Jarabta 8
“But gobe in Allah ya kaimu da safe sai mu kaishi clinic dinmu a dubashi” kowa kasa magana yay afalon da kyar Abba yace “mungode” Sallama yamusu yatafi zuciyar shi cike da tausayin Khaleel, Aisha bata amma Khaleel kai Allah gamu gareka, girgiza kai yayi yatafi kawai. Gabaki dayan su a falon suka kwana dan sosai Khaleel ke surutai cikin bacci.
Around 8 baban Aisha yazo shirye cikin suit bakake da kyar Yusuf suka fito dashi suka sashi amota sanan aka tafi asibitin wani babban likita daya kware a bangaren mental Baban Eesha ya kaisu wajen shi, nan yazo gaban Khaleel ya tsaya ya dudduba shi sanan ya Kalli Daddy dayay shiru yana kallon ikon Allah yace “Ya sunan shi?” Abba ne ya iya yay magana yace “Muhammad Khaleel” rubuta wa Dr yay a file din daya shigo dashi ya maida duban shi ga Khaleel daketa motsi da bakin shi, “Khaleel” Dr yakira sunan shi, shiru kaman ma bada shi akeba, Yusuf ne ya matso wajen ahankali yace “Dr tun randa abin yafaru bai kara mana magana ba, is as if baima sanmu ba” rubuce rubuce Dr yayi, ya dauko wani abu kaman bindiga ya daura akanshi nakusa 1min sanan ya cire, rubuce rubuce yayi sanan yamika musu prescription sheet yace “asiyo mai wanan magungunan” Ahankali Abba yace “meke damunshi?” murmushi Dr yayi yace “post traumatic stress disorder, but zai dinga zuwa therapy bayan kwana bibbiyu, and zan sashi a medication, bayan 2 weeks inhar babu improvement sai musan abin yi” godiya sukamai sanan Yusuf yatafi siyo maganin suka tafi gida.
Yau kimanin 2 weeks kenan gidan nan babu wanda bai rame ba sabida Khaleel, babu wanda yake yadda dashi baya wanka, baya ma kowa magana abinci ma ko Ammi tasamai abaki wanda yaga damane zai hadiye sauran akasa, har yanzu Baffa da Family shi basu komaba dan bazai taba iya tafiya yabar kaninshi da wanan wahalar ba yasan yanda kaninshi keson Khaleel, bashi kadai ba duka familyn ma akwai wanda bayason Khaleel ne.
10 a office din Dr yamusu ajiyar zuciya Dr ya sauke kafin ya Kalli Abba yace “Sir Khaleel yaki responding to treatment, inda acema ya yarda yay magana ne ko awajen therapy dinshi ne it would have been a great difference dakomi yazo mana da sauri” “to to Dr yaza ayi yanzu?” cewar Abba “Alhaji yanzu is time for the second treatment abinda nakeso daku shine ku cire, kokuma ku fitar dashi daga environment din incident dinan, inma da hali yabar Abuja for now, ai zaku iya daukar mai excuse a wajen aiki na medical leave ni zanmai recommending, duk wani abu dazai dinga tunama kwakwalwan shi Aishan ku nisan tashi daga abin, kana ganinshi ahaka kome daya dangan ci Aisha yasani so ku nisan tashi daga memory and ku dinga cheering dinshi up now more than ever he needs love da pampering kome yakeso kumai koma menene shizai sa yay healing fast” godiya sosai suka mai sanan suka tafi.
Koda suka kai gida kwantar da Khaleel sukayi a dakin shi Yusuf ya zauna dashi, Ammi dasu Umma Abba ya kalla yace “kubiyo ni” falo suka fita suka zazzauna Abba ne ya Kalli Daddyn Khaleel yace “inason na wuce da Khaleel yola kaman yanda Dr yabamu shawar anisan tashi daga nan koya kagani achan saimuga Yaya zaiyi healing idan babu improvement saimu fita dashi waje koya kagani” gyada kai Daddy yayi ahankali yace “to Yaya nima nafison hakan, ke Amina saiki hadamai kayan shi ko” gyada kai Ammi tayi da sauri, Ihsan da hawaye ya cika mata ido tace “Abba nima zan biku” Ammi ne ta kalleta tace “exam dazaku fara next week fa? Don’t worry duk lokacin dakukai hutu saikuje ku dubashi” murmushi Umma tayi tace “addu’an ku Khaleel yafi bukata yanzu bawani abuba, Alhaji tun jiya Gwaggo ke kirana tana tambayana yaushe zamu dawo bansan mezan cemata ba” “banason na tada mata da hankali ne, idan mukoma ma fadi mata meya faru” wani irin murmushi Mujiba tayi tana kallon fuskar Daddy Khaleel tana kada kafa.