Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 52

Sponsored Links

Shiga malaman sukayi suna kallon abinda ke faruwa da karfi liman din ganin yanda baban zobe ke fitar da kudi yafara karanto addu’a. “Bismillahil lazi la yadurru ma’ ismihi shai’un fil-ardi wa-laa fil-samaa’i wa huwas Samee’ul Aleem” yakaranto addu’an yana tsugunnawa yakai hanunshi kan saman idanun Aadil dake hanun Aabid yabude idanun yana ganin yanda idanunshi suka juya sama baka ganin bakin ko kadan, jinin jikinshi yasha batare dayay magana ba ya kalli sauran malaman dake tareda shi, hakan yasa daya daga cikinsu yakalli baffa yace “muna bukatan ruwa a gora Alhaji danka kodai aljanu sun shafeshi kokuma da sihiri ajikinshi” gyara zama limam yayi yana kallon zoben dayake fitar da kudi har lokacin yafara karatun al Qur’ani, sauran malaman suka zauna kusa dashi suka jonashi suna karantowa atare da karfi sosai kaman zasu fasa dakin da zakin murya, wani irin girma zoben yakarayi kaman an huramai iska, Suleman Big Mum tarike gam dan wani irin tsoro taji tanaji kowani mutum na dakin tambayoyine fal aransu daga ina zoben nan yake? Daga ina tayaya yazo dakin nan?

Abie ko kyafta ido bayayi yay kokarin dazaiyi yay magana yakasa kaman wanda aka dinkemai baki yana kallon yanda zoben ke kumbura yana kumbura yana kumbura.
Ayoyi daban daban suke karantawa suna fuskantar zoben wani irin girgiza zoben yafara yana rawa rawa kaman abinda ke shirin fashewa kafin tuss yawani irin fashe ya tarwatse, kumfane yafara fita daga bakin Aadil jikinshi na girgiza kaman mai ciwon farfadiya yana mikewa yana bankarewa da sauri Aabid dake rike yana neman fizgemai yace “innalillah, Malam my brother meke faruwa dashi” cigaba da karatu malam yayi batare daya amsa Aadil ba, wani irin girgiza dakin yafara kaman saukan aradu hakan yasa malaman suka kara karfin karatu suna kiran Allah, rike Baffa Muhammad yayi gam yayi dakin na kara yana making sound kaman sound din guguwa, wutan dakinne sukai kara suka fashe tareda tarwatse wa dakin yay duhu dumdun abunku dadama darene kara karfi karatu malaman sukayi Aabid ya rungume Aadil da jikinshi ke rawa sosai har lokacin miyau nafita daga bakinshi yana zuba awuyanshi.

 

Related Articles

Wani irin bulluwo Ozo yayi da kwarangwal dinshi jikinsu na hayaki sosai ta bango, magana sukaji kaman daga sama maikama da murya irin ta abumai tsoratarwa. “Tursoso kanagani ana konamu kai shiru bakace komiba, Tursosooo!” yakira sunan Abie cikin wani irin fushi tone, tundaga silin gashin Abie nakai har zuwa karkashin tafin kafarshi rawa yake jin muryan Ozo, cikin wani irin yanayi na daburcewa da rashin sanin mai yake fadi yace “O…Ozo the g..great bansan cewa anan nabar zobena ba hala danazo inajan Aadil ne yana fada dani shine zoben yafita daga hannuna, Ozo dan Allah karafumin asiri kayakuri” Abie yakarashe maganan cikin tone din kuka, waya Baffa yaciro tsabagen son ya gasgasata me kunnuwanshi suka gama jiyemai ya kunna flash kaman dukansu sun hada bakine gabaki dayansu harda Aabid wayoyinsu atare suka ciro suka kunna flash light dakin yay haske bauu duk suna kallon Abie da idanunshi yay kuri alamun mara gaskiya sunyi jajir kirjinshi nawani irin bugawa gabaki daya yay wani iri yana kallon Ozo da kwarangwal dinshi dake jikin bangon dakin jikinsu na hayaki while malaman na karatun su har lokacin batare dasun yankeba, wani irin kara Ozo yayi ya buga karfen hanunshi sabida konewan dayakeyi yace “bazaka hanasu konamu ba Tursoso” da sauri Abie kaman mahaukaci ya tsugunna yanajan gwuiwa ya zagayo tagaban malaman yace “kuwa Allah, kuwa Allah nace baniba kudena karatun nan zan fadi muku komi, kunga ran Ozo the great yariga yabaci, inhar kuka konashi kashe Aadil zaiyi, wlh, wlh, billahillazi la’ilaha illahuwa kuruwan Aadil na tareda shi, kai rayuwan Aadil gabaki dayanta ma yana wurinshi, shine ya shanye rayuwan Aadil ya shafemai kwakwalwa, shine ya zamad da Aadil abinan dakuke gani, inhar baku denaba mutuwa zaiyi, zuge jinin Aadil zaiyi tass” babu wanda bai girgiza ba dajin kalaman Abie ba, shiko Abie ko kadan bai damuda wanan ba yasan dukansu babu abinda suka isa sumai, yanada kudin da zai iya kullesu dukansu, yanada kudin dazai iya batar dasu aduniyan nan gabaki daya anemesu arasa, sanan yanada kudin da zaije daganan harbangon duniya inyanaso yaje just to free his self daga shame and talk of the town. Wani jarababben tsawa Ozo yadakamai karfen hanunshi yay haske yace “bazaka hanasu ba Tursoso” da sauri Abie yasa hannayenshi ya rufe bakin limam kaman zaiyi kuka yace “kudena konamin Ozo, Ozo ne rayuwata, shine gatana, yabani abinda wanan mutumin marikina bai baniba dudda uwarshi tacemai yasoni sama da yaran daya haifa amma tana mutuwa ya manta da batun, Ozo ya soni ya fifitani akan duka members yan cult, shiko wanan tsohon yaranshi yafiso, suya sani baniba, dudda nafi yaranshi ilimi nafisu iya aiki, nafisu kaifin basira kullum ninake samamai customers da ciniki a kampani amma daya tashi raba motoci bai baniba yabama yaranshi, Ozo shiya bani kudi saisama har yarshi ta yarda zata aureni da bata aureniba ai, sanan Ozo ya zamaddani popular yabani fame akasanni globally aduka kasashen duniya, nazama babban mutum, kuduba fa duka abubuwan nan dayamin abu daya kawai ya nema awurina shine jinin dan farina, amma dana haifi Aadil nakasa badawa, nama Ozo daya sharemin hawaye butulci sabida yanda nake son Aadil, gadai yaron imbecile amma shine rayuwata duka, Allah ya jarabeni da masifaffen son Aadil, na roki alfarma Ozo yamin da sharadin duk cikin da Maryama zata kara samu tun kafin ahaifa zasu shanye duka, barin Maryama sau uku ba bari bane Ozo nabama yaran nawa tun suna cikin cikin uwarsu, dan Ozo ya chanchanci abinda yafi haka agareni ma, yamin komi a duniya, yaban duk abinda nabukata, inhar kundena konamin Ozo na zan baku ganamasgo manya manya na dollars guda dari uku na rantse da zatin Allah” yafada ahaukace, kabar da hanunshi limam yayi yacigaba da karatun da karfi dan maganganun Abie kara musu karfin guwiwa yin karatun more and more yayi, dole yau su babbaka matsafan nan da ayoyin Allah, su kawo karshen su sanan su kubutar da Aadil, wani irin haske karfen Ozo yafara ran Ozo amasifar bace, kwarangwal dinshi tafara rawa tana narkewa kafafunta sun narke suna diddiga kaman roba da akai melting da wuta, wani irin girgiza karfen Ozo yayi yana nishi yana kallon Aadil da Aabid da gudu Abie kaman zarare ya tube riga yay wani irin tsalle ya tare Aadil da Aabid ya karesu yace “dont kill my children Ozo, na rokeka idan akwai any atom of son dakake min aranka karka kashemin yaran nan, amma nabaka izini ka kashe kowane ne agidanan, kama kashesu gabaki daya banda asara, they’re all bloodline but don’t touch my children please Ozo, Ozo karka kashemin boys dina, Aadil baisan dadin asalin duniya ba, na tauyemai 30yrs of fresh life, kabarmin shi har lokacin da Allah ya kindayamai aduniya su cika karka kashemin Aadil Ozo na rokeka” wani irin hayaki ne ke fitowa daga bakin Ozo idanunshi na fitar da bakin ruwa, karfenshi na wuta sosai yana hayaki, ganin haka yasa Abie ya warware mazariyan wandonshi yace “Ozo kawa Allah karka kashemin yara, kai nace karka tabamin yarana fa, bakajina ne? Karka tabamin yara, Aadil zuciyata ne, karka tabamin yan biyuna, zanyi tsirara agaban duka duniya inhar bazaka kashemin yarana ba, karka tabamin yan biyuna Ozo” kana ganin Abie kasan ya haukace bil hakki dan maganganun dayakeyi basuda kan gado, daidai lokacin Hamida ta shigo dakin da gudu sanye da dogon hijabin Mami hankalinta atashe tana kallon fuskar Aadil dahar lokacin ke kulle bakinshi na fitar da yellowish kumfa tareda hancishi, mugun rudewa tayi batare data lura dasu Ozo ba tai wajen Aabid dake rungume da Aadil da mugun gudu tana kallon fuskar Aadil din ganin kaman yamutu daidai lokacin Ozo yasaki wutan tsafin karfenshi direct sai wutan tsafi yay saitin cikin Hamida ya shige, tsayawa Hamida tayi chak daidai ta karaso kusada Aabid ta mika hannu tana shirin taba kan Aadil dake kan kafadar Aabid ta zaro idanunta gabaki daya tareda daura hanunta akan cikinta tawani irin ja numfashi. “uhhh ahhhhh” sakin Aadil Aabid yayi yawani irin tashi da mugun sauri yatarota yakira sunanta cikin zafin rai. “Hamida!” lumshe ido tayi tabudesu ahankali ta kallai wasu irin hawaye masu dumi na fitowa ta gefen idanunta kafin ahankali wani irin jini with force yagangaro yana bulbulowa ta hancinta da gefen bakinta tai luuuuu hanunta na lilo akasa, riketa gam Aabid yayi zuciyarshi nawani irin bugawa dabai taba yiba in his life yace “ke Amatullah where do you think you are going? Stay with me, i said stay with me okay me and my brother, Aadil needs you, and…and…I..I need you too Amatullah” yay maganan yana jijiga fuskarta hakan yasa kanta yay luu ya kife akan kirjinshi ba alamun numfashi ko kadan atattare da ita wani irin ihu Aabid yayi da mugun karfi. “Nooooooooo! Jewel Noooo!” wani irin tsalle Abie yayi yana sosa kunne yatube boxer din jikinshi yace “yesssss, Ozona you spare my children once again Ozo” kara karfin karatu malaman sukayi trying to handle one situation at a time shine Ozo, hakan yasa jikin Ozo yakama da wuta sosai yana narkewa, ihu Abie yayi yace “noooo Ozo, na shiga uku” yarike kashiyarshi yasaki fitsari yana dariya yace “bari nakashe wutan da fitsari na Ozo na, yauwa kagani, kagani, kagani fitsarina dayawa karka damu saina rama maka zan dauresu, zanyi amfani da kudina na batar dasu a duniya, saimun sha jinin yaransu harda na jikokin su” kara karfin karatun sukayi hakan yasa sosai Ozo keci da wuta yana narkewa kaman dalma yana diddiga hakan yasa kudaden wurin ma suka shiga ci da wuta, alamu Malam yamusu dasu fice daga dakin, Suleman da Muhammad sukadau Aadil dake kwance flat akasa, Aabid narike da Hamida suka fice malaman kuma suka tsaya abakin kofa suna karatun sosai, Abie na ihu batare daya bar wurin wutanba yace “kubar konamin Ozo na, Ozo zan mutu taredakai yau zan mutu taredakai yau” dakin yakama da wuta sosai sukaji Abie yafara ihu kafin yafito daga dakin da sauri yana sossosa jiki yana zaro ido yana dariya, tashin hankali shine abinda idanuwansu yagane musu dis night, wanan abin shine definition of tashin hankali.

 

Jin yanda jikin Hamida yay sanyi ahanun Aabid yasa hawaye ya gangaro daga idanunshi da sauri yay hanyar fita da ita su Suleman da Muhammad dake rike da Aadil biye dasu, Baffa da Big Mum suka rike Big Mum dake wani irin kuka kaman zata shide dan gabaki daya taji bayanin Abie, har sunkai falo tasake fizge hanunta cikin kuka sosai daga na Big Mum takoma Corridor inda Abie ke tsaye yana kallon malaman dake karatu har lokacin yana sosa jikinshi, wani irin mari Mami ta daukeshi dashi cikin kuka tace “ka cuceni, ka cuceni, ka cuceni Abdullahi, ka cuci danmu, ka kashemin yara har uku, yaran da Allah yabani akan son duniya, Allah ya isa tsakanina dakai, all dis while dakai muke wahalan Aadil kaishi asibitici gari gari, daban daban, ashe harda sa hanunka, kawai kallona kake kasan bazai taba warkewaba, Abdullahi, Abdullahi i will never forgive you, all pains din wankin ciki da azaban daduk nasha a wuraren barin yara ukun nan are still fresh a heart dina ashe u were behind it banyafema ba wlh, banyafema ba” tarufe Abie da duka sosai yana mata dariya. “hahahhahah, kekekekee, kyalkyalkyal kyal” fizgota Big Mum tayi tace “let it goo is too late gashinan Allah yafara nunamai ai tajata suka fita daga dakin, sukai tsakar gida, sosai wuta ya shiga ci adakin yana fitowa falo hakan yasa malaman suka fito shashin da sauri daidai Abie yafito yana tsalle ginin part din yawani irin rushe sukayi ginin ya zubo kanshi agabansu kan Abie ya tarwatse Aabid ya runtse ido da karfi hawaye masu mugun zafi suna fitowa daga idanunshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button