Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 35

Sponsored Links

PAGE THIRTY-FIVE*

 

Sukuwa su Daddy suna zuwa gdan Hajiya ta figi hanunta suka shiga ciki a parlour ta zaunar da ita itama ta zauna ta hada kai da gwiwa itako Umaimah banda kuka babu abinda takeyi haushi da takaici ne yasa Hajiya cewa.
“Tun yanzu kika fara kuka Umaimah me akayi da zakiyi kuka? ai baki fara kukaba sai lkcn da kuka fara girbar abinda kuka shuka sai lkcn da kika haife abinda ke cikinki ya girma ya tambayeki meyasa baki haifeshi da aureba meyasa kika bata masa nasaba lkcn ne zaki kukan da babu mai rarrashin ki lkcn ne zakiyi nadama mara amfani Umaimah…”

 

Fasali Hajiya taja kana ta dora da cewa “kin bani mamaki Umaimah koda yake babu abin mamaki cikin lamarinku duba da sakacin namune tun farko da ace mun riqeki a gurinmu mun tsaya kaida fata wajen tarbiyyarki da bamu bashi ke tun kina qarama ba da mun nuna miki cewa shidin ba kowa bane kuma duk da yake dan’uwanki amma akwai bambamci tsakaninku ke mace ce shi namiji ne da ace bamu barki kin saba dashi ba irin sabon daya zama matsala yanzu tsakaninku har kuke tunanin bazaku iya rayuwa babu juna ba nasan da bakiyi masa biyayya akan son kansa dason zuciyarsa ba kema da baki biyewa zuciyarki ba kin gudu har yasamu damar kama miki gda ya killaceki kunci gaba da mu’amalar aure bayan dukkanku babu jahili ya sauki kin sauke yasan fiqihu yasan hadisi kema kuma kinsani kunsan komai amma kuka take yau ga ribar soyayya nan a jikinki”

 

Daddy ne ya amshe da cewa “wai ma ni ya akayi har suka hadu kuma Ina cikin da kika bar gda dashi?” Kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita Daddy ne ya kuma daka mata tsawa yace “ba mgn nake miki bane sai kinji a jikinki?”
Cikin kuka da in…ina ta fara zayyane musu komai…
Mamaki da tsoro gami da al’ajabi ya cika zuqatansu koda wasa basu taba tunanin tun batan Umaiman Hameed ne yayi kidnapping nataba gashi tun ranar da abin ya faru tayi bari aura kuma ya riga ya furta kalmar sakin duk da bai qarasa ba amma ai sakin yasaku tunda saki yana faruwa ne ta hanyar furtawa koda baa qididdige adadi ba shikuma ya riga ya furta na sakeki saki day saboda haka saki ya saku.

 

Miqewa Daddy yayi ya haura samansa ya kwanta yana tunanin abinda ya dace yayi amma bai hango wata mafita ba.
Itama Hajiya miqewa tayi ta kama hanun Umaimah ta shiga da ita daki gurin Hajiya Kaka tace “kaka kisa ido akan sha’anin yaran nan ni tsoroma suke bani wlh” amshewa Kaka tayi da cewa “suke baki tsoro ko suke bani nikam lamarin Umaimah da Hameed ya girmi tunanina Allah dai ya kiyaye daba yakuma rufa mana asiri wannan abin kunya har ina niko a labarin tatsuniya irin tamu ta mutanen dauri ban tabajin wannan kwamacala ba to kodai suna tunanin da aure tsakaninsu ne?”

 

Hawaye Hajiya ta dauke tace “ba wannan tunanin bane Kaka dukkansu babu wanda baisan shari’a ba kuma ma wannan ai budaddiyar mas’ala ce ya saketa kafin yakai ga mayar da ita ita kuma tayi bari kinga aure ya warware gaba daya koda a ranar ya farfado yakeson mayar da matarsa sai ya sake biyan sadaki anyi siga an sake daurin aure to Kaka cikinsu waye baisan wannan ba ko wanda baije islamiyyah ba indai yana zuwa masallaci kuma yana zama cikin musulmi zaisan wannan ballesu da daidai gwargwado mun basu ilimi kawai tsagwaron rashin mutunci ne ba wani abu ba.

 

Tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin ita kuma Umaimah ta zauna a gefen gadon dafe da habarta har yanzu bata daina hawayen nadama da danasanin biyewa rudin zuciyarta takaita ta baro idan ta tuna cikin dake jikinta sai taji wani malolon baqin ciki da takaici ya tokare mata maqoshi.
Mugun haushi da tsanar Hameed takeji a ranta saboda tasani badon Shiba da komai baizo Mata a haka ba da wannan tunanin ta kwanta bawai don tayi bacci ba saidon kwanyarta ta huta amma ta kasa samun sauqin tananan kwance tana juyi wayarta tayi Ring ta dauka ta duba sunan Sa’ud ce mayarwa tayi ta ajiye saboda har Sa’ud din haushinta takeji don tasani da ace batazo ta dauketa daga gdan ba da abubuwan da suka faru duk basu faru ba tanajin wayar tana Ring amma taqi dagawa bayan kamar 2 minutes wani kiran ya shigo tana dubawa taga My Spirit sunan da tayi saved number Hameed da ita kenan.

 

Kawar dakai tayi tare da danna wayar a silent yayi kira yafi ashirin amma taqi dagawa hakan ba qaramin daga masa hankali yayi ba yinin ranar haka ta qarasa shi a daki kwance ko parlourn taqi fita tunaninta kawai yanda zatayi da cikin jikinta.
Da dare yazo gdan ya jima a parlourn babu kowa kasancewar yasan asabarce yasashi haurawa sama gurin Daddy a zaune ya tarar dasu shida Hajiya suna tattaunawa akan matsalar ya samu guri ya zauna yanata gada zuffa kallonsa Daddy yayi da fuskarsa ta rahma yace.

 

“Babana ya akayine Allah yasa dai lfy kazo kasamu gaba?” Sosa qeyarsa yayi cikin kunya yace “Daddy din Allah kuyi hqr kuskure ne nayishi abani dama ta qarshe bazan sake ba”
Kallonsa Daddy yayi yana murmushi yace “to yanzu ya kakeso ayi babana idan anyi maka afuwar?” Sake marairaice murya yayi yace “ku bani ita mu zauna harta haihu in yaso sai a mayar da aurenmu wlh babu abinda zai sake shiga tsakaninmu nayi muku wannan alqawarin”

 

Dagowa Hajiya tayi zatayi mgn Daddy ya daga Mata hannu ya dubi Hameed da kyau yace “yanzu kuma idan nace bazanyi ba kuma mene zai faru?” Dagowa yayi da sauri yace “ka taimakeni Daddy wlh inason cikina kada kuyi sakacin da zata zubarmin dashi Daddy shine na uku fah duk sauran sumbi ruwa shima kada ya salwanta plz nafison basu kulawa da kaina” dakatar dashi Daddy yayi yace “yanzunma Kaine zaka kula da abinka nawane ma albashinka?”

 

Dago kansa yayi ba tare da tunanin komai ba yace “dubu dari hudu da tamanin” murmushi Daddy yayi yace “kayy Masha Allah Nice salery sai kuma mene yake kawo maka kudi kuma ribar nawa kake samu a wata?” Murmushi yayi yace “ina harkar kiwon kaji da kifi a qallah duk wata ina fitar da kaji guda dubu takwas a kowacce kaza daya zan samu ribar dari uku da hamsin da biyar kaga kenan inada million biyu da dubu dari takwas da arba’in sannan ina fitar da qwai guda million daya da rabi shikuma kifi duk wata ina fitar da conterner daya duk conterner ana samun ribar million uku da dubu dari bakwai da ashirin”

 

Murmushi Daddy ya fadada yace “kayy alhmdllh amma dai duk wannan ribace babu uwa a cikinta ko?” Daga kai yayi da sauri cikin qosawa da mgnr yace “kafin nayi lissafin riba saina fitar da uwa tukunna” dariya sosai Daddy yayi yace “kana samun million bakwai da kusan rabi a duk watan duniya kenan ko? Kayy naji dadi sosai” dakatar da dariyar yayi yace “am dubeni da kyau babana daga wannan watan inaso dole bisa umarnina idan ka hada kan kudadenka kazo ka kawomin million uku da dubu dari bakwai da hamsin wannan shine kason da zakake warewa na kula da lfyr Umaimah da cikin jikinta harsai ta haihu sannan a sake sabon lissafi tashi maza ka tafi gda dare yayi”

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/20, 9:30 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *GIDAN UNCLE*

 

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button