Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 51

Sponsored Links

51…..

 

 

Related Articles

_karki karanta in baki biyaba in kika karanta ina binki bashi pay anan or pay achan_

_Zaki tura 300 kota card kota bank sai nai adding dinki a group din danake posting, 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461, you can also send MTN card to watsapp number na 07012181461_

_masu fitarmin da book kuda Allah_

Hanyar bedroom Abie yayi ganin babu kowa afalon straight cikin fushi yana daga murya yace “ina take zoki barmin gidana, mai bakin jini, mai kashin tsiya daga auroki kindawo mana bala’i” Hamida dake baki bakin kofar bedroom dinne tafara juyowa jin hayaniya da sahun tafiyan mutane, tana ganin Abie tareda Aadil daya fara tsalle zaiyo kanta gabanta yawani irin mummunan fadi sabida wani mugun kallo da Abie yake mata kaman zai chaka mata wuka, batasan lokacin data rike hanun mutum din dataji kusada itaba, hanun big Mum takama tarike gam da
sauri big Mum ta juyo jin anrike mata hannu ganin Abie da Aadil da yarike gama yasa tace “Baban yan biyu yauwa zokaga ikon Allah” daidai lokacin Baffa daya gama kiran liman din masallaci dan d whole scene looks spiritual da jinnish ya kalli Suleman da Muhammadu dasuke kafe a tsaye suna ganin abinda basu tabaganiba aduniya yace “kuje ku shigo da liman koma menene wanan abin ayar Allah yau zata kona manashi” da sauri suka jujjuya suka fita daga dakin ganin Abie a corridor rike da Aadil dayake kokarin fizge kanshi yana kuka yasa sukace “jeka gani kaima Abdullahi, abin mamaki” matsawa Mami databi Abie da kallo asanyaye tayi ganin yafara tafiya big Mum ma ta matsamai suka bashi wuri abakin kofan, sakin hanun Aadil yayi ganin yakaraso kuda da Mami da wani irin gudu Aadil yay wani irin tsalle ya rungume Hamida data makale ajikin big mum yace “oyoyo My Hamida” fashewa da kuka tayi sosai ajikinshi ta kankameshi tama kasa magana but she just miss him, jin muryan Aadil yasa Aabid yajuyo da sauri hada ido sukayi da Aadil daya rungume Hamida yana mata kuka ahankali itama tana kuka, ganin Aabid acikin daki yasa yasaki Hamida da sauri yawani irin ware manyan idanunshi yace “Bid” wani irin tsalle yayi ya shigo dakin batare daya lura da komiba yay wani irin jumping ya rungume Aabid kaman zai kadashi yace “oyoyo Bid” kyam idanunshi suka sauka akan ring din dake aman kudin har lokacin daidai lokacin Abie shima ya shigo cikin dakin, yanda gabanshi yafadi saida dan gajeren fitsari yazubomai daga wando yana tuna warning din OZo aranan da akabashi zoben kudin nan. “koda wasa karka bari zoben nan yay aman kudi agaban idanun wayanda basu taba shan jini ba, danka na zoben nan, karka bari zoben nan yay amai agaban mutanen daba yan gidaba, ka kiyaye, ka kiyaye idanu mashan jini ne kadai aka yarda su kalli zoben nan alokacin dayake baka kudi, idanun masu tsarki wanda suke gauraye da jini kadai sukeda ikon ganin lokacin aman kudin zoben nan, kariga kasan ranan dayake aman kudi sanan kariga kasan lokacin dazaima aman kudi ka kiyaye Tursoso, kakiyayeee”.

Wani irin race da zuciyarshi Abie yafara yasa yaji saliva bakinshi ya bushe gabaki daya zaiyi magana, yana kokarin magana amma maganan taki fitowa sai iska yake fita. “ahhh, huuuu”….

Ahankali Aadil yasaki Aabid yamike tsaye kanshi narawa sosai miyau nazuba daga bakinshi, kafe zoben Aadil yayi da ido yana kallon kullutun jikin zoben yaga yakawo wuta a jan wuta a idanunshi, kanshi yagani ajikin kullutun amma dan karamin shi, yana cikin keji an rufe, ganin Aadil karami yayi yarike karfen kejin yana girgizawa yana mai magana directly. “free me, free me kafin yagama aman nan, ninekai dasuka shanye, nine brain dinka dasuka shanye, free meee nowww, yakusa gamawa” wani irin juyawa idanun Aadil sukayi sama gabaki daya kafafunshi su lankwashe, duk dakin babu wanda ya lura dashi asandare yay baya ya zube akasa gabaki daya asume akan kudaden, ihu Hamida tayi ta shigo dakin da gudu kafin ta iso Aabid ya dagashi afirgice ya rungume kanshi a kirjinshi Mami ma ta shigo daidai nan su Muhammad suka shigo da limam dawasu malamai guda biyu alarammomi, dago kai Aabid yayi ya kalli Hamida data tsaya gefe takasa zuwa kusada shi tafashe da kuka sosai tana kallon Aadil datake so ta taba amma takasa sabida yanda Aabid yarikeshi, kallan Mami Aabid yayi yace “Mami take her to your room ta nemi hijabi tasaka please” tashi Mami tayi takama hanunta suka fita daga dakin Mami ta karbo mata hijabi
.

 

_karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan_

_this book is for sale, just 300 naira zaki turo ta 3107021073 first bank aisha Muhammad, idan baki da account u can send MTN card, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button