Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 49

Sponsored Links

49…

Agaban wani katafaren mansion Abie ya tsaya ya dauko wani remote ya danna gate din yabude yaja motar ciki, babban gidane da yaci uwar na Baffanau kyau sama da sau miliyan gidan kaman a turai, murmushi yayi ya kashe motar yajuyo ya kalli Aadil din daya ke kuka sosai har lokacin yace “stop crying nakawo ka hadadden gidana wanda yafi na kakan ku kyau, akwai wurin buga basketball aciki, akwai wurin table teble tennis kaga har gym namaka aciki ga alot of teddies and all sort of chocolate you could think of dakasani su favorite dinka duk akwaisu aciki, yauwa Aadil dina come and have a look kagani inka gansu you will forget su Mami ma trust me pure enjoyment ne gidan nan” yafito daga motar ya zagayo ta baya yabude kofan bayan ya mikomai hannu yana murmushi yace “yauwa My Aadil, Abie big Boy, har fish pond akwai aciki ga lift ga stairs you take anyone your heart desires, akwai video games, i have alot of money sama dana kakan ku i will give you anything you want my boy i mean anything kome kakeso” makemai kafada Aadil yayi yana kuka sosai yace “My Hamidaaaa” harara Abie ya watsamai cikin takaici ya fizgoshi da karfi da yaji yafito dashi daga motar yay hanyar cikin gidan dashi da fingerprint yabude door din mini palor din kafin su shiga hadadden falon kaman ba’a Nigeria ba, murmushi yayi yana nunama Aadil dake kuka sosai yace “kaga falon ka, muhau lift muje ma sama kagani tukunna” shiga sukayi ya danna one yakaisu first floor transperent glass tiles ne akasan kana hango falo daga wurin, ganin yanda yakemai kuka jikinshi harya dau zafi yasa yabude wani daki ya shigar dashi ya subhanallah dakin yahadu to d core, zaunar dashi akan lumtsetsen gadon yayi yana murmushi da sauri yajuya yabude wardrobe ya ciro wasu sababbin kaya daga hanger yakawo ya ijiyemai yanamai murmushi yace “yauwa My Aadil tashi kasa kayan, bari kaga na kunnama video game kabuga” tv bangon dakin ya kunna yajuya yafita da sauri sai gashi ya shigo da basket of different expensive chocolate and sweets yakawomai yana murmushi yace “yauwa my Aadil sha kadena kuka, kaga dare yayi bacci yakamata kayi yanzu kaida kake bacci dawuri” kabar da sweet din Aadil yayi cikin kuka sosai duk suka zube akasa, dawani irin fushi ya makema Abie kafada yana kuka, ajiyan zuciya Abie ya sauke kanshi na daukan mugun chaji dan baiso yaga abu yasami Aadil barinma in yana kuka, ahankali ya zare babban rigan jikinshi ya ijiye kan gadon ya ciro handkerchief daga aljihun shi ya share gumin dake keto mai yana kallon Aadil din dake wani irin kuka dake tsumamai rai har wani irin ajiyan zuciya yake saukewa cikin kuka idanunshi sunyi jajir jijiyoyin kanshi sun fito radau, tsaki yaja yana karajin wani irin tsanar Hamida aranshi duk haduwanta da dan shine ya zaman mai wani irin mugun matsala da kalubale arayuwa, ahankali yasa guiwanshi akasa yana kallon Aadil din yakama kunenshi kaman zaiyi kuka yace “dan Allah kayi shiru Aadil, i promise kome kakeso i will do it for you i promise, but dan Allah kai shiru kaji, kukan ka zai karasa kasheni, idan da kasan matsalolin danake ciki ayanzu haka daka tausayamin, kadena damuwa da wanan shegiyar yarinyar yar matsiyatan wanda ubanta ke saida kaji, kaji da kullum anacin sama da arba’in a gidanku gasunan him a frozen fridge, babanka nada kudi Son, kome kakeso zan makashi, kome kakeso daganan har zuwa bangon duniya inada kudin zansa akawo ma, barima kaga nakawo ma kudi kome zakayi dasu kayi” tashi yayi kaman mahaukaci yafita daga dakin baiwani jimaba yashigo dakin yana jan wani babban ganamasgo dake nan zin din a kulle yana kallon Aadil din dake kuka yanamai murmushi, zama yayi abakin gadon kusadashi yasa hannu ya zage zip din ganamasgon uban kudi dake nan dollars note suka bayyana cike a jakan, wani irin murmushin dadi Abie yayi yajuyo ya kalli Aadil din dake kuka yana kallonshi ya lashe baki kaman tsohon maye, yasa hanunshi da sauri ya ciro wraps din dollars note din guda hudu dake kyalli yawani bubbuga kudin together agaban fuskar Aadil yace “kasan menene wanan My son?” yay maganan yana wani irin murmushin jin dadi yace “this is money Boy, manny, hausawa sukace milamila, kaga kudin nan na ganamasgon nan” yay maganan yana karkatamai ganamasgon da kyar sabida nauyinta dan acike take da kudi yace “duka kudin nan nakane kai yanda kakeso dasu nabaka, kai bacci akansu kayi bari dasu duk yanda zakai dasu, kaganni nan your Abie have money Aadil, plenty plenty money enough to buy all this kano kai Nigeria ma gabaki daya, kudin Abie ka basa karewa duk sati sati nake samin kudin da zan iya cika irin manyan ganamasgon nan guda goma sha biyar dasu, inhar you are a good boy kanajin magana na zan karoma irin ganamasgon kudin nan guda biyar kaji my son, my handsome boy kaji ko” makemai kafada Aadil yayi cikin fushi ya fizge kudin hanun Abie ya cillar dasu chan har suna tsalle suna fita daga dakin wasu kuma sukai wurin TV, cikin kuka sosai da muryanshi data dishashe yace “take me back to Mami, Mamiiiiiii, My Hamidaaaaaaa” yaja sunan Mami da Hamidan yana kuka kaman zai sume, tagumi Abie yayi yana tsinema Hamida aranshi yana tunanin wani dubara kuma zaimai ganin har wurin dayan dare Aadil kuka yake jikinshi yay zafi idanunshi kaman jan gauta yasa hankalinshi yatashi ainun, babu kallan dabaran dabai maiba amma sam Aadil Hamida yake kira hakan yasa Abie ya yanke sharawan kaishi wajen Ozo gobe dama gobe sunada meeting karfe taran dare, da kyar yasamu wani wahalallen bacci ya kwasheshi hakan yasa yadau bargo ya lullubeshi dashi ya zauna agefenshi yana tunane tunane, bayan kudi arayuwan nan d next abu dayake so da duka zuciyanshi is Aadil, maisa Allah yake testing dinshi da abu mafi soyuwa agareshi Aadil and Money?.

 

Related Articles

***
Wuraren shidda na safiya Mami ta bude ido, ganin yanda ta makara gari haryadan soma wayewa yasa tai bathroom agurguje, wanke baki tayi sanan tafito daga bayin daure da alwala, dadduma ta shinfida tai sallan bayan ta idar tai azkar sama sama ta mike da sauri dan zuwa tada Hamida, ahankali tabude kofar dakin bakinta dauke da sallama tana kallon yanda Hamidan ta kudundune kan dadduma tana bacci tana sanye da hijabin Mami, maida kofar Mami tayi tarufe takaraso cikin dakin tana kallon fuskar nata ganin yadan washe shaidan hanun Abie, tsugunnawa tayi agabanta takama hanunta tadan bubbuga tareda kiran sunanta. “Amatullah” saida takira sunan kusan sau uku sanan taji tabude kodaddun idanun nata dake cike da bacci, ahankali Mami ta mika hannu ta dagata zaune tana kallon fuskarta tace “kinyi sallan subhi?” girgiza kai tayi tana sosa ido, hakan yasa Mami tace “but naganki da hijabi akan daduma” cikin siriruwar muryanta dake cike da bacci tace “nakasa bacci ne shine natashi naita salloli” “sorry bansan kin kasa bacci ba ai danazo, tashi yanzu kije ki dauro alwala kiyi sallan kinji” gyadama Mami kai tayi Mami ta taimaka mata ta mikar da ita ta tashi ta shiga bayin itakuma Mami tawuce tafita daga dakin danzuwa fadinma masu aiki abinda za’a dafa, fitowa tayi tai wani irin mugun yaushi gabaki daya tunanin Aadil take jiya takasa bacci hakan yasa ta tashi ta dinga salloli tanamai addu’a ita kadan batasan lokacin data fara damuwa da Aadil hakaba, batasan lokacin daya shiga ranta hakaba, share hawayen dasuka zubomata tayi tasa hijabin Mami ta kabbarta salla, bayan ta idar tai azkar sanan tafara neman Al Qur’ani, akan drawer Mami taga wani hakan yasa ta dauko ta zauna tafara karatu har sai wuraren tara da rabi ta ijiye nan tasamu tadanji dama dama zuciyarta yadan yimata wasai. Tashi tayi ta linke dadduman ta cire hijabin ta ta linke ta ijiye sanan ta shiga gyara dakin gadon da baiwani yamutse ba ta gyara tsaf sanan ta zauna akan gado, shigowa Mami tayi tareda wata yar aikinta data riko tray ta nunamata idan zata ijiye tawuce tafita, ahankali tace “ina kwana Mum” murmushi Mami tayi tace “kintashi lpy daughter na, taso kiyi breakfast nabaki magani kisha kinji” gyadama Mami kai tayi ta sauko daga kan gadon kaman yanda Mami ta umurceta tahada tea tasha da su chips da egg da aka kawo mata tama kasa cinyewa dan sunmata yawa Mami takawo paracetamol takara bata tana murmushi dan sosai takeso ta danne damuwanta kotabama yarinyar strength but itama tunanin Aadil da Abie takeyi bana wasaba.
Sawa Mami tayi akazo aka fitar da tray din ta zauna kusada Hamidan tana janta da hira kadan kadan Hamida ke amsawa sallama akayi big Mum ta shigo dakin cikeda damuwa tace “meya faru sis? Ina Abban su yakai Aadil?” dan murmushi Mami tayi tana kokarin rike kukanta, ahankali Hamida tace “ina kwana Mummy” murmushi Big Mum tayi sosai tace “sannu daughter ya kk” tashi tayi ta kalli tace “lpy lau” ta kalli Mami tace “zanje nai wanka” gyadamata kai Mami tayi ganin yarinyar daurewa itama kawai take tace “dau hijabina kisa karki fita ahaka” hijabin ta dauka tasaka sanan tafita daga dakin tai shashinsu, ahankali tabude kofar shashinsu ta shiga tana kallon ko ina, kafin ta tadaga kafa kaman mai koyan tatata tai hanyar bathroom dinsu bude kofan tayi ta shiga idanunta suka sauka akan some few chocolate dake kasa wanda Aadil yakawo mata jiya, wani kuka ne yazo mata da sauri ta rufe fuskarta da hijabi tanayi kafin tafada kan gadon taja rigan Aadil din datagani akan gadon ta rungume sosai tanajin kamshin shi tana kuka ahankali tace “come back Aadil kaji, come back to me kaji My Aadil, inaso na kula dakai and watch you koda yaushe atare dani kanamin that ur cute smile and talk, i miss you so much” tafashe da kuka ahaka bacci yy gaba da ita sai wuraren azahar ta tashi gyara gadon tayi sanan ta shiga wanka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button