Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 24

Sponsored Links

Washegari zazzabi ne yarufe Farida hakan yasa Anty Hindu tace ta zauna kartaje school yau Abba Kuma yakira Dr.
Bala ne ya dauketa a mota ana wangale gate ta ganshi yana jogging yauma, baki ta tabe ta dauke kai abinta suka wuce shi dudda haka saida ya daga mata hannu.

Da yamma ma data dawo haka ta ganshi zaune shida mai gadi suna hira murmushi yamata yace “welcome” dauke kai tayi da sauri dan duk inta kalleshi heart dinta bugawa yakeyi ta shige cikin gida da sauri.

Ba karamin murna yay ba da Ammi ta turo mishi su Ilham da Ihsan suzu suyi hutu, ga Fa’iza ma sun suma mid term break hakan yasa gidan yacika da hayaniyan su.
Zaune suka dukan su a katoton falon Goggo wanan Karan ma harda Umma duk sai hira ake shi kadai ne ke kwance ya lumshe ido kawai yana jinsu. Yusuf ne yace “why not mu dan hada get together gobe Saturday da yamma” ihu Ihsan tayi harda tsalle tace “Ya Yusuf wlh is gonna be fun to a ina zamuyi?” shiru yadanyi yana tunani sanan yace “anan falon Goggo but zamuyi decorating, and zaku iya inviting anyone, kawai games zamu buga sai Kuma drinks and have fun shikenan” ya dakama Khaleel duka yace “Ya kagani” batare daya bude ido ba yace “yea” finciko hanunshi yayi yace “bawai Yea ba ATM dinka zaka basu suje kasuwa su siyo abubuwan decorating dakin tsohuwar nan” hararan shi yayi yace “kai maiya sami ATM dinka” dariya Yusuf yayi yace “ai am d organizer ni zanyi handling inviting guest, kai a cash aspect din kawai anan muke bakatan ka, dan ban wayar kama” mikamai wayar yayi ya amsa yace “mezakai dashi?” tashi Yusuf yayi saida yakai bakin kofa sanan yace “I want to invite your Farida” yafita da gudu, da sauri Khaleel yatashi ya bishi yana kiran shi Yusuf Yusuf.
Part dinsu Yusuf ya shiga kafin Khaleel yazo ya kulle yana jinshi yana kiran shi amma yay bedroom ya rufe kofa, zama yay akan gado ya bude wayar dan dama babu key, duba contact dinshi yayi yaga babu wani suna Farida, wajen kira yaduba nan yaga wani number daketa kirashi baya dauka hakanan yaji ajikin shi wanan ne number yay dailing ringing daya ta dauka da sauri tace “Mk” dan dariya Yusuf yayi yace “ba MK bane Yusuf neto” ahankali tace “ina Mk inata kiranshi baya dauka” yace “eh baida lpy ne saisa yasani na kiranki ma, dama munada family get together ne yace he will be happy idan you come” wani murmushi tayi tace “dagaske?” “why not ai yanzu u are part of the family, anyways karna cikaki da surutu gobe ne 4pm sharp, zan miki forwarding address din” da sauri ya kashe wayar jin Khaleel kaman zai cire kofar da bugu ya tura mata address din gidan su sanan ya ijiye wayar yazo ya bude kofan ya ruga da gudu yana kiran Goggo.

Related Articles

*JARABTA*

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button