Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 26

Sponsored Links

PAGE TWENTY-SIX*

 

Cikin in..Ina Hajiya tace “ba…babu komai Alh kawai dai dama bashi da lfy ne kawai ita kuma Umaimah batajin dadi don harma tayi bacci” haka kawai yaji bai gamsu da abinda take fada ba amma bayason musu da ita saboda haka ya ajiye wayar da qudurin gobe zaiyi asubanci ya diro Kano tunda dama ba nisa yayi ba South Africa yaje.

Related Articles

 

*************************

 

Kwance take saman kujerar parlourn washegarin ranar da abin ya faru zuciyarta tana mata wani irin suya tanajin takaici da tsanar Hajiya data rabata da farin cikinta taji shigowar Sa’ud miqewa tayi da sauri tana kallon Sa’ud din dake sanye cikin rigar bacci ta zauna a kusa da ita tana miqa tace “jiya bamu samu zama ba na shiga naga kinyi bacci da wuri yanzun dai me zakici?”

 

Idonta a lumshe yake amma hawaye take fitarwa tace “Abdulhameed” kallonta Sa’ud tayi tana mamakin kalmar bakinta tace “kinsan kuwa me kike cewa bloody” bude idanunta tayi tar akan Sa’ud tace “nasani Sa’ud shi kadai nakeson ci shi nakeson gani kuma shi nakeso naji a jikina jiya ban iya bacci ba Sa’ud saboda tunanin halin da mijina yake ciki yanzu shikenan na tabbata sakakkiya na tabbata ba matsayin matarsa ba wannan wacce irin rayuwa ce meyasa banida saa a rayuwata Sa’ud son Hameed shine zai kasheni a jinina yake ya zanyi na rayu babu Hameed Sa’ud na saba dashi…..” kukane yaci qarfinta Sa’ud ta kamota ta rungume ta tana sharar hawaye cikin kuka itama tace “yanzu Ina Uncle din yake” kuka takeyi sosai tace “yana asibiti bansan halin da yake ciki ba inajin tsoron kada na rasashi Sa’ud ruhi nane a jikinsa nasane a jikina Sa’ud farin cikin Hameed shine nawa bazan taba iya rayuwar da babushi a cikinta ba”

Daqyar Sa’ud ta rarrasheta tayi shiru tare dayi mata alqawarin zasu tsayawa juna kaida fata wajan dawowar farin cikin rayuwarsu rungume juna sukayi suna kuka Sa’ud ce tace “Umaimah rayuwarmu tana fuskanta matsala sati uku kenan da su Hajiya suka koreni daga gdansu saboda nace bazan auri Yaya Auwal ba Umaimah banida da kowa a Kano bansan kowa ba saisu haka na dauki kayana na fito bansan inda zan dosa ba gashi babu waya a hanuna saboda tun kafin wannan lkcn aka karbe wayata aka iyakar layin ne a hanuna nayi tunanin zuwa gdanki sai naji tsoron kada naja miki matsala kema a wajan yan garuwar unguwar mu na ari waya nasa layina na Kira Anwar nake fada masa halin da nake ciki banyi tunanin samun taimako daga gurinsa ba saboda irin cin mutuncin da yan uwana sukayi masa shida mahaifinsa amma ga mamakina sai naji hankalinsa ya tashi yacemin na jirashi gashina baifi minti biyar ba ya iso ya daukeni ya mayar dani gda amma Hajiya da Abba suka rufe ido sukaci mutuncin mu qarshe suka koromu harda cemin ai dama karuwanci nakeyi abinda ya karbeni kenan saboda haka naje nayi abinda na zaba karna qara sanya kaina cikin zuri’ar su”

 

Dakatawa tayi saboda muryarta dake shaqewa saida tayi kuka me isarta sannan tace “muna fitowa Umaimah Anwar ya figi hanuna a fusace ya cillani motarsa yaja muka nufi wani hotel dake na’ibawa mai suna Rayhan ya kama mana daki suit anan muka kwana dagani harshi babu wanda yayi bacci kwana yayi yana rarrashina daqyar ya samu nayi shiru muka fara abinda muka saba.
Da safe ya fita yace zaije ya nemamin gdan da zan zauna kafin komai ya daidaita tunda ya fita sai yamma ya dawo yacemin ya samu gda anan Farawa layout harya siya ya biya kudin komai akwai a cikinsa ban wani bata lkc ba na taso muka taho tun daga ranar shima ya dawo nan da zama kasancewar dama aikine ya kawoshi nan asalinsa dan kaduna ne Umaimah kowa dake unguwar nan dauka yake zaman aure mukeyi da Anwar bayan ke babu wanda yasan zaman dadiro mukeyi dashi Umaimah banason rayuwar nan da mukeyi amma ya zanyi haka qaddara ta zabamin”

A hankali Umaimah ta janye jikinta daga na Sa’ud tana girgiza Mata kai tace “meyasa Sa’ud meyasa kike da qaramar kwakwalwa meyasa baki tafi Niger gurin dangin mamanki ba wlh danice ke bazanyi wannan qazamar rayuwar ba” rufe Mata baki tayi tace “kinsan nasan komai Bloody laifin da kayishi tsakaninka da ubangijinka me sauqi ne da ace haqqin wani na dauka ko giba nayi shine zai zamemin matsala kiyi hqr bazan saurari uzurin da zaki bani ba Umaimah inada burin fansa akan abubuwa da yawa na farko korar karen da akayimin na biyu haqqin gadona da Abba da Hajiya suka cinyemin dole zanyi fito na fito dasu domin qwatar yancina”

 

Tana fadin hakan ta shige kitchen ta dora musu abinci ta gama ta fito ta zube musu a parlourn itadai Umaimah bata iyacin na kirki ba ta tashi ta shige dakin da aka bata ta kwanta tare da daukan wayarta ta cire layukan saboda batason kiran kowa yanzun tananan kwance tajiyo dariyar Sa’ud tana qyalqyala dariya tana cewa “nikam honey ka kyaleni gindina ya gaji jiya ko baccin kirki baka barni nayi ba” tashin hankali take Umaimah taji nata gindin yabada wani zut² tayi saurin dafeshi tanajin wani yar a jikinta yau ga ranar Uncle Hameed tunda suke tare bata tabajin feeling ba saboda ko yaushe cikin qwaqularta yake rub da ciki tayi cikin wani irin yanayi tana sharar hawaye Hajiya ta cuceta data rabata dashi yanzu da tana nuna masa alama zai gane ya rigata karbar saqon ma.

 

Tun tana jiyo yananiyarsu har tajisu shiru sun shige daki sun kullo itadai Umaimah juyi kawai takeyi ita kadai tasan abinda takeji duk da jinin da har yanzu bai tsaya Mata ba amma tanajin tsananin buqatar mijinta bayan kamar minti talatin taji sun sake fitowa tana cewa “ka gajiyar dani yau wai me kasha ne ni naga wani qarfi kakeji” mamaki ne ya cika Umaimah wai ya gajiyar da ita to wannan mema sukayi ai ko rabin lkcn wasan Uncle baiyi ba balle akai ga sex.
Tabe baki tayi tanajin Sa’ud na cewa Bloody ki fito ku gaisa da honey zai fita” komawa tayi tayi luf kamar me bacci har ta qari kiranta ta hqr tace “ta koma bacci kasan ba cikkakiyar lfy ce da ita ba saidai idan ka dawo kwa gaisa”

 

Haka Anwar ya fice ita kuma ta koma ta dalama Umaimah duka tace “shegiya ai nasan ba bacci kikeyi ba kawai iskanci ne ya hanaki ki fito ku gaisa da gwarzona” juyowa tayi tayi tsaki tace “me zaisa na fito mu gaisa bayan ba mijinki bane” bata kuma yimata mgn ba tabar mata dakin ita kuma taci gaba da kwanciya har zuwa wani lkc sai yamma sannan ta fito daga dakin suka zamna a parlourn bawai don tanajin dadin zaman ba saidon kawai tanason rage tsayin lkc zuciyarta da hankalinta gaba daya yana gurin Hameed inda ita kuma Sa’ud ta dage cusa mata raayin qin komawa gdan tana cewa da ita ta bari sai sun gwaru wajen nemanta sannan ta koma tun hudubar ta Sa’ud bata shigarta harta fara shigarta itama ta fara yarda tunaninta abinda yake qara burge Umaimah game da Sa’ud duk iskancin ta bata wasa da sallah duk sanda aka kira sallah saita tashi tayi.

 

Suna zaune a parlourn da daddare wayar Sa’ud tayi ring tana dubawa taga baquwar number ta saita nutsuwarta kana ta daga tayi sallama a daya bangaren aka amsa da sauri ta shiga taitayinta jin muryar dake mata mgn cikin in…Ina tace “Eh aa banganta ba rabona da ita tun zuwana na qarshe gdanku ina take Hameed meye ya faru…..” qit taji ya kashe wayar ta juyo sukayi ido hudu da Umaimah data kafeta da ido cike da mamaki tace “meyasa kikace masa bananan Sa’ud bashi fah da laifi ko daya cikin lamarin nan kuma shima abin tausayi ne” Kallonta tayi murmushi tace “bazaki gane ba Umaimah yanzu idan yasan inda kike bazai haukacewa Hajiya ba balle ta fahimci tayi kuskure ki qyaleni dashi da kaina zan fada masa inda kike amma sai naje naga yanayin da yake ciki zuwa jibi kinga kafin nan hankalin kowa ya tashi”

 

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/16, 10:02 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🅱RILLIANT WRITERS* *ASSOCIATION* 🖊
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_

 

*GIDAN UNCLE*
( _Love and romantic story_)

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

 

*MALLAKAR*
👇🏻
*FAUZIYYA TASI’U UMAR*
*®FAUZAH*

 

[email protected]

 

Ki biya kafin ki karanta ta GTbank akan wannan account number: 0255526235; sai kiyi screenshot ki tura wannan number: 09013718241;
Ko katin waya MTN or Airtel ta wannan number:09031307566:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button