Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 16

Sponsored Links

16….

 

_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba_

Related Articles

_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na 07012181461_

 

 

Kafafunta yajawo tafasa ihu sosai tana kuka ta dibi kasan wajen da hannuwanta biyu ta juyo da kanta cikin kuka, watsa musu kasan tayi a idanu hakan yasa ya saketa da sauri yay ihu shida sauran suna sosa ido suna kokarin budewa sun kasa, dawani irin sauri ta tashi tadau jakanta taruga aguje suka biyota, fitowa tayi tana gudu sosai tana kuka, black hijabin ta gabaki daya ya baci da kasa tana gudu suna binta….

Anatse Mami ke tuki taci gayu sosai tasa wani hadadden exclusive atampa brown da yellow dayay mata kyau tayafa wani babban mayafi brown tana tuki, gefenta kuma Aadil ne yana zaune agaba yana wasa da fingers dinshi yana counting dinsu one, two, three, yana sanye cikin wani Fendi white t-shirt daya kama jikinshi sosai, hanun rigan are dark brown, yana sanye da dogon brown pant yasanya white sneaker na Fendi, wrist dinshi daure da agogo na rolex gashin kanshi a kwance yana kara bubbude manyan idanunshi yana magana kasa kasa yana counting yatsunshi sai wani hadadden kamshi dake tashi ajikinshi, murmushi Mami tayi tadan kalleshi ta maida hankalinta kan tukin datake yi tana tunani Aadil kenan, Ball fa suke bugawa a compound shida Aabid Baffa kuma na zaune acikin bukkan dake compound din yana kallonsu yana murmushi, yana ganin Mami tafito rike da car key gidan BigMum zata yafashe da kuka ya yarda kallon zai bita shine ta taho dashi.
Ahankali takira sunanshi. “Son” dan juyowa yayi ya kalleta da manya manyan idanunshi yadan daga cikakken gyararren giranshi sama kaman na tamace yana kallonta, itama dan kallonshi tayi ta maida hankalinta kan tuki tace “wat are you counting Son” turo mata baki yayi kafin ya maida kanshi kan hanya yana lankwasa kan yana cizan wet lips dinshi batare dayace mata komiba yafara counting motocin gabansu. Dawani irin mugun gudu Hamida tafado kan titin tana waigen baya saura kiris Mami ta bigeta ta gitta, dan batakai ga taka birki ba ta buga salati. “subhannallahi wanan lafiyanta kuwa” wani irin ganin gittawan ta yayi kaman flash of light, dasauri yakara ware ido yabi bayanta da kallo harta karasa tsallake titin da gudu tana waigen baya tana kuka tana share fuskarta da hijabi dan gani tayi kaman suna binta, da sauri cikin wani irin rudewa kirjinshi nawani irin bugawa kaman zai tsage yasaki lips dinshi daya rike da hakori tun dazu dayake wasa yana waigenta ta baya dan sunriga sun mata dan nisa, arude yay pointing saitin Hamida yana kyafkyfata ido kaman mai stammering yace “s…s…she Mami” wani irin juyawa yayi batare daya damu tafiya suke akan titi ba ya tuge sitbelt din jikinshi yawani irin bude kofan motan iska yaja kofan, kofan ya bude gaba daya ya daki wani mai machine dake tafiya, salati Mami tayi arude dan bama ta lura dazai bude motar ba saida taji wani irin iska, kafin kyaftawan ido yafita daga motan kanshi na rawa sosai yawani irin fadi akasa sosai dan da wuya in baiji ciwo ba, ihu Mami tayi tawani irin taka brake din motarta duka tana kallonshi kar wani abin hawa ko babban mota yatakeshi before you know it motar dake bayan Mami dat was on speed tazo da gudu ta bugi boot din motan Mami danta taka burki ne unexpectedly ta tsaya, motar Mami tai gaba kan Mami dayake ta lekone tana kallon Aadil arude kanta yawani irin bugu da starring, cikin ikon Allah mota bata bugeshi ba, da sauri batare daya lura da Mami bama yatashi yana waige waige kanshi na rawa sosai yana yarfe hannu danya bugu sosai akafa baima damu da mutanen dake salati ba ana kallonshi ana kallon mai machine dayay hatsari da two cars ya shiga gudu yana hango Hamida datamai nisa sosai yana yarfa hannu yafashe da kuka yace “she noo, don’t go” yacigaba da gudu, gajiya yayi sosai kaman zai suma yafashe da kuka yana kallon titin dan baitaba gudu hakaba a rayuwan shiba, wani mai machine ne dayazo wucewa ya tsaya yana kallonshi cikeda mamaki yace “malam amma mutuwa ne kake kuka haka miyau na zuba” cikin kuka sosai yamai pointing Hamida dake shirin yin kwana tai nisa sosai yace “she” kallon inda yake nunamai yayi sanan ya kalleshi ganin yanda yake kaman mara lafiya sanan wanda yake nunamai itama gudu take yasa yakawo aranshi halama mai gudun shi take nema itama, tausayi yabashi hakan yasa yace “hauna kaikah wurinta to” tsayawa yayi yana kallon machine din yana kuka hannu mai machine din yamika mai da sauri yarike shi ya dafa shi sanan ya iya hawa kan machine din, mai machine din ya kunna yaja machine din, rikeshi yayi a tsorace yana kuka, adaidai bakin layin lokacin harta shiga layin mai machine din ya tsaya yace “sauko ka bita bazan shiga layin nanba, machine dinan daga wajen wanki na karbota yanzu haka, layin nan duk chabalbali” lekoshi yayi da kai yana kallon fuskanshi dan baicika gane manyan hausaba, ahankali mai machine din yace “come down” saukowa yayi yana kallonta yana kuka da karfi ya kwala mata kira. “sheeee” arude Hamida dake gudu har lokacin tana kuka sosai tafada wani uncompleted building ta tsugunna tana kuka sosai tana addu’a Allah yasa basu ganta ba, tabude jakanta arude ta shiga neman wayanta tanaso takira Ya Faruk amma bataga wayanba hala tafadi awurin, tafashe da wani sabon kuka tana kare fuskarta ta hijabi ta.

Da gudu yay cikin layin clean white sneaker dinshi na shiga cikin chabali, bai damuba burunshi yakai gidan data shiga yaganta, wani irin mugun faduwa yayi cikin ruwan chabalin white rigan shi da wandonshi suka baci sosai, tashi yayi ahankali yana kuka sosai yana kallon hanunshi da jikinshi danko kadan ya tsani datti yacigaba da gudu yakai gaban gidan, da gudu shima ya shiga haryana neman faduwa sabida block dake wajen ya buge kafanshi ya kwala mata kira yana kalle kalle. “shee” amugun tsorace Hamida ta dagokai ta mike tsaye da mugun sauri tana kuka tana komawa baya, tsabagen yanda tai gudu tana haki, ga heart dinta dake beating way to fast yasa har dishi dishi take gani, zaro idanun dabata gani sosai tayi ta kalleshi kaman yanda yake kuka sosai yake wani irin kallonta cikin wani irin low and calm voice yace “uhmm is me” yay maganan yana takowa gabanta kanshi na rawa yanadan dingishi danya buge kafanshi sosai, zaro ido Hamida tayi tana komawa da baya tana ganin dishi dishi tana ganin mutum na tahowa amma bata ganin fuskarshi da kyau tsabagen dishi dishin dayake gani, ahankali take komawa baya yana tafiya ahankali shima yana goge kukan dayake yi yakeyi yana tafiya ahankali yana kallonta yana biyota hartakai jikin bango ta tsaya, karasawa yayi shima har inda take yana breathing fast sosai yana wani irin kallonta numfashin duka na sauka akan fuskarta, wani irin kallonshi take da idanunta that went completely blind tsabagen yanda zuciyata ke bugu shima kallonta yake zuciyarshi nawani irin bugawan da tunda yake baitaba jin yamai irin bugun ba, wani irin nishi yayi yana kara matso ta har kafafunshi na gogan nata, dawata irin murya chan kasa yar karama chan ciki yasakin mata wani irin kuka dako su Aabid baitaba sakin musu irinshi ba yabude hannayenshi ahankali yafada jikinta yana kuka yay cuddling nata so tight not knowing what exactly yakeyi and yake feeling but he just wanna cuddle and cuddle and cuddle her, dip wuta ya daukemata tai wani irin passing out instantly kafafunta suka lankwashe zatai kasa, ahankali yadaga kanshi daga wuyanta yana kuka sosai yana kallonta dukya jika mata wuyan hijabi da hawaye da miyau, binta yay da kallo ta yanda arms dinshi ne are d only things dake rike da ita danda tuni tazube akasa asume, jijjigata yayi ahankali ya fashe da kuka kaman karamin yaro yace “wake up, are you sleeping?”.
_🌹IN BANI 🌹_

 

_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan_

_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na sainai adding a group din danake posting_

 

Maman Abd Shakur

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button