinin larabawa,
murmushi mai cike da jin daɗi ƙauna haɗida bege Sitti tayi tare dasa hannunta tsakiyar kanshi tace.
“Masha Allah, ɗan uwana na sameku lfy?”.
Saketa yayi tare da ruggume Sheykh yana murmushi tare da cewa.
“Alhamdulillah yar uwata, Barka da zuwa lfy”.
Cikin kula da zaƙuwa tace.
“Yaya jikin Baba”.
Murmushi ya kumayi still yana ruggume da Sheykh yana shafa bayanshi, yace.
“Alhamdulillah jikin baba da sauƙi kewarkice tafi damunshi”.
Sai kuma ya kalli Sheykh bayan ya sakeshi yace.
“Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero, barka da zuwa Doctor, ya gida ina Jafar da ƙannenka”.
Cikin son dottijon Sheykh ya ɗanyi wani ɗan guntun murmushi wanda shima sai yayi tsawon lokaci bai yishiba, cikin sassanyan murya yace.
“Suna lfy, sun gaidaka”.
Haroon ya tura baki tare da cewa.
“Wato mu ko ƴar ruggumar ma ta zumunci baza’ayi manaba, dan mu mun dade, nima zamu koma ƙasarmu mu rinƙa kawo muku ziyara jifa-jifa dan naga baƙi farinjini garesu a ahlinmu”.
Dariya sukayi baki ɗayansu,. Yayinda duk mgnar da sukeyi da harshen larabci sukeyi.

Wani faffaɗan corridor mai girma suka ratsa, wanda suka riski wani babbanshi na musamman, inda gaba ɗaya yayan family suke nan zaune dan mahaifin nasu a tsakiyarsu.
Wanda yake tsakiyar gatan duniya, farin dattijone wanda tsabar tsufa har ya juye ya koma tamkar ƙaramin yaro, ya ƙanƙance, yana hango Sitti, ya rinƙa sakin murmushi tare da miƙa mata hannunshi alamun tazo.
Da sauri ta nufi inda yake su Sheykh na biye da ita a baya, yayinda duk sauran mutanen ketayi musu barka da zuwa.
A gaban tsohon ta rusuna, tare da sunkuyowa, hannunshi ya saka bisa kanta yana jero mata addu’o’in da sanya mata al’barka, ita kam sitti da sauran ƙannenenta wanda a ƙalla sun kai arba’in sai Amin Amin suke amsawa,
Koda ya gama da Sitti jawo Sheykh yayi ya manna kanshi da cinyarshi,
Shikuwa Sheykh. Motsoshi yayi da kyau Cikin wani irin mashahurin daɗin da sai in yana gaban tsohon nan yakejin daɗi yasa hannunshi biyu ya kamo hannun dattijon ya ɗaura tsakiyar kanshi kana ya ƙara manna kanshi da cinyar tsohon tasbihi yakeyiwa Allah mai rayawa mai kashewa.
Ya sani shi kanshi da macece shi da yanzu yanada ya budurwa amman gashi wai a gaban kakan mamanshi, ga kuma kakar tashi da sukewa kallon tsohuwa itama gata gaban mahaifinta wannan abu shine abu ɗaya da yake sashi kuka muddin yana gaban tsohonda kullum in yazo irin gaisuwar da sukeyi kenan.
Shi kuwa Sarki Abdulkareem cikin rawan jiki irin na tsoffi yake shafa kan Sheykh tare da kallon taron ahlin naahi cikin muryarsa da bata fita sosai yasa suke sanƙala mishi na’urar ɗaga sauti a jikin alkyabbarsa, shiru sukayi gaba ɗayansu suka dakata da ruggume-ruggumen da sukewa Sitti,
Cikin rawan muryan da alamu tsohon kuka yakeyi a hankali yace.
“Ku bashi dukkan kulawarku, domin yana cikin Magauta, yanada tarin ƙunci da ƙuna a rayuwarshi, matsalolin rayuwar duniya sun mishi ƙawanya, saukinshi ɗaya Allah yayi mushi dafa’i da hasken imani da riƙo da ibada, damuwar tana daƙushe duk wani farin cikin rayuwarsa rashin fara’a ba izza bace damuwace, yana cike da al’hinin kula da ahlinshi,”.
Shiru ya ɗanyi tare da zubawa gaba ɗaya ahlin nashi idanu, sawon wasu daƙiƙu shiru falon babu sautin komai sai sassanyan sautin shessheƙan kuka da Sheykh a hankali, sai kuma sautin ƙaran A/C.

A hankali Dottijon yaci gaba da cewa.
“Kanshi akwai wani abu mai girma a tare dashi, yanada manyan baiwowi a jikinshi, sai dai kuma akwai tarin ƙalubale, zai ɗauki nauyi da yawa a kanshi”.
Ya ƙarishe mgnar yana shafa tattausan suman Sheykh.
Shiru sukayi baki ɗayansu Sitti kuwa Hannu tasa bisa haɓar Sheykh tana share masa hawaye, Haroon kuwa Umaymah ya kira tun shigarsu tana jin duk kalaman kakan nasu haka yasa taketa kuka.

Sosai yayi jawabai masu ratsa zuciya kafin daga bisani, ma’aikatan gidan suka shigo suka rinƙa gabatar musu da abubuwan ci da sha a nan suka zauna ana ɗan ciye-ciye da taɓa hira,
Ganin lokacin salla yayine kab kowa ya miƙe dan yin al’wala su tafi harami.

Kamar koda yaushe Sashin Sitti suka wuce wanda yake a gyare, Jannart da Sitti side ɗaya suka shiga.
Haroon da Sheykh kuwa Side ɗaya suka shiga.
Ruwa suka ɗan watsa sannan duk sukayi al’wala suka fito suka kimtsa cikin manyan alkyebbars masu taushi da masifar kyau wanda sabbine dal akazo aka shirya musu a drower’n. Koda suka gama a tare duk mazan suku tafi Harami.

 

Haka dai rayuwa tai ta gudana a cikin kwanakin nan.

Randa suka cika kwana uku da zuwa a ranar ne Sitti ta samu mahaifinta da ƙaninta a kan batun tana son kafin tabar ƙasar nan ayiwa Sheykh aure, ta kuma bada zaɓin yaran yan uwa wanda suke larabawa, nan take kuma Sheykh Aliyu da kanshi yace ya bawa Sheykh Jabeer auren diyarsa Jazrah…

Rugar Bani Ɓadamaya state.

Yau kusan kwanan Shatu biyar da dawowa hutu, kuma kullum da salon da Ba’ana yake zuwar mata dashi, wannan abu shine abinda yafi tada hankalin Malam Liman Bappa kenan, wanda yana yawan tattauna matsalar da Ardo Bani kamar yadda yanzuma haka suke tare su daddatawa biyar,
Cikin kamala da harshen fillanci Arɗo Bani yayi gyaran murya tare da cewa.
“Koda Hashimu ya rasu, in sha Allahu bazamu zuba ido a aurawa Shatu wannan fasiƙi fajiri mushirkin yaron nanba, Salmanu zai fito zai nemi aurenta,in Allah ya yarda kuma zamu cire batun shaɗi tunda, mun sani cewa, bulalin da Ba’ana yake amfanin dasu wurin shaɗi da manema auren Shatu bulalin sihirine wanda duk wanda ya daka dasu ƙarshe mutuwa yakeyi ko ya haukace, to a karon nan zamuce babu shaɗi domin ai shi shaɗi al’adace ba shariya ba.
Zamu kuma bawa salmanu dakarun tsaro masu bibiyar lamuranshi a sirri dan gudun kada ayi mishi yankan rago kamar yadda akayiwa Hashimu duk da dai bamu da sanin shin Ba’ana ne koko kafuran Ɓachamawa ne”.
Da sauri ɗaya daga cikin dottawan yace.
“Yo ai shima Ba’ana kusan kafurin ne, tunda baya salla kuma matsafine”.
Bappa ne ya nisa tare da jan dogon numfashi mai tsawo sannan yace.
“Bazai yardaba duk yadda za’ayi sai yace dole ayi bulalin Shaɗi, kana kuma muddin akace baza’ayi Shaɗi ba to haƙƙun zai kashe Salmanu kisan da bazamu samu huja ko madafaba”.
Shiru sukayi baki ɗayansu cikin kamala da nitsuwa da rauni Bappa yace.
“Kaɗan kenan daga illar riƙo da Al’adar daba addini ne ya tanadar dashi ba”.
Ardonne yayi gyaran murya cikin sanyi yace.
“Ya Allah ka kawo mana mafita kan wannan bawa naka Ba’ana daya zame mana masifa a rayuwarmu”.
Ɗaya daga cikinsu wanda tunda suka zauna baiyi mgna bane ya gyara zama tare da cewa.
“Gashi shi kamar ibilis yake, ya rigada ya gama dafa kanshi wuƙa ko bindiga basa shigarsa bare banzan abu shi bulalan Shaɗi shiyasa kullum shine da nasara a rayuwarsa”.
Shiru sukayi suna kallon ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance malamin da suke sawa yana bincikar musu jikin Ba’ana wato Chubaɗo yana cewa.
“Akwai bulalin da zasu shigeshi su kuma karya duk wasu manyan sirrukan dake jikinshi, ta kuma sashi yayi kuka,cur-cur da hawayenshi, to amman bazasu taɓa samuwaba bamu da hanya ko damar samunsu, domin bulaline da a ƙalla sun shekara ɗari biyu a murde kuma suna cikin tsumin ma’jiya mai cikar tarihi da girma bulaline da tsawon shekara ɗari da ashirin da biyar kenan rabon da ayi amfani dasu, kuma an killacesu, killacewa mai tsauri, shi kanshi Ba’ana yana neman bulalin ruwa a jillo domin babban dodon tsafin Bonon ya sanar mishi saida bulalin zai samu nasarar da yake so, to amman bai san bulalin ina bane baisan a ina sukeba bai kuma san ta ina yake nemansuba an dai bashi yaƙini a hannun Fulani yake wannan dalilin ne yasa ya baza jakadunshi duk ƙasar da takeda Fulani.”
Da sauri Suka zuba mushi idanu baki ɗayansu cikin zaƙuwa sukace.
“To Chuɓaɗo kai kasan inda bulalin suke e?”.
Kanshi ya jinjina musu tare dayin ƙasa da murya yace.
“Eh na sani”.
Cikin sauri sukace.
“Bulalin inane a wacce ƙasar suke?”.
Cikin tsoro yace.
“Bazan fadaba bazaiyiwu in faɗaba”.
Magiya suka fara yi mishi amman fir yaƙi yace mutanen jikinshi sun hanashi faɗa, dole haka suka haƙura suka tashi daga taron ganin dare ya raba tsakiya kowa ya koma gidanshi.

Washe gari da Asuban fari Rasuwar Chubaɗo ya zagaya garin Rugar Bani wanda akayi hira dashi lfy lau kawai washe gari aka riski ya rasu da alamun kuma ɗaure mishi wuya akayi ya rasu har lahira.
Wannan rasuwa ya jijjiga zuƙatan dottawan nan huɗu da suka rage Arɗo Yabani da Bappa, da kuma Alhaji Ja’eh da kuma Malam Umaru.
Sun shiga jimami mai yawa.
A haka dai akayi mishi sutura aka binneshi akayi zaman makoki na tsawon kwana uku, randa akayi sadan uku duk hankali mutane huɗun nan ya ɗan konta ganin ba’a sake kashe wani ba a cikinsu.

Yau tun da yamma Ba’ana ya matsa aka kira mishi Shatu wacce dolece tasa taje, inda yake har rugar shanunsu bata damuba sanin bai taɓa koda yunƙurin cewa zai taɓa koda ƴar yatsartace,
Cikin sanyin jiki ta sallami aminiyarta Bintu ƴar gidan malam Umaru, sannan ta tafi bakin rugagen.

Zaune ta sameshi cikin ƴar bukkarshi da yayi a cikin tsakiyar turken garken nasu,
A hankali ta ƙaraso wurin ta sunkuya zata zauna ne a saman farin yashin dake wurin yayi maza yace.
“Mata a ƙasa kuma? A a gskiya kada ki zauna a ƙasa.
Ga buzuna zauna a kai”.
Kanta kawai ta jinjina shi kuwa shimfiɗa mata buzun yayi, a hankali ta zauna tana fuskantar cikin ƴar bukkar da yake zaune a cikinta ɗin.
Shima gyara zama yayi tare da fuskantarta,
Kwaryar dake gabanshi ta zubawa ido, shi kuwa. Cikin yin murmushi ya sa hannunshi yana gauraye magungunan dake ciki tare da cewa.
“Matar dafaki nakeso inyi, irin dafar da muddin mutun ya tuna zai miki sihiri, misali ya miƙa hannu zai amshi mgnanin da zai samiki to zai kuturce in kuma baki ya buɗe zaiyi mgna kan a miki sihiri to zai kuramce”.
Cikin sanyi ta kwaɓe fuska tare da cewa.
“To ni kuma wa zaimin sihiri a duniya wayama damu dani?”.
Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace.
“In an nemi mijinki ba’a sameshiba dole kanki za’a dawo shiyasa nake shiryaki sabida kar Ni in an jefeni bai sameniba ya sauƙa kanki”.
Ya ƙarishe mgnar da miƙo mata ɗan ƙaramin korya yace.
“Ingo ki fara shan wannan”.
Kai ta gyaɗa ganin madarar shanuce da aka tatsa da ɗuminta.
Cikin takaicin halinsa tace.
“Me wannan kuma?”. dariya yayi tare da cewa.
“Baki da yarda ki yarda dani wata rana zaki tuna nayi miki gata, wlh bazan taɓa cutar da keba mata, kisha madarace da zuma nasan kinaso”.
Cikin sanyi tace.
“Sai dai in na koma gida zansha”.
Murmushi yayi tare da zuba mata ido kana a hankali yace.
“Fulaku ko? Nasanku fulanin da kunya wato irin bazakici abu a gabana ba, to ai kafin ki koma gida zaiyi sanyi, bari in tafi can bayan bishiya in barki ke ɗaya kisha abunki da ɗuminshi”.
Ido kawai ta zuba mishi domin tabbas badon halin banza da Ya Ba’ana yake dashiba ya cancanci ta soshi tabbas tasan ko ba yayi mata alherin da bazata taɓa mancewa ba a rayuwarta.
Ko komai nashi na duniya mara kyau ne to soyayyarta kekkyawace a zuciyarshi ya sota tun tana yar mitsitsiyarta kuma bai taɓa yunƙurin cutar da itaba ya kuma yi mata halacci.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Mata nayi miki kyau ne?”.
Kanta ta gyaɗa mishi alamar eh, cikin jin daɗi ya juya ya tafi, can nesa ya ɓuya, ita kuwa a hankali ta fara shan madarar nonon da yaji zuma mai daɗi, kasan cewar nonon ɗan kaɗanne a take ta shanye.
Saida ta goge bakinta tace mishi.
“Na shanye kazo”. Da sauri ya fito ya dawo gareta cikin bukkar ya koma ya zauna wani nonon ya ɗibo ya miƙa mata amsa tayi cikin sanyi yace.
“Me kika gani a ciki?”.
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
“Nono fari ƙal mana”.
Amsar ƙoryar yayi ya koma cikin bukkar dashi, jin kaɗan ya kuma fitowa ya miƙa mata tare da cewa.
“Me kika gani?”. Tura baki tayi tace.
“Farin nono mana”. Kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Da kyau, yanzu kiyi kamar zakisha ki gani”.
Ido ta zuba mishi tare da cewa.
“Sha kuma?”.
Kai ya jijina mata kana yace.
“Eh amman ba shan zakiyiba kiyi dai kamar zaki kaishi bakinki da niyar sha zakiga wani abu”.
Jim kaɗan tayi jin yana ce mata sha mana, yasa ta ɗan ɗago kwaryar ta nufi bakinda kamar zata sha.

Wani irin wawan zabura tayi jiki na tsuma da karkarwa cikin tsananin firgita da tarin tsoro ta sake kwaryar….!

 

 

 

By
*GARKUWAR FULANI*📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button