Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 3

Sponsored Links

3…
Around 9 yakirata ringing uku ta dauka cike da damuwa yace “my Eesha ya muran?” cikin wata irin siririyar murya tace “Alhamdulillah yadena” da sauri yace “are u sure kodai you are just scared ne Kisha maganin daren ki” dan dariya tayi tace “am serious fa, yaragu sosai nasha ma ginger tea dazu Mama tamini” dan ajiyar zuciya ya sauke yace “okay” shiru suka danyi ahankali yace “My Eesha inaso nadan fita” shiru tadanyi kafin tace “ina zakaje?” “just wanna hang out with some friends, colleague dina na birthday yau” kaman mara lafiya tace “okay” kara sassauta muryanshi yayi yace “what? Menene saheeba” girgizamai kai tayi tace “babu komi kawai zanyi kewanka ne” murmushi yayi yace “don’t worry khaleel naki ne my Eesha and I promise dazaran nadawo I will call u is dat okay?” gyada mai kai tayi tace “uhm” “okay I love you bye” ajiye wayar tayi ta tashi tafita jin Mama na kiranta dakin Mama ta shiga ta zauna akan gado tace “Maman mu gani” spoon Mama tacire acikin cup din dake hanunta tace “gashi shanye” karban cup din tayi tana yatmuse baki ita wlh tagaji da wayan nan abun da Mama kebata daga mai bauri, sai mai gishiri da mai daci, gashi ba halin zubarwa agaban ta kesata tasha, ajiye cup din tayi tadau ruwan dake gaban mirror tasha da sauri tana yatsine fuska tace “haaaa Mama daci wlh” hararan ta Mama tayi tace “gulmamma ashe keda Khaleelu so kuke ayi auren dazaran kin gama exam ran Friday nan ko, oh ni ya’su wanan wasu irin yaran zamani ne” Mama tarike baki, zaro ido tayi waje dan bama tagane inda zancen Mama din tadosa ba tace “ni Maman mu” Mama dataji kaman ta make ta tace “eh kefa, to ai bukatun ku yabiya Abban ki yace dazaran kingama final exam dinki dis Friday upper Saturday bikin ki, Kinga yau saura kwana 9 kenan happy?” arude ta dafa kirji tareda zubewa nan kasa afalon tafara rantse rantse cikin kuka “wlh Maa nidai abari sai nan da 4 weeks din, Mama I don’t know wanna leave you please” yanda tadage tana kuka yasa Mama sakin salati da tafi da hannu tace “da jiya kuka gama shirya abunku bakisan zakiyi kuka ba, keda naso immediately bayan kin gama exam natura ki Sudan amiki gyaran jikin 3 weeks shine kukai hadahaden kuko, ai bari Khaleelu yazo Shima jiranshi nakeyi marasa kunyan yara kawai” sosai tafashe da kuka hakan yasa Mama tafita daga dakin tace “inkin gama kije ki dafama auta indomie” nan tabarta sosai taci kukan ta sanan tabar dakin tareda yin kwafa.
koda yadawo yakira yakira taki dauka yasan bata bacci saisunyi waya da kyar ya iya yay bacci batare dayaji muryan taba, da safe ma haka yakira taki dauka karshen ta ma kashe wayar tayi. 11 a makaran tar su tamai yay parking yana jiran tafito daga exam hall sabida 12 zasu gama, 11: 45 tafito tana sanye da milk color Hijab har kasa da bakin flat shoe karasowa yay gabanta ya karbi handbag dinta as usual bata hanashi saidai taki bari suhada ido hakan yasa yagane tana fushi dashi, bude mata gaba yayi saida ta zauna ya rufe sanan yakoma ta dayan bangaren Shima ya zauna yay facing dinta yace “are u happy now kin hanani bacci jiya sanan kuma kin hanani zama nai aiki” wasa tacigaba dayi da yatsun ta batare data kalleshi ba hakan yasa yace “My Eesha menayi talk to me I can’t take dis punishment” shiru tasake mai hakan yasa yace “please” kwallan daya zubo mata ta share da sauri tace “mesa kasa aka maida bikin upper Saturday” takarashe maganan tareda rera mai wani sabon kuka ahankali, dan murmushi yayi tareda shafa kanshi yace “to everyday u keep driving me crazy nakosa ki zama tawa” yakarashe maganan yana dan dariya ciki ciki hakan yasa tasake harzuka takara narkemai da kuka kama bakin shi yayi yay shiru yadan daure fuska ya dafa kanshi tsayar da kukan tayi ta kalleshi cikin shagwaba tace “what?” kaman zaiyi kuka yace “bakomi yaune na gane cewa am just wasting my time amma baki taba sona ba my Eesha, I feel like hanging my self nahuta, no I feel like na shiga beach ruwa yatafi dani, no I feel like namaida kaina kifi kawai asoyani aisaiki huta ko” yakarashe maganar tareda kifa kanshi a sitiyari mota dan inyacigaba da kallon ta dariya zaiyi sabida yanda yaga tashin hankali karara akan fuskarta, ta tsani ta ganshi cikin damuwa hankalin ta tashi take. Dawata irin calm voice tace “am sorry” girgiza kai yayi batare daya kalleta ba yace “No my Eesha u are not, kawai ki barni naji dakai na” kaman mara gaskiya tace ” kayakuri to na yarda” murmushi yayi ya dago kanshi ya kalleta tareda kara narke mata yace “a’a abarshi in four weeks time din kinsan bazan iya jure kina fushi dani ba, I can manage myself tunda baki damu daniba” da kyar ta shawo kanshi sanan suka shirya yay parking agaban gidansu ya kashe motar dago da kanta tai ta kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta sakinmai murmushi tace “infadama wani secret?” da sauri yace “yes my Eesha” bakin hijabin ta tarike tana dan murmushi hakan yasa yace “ha’an tell me nakosa” shiru tadanyi tana dan waswasi kafin tace “kasan mesa at first I was angry danaji an matso da bikin kusa?” “No” kaman zatai kuka tace “naga wani agogo” tadanyi shiru tare da juyar da kanta ta kalli window motar tace “dama tara kudin dinkin danake yi nakeyi har kudin yacika in saima, ranar bikin mu agogon nakeso kasa, but kaga yanzu bangama tara kudinba kuma kasa anmatso da bikin kusa” jin yay shiru baice komiba yasa ta juyo da kanta ta kalleshi tsantsar sonta tagani kwance akan fuskar shi hakan yasa tamai murmushi wani irin gauron ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe ido danji yake kaman yajawota ya rungume iska yaji anhuramai a fuska hakan yasa ya bude ido ya saukesu akan kakkyawar fuskarta cikin tsantsar kauna dawata irin calm voice yace “incika miki kudin kisaimin my Eesha?” girgiza mai kai tayi tace “I want to use my hard earned money, da gumina nakeso nasai ma dashi inda bahaka ba danai amfani da kudin da Abba da Ammi keban tuntuni, nasan zan sami dinki I will be able to complete the money” hannunta yakai zai kama da sauri ta janye tana hararanshi ahankali tareda murguda mai baki ta bude kofar motar tafita ta bude gate ta shiga gida.
Hannu shi ya daura kan kirjinshi dake bugawa very fast ahankali yace “Ya Allah kabani Eesha” kunna motar yayi yabar anguwan.

Bude ido yayi afirgice ya kalli agogo zaro ido yayi yace “wat those girls will kill me today” agurguje yafada bayi yay wanka yafito ya shirya cikin farin shadda gizna dayay mugun karban shi yadau turare ya feshe kanshi dashi sanan yadau waya da car keys dinshi yafita daga dakin da sauri dakin mum ya shiga yace “morning Ammi” ajiye littafin Azkar din dake hannunta tayi ta kalleshi tace “ango in the next seven days antashi lafiya” murmushi yayi kaman baijiba yadau mug din tea daya gani akan stool din dake gaban Ammi ya kwankwande sanan ya ijiye mug din yace “Ammi ina su Ihsan” tabe baki tayi tace “nizaka tambaya kasan kunyi alkawarin yau asabar karfe tara zaka kaisu shine yanzu ake ganinka ai sunce sunfasa zuwa hanyar kofa yayi zai fita Ammi tace” Son” juyowa yay yace “Na’am Ammi” mayar da kanta tayi kan littafin hannunta kafin tace “anjima yan uwan babanku da babar ka zasuzo yau za’akai akwatin” takarashe maganan tareda dago kanta tana kallon fuskar shi wani kunyar Ammi yaji yakamashi hakan yasa yafita dakin da sauri ya shiga dakin su Ihsan. Dariya Ammi tai kawai ta kada kai babu wanda yasan halin dan nata kaman ita.
[6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button