Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 73

Sponsored Links

Miqewa tayi ta shige dakinta ta kwanta tanajin haushi da tsanar duk wanda ya kasa yi mata gaisuwar rashin mijinta da takejin bazata mayar da kamarsa ba a duniya.
Shima ya jima yana kallon Nawwas da Nawwarah yana kuka yaran sai wasa sukeyi da gashin qirjinsa sunayi masa dariya kamar Nawwas da mahaifinsa har tayi yawa kamar dai shida Shuraif abubuwan da yayiwa D.S suna sake bijiro masa musamman haduwarsu ta qarshe lkcn mutuwar Nihal da Shurafah da yazo daukarta yana ganinsa yana miqa masa hanu ya bige hanunsa ya wucce hakan baisa yaji haushi ba washe gari ma daya dawo karba mawa Umaimah yajin daddawa lkcn da cikin yaran saida ya sake miqa masa hanu da yaqi bashi nasa kawai sai yaga ya share qwallah ya rungumeshi yace.

 

“Kada ka qullaceni a zuciyarka Yaya banine na rabaka da Umaimah ba qaddara ce kuma nima itace ta hadani da ita wlh da inada ikon halatta maka Umaimah tun kafin muyi aure zan halatta maka ita saboda nasani kaine Umaimah takeso kaima kuma ita kakeso amma Ina banida damar hakan abu dayane zai hanani dawo maka da Umaimah saboda ina burin rayuwarta ta samu farin ciki Hameed ka qaddara idan Umaimah rabonka ce zata dawo gareka amma bayan qasa ta rufe idona saboda a tsarin rayuwata mace ko cutar dani take indai bazata cutar da Umaimah ba zan rayu da ita balle Umaimah da kullum burinta farin cikina Hameed idan na mutu bana fatan kabar Umaimah ta auri wani bakai ba saboda Ina kishinta kuma nasan zaka riqemin dana saboda kanada imani kuma kanason uwarsu”

Related Articles

 

Yana fadin haka ya sakeshi ya shiga motarsa yaja yana daga masa hannu yanayi masa murmushinsa me tsayawa s zuciya “kyakkyawan namiji me kyakkyawan hali da sanyin zuciya ya mutu” ya fada yana rungume yaran a jikinsa yace “dole Umaimah tayi kuka saboda tayi rashin miji na qwarai amma nasani bazai fini sonta ba kuma zanyi iyakar qoqarina naga na bata farin ciki fiye da wanda yake burin bata zan riqe maka yayanka kamar nawa har qarshan numfashina Sulaiman Allah ya gafarts maka”

 

Yana mgnr yana kuka da shishi kamar qaramin yaro tunda yake baitabajin mutuwar data girgiza shi kamar ta Sulaiman ba ko mutuwar yayanss biyu batayi masa dukan mutuwar Sulaiman ba musamman idan ya kalli yaran sai yace “yanzu fah yanason rayuwa dasu Allah ya karbi rayuwarsa ko? Meyesa a duniya mutanen kirki basa dadewa?” Ya tambayi kansa tare da kwantar da yaran da sukayi bacci a gefensa ya ja blanket ya rufesu ya tashi ya dauro alwala yayi sallar Isha yayi shafa’i da wuturi yaci gaba da addu’a rabin addu’ar tasa ga Sulaiman ne yana kuka yana roqon Allah ya bashi hqr da kyawawan halaye da kyakkyawar mu’amala irinta Sulaiman.

 

Bayan ya gama ya fita ya nufi kitchen domin dauko fresh milk sukayi clear da ido ido cikin ido amma sai ta dauke kai duk da ramar da tayi amma kyawunta yananan rabawa tayi ta gefensa ta wucce yabi bayanta da kallo bakinsa ya kulle ya kasa yi mata mgn gaisuwa yakeson yi mata amma ya kasa harta shige dakinta sannan ya juya kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya dauki madarar ya fita ya koma ya zauna gabansa na faduwa yana korar shaidan saboda yanda yake qawata nasa surar qanwar tasa bayan tana cikin halin takaba wanda ko kalma ta so baa so ta shiga tsakinsu hakan wani zunubi ne me girma.

 

Itama tana shiga ta kwanta badon tayi bacci ba saidon ta bawa zuciyarta hutu da tunanin mijinta Sulaiman daya kasa gogewa a ranta tanason taji yayanta a kusa da ita amma babu dama taso tambayar sa yaranta amma tana tsoron tujararsa don tasan ba mutunci ya cika ba bare yau da take ganinsa duk a firgice da haka dai bacci ya dauketa tunda ba sallah zatayi ba sai asuba ta tashi tayi wankan tsarki tayi sallah sannan ta gyara jikinta ta koma ta kwanta bata fito daga dakin ba sai goma saura ta fito sanye da hijjabin ta har qasa lkcn suna parlourn shida Hajiya da Daddy yanata tura twince din a motocinsu na wasa suna zagaya dakin sunata dariya shima yana tayasu qasan zuciyarsa cunkushe da tunanin ta inda zai fara da uwarsu don baiga alamun sauqi daga gareta ba ya lura tausayin ma nasa da takeji ya goge a idonta yanzj tsanarsa kawai yake hangowa a qwayar idonta zama tayi kusa da Hajiya tace.

 

“Morning Dad ” murmushi yayi yace “Uwata tafi ta kowa kin tash lfy ya kayan lada” qasa tayi da kanta tace “alhmdllh” suka gaisa da Hajiya shima yazo ya zauna shine ya karya billen da cewa “qanwata ba fada meye ya kawo gaba?” Qasa tayi da idonta ya kumayin murmushi ya matsa ya zauna a kujerar dake kusa da ita yace “wlh ba laifina bane bansan Abu Nawwas ya rasu ba sai shekaran jiya Daddy yake fadamin kiyi hqr Allah ya jiqanshi ya gafarta masa Allah ya raya mana twins dinmu cikin imani”

 

Amsawa sukayi da amin ta daidai lkcn da Nawwas ya turo motarsa yazo ya riqeta ta dagoshi tana dariya tana cewa “Ehhh yarona bature na Ina kuka kwana ne yau Hajiya a gurinki suka kwana?” Dariya Hajiya tayi tace “aa nikam ai bana gayyar fitsari gurin ubansu suka kwana” yayi dariya yace “aikuwa nasha fitsari ta ko ina har gara Little ita nata da sauqi amma wannan fumfumgaron daya rinqa antaya min fitsari saida nayi zaton a swimming pool nake yasin” ba Hajiya da Daddy ba hatta Umaimah saida tayi dariya kyawawan haqoranta suka bayyana da yar siririyar wushiryarta dimples dinta suka lotsa sosai tuni Hameed ya shagala da kallonta rabonsa da ganin dariyar Umaimah haka tun tana gdansa shekara kusan biyu kenan da rabi.

 

Hajiya ce ta lura da inda hankalinsa yake ta dauki pillow ta jefeshi yayi firgigit ya dawo hayyacinsa yana sauke ajiyar zuciya ya miqe yace “a bawa twins abincinsu susha zasu rakani anguwa” yana fadin haka ya shige dakinsa ya fada gadi yanajin wani farin ciki a ransa yaudai yaga dariyar Umaimatu wanka ya shiga ya fito ya shirya cikin qananun kaya ya taje kwantacciyar sumarsa data qara kwanciya chocolate din fatarsa tayi wani mugun kyau da haske ya zama fari ma zaace saboda hutun California.
Fitowa yayi ya tarar sai Umaimah kadai a parlourn tana riqe da qaramin qur’ani a hanunta ya jima yana kallonta kafin ta dago suka hada ido yace “ina yarana an shirya su?” Daga masa kai kawai tayi taci gaba da karatun ta baiji dadin yanda tayi masa ba amma haka ya danne ya nufi dakin da yake jiyo hayaniyar su ya daukosu suka fice.

 

Basu dawo gdan ba sai yamma liqis yana zuwa ya tarar da Hajiya Sa’adatu kakar twins da Nazir Sulaiman wanda suke tsananin kama da Sulaiman din suna zaune a parlourn Umaimah na gefe sunata hirarsu da Nazir yana bata lbrn aikin daya samu a Abuja ba qaramin faduwa gabansa yayi ba da ganin Nazir saboda tsananin kamarsa da Sulaiman har tayi yawa jiki kawai Sulaiman zai fishi da kuma shekaru.
Nazir yana ganinsa ya miqe ya miqa masa hanu ya karbi Nawwas da yaketa washe baki yace “oyoyo my son inata missing dinka long time aiki ya boyeni” yana mgn yana miqawa Hameed hannu shima ya miqa masa daqyar ya tsaya suka gaisa da Hajiya Sa’adatu yayi musu ta’aziyya ya shige daki yana kaiwa da komowa yana ayyanawa a ransa “dama Sulaiman yanada qani karfa qanin yace yanason zai auri Umaimah” gabansa ya sake bada wani rasss yace “aa ne bama zai yuwu ba wlh Umaimah tawace wannan karon da yardar Allah” komawa yayi ya zauna zuciyarsa nayi masa zafi a fili yace “Allah kada ka qara jarabtata da rasa bloody a wannan karon Allah kafi kowa sanin halin da nake ciki ka qadarta min rabuwa da ita nace ka kasheni kaqi yanzun kuma ka sake rabani da ita Allah kada kayimin haka idan laifin dana aikata makane na tuba Allah astagfurullah ya Allah” su Uncle manya🤣
Kwanansa tara a garin Kano ya koma California.

 

Kwanci tashi babu wuya gurin lillahi yau litinin ta kama ranar da Umaimah ta gama takabarta takaba mai tsarki tayiwa Sulaiman ba irin takabar matan zamanin nan ba.
A washe garin ranar kuwa Hameed ya shigo garin cike da farin ciki amma me daga bakin get yayi turus ganin baquwar mota a gdan Umaimah ce tsaye sanye da hijjab dinta har qasa ita da Nazir ya kawo Mata wasu takardun filayen Sulaiman yana tsokanarta kan cewa taba dakai bori ya hau kawai ya taimaketa ya aureta tunda Sulaiman ya wullah takai masa duka tana dariya ya kauce tace “yaron nan ka rainani da yawa kalleni dakyau ka gani ni saarka ce?”

 

Suna dariya driven ya fito a mota ya bude masa shima ya fito ya zuba idonsa akanta idonsu ya sarqe da juna duk da nasa a cikin glass yake gabanta ya fadi sosai da taga ya nufosu ga mamakinta yana zuwa taga ya miqawa Nazir hanu sunyi musabiha ya cire glass din idonsa ya zuba idonsa akanta sosai yace “barka bloody sister”…….

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[2/3, 7:16 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *_GU_*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button