Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 24

Sponsored Links

PAGE TWENTY FOUR*

 

Kallon Hajiya yayi da sauri tare dayin baya taga² zai fadi Daddy yayi saurin tarosa zamewa yayi ya zauna a qasa dabar kamar dan bori yana karanto “Innanillahi wa innah ilaihir raji’un” yanabin kowa dake dakin da kallo idonsa yana yawo a tsakanin mutum ukun yama rasa tunanin daya kamata zuciyarsa tayi masa,
Hada kaya Hajiya tahau yi tana ta fada tare da mitar babu wanda ya isa yasa ta sake bashi Umaimah shidai kallonta kawai yake har ta gama hada kayan ta fita tana fita ya miqe ya damqo hanun Umaimah ya damqeta sosai jikinsa na rawa yace “kada ki yarda a rabamu Umaimah wlh bazaki taba iya rayuwa da wani namiji ba saboda nariga na horaki da yanayi na nima kuma bazan iya rayuwa babu keba ki fahimci hakan kafin Hajiya tayi nasarar rabamu”

Related Articles

Bin hanunsa takeyi da kallo tanajin wani mugun tausayin sa Allah ya sani tanason mijinta amma wannan karon bazata bawa Hajiya kunya ba gara a rabasu din tunda Allah bai haliccesu iri daya ba yafi qarfinta sunkuyar da kansa yayi daidai wuyanta ya dora dan qaramin bakinsa ya sauke mata wani hot kiss me gardi suka sauke ajiyar zuciya tare yaci gaba da tafiya da yawo da harshensa har zuwa bakinta ya dora lips dinsa a saman bakinta ya fara sake mata zafafan saqonninsa bata iya hanashi ba saidai hawaye da yakebin kuncinta jin dumin hawayen natane yasashi janye bakinsa daga nata daidai lkcn Hajiya ta bude qofar ta shigo tsayawa tayi turus ganin yanda yayi kneeling a gabanta ya dora kansa a cinyarta yana sauke ajiyar zuciya ita kuma hanunta yana saman kafadarsa.

Wani takaicine yasa Hajiya qarasa shigowa dakin ta matsa ta sanya hanunta ta tureshi ta figi hanunta ta miqe daqyar saboda rashin qwarin jikin suka fita binsu yayi da kallo shi kansa yasani daga lkcn daya fara heaving dinta zuwa yanzun ba qaramar rama Umaimah tayi ba.
Daqyar ya iya miqewa yabi bayansu jikinsa a matuqar sanyaye ga mamakinsa maimakon yaga Hajiya sun nufi motarsa yakaisu gda sai yaga sun shiga motar Daddy yaja sun tafi shima tasa motar ya shiga yanabin bayansu maimakon suyi hanyar da zata kaisu Zangero road sai yaga sunyi kwana sun nufi hanyar da zata mayar dasu Sokoto road mamaki ne ya kamashi bla bla ya juya kan motarsa shima ya bisu yaga inda zaakai masa matarsa.

 

Suna shiga sukayi parking suka fito a tare idonsu ya sarqe dana juna kallonsu Hajiya tayi ta matsa gabansa taja hanunsa ta mayar dashi jikin motarsa tace “oya maza juya ka tafi gdanka yau dai bama buqatarka ajiyar zuciya yayi yace “to Hajiya ki bani ita mu tafi gdanmu dare yayi sosai kuma tana buqatar hutu….” mari yaji an daukesa dashi suka dafe kunci a tare ba ita aka mara ba amma saida taji cikinta ya hautsina tayi saurin kallonsa suka hada ido yana cije da lebansa kada masa kai tayi ta juya ta shige gdan da sauri ta nufi tsohon dakinta ta fada saman gadon ta saki kukan da ita kanta batasan dalilinsa ba.

 

Tananan kwance batasan ya sukayi ba taji Hajiya tanata sababin bala’in ta wai idan har ya qara zuwa gdan ma saita ci mutuncinsa jikin Umaimah ba qaramin sanyi yayi ba lamarin Hajiya yana bata tsoro ta rasa meyasa ita uwar data haifesa bata tausayinsa batayi masa uzuri itadai koma yane tanason mijinta a haka amma bazata qara musa musu ba zatayi musu biyayya.
Da wannan tunanin ta tashi tayi wanka ta dawo ta kwanta da tunanin Uncle Hameed dinta aranta juyi kawai takeyi tana tunanin yanzu da suna tare da tuni tana kwance a jikinsa yana shayar da ita salonsa da haka bacci ya dauketa.

 

Cikin dare wajan qarfe biyu taji wayarta tana Ring bacci takeyi amma ba sosai ba don haka bugu biyu ta dauki wayar number Hameed ta gani tayi ajiyar zuciya ta kara a kunnenta tace “hello Uncle bakayi bacci ba?” numfashi taji ya sauke tare da gyara kwanciyarsa yace “ina zanyi bacci Baby bayan nasan ana shirin rabani dake kuma kin bada hadinkai yanzun ashe Umaimah zaki iya yarda a rabamu bayan kinsan cewa inasonki wlh Baby bazan taba yarda a rabani dake ba don Allah kada ki bada qofa kinji?”

Yayi mgnr da sigar tambaya itadai bata iya cemasa komai ba sai ajiyar zuciya da tayi ya sake cewa “nasan kinsani inasonki zanyi miki komai Baby zan daina takura miki wlh kada ki yarda Hajiya tayi nasarar rabamu wlh mutuwa zanyi Umaimah tun bakisan kanki ba nake sonki da sonki aka halicci zuciyata bazan iya rayuwa babu ke ba….” Saurin katse wayar tayi saboda karya mata zuciyar da muryarsa take qoqarin yi cilla wayar tayi cikin bedsat drower ta koma ta kwanta tare da jan bargo taci gaba da baccinta wanda badon cikin jikinta ba da babu yanda zaayi tayi bacci saboda zuciyarta babu nutsuwa.

Washegari da sassafe ta tashi tayi wanka tayi sallah qwata² ta manta da Nihal da Maliha suna gdan saida taji ihunsu a parlourn ta fita da sauri suka taso da gudu suka rungumeta suna murna ta daga Nihal daqyar saboda rashin qwarin jikinta ta rungumeta tana murmushi tace “ashe har yanzu kunanan yarana nayi missing dinku da yawa Abbanku yaqi kaimin ku ko?” Maliha ce tace “amma aunty kin dawo nan gdan ko?” Kallon Hajiya tayi ta gefen ido tace “aa idan naji sauqi zan tafi gdana nima” Nihal ce ta shafa cikinta tace “aunty Uncle yace kin kusa ki haifa mana babyn wasa ko?”

 

Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya ta zauna a qasa tace “ina kwana Hajiya” kawar dakai Hajiya tayi tace “qlau na kwana sai baqin cikin ki keda sakaran yaron nan da baisan annabi ya faku ba wato saboda kin rainani kin mayar dani qunzugun hailarki jiya saboda Ina yiwa mijinki fada kika bar gurin kewai dadi miji ko? To bari kiji wani abu Umaimah bawai don inaqin Abdulhameed ne yasa nace sai an rabaku ba saboda ceton rayuwarki ne waike dadi miji to inama kikasan dadin mijin wannan mijin naki banda wahala me kika tsinta a gurinsa tunda ya hudaki ya shigeki banajin kin taba cikakken awa uku batare daya azabtar dake ba kullum cikin qwaqular ki yakeyi bandama ke sokuwa ce iyakar zamanki a gdansa kin taba ganin yana yima uwargidansa wannan haukan sex din ina da bakinki kike cewa basa kwana daki daya ma amma ke kin bude masa tsuliya sai haqeki yakeyi kamar ya samu rami to wlh bazaayi wannan haukan dani ba kina gani yanzu badan Allah yasa anyi gaggawar qulle mahaifarki ba da tuni shima wannan cikin yayi miki sanadinsa saboda haka babu batun shawara umarni ne babu ke babu shi ke garin ma zan bari dake gaba daya gara kiyi nesa dashi idan ba haka ba sai yasan yanda yayi ya yaudareki tunda kedin sakarya ce”

 

Batayi mgn ba har Hajiya ta gaba fadanta ta tashi ta nufi kitchen miqewa tayi a sanyaye tabita suka gama aikin suna gamawa suka dawo parlourn lkcn Hajiya ta shiga dakinta zama tayi a dinning din ta dora kanta a hannuta zuciyarta nayi mata wani irin ciwo bataso kuma bata qaunar taji Hajiya na fadin mugayen kalamai akan Hameed.
Jitayi an rufe mata ido qamshin turarensa ne yasata sauke ajiyar zuciya hakanan taji wani sanyi da farin ciki yana ziyartar zuciyarta janye hanunsa tayi tayi kissing din tafin hanunsa tare da daga kanta suka hada ido ya lumshe idonsa tare da sakin mata kyakkyawan smile dinsa dake qara narkar da zuciyarta sunkuyawa yayi ya dora bakinsa saman nata ya hadesu yana yawo da harshensa cikin bakinta yana sakin ajiyar zuciya.
Hannunta ta dora saman kansa ta janye bakinta a nutse tanajin wata ninki qaunarsa na zagaya jikinta duk abinda ke faruwa tsakaninta dashi bata tabajin haushinsa ba saima tarin tausayinsa daya samu guri ya zauna a zuciyarta yasani mijinta dabanne bashi da wani aibi bayan matsalarsa wadda ta riga ta yarda kuma ta karbeta amatsayin kaddararsu tasani rabata dashi kamar rabata da rayuwarta ne.

 

Duk tayi wannan tunanin ne cikin abinda bai wucce minti daya ba “banda kamarki Umaimah dake kadai nake kambunki na riqe babu ranar dazan sake Umaimah keta dabance dake kadai nake burin gama rayuwata Umaimah duk inda nake tunanin samun sauqi na kasa samu hatta kaka da nake tunanin zata fahimceni jiya na kirata taqi daga wayata wlh banida burin cutar dake Umaimah ke tawace ni nakine ko babu aure tsakaninmu ni nakine kada ki barni na zama maraya Umaimah na qaddara banida kowa a duniya bayan ke saboda ke kadaice kike tausayina kece kika zabi farin cikina fiye da naki na rantse miki da ubangijin da yake busamin numfashi da ace zaa dawomin da littafin qaddarata saina soke wannan saboda ba kyakkyawar qaddara bace bansan sanda nake yi miki irin wannan cin ba Umaimah nafi kowa son naga rayuwarki ta inganta saboda nafi kowa sonki Umaimah kada ki daina tausayina don Allah kada ki amince a rabamu…….”

 

Rufe masa baki tayi da sauri tana hawaye sosai kalamansa suka kashe mata jiki fadawa tayi jikinsa tanajin ninkin tausayinsa da qaunarsa tace “ya isa nace ya isa Abdulhameed na yarda kai nawa ne ni takace bazan taba gudunka ba kuma bazan taba daina tausayinka ba inasonka fiye da son da nakewa cikinnan dake jikina nafi buqatarka fiye da kowa da komai a duniya amma hakan bazai hana muyima iyayenmu biyayya ba kayi hqr duk inda zani a duniya bani da gwanin daya fika kaine gwarzona kuma kaine jarumi na dole ko anaso ko baasa abarni dakai saboda sun sani bazan taba iya rayuwa da wani bakai……”

 

Marin da taji ne ya sanyata saurin janye jikinta Hajiya ta gani tsaye a kansu shikuma yana dafe da kuncinsa hawayen dake bin fuskarsa sun nunku bakinsa yana rawa itama nata yana rawa tace “Hajiya kika mareshi….” bata ida rufe bakinta ba itama takai mata marin yayi saurin janyeta ta sake samunsa ya miqe jikinsa na bari ya figi hanunta amma Hajiyan tayi saurin riqeta tace “indai nonona kasha ka girma har ka kawo yanzu to Ina baka umarnin ka saki Umaimah a yanzun nan ba tare daka qara daga qafarka ba idan ba haka ba kuma na debe maka albarkar da kake taqama da ita”……

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/15, 9:05 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🅱RILLIANT WRITERS* *ASSOCIATION* 🖊
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_

 

*GIDAN UNCLE*
( _Love and romantic story_)

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

 

*MALLAKAR*
👇🏻
*FAUZIYYA TASI’U UMAR*
*®FAUZAH*

 

[email protected]

 

Ki biya kafin ki karanta ta GTbank akan wannan account number: 0255526235; sai kiyi screenshot ki tura wannan number: 09013718241;
Ko katin waya MTN or Airtel ta wannan number:09031307566:

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button