Mijin Malama Book 1 Page 12
MIJIN MALAMA na kuɗi ki biya ki karanta….If you read for free🤷🏾♀️🤷🏾♀️🤷🏾♀️🤷🏾♀️0811923761613
Abraham ya zubawa Maminsa Malama Majeederh narkakkun idanunsa, a hankali ya ƙara tura hannunsa cikin sumar kansa cikin huci ya sa ƙafa ya daki frame ɗin gadon ya ce “Ki daina” ya furta yana ƙara matsawa inda take zaune. Ta ɗaga Idanunta da yanzu su ka yi farare tas babu alamun tashin hankalin sai jaa da fatar fuskarta tayi. Ciki nutsuwa ta kame kanta da kyau ta kalli yatsun ƙafafuwan shi da suke dogwaye masu tsari da fasali, da sauri ta ɗauke Idanunta jin tsigar jikinta na ta shi ba tare da sanin dalili ba. Ta miƙe a hankali zata bar wajan ta ji ya yi saurin tare ta ƙamshin Boadicea The Victorious ya daki hancinta cikin ranta take furta “Asstagafirullah”
“What? Magana kina yi?”
Still tayi ignore na shi
A yanzu gani take kallonsa ma Haramcin ne a gare ta tunda da igiyar wani a kanta, wanin data rasa ta ƙamaimai abinda take ji a gare shi, So ne ko tausayi? Ko kuma karamcin taimakonsa a gareta?. she did not want her marriage with Abuturab to be a marriage of mutual help,bata son aurenta da Abuturab ya zama auren taimakon juna. Tana son ya zama auren da zai kafa tarihin rashin abokin rayuwa da ta yi tsayin shekaru talatin da biyar, tana ta samu nutsuwa, nutsuwa tare da mijinta Abu-turab, It is a very difficult thing.
Ciki yanayi na jin tausayin kansa na irin tsanar da Maminsa tayi masa ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa, ta runtse idanu Muryata a ɗan rarrabe sbd faruwar wani al’amari daya shuɗe mata ta ce “Kada ka bari tsanarki ta fi t da, bana son ganinka ka rabani da Mahaifina” Ya ware idanu yana sakin hannunta ya ce “Wow, that’s the reason? I’ll Tajju before I leave na bar masa wasiƙa” ya zura hannunsa a aljihu ya ji ba wayar shi. Da hannunta ta nuna masa ƙofa tana rufe jikinta. Ya yi cute smile wanda ya saba tun yana yaro idan yana son abu ya ce “Uhm, ni wannan abin yana sunan shi, in Hausa language? I like it” Malama Majeederh kamar ƙasa ta tsage ta shige domin ta san mai yake nufi tunda tana kallon direction ɗin da idanunsa suke bi.
“Get out, ka barni tsayin rayuwa” “I can’t, kene rayuwana dole zan sameki soona or later” Ya zube a ƙasan gwiwar shi y dafa ƙafarta yana faɗin. “Zan koma wajan family na, ba zan dawo ba sai lokacin daya dace lokacin da zaki san i am in love with you, madly love, crazy love, zaki ne meni da kan ki” ya kalleta duk da yadda Magana ke masa nauyi amma da yawan lokaci idan Jee ce gabansa baya sanin time ɗin da bakinsa ke buɗewa ya miƙe tsaye ya ce “At this time I will force you to marry me”
Zuciyarta bugawa take sosai bata ƙaunar kuma ya sani addu’a take kada ta sake ganinsa a gabanta har ɗaukewar numfashinta na ƙarshe. Ya matsa daga kusa da ita tare da nufar inda Ibrahimul-khalil ke barci ya ɗauke shi ya rungume a jikinsa, kana ya sumbaci kumatun shi sai a lokacin gabaɗaya kamanninsa ke ƙara juyewa irin na Abraham Daniel David. Musamman manyan idanunsa da suke farare tas kusan koda yaushe suna lumshe. Ya koma wajan Majeederh ya kalli Khalil ya kalleta cikin ƙasan maƙoshi ya ce
“I love both, I love Mulumana and her son”
Ya rungume Khalil yana jin kamar zai bar gabaɗaya rayuwar shi ne zai bari a tare da Jee. Tana tsaye bata motsa tsoro take kata ta shige bathroom ya gudar mata da ɗan ta, domin akan Khalil babu abinda ba zata iya ba, akan Khalil tsaf zata haƙura da zama da Abu-turab, bata son ya gane Ibrahimul-khalil shi ne rauninta bata son yadda mahaifinta ya wofintar da rayuwarta ita ma ta yiwa gudan jininta haka.
Ya sauke shi tare da kwantar da shi ya ɗauki ƙaramin zobe ya ajjiye a gefen shi.
“.….If you miss your father, just watch this…!”
Ya dubi ɗan da kyau! Ya ce “I love you Son”
Ya zuba hannu a aljihu kafin ya walking slowly ya tsaya gabanta yana kallon fuskarta tare da son haɗa idanu da ita. “Ƴar Madara!”
Ya furta can ƙasa, domin da iya abinda zai iya kiranta kenan, Mamina or Jee or ƴar Madara.
“I’ll leave, to my country” ya sauke numfashi kana ya tallafo haɓarta numfashinsa na sauka ya ce “Zan dawo, zan dawo, zan dawo, kafin nan kin gama yawon nema kina buƙatata, sbd ni ne namijin daya dace da duniyarki, zan dawo lokacin da zan zo miki da bazata, zan dawo lokacin da zaki san sbd ni aka yoki a mace zan dawo sbd babu wanda zai iya baki abinda na baki” ya ja aya yana riƙe saitin zuciyarsa baya ƙaunar depression ya sake kama shi a wannan lokacin so yake ya sauya sauyin da dole zata dawo gare shi, zai dawo da tarin soyayya mai tsafta da nagarta.
She don’t know what comes over her ta ji gabanta ya faɗi, ta san barinsa alheri ne ga duniyyarta, domin ta fahimci shine ƙaddararta ta san tubalin ginin rayuwarta da farin cikinta zuwa mataki na ko wacce mace mai nagarta a gidan mijinta to dole sai babu shi. Ya zame mata kumurcin maciji, ya zama duhun damina, babu komai a cikin lamarinta sai tarin ƙalubale da ko wacce mace kan iya fuskanta a gaban iyayenta. Shi ne ya zama tsaunin daya kai mizanin da ake mata kallon Shaiɗaniyya uwar shaiɗanu ya sa ake mata duba irin duban da akewa Magajiya.
“If I don’t come back, I was already dead, Let see waye MIJIN MALUMA” Yana faɗin haka he just give a small deep kiss in her lip’s tare da side hug he quickly leave the room.
Ji ta yi kamar ya tafi da baƙin cikin dake manne a zuciyarta wanda ya haifar mata da shi, nauyin ƙirjinta ya rago. Ta samu rauni irin raunin,rauni na ɗiya mace wanda bashi da mara ba da auren lokaci guda da akai mata. Ta sulale a wajan tare da ɗaukan Ibrahimul-khalil ta rungume tana jin shi ne abu ɗaya da yake sawa ta ji tana da raguwar farin ciki.
Abraham na fita ya samu Uncle Isma’il zaune a main parlour fuska a haɗe ganin yanayin Abraham ya sa ya sauke nasa fushin domin ba ƙaramin tsoro idanunsa suka bashi ba. “Abraham”
“Uncle” Abraham ya faɗa yana zama a ƙasan kusa da ƙafafuwan Uncle Isma’il, Hajiya Luba na gefe ta dinga kallon Abraham kafin Uncle ya yi magana ya ce.
“Promise me that you will marry me Malumana, idan na sauya na amshi musulunci?”
“Yes, I promise you that but…..,” “But what?” Cewar Abraham idanunsa kamar za su faɗo sbd tsabar ciwon da zuciyarsa ke masa na ganin yadda Majeederh take sanya hijabi a tsakanin su speaking calmly ya ce.
“Idan bana kusa da ita, zan fi gane dalilin da ya sa nake son musulunta tunda ba ayi wa addininku wayo da dabara ko Uncle?” Uncle Isma’il ya zuba masa ido, bai damu ba ya ce.
“Ina da sa a koda yaushe, babban dalilin daya sanya na haɗu da Jee kenan tun ina ƙarami, Uncle zan koma zan je wajan Daddyna duk da abinda nayi masa amma dole na je, please keep your words idan na cika sharuɗa zaka bani Ƴar Madara, ba zan dawo ba sai na zama yadda ka ce” yana faɗin haka ya miƙe tare da ficewa daga cikin gidan bakiɗaya.
“Abraham, Abraham wait tsaya akwai bayanin da zan maka…!” Amma ina tuni ya fice ko kiran Uncle da ya ji ya ɗauka zai hana shi tafiya ne.
“Me zakai masa? Kayi masa al’ƙawarin auren Majeederh shi ne ka bata Abu-turab?” Uncle Isma’il ya rasa me zai ce ya ce
“Abinda nake jira ya fito daga ɗakin Hawwa’u na faɗa masa kenan, zan faɗa masa ya haƙura da ita babu rabon aure tsakanin su”
“Tab ɗin, ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu, kada hangen hadari ya sa a yi wanka da kasha” Hajiya Luba ta ƙara da cewa “Yaron nan yana da naci da ƙulafucin abu baya da haƙuri ga taurin zuciya”
“….. Tsorona ɗaya kada ya ƙara ɓata rawar shi da talle a wajan Daniel…”
“Yana son ɗan shi” “Amma baya son addinin da ɗan yake so, su ɗin cikakkun mabiya addinin kiristan ne wanda sukai imani da shi imani bai tsauri, ba zai taɓa barin Abraham ya musulunta ba da wannan hujjar na dogara har na yi masa al’ƙawarin aure sbd duk a rabo lafiya” Hajiya Luba ta ce “Sam ni dai banga da cewar hakan ba”
Abraham na fita akan ƙafafuwan shi ya dinga takawa, duk da irin kuɗi na mahaifinsa amma yanzu babu ko biyar a jikinsa wayar hannunsa ma babu. Abu biyu ya ke buƙata ya sha barasa ya kuma shiga church ya nemi sa a ga abinda zai yi. A Wannan lokacin ko dai ya samu Majeederh, ko dai ya rabauta da addinin Musulunci ko kuma ya samu damar kawo ƙarshen rayuwar shi Life ending.
Barrister Aliyu Zaki yana zaune cikin kyakkyawar shigar shi mai nuna zallar mutuntakar shi ya dubi Latifa cikin damuwa ya ce “Kina son rabauta da rahamar Ubangiji kowa?” Latifa ta ce
“Babu wanda baya buƙatar wannan” Ya ce “Banda ke, bana tunanin kin shirya samun aljanarki a wajena” Ta dube shi fuskarsa ta faɗa sosai ya ce “Kina sane da adadin lokacin da ki ka ɗauka baki sauke hakƙin aure ba? Kullum idan na shigo cikin gidan nan gabana faɗuwa yake, bana da burin zama da mace zama da ɗaya Latifa, ƙaddara ta haɗani dake tare da sauyani ba tare dana sani ba, duk da cewa tun bayan zuciyata na wani wajan, Latifa ban san abinda ake ji a zaman Majalissa ba tun bayan iya ba har na saba, ke kika bani dama na zama Majalissa mata na shigewa idanunmu na gani, ki sani duk macen da ki ka sanya na ji na yi sha’awar ta to ba zan taɓa yafewa ba, domin kamar na yi zinar idanu ne” Lafita Shocked ta ce
“Me na yi?” “Oh! Baki sani ba?” Ya jinjina kai ta ce “Da gaske” Aliyu Zaki ya gyara zama sosai ya ce
“Firstly duk abinda ya halatta mace taiwa mijinta to ke zero ki ke a nan, ba sani ba ko baki da lafiya ne ko sha’awa ce babu da bakya buƙatar mijinki, baki iya girki ba kullum ina yawon zuwa restaurant sbd kunyar zuwa nake wajan Hajia na ce zanci abinci bayan ina da mata, irin kwalliyya ta mata baki iya ba, ba kitso ba wannan zanen abun ƙunshi, sai tara ƙawayen banza da iska da masifar kishin da bashi da amfani, wallahi wallahi ko zina na fara kece sila Latifa Allah ba zai barki ba, Allah kana kallo duk nauyin daka ɗora mini a matsayina na miji na sauke, kuma in sha Allah sai na auri Majeederh ita ce zata bani abinda nake buƙata ina son mace mai ƙarfin addini da iya soyayya amma ke text message wannan baki sani ba, Mrs zero!”
Yana faɗin hakan ya zari key tare da ficewa daga cikin gidan ya nufi Chikenza Park and Restaurant.
Misalin Tara na dare motocin His Excellency Abu-turab suka sauka gidan Uncle Isma’il, cikin sauri P.a ya fito tare da buɗe masa ƙofar mota a hankali ya fito yana zabga ƙamshi Dolce and Gabbana wanda sanyin ƙamshin ke fita a hankali cike da gamsar da mai shaƙar shi. Yana sanye da wata dakakkiyar shadda sky blue ɗinkin jamper da babbar riga ta zauna a jikinsa sosai a wannan lokaci babu ko hula a kansa sbd so yake yau Jiddo taga ainahin kyan da yake da shi, cikin takun ƙasaita kamar wahainiya haka ya nufi cikin gidan Uncle dake sun da zuwan na shi, Jawaad na parlour yana kallon ball ya yi saurin miƙewa ganin His Excellency Abu-turab da kan shi ya durƙosa da girmamawa ya ce
“Wlcm sir” Murmushi Abu-turab ya yi yana jinjina kai “Kana lafiya?” Ya ce “Allahamdulillah, sannu da zuwa” ya ƙara murmushi kawai. Jawaad ya yi masa rakiya zuwa parlour part ɗin da Majeederh ke ciki kana ya shiga ciki ya sanar mata lokacin tana zaune har yanzu ko sauya kaya ba tayi ba ta zubawa Ibrahimul-khalil Idanu. Ta jinjina kai kawai ya san ba zatai magana ba sai kawai ya fi ce. Abu-turab ya kasa zama har tsayin mintuna kusan goma kafin ya ji motsi a bayan shi. A hankali ya sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya ƙarasa gabanta yana binta da kallo.
“Barka” ta furta can ƙasa ya ce “Can You remove the cover? Please i want see my wife ba wannan hijabin” Ta ɗago kai ta kalle shi tana son ce masa ya jiki tunda taga harda carnoner a hannunsa. “Please Jiddo, My wife aure ya halatta mini ganinki” ta runtse idanu sosai lokacin daya zare hijabin jikinta a hankali ya jata jikinsa ya rungume sosai yana sauke numfashi da ajjiyar zuciya ya ce “Allahamdulillah, Allahamdulillah, Allhamdulillah! Ina son ki Jiddertul-khair” Rayuwa Kenan bayan tarin ƙalubalan rayuwa data sha ta tsallake ƙaddarori da surutu da zunɗen jama’a yau ita ce matar babban mutum, ita ce first lady? Ita ce jikin Governor Abu-turab Alƙasim rungume da ita yana faɗa mata yana son ta? Sai a lokacin wasu hawaye Masu zafi suka shige fitowa daga cikin idanunta har bata san lokacin data ɗan ƙanƙame jikin Abu-turab ba. Sannu a hankali kamar gilmar fitila cikin duhu rayuwarta ta baya ta fara dawowa cikin Idanunta da tunaninta…. THE BEGIN OF THE BEGINING. Shekaru talatin da biyar da suka shige a baya al’amarin ya fara……