Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 10

Sponsored Links

10…

Da sallama ya shigo dakin Goggo, ganinshi dayayi kwance akan katuwar dogon kujera ear piece akunenshi ya lumshe ido yana sanye da white t-shirt sai dogon black jeans yasa yakarasa shigowa dakin, hannu Yusuf yasa ya cire earpiece din daga kunenshi ya jawo hanunshi ya zaunar dashi bude idonshi yayi ahankali yadaura akan Yusuf yay shiru as usual batare dayace komi ba yana kallon shi da idanunshi masu kama da madara, hanunshi Yusuf yaja yana kokarin tadashi tsaye yace “zomuje karakani jor let’s go out” kaman marason yin magana yace “am not going” fitowa daga uwar daka Goggo tayi hanunta rike da goro tace “waye yanzu yatada min da Babana” baki tarike tana hararan Yusuf tace “shine kadatashi Yusufa? Yaro na hutawa abinshi dan bakin ciki” wajen Goggo yaje yace “goggo tayani mai magana please kicemai ya rakani mufita” zama kusadashi Goggo tayi tace “Babana katashi mana kabi dan uwanka kufita, yau kusan wata shidafa kenan baka taba fitaba banda masallaci, jibi kanka kaki aski iye, aya aya tashi kabishi kafin kadawo zan dafama dambu dakaina kaji Dan’nan” ahankali shima Yusuf yace “please Bro for my sake” shiru yadan yi sanan yay musu murmushi yace “okay” sabida murna Yusuf saida ya rungume Goggo suka tafa, tashi sukayi Goggo tarakasu har wajen mota tana musu adawo lafiya kafin sufita tadawo cikin gida.
Dukan glass din window Mujiba tayi zuciyar ta nazafi wani irin ihu tayi ta cire dankwalin kanta tayar “no.. No ooo” kaman mahaukaciya taje wajen fridge ta bude goran ruwa ta dauko ta bude tasha sanan ta ijiye, jin har lokacin zuciyanta bai dena zafiba yasa tace “nooooo nooo yaushe har yawarke daga haukan?? Yaushe, dahar zai fara fita” wani irin ajiyar zuciya ta sauke tace “I have to do something bazan taba bari ka warke daga haukan dakake ba, banason nataba ganin koda digin farin ciki a fuskan iyayenka khaleel, inaso mahaifinka ya daddana azabar dayasani na shiga” goran ruwan takara dauka tasha ruwa sanan ta ijiye tace “Khaleel nadau alkawari bazaka taba samu farin ciki da haske arayuwan kaba har abada, yanda mutuwar Aisha yasa kasami ciwon hauka kashiga kunci da bakin ciki ahaka rayuwar ka zata kare harka koma ga ubangijin ka wanan alkawari nane ni Mujiba agareka” tawani fashe da kuka kafin ta kwallama mai aikinta kira dagudu tazo wani irin tsawa tamata tace “zoki gyaramin kumbana”.

Saida suka shiga hanya sanan Yusuf ya kalleshi ganin yay shiru yana kallon motocin dake tafiya akan titin yasa yace “kasan inda zamu kuwa” girgizamai kai yayi, murmushin jin dadi Yusuf yayi at least yau yana amsamai yace “anguwar tsamiya, Abba yaturani nakai ma Malam Isya wanan kudin” yanunamai wani katon envelope dake tsakakanin su sanan yace “Malam Isya yanada kirki shike kulan ma Abba da gonakin shi saisa duk idan Abba yay zakka yake bashi” shiru yayi yana sauraron shi hakan yasa Yusuf yace “gaskiya yau zakayi aski gashin nan naka yataru dayawa ga sajenka yay bususu, idan zamu koma saimuyi branching barbing saloon ko” shiru yayi baice komiba haka Yusuf yay ta janshi da hira sabida Ya Mustapha yace adena barinshi alone adinga yawan mai hira, Kuma Alhamdulillah ga so much improvement yanzu yau dakanshi yaje dakin Goggo at least yana amsa magana, jiyama shiya koyama Fa’iza assignment dinta, gashi yau ya yarda yabiyoshi sunfita. Lumshe ido yasake yi ya maida hankalin shi sosai Kan tukin dayake yi yana tunanin zuci yace “Ya Allah ka warkar da bawan nan naka gabaki daya, ya Allah kadawomai da farin ciki rayuwar shi, ya Allah kasanya mai danganar rashin Aisha kabashi wacce tafita, itakuma Allah ka jikan ta” haka yayta tunanin zuci harsukakai kai kofar gidan Malam Isya. Parking yayi yafito yadawo ta bangarenshi ya budemai kofan yace “zomu shiga ciki” yatsine fuska yayi “am not going” murmushin jin dadi Yusuf yakara yi ganin yanda yay dogon magana yau yace “okay I will be right back bazan dadeba”. Barin wajen yayi shikuma yadan kwantar da kujeran yay relaxing bayan shi tareda lumshe ido.
Dadan sauri take tafiya wanda yay kama da ahankali, goyone abayan ta wanda yarinyar data goya ke kuka sosai kaman ansatota adaburce Yarinyar tace “yakuri Miemie gawani shago chan muje nasai miki ruwa” ahankali takara sauri harta wuce motarsu Yusuf, Dumm yaji kirjinshi yawani irin mugun bugawa, hannu ya daura akan kirjin tareda kara lumshe idanunshi.
Karasawa tayi shagon abirkice tacema mai shagon “Malam a bani ruwa guda daya” kwanto Miemie tayi daga bayanta tariketa a hannu sanan ta ciro naira hamsin daga jakanta tabama mai shagon takarbi pure water tasa abaki ta bude, sama yarinyar tayi abaki da sauri yarinyar tafara zukan ruwan hakan yasa budurwan tasaki wani murmushin kwanciyan hankalin tace “dats my gurl dama kishi kikeji shine kikemin ihu kaman nasa to kiko, ke wlh Miemie kin iya jarababben ihu” ganin yarinyar na neman shanye ruwan yasa ta fizge daga bakinta tace “cikin ki zai fashe, is okay Miemie” wani irin ihu yarinyar tayi da saida ya amsa ko ina a anguwan dan ihu tayi kaman an yankata, ahankali ya bude ido yana waige waige jin ihu dan kokadan yanzu bayason hayaniya, idanunshi ne suka kai kan yar karaman yarinya dake kan shoulder wata data bashi baya tana jijjiga yarinyar.. “Miemie I promise bazan kara fita dakeba, saidai nabarki agida, sai mutum zai fita kiyita binshi kina kuka kaman zaki mutu inmun fito kiyita min kuka” Mai shagon ne yay dariya yace “hajiya ai haka yara suke ungo chanjin ki” ahankali ta juyo sabida batason ta tada Miemie dataji tafara gyangyadi akafadanta chanjin takarba daga hanun mai shagon sanan ta juyo… Goge idanunshi yayi dan yakara tabbatar da abinda yagani lips din shine suka fara rawa “My.. My… My.. My Eee.. My Eesha”.
[6/9, 3:34 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Related Articles

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button