Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 57

Sponsored Links

Batare daya dago kaiba yace “Islaaam” kadan ta kallai dan wahalan bude idanunta duka takeji sosai, murmushi yay ya matso da kujeran saitin fuskarta yasa hannu yana shafa kitson kanta ahankali ya sumbaci forehead dinta sanan ya shafa wurin yana kallon fuskarta murya chan ciki yace “I have to go yanzu 7 ake koran mutane but da sassafe zanzo gobe” shiru yay yana kallon fuskar ta ganin kaman tai bacci danta lumshe ido, addu’an bacci ya tofa mata sanan ya matsar da kujeran baya yatashi, yadade a tsaye kafin ya juya da zumin tafiya hanunshi yaji takama da sauri ya juyo ya kalleta, girgiza mai kai yaga tanayi da dan idanunta data bude kadan ga wasu hawaye dasuke gangarowa ta gefen idon, da sauri ya kwanto da kanshi daidai saitin fuskar ta yasa hannu ya share hawayen ahankali yace “u don’t want me to go” daga kai tayi wanan karan tana kuka sosai, “okay nafasa tafiya” yafada tareda zama ya riko hanun nata data rike shi dashi yana shafawa kadan kadan, dayan hanun Kuma yana share mata hawayen datakeyi sanan ya ijiye hanun agefen filon yana shafa gaban goshin ta, ahankali tasanya fuskarta cikin hanun tareda sauke ijiyan zuciya sanan ta lumshe ido within 3min bacci yay gaba da ita, numfashin ta dayaji yana sauka ahankali ahanunshi yasa yagane tai bacci, ahaka wata nurse ta shigo dakin cikin harshen turenci tacemai lokacin tafiya yayi yatashi yatafi itace mai kula da ita, kallon fuskarta yayi kafin ahankali ya zare hanunshi ya mike tsaye tareda sanya hannayen acikin aljihu ya tsaya yana kallonta kara komawa yayi ya tofeta da addu’a sanan ya juya yafita daga dakin yana leken fuskarta. A reception yasami Ihsan sanan suka fito daga asibitin taxi yatare musu suka shiga, tafiyan kusan 20min sukayi sanan sukai parking agaban wani dan madaidaicin gida, kofar ya bude ya shiga Ihsan na biye dashi Yaron dazu suka tarar yanata mopping kasan dakin murmushi yamai yace “weldone Raymond” zama akan daya daga cikin kujerun yay yana kara karema gidan kallo, babban falone da akamai penti off white irin dakunan turawan nan saita bangare daya kuma kitchen ne wanda komi yake a gyare, sai dan corridor da dakuna biyu ne awajen kowanensu da bayi aciki, saida Raymond yagama yamusu sallama yatafi shikuma yatashi ya shiga daya daga cikin dakunan hakan yasa Ihsan ta tashi itama ta shiga dayan dakin dan yin wanka tai salla saita fito tadan sama musu abinci.

Zaune yake shida Anty Hindu suna magana akai sallama jin muryan su Abban Khaleel yasa yatashi tsaye yana murmushi tareda basu izinin shigowa ganinsu tareda Farida idanunta sunyi zuru zuru yasa ya daure fuska ya nuna mata kofa “fitan min daga gida, fita nace” fashewa tai da kuka ta tsugunna jikinta har wani barbar yake tace “Abba dan Allah kayakuri kayafe min” Su Abban Khaleel ne suka saka baki suna tausasa shi da kyar ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Anty Hindu gyadamai kai tayi hakan yasa ya kalleta ya gyara murya yace “shikenan na hakura amma inada sharadi daya kifito da miji nan da sati biyu kokuma nahada ki daduk wanda naga dama namuku aure” sosai take kuka tana share ido, Anty Hindu sai wanke ta da harara take tace “tayaya ma Farida har kikasan da sniper kika bama yar uwarki, Farida bamu baki irin tarbiyan nanbafa, maisa kika bama yar uwarki guba?” shiru tayi tana matso kwalla Anty Hindu tace “badake nake magana ba” da sauri ta share hawaye da kyar tace “ranan da Bala ya kaini gidan tun kafin yay parking akofar gidan mukaga wata mata a tsaye baka tanada dan jiki, yana parking nafito zan bude gate na shiga sai kawai naga takira sunana Farida, nace mata Na’am, na tambayeta ya akayi kikasan sunana, murmushi tamin tace ai taganni randa nazo gidansu get-together, shine tacemin wai yanzu na yarda kanwata ta aure wanda nakeso bazan yi komiba niba mace bace, shiru nayi bance mata komiba, shine tacemin Ina sonshi? Ahankali nace eh, tace amma ai nasan idan kanwata ta mutu zai aureni nace mata eh, shine tabude jaka tabani sniper tace gashinan nasan yanda zanyi nabata idan tamutu ai shikenan zan auri wanda nakeso” shiru tadanyi tana goge hawaye kowa na falon na kallonta ahankali tace “wlh Abba banyi niyyan bata ba, nidai kawai na karba ne dan kaman tamin asiri tana bani na karba nasa ajaka na shiga cikin gidan, to Ina ganin fuskar Khaleel dinne shine shine wlh bansan meya shigeniba shine na a.. ” takasa karashe maganan tana kuka sosai da kyar tai shiru Abban Yusuf ne yace “matar tafadi miki sunanta?” girgiza kai tayi tace “a’a tadaice taganni randa nazo get together, ni bansan taba” shiru kowa yay na falon Kafin Abban Khaleel yay dan murmushi yace “komi yawuce Allah ya yafemana gabaki dayan mu, tashi kitafi abinki” Ahankali ta tashi tafita daga dakin dakin Mum ta shiga ta rungume Mum tana kuka, tureta Mum tayi ta harare ta tace “Farida kinsan kai, haba Farida a ina kika koyo wanan mugun halin, tausayi kawai kikabani saisa na rokesu ayafe miki amma da wlh bazan yiba, haba wanan bakin hali har ina” shiru Mum tayi jin tasake rungume ta tana kuka kaman zata mutu hakan yasa tashiga bubbuga bayanta tana bata hakuri tace “bakomi zakaso ka sameshi ba Farida, Allah ya jarabce ki dason bawan Allah nan amma hakanan zaki dau dangana danba mijinki bane” tai maganan tana share mata hawayen dake zuba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button