Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 19

Sponsored Links

[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *#I’ll take a revenging*

Ruma ce tsaye a tsakiyar parlourn hannunta ɗaya a kanta tana zunduma ihu ɗaya hannu kuma riƙe da trolley ɗinta cike da kayanta, ta zube a ƙasan carpet tare da yin zaman ƴan bori ta ƙara zunduma ihu ta ce “Na shiga uku na lalace, na shiga uku Shikenan mutuwa zan yi na gama yawo ajalina ya zo, innalillahi wa’inna ilahir raji’un” Kuka take da kururuwa wanda hakan ya ƙara ɗaga hankalin duk wanda yake wajan, Abbu dake part ɗinsa kwance ba lafiya ya fito da ƙyar tare da jingina da jikin bango yana shigowa kuma abin da idanunsa ya fara gani shi ne Majeederh, ya tsura mata Idanu kafin ya sauke numfashi yana rufe Idanu, a rikice Yaya Bilkisu ta nufi wajan Ruma ta ce “Ke lafiya? Waye ya mutu mijin naki ne ko?” Ruma na kuka wiwi ta ce “Ni na mutum Yaya, ni ce na mutu na shiga uku na lalace wayyo rayuwata” Maman Alpha ta ce “Don’t Force her, ku bata bottle water mai sanyi” Majeederh ta nufi wajan fridge ta ɗakko ruwa tare ɓalle murfin ta zuba mata a cup, Yaya Bilkisu ta amsa ta bata ta sha sosai, tana gama sha ta kifa kanta tana sauke ajjiyar zuciya sai kuma ta ƙara fashewa da kuka, ba wanda ya ce mata komai, Mami zuciyarta ta tsinke ta shin ya nuna ƙarara akan fuskarta, daman ita bata iya fargaba ba ta miƙe da sauri sbd cikinta daya juya ta nufi toilet, Yaya Bilkisu ta kalli Abbu cike da tausayawa ta ce “Ka zauna mana kai da ba lafiya ba” Ya zame idanunsa daga kan Majeederh wacce take ɗan danna waya tana son kiran Aaliyyah ta ji ina ta tsaya, calmly yana rufe Idanu ya ce “No, am ok here” Ta ce “To Allah ya kyauta, Ubangiji ya rufa mana asiri abu daga wannan sai wannan Allah mun tuba ka yafe mana” Maman Alpha ta kalli Ruma ta ce “What’s happening to you dear?” Ruma ta miƙawa Maman Alpha gwajin da Dr ya bata, ta miƙe tsaye da sauri bayan ta duba zufa na yanko mata all over herself ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Hasbunallahu wani’imal wakil, what is this? How can that be possible?” Ruma ta sake fashewa da kuka,Maman Alpha ta ce “Don ubanki maza kike bi ko me? Garin yaya haka jama’a mun shiga uku” Cikin Mami ya ƙara juyawa ta miƙe da sauri zuwa toilet a karo na babu adadi Ruma ta ce “Wlh tallahi ni ba ƴar iska bace, bani da lafiya zazzaɓi ciwon kai ga rama shi ne naje ganin Dr ya bani text na na wannan ina dubawa naga the result was positive, amma ban taɓa iskanci ba wlh” Yaya Bilkisu ta ce “Wai dan kwatagwal ubanku meke faruwa ne, kun sa ina jin kamar na yi zayo a wando” Maman Alpha ta ce “Yaya wai fa Hiv ne da ita” Yaya Bilkisu ta ce “Uban uwar meye kuma Hiv, wani abu ne haka” Ta ce “Ƙanjamau fa Yaya” Yaya Bilkisu ta ce “Sunan waye haka kuma ba daɗin ji” Maman Alpha ta lura ruɗewa ta sanya Yaya Bilkisu faɗin hakan, ta ce “Ciwon ƙanjamau fa” Yaya Bilkisu tayi shiru kamar mai tunani ta ce “Hiv, ƙanjamau cuta mai karya karkuwar jiki fa?” Ta fashe da kuka ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, Ubangiji Meke faruwa da iyalan khan ne? ALLAH mun tuba Allah, Ubangiji ka dube mu da idon rahama” Mami ta kasa cewa komai sai ajjiyar zuciya take saukewa, Majeederh kukan tausayin ƙanwarta ya kama ta mance da abubuwan da suka dinga mata, har murna take ta ƙwace mata saurayi, ke nan da tuni itace da wannan wahalar? Maman Alpha ta ce “Ina Imran ɗin to?” Ta ce “Ashe all this year’s soldier ne, na air force he just pretend, da aikin shi da iyayensa duk na bugi ne, wani babban aiki ya kawo shi ne wanda zai ɗauki shekaru shi ne ya yanke hukuncin yin aure, before he leave the country, tunda mukai aure bai taɓa cikakken kwana uku a gidana ashe yawon neman mata kawai yake son ran shi, zai zube kayan abinci kuɗi da komai amma babu kulawa bai damu dani ba, idan naga murmushi a fuskarsa to dare ne buƙata ce ta kawo shi, wlh ban taɓa sanin bashi da lafiya ba, i didn’t noticed that, wlh ni an cuceni da aka haɗani aure da shi bayan kun san bashi da Iyaye a nan gashi ya saka mini ciwo mutuwa zan yi ban mori komai a duniya ba, ba ɗa ba jika tunda sai zubar mini da ciki yake har ƙwayoyi sun daina aiki a jikina” Gabaɗaya wajan ya yi shiru, aka rasa wanda zai magana musamman Abbu da Mami, shi tunani yake waye kuma Imran ya akai aka bashi auren Rumana? Ruma na kuka ta ce “Me ya sa Abbu? Anti Jeederh Imran ya ce yana so, me ya sa ka bashi kuɗi masu yawa sbd rabo da ita ni kuma ya aureni, why Abbu sbd ni baka so na Anti Jeederh kawai kake so? Kasan halinsa shi ya kaƙi yarda ya aureta sai ni, to ni me na yi maka? I’m not your child or what?” Mami ce ta ɗaga hannu tare da zabgawa Ruma tagwayen maruka ta ce “Enough Ruma, zafin ciwo da ƙaddara ba hauka bane mahaifinki bai yi lalacewar da zaki faɗa masa haka ba” Ruma ta dafe kunci ta ce “Ƙaddara? Me ya sa za ayi wa ƙaddara ƙarya? Bayan babu ruwanta ko da ruwanta to siya mini ita akai, Abbu plan everything, shi ne ya siya mini wannan ƙaddarar” Kuka take sosai, Maman Alpha batai mamakin ƙaddarar data faɗawa Ruma ba, da kuma rashin kunyar da take shimfiɗawa Abbu, ko da Abbu baya cikin hayyacinsa ya yi wa Majeederh all abubuwa da ya yi mata, to fa Ubangiji ya ba zai barshi haka ba, Majeederh yarinya mai tsananin biyayya haƙuri, komai zai ce mata she never said no! To her father.
“Ruma what are you saying? Me kike cewa haka? Abbu ne fa your father?” Ruma ta ce “And so f***ck what? Ki saurara mini Anti Jeederh kuma dole ki ce haka sbd ya kuɓutar da rayuwarki ya hanaki auren Imran ni ya bani, sbd ya fi so da ƙaunarki, sbd ya fifitaki daga cikinmu, sbd ke arziƙin shi ce kina kawo mishi kuɗi, to halayyata tayi bambam da naki, I’ll take a revenge on it” Ta yi murmushi ta ce “I’m still wondering bayan ga Aaliyyah why he choose me? Wonderful”
“Kin san wanne kalaman bakin ki ke furtawa haka Ruma? Ta ya ya kike tunanin mahaifinki zai zaɓa miki mijin da ba na gari ba?” Ruma ta yiwa Majeederh wani wulaƙantaccen kallo ta ce “Zahiri, baki san zafi da raɗaɗin da zuciyata ke mini ba, shi ya sa har kike iya tsayawa a gabana kike fada mini magana banza da wofi, My life is ruined because of you and your father” Majeederh ta saki baki, zuciyarta na tsinkewa sbd jin abinda da Ruma ta faɗa, ta ji ƙirjinta na ya mata nauyi, ta rasa madafa da kuma ma’adanar da zata saka mugwayen maganganun na Ruma, masarrafar da zata samawa jirkitaccen zancen nata tubalin ginawa da kuma fahimtar shi da kyau ya tsaya mata da aiki, tayi jigum da ƙyar kuma ta haɗiye wani bushasshen yawo ta ce “Ruma!”
“Baki da iko ko zarafin yi mini ihu akai na, ki barni da abinda mahaifinki ya jaza mini just because of you! Sbd kawai ke” Majeederhn was thinking akan anya Ruma hankalinta ɗaya, ta ja numfashi ta kalli Maman Alpha ta ce “Mene laifina? Me na yi mata da zata alaƙanta hakan dani? Me ya sa kullum zuciyata bata rabuwa da damuwa ne?”
Maman Alpha da tayi shiru sbd tashin hankali da mamakin sabon hali irin na Ruma ta ce “Hisabin duniya ya bata nata kason, you sow and you reap” Ta juya ta kalli Ruma ta ce “Kin san duka nan ba sa’anki ko? Ba kuma wanda zai ɗauki sabon iskancin da kika zo da shi, don haka ki saurara ki nutsu ki rungumi ƙaddararki mu taru mu nemawa juna mafita, babu wanda bashi da abinda ke damunsa a wannan rayuwar kin gane? Don haka let by gones be by gones” Ruma ta ce “Wannan ƙaddarar tare daku zan rabata, zaku ce na faɗa muku” Mami ta zabga mata mari zata ƙara mata mari ta ce “Stop! Mami kada ki sake marina, ai kina kallo aka yi auren You neva said anything balle ki yi yunƙurin hanawa” Yaya Bilkisu ta ce “Ah to! Ke banza ce kuma baki zama abar tausayi ba wallahi tallahi, ki fito ki ce sbd a hana Majeederh aure ke ki auro aka tauye hakƙinta aka rabata da shi ta ƙarfi da ya ji ba don bata son shi ba, kuma da rabon ba zai zama Mijin Malama ba, kwaɗayi da son abin duniya ya sanya kika miƙa hannu bibbiyu kika amshi soyayyar shi ba tare da kunya ko shakkar ƴar uwar taki ba, babu kalan wulaƙancin da ba ku yi mata ba sai wanda kuka manta, rashin kunya kowa kamar ba gaba take da ku ba, Kinga kenan hakƙinta ke binki shi ya sa kika tsinci kan ki a haka warrrrr” Yaya Bilkisu ta faɗa tana buga cinya kafin ta kalli Abbu ta ce
“Sai ka shirya domin yanzu ka fara gani, ta ce ƙaddarar tare zaku ɗauka ku rabata kashin dankali, amma babu abinda zai samu Majeederh da izinin Allah, ka cire Majeederh daga cikin zuri’ar ka, ka mayar da ita matacciyya bayan tana numfashi a duniya, ka ce baka da wata yarinya mai irin sunan Majeederh, to Allahamdulillah! Ni na ji daɗin hakan gashi nan ƴar cikinka a kan idanunka a gabanka da hankalin ta da komai ta ce bata da haɗi da kai, kayi zaton Majeederh zata lalata maka sunanka dana family ko? To gashi nan ita Ruma ta ɗakko hanyar yin gutsi-gutsi da sunan” Ta juya kan Mami ta ce “Ke ma ishara ce, akan idanunki sukewa Majeederh tsiwa da baƙaƙen maganganun amma sai kin yi niyya kika tsawatar da su, kunnen uwar shegu kike ai, da aka zo da maganar auren Imran hadda ke a amsar auren bayan kin san akwai alkunya a haka, ai duk wanda ya sai rariya ya san zata zubar da ruwa, uhm! Rayuwa kenan wai anwa uwar kwarto Fyaɗe ya ce mama riƙe mini wando ina dawowa” Yaya Bilkisu tayi musu tas, Majeederh ta zauna banda kuka babu abinda take bata son tashin hankali bakiɗaya a rayuwarta, Abbu jin zancen kawai yake baya fahimta, shi tun abinda ya yi wa Majeederh har yanzu bai ƙara jin abin da ya sanya shi shocked ba irin aurenta da Khalil ba, Uncle Isma’il daya shigo yanzu ya ce “What did i missed?” Yaya Bilkisu ta ce “Gulma” Mami ta shige ɗaki ita ko kukan ma ta gagara yi, Ruma ta miƙe ta kalli kowa sai kuma ta ja trolley ɗinta tayi waje…
Yaya Bilkisu ta ce “An jima ki shirya zaki ƙunshi da saloon” Majeederh ta marairaice fuska ta ce “A’a” Domin haka kurum tsinkewar gaba ke damunta da kuma wani irin sabon yanayi dake saukar mata yaba tsirga mata a zuciya. “Ke daman duk wata harkar mata na kwalliya baki sani ba, haka zaki gidan mijin da farar ƙafa kamar ƙafar tinkiya? Maza tashi” Maman Alpha ta ce “Ki sanar masa zaki fita” Ta ce “Ni na ce masa me? Bani da number shi ma” Maman Alpha ta zaro wayarta ta kira Khalil ta jima tana ringing kafin a ɗauka, cikin kamilalliyar muryarsa mai nutsu da sanyi mara hargitsi ya ce “Uhm” Ta ce “Ibrahim ur wife want to speak with you” Ta bawa Majeederh wayar ta yi shiru, yana jin yadda numfashinta ke sauka, a hankali ya jingina da jikin motarsa wacce driver ya kawo shi airport Maman Alpha sai zabga mata harara take, shi dai ya na ji so yake yaga ƙarshen girman kan nata yau, muryarta na rawa ta ce “Zan fita ne” Ya ce “To where?” Ta yi ƙasa da murya sosai har sai daya lumshe idanunsa yana jin gajiya da kasala na saukar masa dalilin numfashinta da yake ji ta ce “Saloon” Ya ja numfashi tare da saukewa yana riƙe kansa sbd wasu abubuwa dake bin jikinsa kamar yana ya ce “To wa za kima?” Ta tura baki ta ce “babu” Ya ɗan girgiza kai kawai ya ce “Take ur time, i keep my wife waiting a jirgi” Yana faɗin hakan ya kashe wayar, Maman Alpha ta ce “Ta shi kije Uncle ɗinki zai bada kuɗin” Majeederh ta ce “Ni na fasa” Ta ce “Baki isa ba” Hawaye ya taro a Idanunta ta ce “Yana tare da matarsa fa ya ce mini” Ta riƙe haɓa ta ce “Ke dai kamar ke kaɗai ce ƴar fari duk wani rashin wayo da wawta an bar miki haba” Wayar majeederh dake wajan anti tayi ƙara alamar zuwan notification taga alert na 200k daga Khalil kuɗin saloon ɗin kenan ya bada a tunanin Maman Alpha
Da daddare Majeederh na zaune sai ga Latifa Omar ta shigo fuska sake ta ce “Kaga Amaryar Bad boy” Majeederh ta ɗauke murmushin da take ta ce “Waye haka?” Ta ce “Bad boy mijin Malama” Ta ce “Idan baki kira real name ɗin shi ba ba dole, idan ba haka ba I’ll show you the other side of me” Latifa ta riƙe haɓa ta ce “Iyee kaga farin shiga” Ta ce “Da tsohon hannu da sabo duk hannu ne, don haka duk matan aure muke” Latifa tayi yaƙe kawai ta ce “You’re right, shawara na zo nema” Tayi shiru ta ɗora da cewa “Aliyu ne zai ƙara aure, waya baturiyar ƴar uwar shi” Majeederhn ta ce “Allah ya haɗe kan ku” Latifa Omar ta ce “Bana son auren, wlh ba zan iya sharing mijina da kowa ba, he’s my husband ni kaɗai and he still be mine forever” Har Majeederh ta yi shiru sai kuma ta ce “Sharing kamar wata idea?” Latifa ta girgiza kai ta ce “Ba zaki gane ba, kin yi tunani kina tare da mijinki ku kwana tare da juna, gida ɗaya ɗaki ɗaya gado ɗaya manne da juna, rana tsaka akawo miki wata? Duk abinda zai miki biyu zai raba fa, duk abinda yake miki a kan gado shi zai mata duk wasu kalaman soyayya da zai faɗa miki itama haka” Gaban Majeederh ya yanke ya faɗi, nan da nan taji kanta ya sara zazzaɓi na neman rufeta ruf, zufa ta shiga yanko mata all over herself “Are you okay? Ina Khalil ɗin wai kowa ba ƙarya ya yi ya ce shi ɗan President ne?” Majeederh ta kalli haka Latifa ta ce “Ko?” Ta ce “Wlh ina faɗa miki” Majeederh ta miƙe ta ce “idan ƊAN MALAM ne shi i love my husband the way he’s” Kwana biyu Majeederh bata saka Khalil a Idanunta ba, ko a waya baya nemanta gabaɗaya, Maman Alpha kullum sai ta zo, yau ma duka familyn duka suna nan Majeederh ta rasa meke faruwa, taga dai kaya iri ɗaya kamar pink color kamar plush pink, Zizi ce ta shigo sai Badi daga nan kuma aka dinga shigo sai akwatuna kamar yaƙi sai da aka shigo da set 6, in a different color pink, white, black, blue black, brown ko wacce ta wani ɗan ƙaramin kwando an ciko shi da abu an ɗora wani white net a sama, jama’ar wajan suka dinga kallon kaya hadda maƙota, Latifa na zaune zufa kawai take so take ta ji na waye, Maman Alpha ta tashi ta zabga wata uwar guɗa “Ayyy yiririri ayy yiririri!” Ta buga cinya ta ce “Allahu Akbar, mahaƙurci mawadaci wlh ko yanzu na mutu Alhmd naga wanda zai tsayawa Majeederh, ku kalli arziƙi ku bar arziƙi a mazauninsa kayan lefen Mrs Ibrahimul-khalil kenan the president’s son” Gabaɗaya ƴan matan suka fito da iPhones ɗin su aka shiga yima mahaukatan kayan vedio da pictures kai tsaye ake ɗorawa a duk wani internet, TICTOK, I.G Twitter aka saka “Kayan lefen Mrs Ibrahimul-khalil Ɗan shugaban ƙasar Jamani” Aka dinga saka waƙar ko sunƙi ko sun so aure ya ɗauro, da kuma waƙar na ji a jikkina Yanzu zan yi aure, sai waƙar turanci ta Johnny-Drille Wait for me nan da nan abin ya shiga viral ko’ina shi ne aka fara sharing group group na WhatsApp, da facebook irin su Sirrin Ƴa mace su Sarauta’s Library, TICTOK ko’ina ka shiga shi ne da masu cewa an yi anbazaranci da masu cewa dama ni ce, wasu kuma surutu suke taya babbar malama zata auri krista? Kuma ɗan ƙaramin yaro arziƙi kawai take kwaɗayi, wasu kuma suce shi ne ya yi mata cikin kenan da shi take karuwancin maganganun kala-kala lefen ya jawo, shi Khalil bai san me ake ba, sbd she’s not interested on social media, gwala-gwale sai wanda ba ayi ba aka zuba, hadda keys na mota Hyundai Ioniq 6, Toyota Corolla, Bugatti Chiron, Mercedes-Benz S-Class, magana ake ta ɗan shugabar ƙasar Germany arziƙi akan ariziƙi, labarin lefen Majeederh ya zama most trending news dake yawo a Kano dama duniya bakiɗaya, Latifa ji akai tana ta surutu ita kaɗai kamar zararriyya idan ta kalli sets ɗin akwatin da keys ɗin motocin sai ta ce “Ina ba zai yiwu ba” sets biyu cif na inner wears ne wasu lalatattun kaya tasan aikinsa ne, Uncle Isma’il ya yi ta kiran Khalil yaƙi ɗagawa sai can bayan komai ya lafa ya ɗaga kiran ya fara faɗa “Ibrahim kai wanne irin yaro ne, gabaɗaya kuɗin zata ƙarar akanta” Khalil ya ce “Me Uncle?” Ya ce “Wannan mahaukatan kayan da aka kawo haba Ibrahim” Khalil ya ce “Oh! Bani na yi ba ƙwandala tawa babu Uncle, Zizi da Badi ne u can ask them ai suna gidan” Uncle ya kashe wayar. Har dare Majeederh kasa fitowa tayi don kunya da kuma mamakin kayan Maman Alpha ta shigo ɗakin tana juya mazaunai ta ce “Allhamd ɗiyata lafiya lou” Ta faɗa tana rungumeta ta nufi wajan blue set ɗin daka ajjiye a bedroom ɗin Majeederh tana cewa “Wannan duk kayan lefenmi mu, duk wanda bai bani wannan ba ni ba zan aure shi ba” Misalin 2:35 na dare tana kwance tana bacci duk da wani zazzafan zazzaɓi ya rufeta jikinta sai rawa yake da ɓari yanzuma da ƙyar tayi baccin, a hankali ta ji ana shafa tafin ƙafarta tare da jan dugwayen yatsun ta juya kaɗan sai kuma ta buɗe idanu zaune ta ganshi daga shi sai Tartan check print white pyjamas dugwaye ce iya qiwwa daga gaba a buɗe ya ɗaure tsakiya ƙirjinsa a bayyane sai kwantaccen sumar wajan dake ƙyalli sosai, ƙafarsa sanye da Scuff faux-shearling slippers da alama bai jima da wanka ba ta ce “You? Yaushe ka shigo” Idanunsa akan zanen ƙunshinta tunda yake bai taɓa ganin irin wannan abun ba, yama yi tunanin mammanawa kawai akai, bai ce mata komai sai ƙafarta da riƙe ya zuba mata idanu a hankali slowly ya ja ƙafar wajan bakinsa cikin nutsuwa zuciyarsa na buɗewa ya zura babban yatsar a cikin bakinsa while yana zare towel ɗin jikinta da ɗaya hannun, wata iriyar tsotsa ta ji ya yiwa yatsar wanda ya sa ta ji kamar fitsari na son ƙwace ba ta yunƙura zata tashi ya saka ɗaya ƙafar ya danneta Idanunsa lumshe ya ƙarasa zura sauran yatsun a cikin bakinsa…..

Idan Monday tayi ba kuga POSITING ba ku ɗauka na je yajin aiki🥰👐🏼 ko ma’aikatan gwamnati na yin ya jin aiki idan aka musu ba daidai ba. A yi haƙuri da typing errors na koma wajan aiki ne
[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *#Ibrahim-Khalil*

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button