Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 43

Sponsored Links

 

 

 

Related Articles

Ajiyar numfashi Daddy yayi cike da jin dadi ya miqe yace “shikenan ki zauna Baby bazan miki dole ba amma kinsan bazaku zauna anan ba tunda kun gama umararku zaku koma gda duk halin da ake ciki ma rinqa waya saboda makarantar ki kuma ma jikin Hameed da sauqi tunda yanzu numfashin sa yana fita sosai kuma wasu bangarori na jikinsa suna motsawa ba kamar baya ba”

 

Ficewa yayi ita kuma ta miqe ta haye gado ta kwanta inda Hajiya ta dauki Shurafah suka fice.
A washe garin ranar aka sake daura auranta da Hameed itadai a ranar yini tayi zuciyarta babu dadi hakanan bata farin ciki da auran nasu duk da ita kanta tasani yaudarar kanta ta rinqayi a baya da takejin kamar zata iya cireshi a ranta, kwana hudu suka qara a qasar Saudia suka dauko hanyar 9ja badan tanaso ba saidon batason yin musu da iyayen nasu musamman Daddy daya matsa akan sai sun tafi kwana uku ta huta Aunty Jameelah ta kama hanyar gdanta ita kuma ta shirya domin fara halattar makaranta micro biology take karanta kuma tanajin dadin course din sosai da yake Umaimah bamai hayaniya bace yasa ko qawa batayi a skul din ba daga ita sai Shurafah dinta suke harkokinsu yarinyar tayi qiba sosai tayi wayo cikin wata biyun idan ka ganta zaka dauka tayi wata hudu yarinya kyakkyawa abarso ga kowa ga Umaimah da sanin darajar kwalliya wa yaro kullum cikin ado Shurafah take hakan yaja Mata farin jini gurin yammatan department din nasu kowa Shurafah hakan yanasa Umaimah taji dadi aranta Saudat Alfah itama sabuwar daluba ce matashiya meji da gayu da tsayuwar naira a jikinta tunda ta shigo makarantar Allah ya hada jininta da Umaimah itama sanadin Shurafah Saudat Alfah itama matar aure ce da yaranta biyu tana auran wani custom tun Umaimah na janyewa abotar tasu harta saki jiki suka zama abokai sosai ita Saudat namiji take goyo Sudais kusan saanni ne da Shurafah.

 

Semester ta fara nisa sosai su Umaimah yan makaranta itadai karatun kawai tasa a gabanta amma rabin hankalinta yana wajen su Daddy da kullum sukayi waya saidai yace musu jiki yana kyau sosai a haka har suka cinye semester sukayi hutu a cikin hutun ta takurawa Daddy kan cewa tanaso taje ta gano jikin Hameed Daddy yaso hanata zuwan amma yanda yaga ta damune yashi dole ya qyaleta dake ya dawo dazai tafi suka tafi tare.

 

Kai tsaye asibitin da yake suka nufa suka shiga dakin tana rungume da Shurafah tunda suka shigo ya Hameed dake zaune jingine da matashin kai ya ya zubawa Umaimah ido ya kasa ko qiftawa sai yawo yake da idanunshi akanta kamar wanda ya warke daga ciwon makanta ajiyar zuciya ya sauke ta dago kanta da tayi qasa dashi tun kallon farko da sukayima juna idonsu ya qara sarqewa da juna a hankali ya daga hanunsa ya miqa mata alamun yana buqatar tabashi wani abu.

 

Cikin sassarfa ta qarasa gabansa ta dora masa Shurafah a jikinsa ya qurawa yarinyar da itama shidin take kallo ta qura masa ido sai bangale masa baki takeyi shima murmushin shima yayi mata tare da dagowa ya dubi Umaimah da taketa kallonsa ya rame sosai hancine kawai da ido sai dan qaramin bakinsa da yake motsawa a hankali alamun magana yakeson yi mata amma muryarsa bata fita sosai.
Shigowar Daddy da likitocin ne yasata neman guri kusa dashi ta zauna a sanyaye taji ya ruqo hanunta ta dago da sauri suka hada ido ya lumshe nasa a hankali ya bude tare da cewa “Kina kulamin da Shurafah yanda ya kamata kuwa?”

 

Yayi mgnr da murya me rauni a salube ta jinjina masa kai ya janye hanunsa daga nata tare da cigaba da kallon yarinyar yanajin qaunar da baitabaji akan sauran yayansa ba game da yarinyar dagata yayi a hankali ya dorata a qirjinsa.

 

 

 

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/23, 8:05 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *G.U*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button