In Bani 30
Ruwa kawai Abban su Ra’is ya dauka yasha sanan ya ijiye ya fuskanci Abba da kyau zaiyi magana saikuma yajuyo ya kalli Hamida dake zaune akasa kusada matarshi kanta akasa gabanta sai wani irin faduwa yake yace “tashi kiwuce ciki Hamida, tafi dakinku” ahankali ta gyada kai tana goge kwalla tawuce ciki Abba yabita dawani irin kallo harta shige corridor, sake kallon Abba yayi sanan ya kalli Mama dake dan murmushi cikin tattausan murya yace “haba, haba, haba dan Allah, a gaskiya raina yay matukar baci saisa nazo har gida namuku fada sanan nadawo da Hamida, ko kadan bakuma yarku adalci ba wlh, kuma nan gaba karku kara yankema yara mata irin hukuncin nan dan irinshi ne ke jafa yaro ga halaka, karuwai da sauran su dakuke gani duddaga haka aka fara daga koransu daga gida ne, to ina amfanin wanan? kome yaro yayi afara bashi damar bayani tukunna kafin a yanke hukunci, sanan adena yankema yaro hukunci cikin fushi, hanunka ai baya rubewa ka yanke ka yar, kai yanzu idan ka kalli Hamida fisabillahi bata baka tausayi?” yay maganan yana karkada kafa yana kallon Abba dake kallonshi asanyaye sanan ya cigaba.”yarinyar nan ta shiga duk bala’in data shigane daga taimako, taimako fa jama’a, taimakon da annabin mu shiyace muyita, jiya har gida iyayen yaron nan sukazo suka mana godiya wlh idan kaji labarin yaron ma saika zubda mai da hawaye abin tausayi……” nan yafara bama Abba labarin da Hamida ta bayar na yanda ta taimakai dana Mami data bayar na Aadil din, dakuma labarin rashin lafiyan shi, sanan yace “yanxu abinda kukayi kun mata adalci?” dan ajiyan zuciya Abba ya sauke yace “nima nasan bamu kyauta ba kuma tun jiyan hankalina yaki kwanciya, naba Kaka hakuri, nabata hakuri harna gaji da bata hakurin amma taki fahimta ta tsaya akan bakanta, abinda yakara batamin rai shine yanda bata attending lectures ko kadan inda tasan bazatai makarantan ba dabatasa nai asaran kudina ba jiya result dinsu na first semester yafito Zainab ta dauko hoton takawomin wlh carry over bakwai gareta acikin courses tara dasukeyi last semester ina amfanin haka fisabillahi? Hamida bayar gidan nan bane? Hamida yarinya ce? Ba nannan ta taso taga yan uwa ta ba? Narasa yanda zanyi da ita, isilamiyan ma inda ba har gida na dauko musu malamin ba shima na tabbatar maka da bazata jeba, yaya zan mata? Saisa na yanke shawara da zaran miji yafito wlh aure kawai zan mata hala ta chanza muma ma huta dan lamarinta sai godiya….” sallaman da Kaka ta rafka yasa duk sukai shiru sai Anty Lami data amsa Kaka ta shigo tana kallonsu daidai, Anty Lami ce tadan zamo daga kujera tana murmushi tace “ina kwana Kaka” wani irin mugun kallo Kaka tamata kafin ta kalli Abba dayay shiru yana kallonta asanyaye tace “Sama’ila me wayan nan sukazo yi gidan nan da sassafen nan? Ince ba yarinyar nan suka kawoba” ahankali Abba yace “itace Umma tanama ciki amma duk ba abinda muke tunani bane, ashe taimakon yaron tayi, yaron kuma baima da lafiyan kwakwalwa, kinsan komu munga haka mun zaci pretending yake ashe da gaske ne baida lafiyan kai ne, jiyama saida iyayen yaron sukazo suka yima su Alhaji Ibrahim godiya, yanzu komi yawuce Umma” wani matsiyacin kallo Kaka tamai tace “idan kai yaro ne sunzo sun wanke ma kwakwalwa bayan Hamida taje ta shirga musu karya ka yarda niba yarinya bace, sanan abinda babba ya hango yaro ko yahau bishiyar kwakwa bazai hango ba, na kori Hamida daga gidan nan kuma ta koru ne, billahillazi la’ilaha illahuwa duk wanda yace zai nunamin ban isaba sainaje naci abincin gidan kajinka na mutun maka a wuya Sama’ila kana jina” tai maganan tana gyara kullin zaninta ta kwalama Hamida kira daga nan inda take tsaye. “Hamida! Hamida, dan uwaki kifito daga dakin nan kafin nazo dan wlh idan kika bari na shigo dakin nan sainai miki ruwan zabori aka, kifito nace” tagumi Mama tayi kawai tana kallon Kakan cikeda mugun takaici, Anty Lami ne ta tashi tace “Haba Kaka ki mata afuwa ki yafe mata mana idan kika korata daga gidan uban ta to ina kikeso taje? Tanada wani ubanne?” nunata Kaka tai da yatsa tace “kinga Lami lamiso kinga ina ganin mutuncun kiko karki kara kiran Hamida diyar Sama’ila, nariga nacireta daga yaranshi karki kara, Hamida!” ta kwalama Hamida kira da mugun karfi daidai lokacin wasu yara suka shigo guda biyu. “salama alaykum wai ana neman megidan awaje, ance ana sallama damai gidan” tashi Abba yayi ya kalli baban Ra’is yace “ina zuwa dan Allah” yawuce yafita, hakan yasa Abban Ra’is yace “Kaka kima Allah ki yakuri ki zauna ki saurareni haba Kaka ta” shiru tayi ganin yadan cika mata ido ta zauna akan kujera ta daure fuska tace “ina jinka yimaganan tun ina ganinka da gashi” sake kwantar dakai yayi yace “yauwa Kakana, wlh yarinyar nan ba iskanci tayiba taimakon mutumin nan tayi na rantse miki bari nabaki labarin yaron kiji….” nan yafara koro mata labarin har karshe zai cigaba da magana Abba yay sallama ya shigo ya kallesu dukansu yace “tareda baki nake ku gyara, iyayen yaron nanne sukazo” tashi Baban Ra’is yayi yace “masha Allah gasunan Kaka kyaji gaskiyan zancen daga bakinsu ai” fita Abba yayi tareda Baban Ra’is ko minti biyu basu dauka ba suka shigo da manya manyan baki sunci manyan kaya, Baffa, Suleman da Abie da idanunshi yay mugun jajir yau yana cikin tashin hankalin da rabonshi daya shiga irinshi tun ranan da aka haifi Aadil, gefe daya Aadil ne rai ahannun Allah yana sambatu yana kiran Hamida yana asibiti ansaka mai oxygen, gefe daya kuma Ozo ne dayace mai karya sake yabari Aadil yay aure, kanshi yadau zafi bana wasaba binsu Baffa kawai yake amma hankalin shi baya jikinshi baimasan me akeyiba, sai Mami da itama idanunta har kumbura sunyi tsabagen kuka saikuma big Mum dake biye da Mami, dawani babban Abokin Baffa wanda yake limamin jumma’a na masallacin dan ja, malam Kabir duk suka shigo dakin aka zazzauna, Mami daurewa kawai take tama kasa zama akan kujeran da kyau Kaka dai saibin manyan mutanen take da kallo danji tayi falon yadau wani irin sabon kamshi, Anty Lami ne ta tashi taje kitchen da kanta ta kwaso lemukan kwali tafito dasu a ijiye a tsakar falon sanan tadawo gefen Mama ta zauna tana kallon yanda su Abba ke gaisawa da mazan ana gaishe gaishe.