Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 13

Sponsored Links

MIJIN MALAMA
Littafin kuɗi ne book 1 and 2 1k ne…. If you read for free🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️
0811923761614
*Duk wata mace yana da kyau, ta nutsu ta bi labarin nan, ko bai zo daidai da rayuwarki babu shakka zai iya zuwa daidai dana wan bak… MATA MA SU JINKIRIN AURE.*

Al’amarin ya fara a garin kano cikin unguwar Ƴan-kaba. Yamma sakaliyya lis unguwar ta yi shiru saboda gabatuwar almuru. Yanayin ginin wajan zai baka tabbacin akwai ƙarancin wadata a cikin mazauna unguwar musamman yadda aka samu kwatoci a gaban ko wanne gida da kuma kan hanya akwai tarin gidaje wanda suke dab da juna kamar tsarin ginin cikin gari. Da sauri magidancin mutumin ke tafiya hannunsa riƙe da wata jakar ƙaramar kai tsaye gidan da ya fi ko wanne muni ya shiga lokacin daya shiga ya samu wata mata tsaye tana goge zufa ya dubeta cikin damuwa ya ce “Ya ya ta sauka ne?” Bilkisu ta girgiza ta ce “Ayya ai sai abin da hali ya yi naƙuda tun jiya ana abu ɗaya sai fama ake, gashi Malam ka ƙi a ta fi asibiti” Malam Abdul’aziz ya haɗe fuska ya ce
“Yanzu nan zata sauka lafiya, ni ban fiya yarda da aikin nasara ba yadda nayi wannan tofin babu shakka zata rabo da cikin salin alin” “Allah ya sa, amma Fulani na shan wahala” cewar Bilkisu.
Ta amshi maganin tare da ɗaga labule ta shiga, rawar dai har yanzu bata sauya zani ba. Domin Nishi ake son ta yi amma abu ya gagara. Bilkisu ta ce “Sannu kin ji Fulani” ta bawa wata mata dake zaune gefen Fulanin ta ce “Yanzu Malam ya kawo wannan tofin, taimaka ki ɗagata ki bata kin ji Asabe” Asabe ta amsa cikin alhini ta tallo kan Fulani ta shiga mata maganin jikinta duk ya riga ya saki.

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, na shiga uku me zan gani ni Asabe Yaya Bilkisu ƙafa ce ta fito, haihuwar dire za ta yi”
“Wanne irin dire ni ƴar nan matsa muga Asabe” Asabe ta matsa Yaya Bilkisu na dubawa ta ga da gaske ƙafa ce guda ɗaya ta fito harta fara bushewa. Suka rasa yadda za su yi hakan alama ce dake nuna musu ruwa ya ƙarewa ɗan-kada. Suka yi rufdugu akan Fulani wacce take jin mawuyacin hali salati kawai take yi gefe guda kuma tana kiran sunan Hawwa’u.
Da ga bakin ƙofa Malam Abdul’aziz ya ce “Ya ake ciki? Ta kusa sauka ko?” Yaya Bilkisu ta ce “Wanne sauka za ta yi dire, Malam ka je ka kawo mota mu je asibiti ko na Murtala ko na nasarawa” sai a lokacin Asabe ta ce “Ai bama za su amsheta ba, domin bata taɓa zuwa awo ba, ko haihuwar Majeederh a haka ta zo mata”
“Ikon Allah, Ubangiji ga mu gareka” da ƙyar suka taimaka mata ɗaya ƙafar ta fito suka dinga yayyafa mata ruwa tare da bata shayi mai zafi cikin sa a nishi mai ƙarfi ya zo mata ta haifi ɗiya mace a karo na biyu. Murna sosai sukai harda hamdala aka yanke cibiya tare da gyara kyakkyawar yarinyar. Malam na waje Yaya Bilkisu ta fito tare da barin Asabe a ɗakin.
“Ga kyautar da Ubangiji ya ƙara yi maka, uban ƴa ƴa mata” Malam ya yi murmushi ya ce “Hakan ma suttura ce Yaya, kuma ina alfahari da ɗiyata Majeederh wacce zata bani abin dana rasa a baya” Yaya Bilkisu ta yi murmushi tana faɗin
“A kan Soyayyar Majeederh baka da ɗauke ƙafa, tana ina ne?”
“Makaranta Yaya Bilkisu, ai tun tana shekaru biyu na sanyata a makaranta gashi yanzu dab take da yin sauka” Yaya Bilkisu ta zare idanu sosai cike da mamaki da al’ajabi ta ce
“Yau na ga abin da ya isheni ni Mai gadon zinare ba bu tausayi shi ya sa gata nan duk a fige saboda tsabar karatu” Wani Uban kira Asabe dage cikin ɗaki ta shiga ƙwalawa Yaya Bilkisu jiki na ɓari har zaninta na faɗowa ta tsuguna zata ɗauka domin gyarawa ashe takalmi ta ɗauka tana faɗin.
“Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Wanne irin ɗaukan alhaki ne haka Asa….,” Abin da idanun Yaya Bilkisu ya gane mata ya hanata ƙarasa duguwar maganar data ɗakko. Fulani ce ke kwance kamar Matacciya sai jijjiga take harshenta ya fito waje ga jinin dake fita a ƙasanta kamar an yanka rago.
Yaya Bilkisu dake zuciyarta da rauni tuni ta fara sharɓar hawaye tana faɗin “Oh, mu mata muna ganin jarrabawa a wajan haihuwa rabu ba a tsira ba” Fulani da numfashinta ke sama fuskarta tayi fari sosai saboda jinin daya ƙare a jikinta ta ce “Ƴa ƴana, Ƴa ƴana Yaya a kira mini Hawwa’u kafin na koma ga mahaliccina”
“Assha, Assha daina faɗa mai haƙuri albarkacin haƙurin ki Ubangiji ba zai amshi rayuwarki yanzu ba, ke zaki raini yaranki da kan ki kamar yadda kika haifa” Fulani tayi shiru banda salati babu abin da take ana haka Malam ya shigo jin shirun ya yi yawa. Wani bugawa ƙirjinsa ya yi ganin halin da matarsa Fulani ke ciki, tsananin kyan da Ubangiji ya yi mata kasancewar ta Fulanin Gombe Usul gaba-da-baya Fulanin kuma makiyaya masu kiwon shanu wanda nono ya zamr musu jarin su wanda a yanzu shi ake sarrafawa zuwa madarar Rufaider yoghurt. Tun tana shekara goma sha biyar da haihuwa aka ɗaura mata aure da Malam Abdul’aziz, a lokacin ya ziyarci garin Yobe shi da abokinsa yin dillacin wata saniyya domin kiwo. At first sight soyayya mai ƙarfi tayi dirar mikiyya a zuciyar matashin saurayin Abdul’aziz. Har Ubangiji ya tabbatar da auren su, bata sami haihuwa ba sai da tayi shekaru ashirin da biyar a gidan shi, sannan ta haifi ƴar ta Hawwa’u Majeederh Abdul’aziz Khan! Wacce kamar ka ki tayi ta zubar saboda zallar kamannin da su ka yi. A nan ya samu wadata ya ƙara aure Majeederh na da shekara wacce ya aura ta haihu ta samu ɗiya mace. Kasancewar kwanika take ta sake haihuwar wata ƴar lokacin Majeederh nada shekara huɗu ana haka Fulani ta samu ciki. Har ya isa mizanin zuwa duniya a daidai gaɓar da Malam ya bar gidan domin kawo tofi a lokacin naƙudar da ta ke tun jiya ta tsanan.

Related Articles

Nishin da Fulani ta yi tare da salati ya dawo da Malam daga tunanin daya lula firgigit ya zube gabanta yana faɗin “Fulani kada kiyi magana haka, ba mu shirya zuwan wannan ranar ba” ta riƙe hannunsa sosai tana salati ta ce “Malam ka kira mini Hawwa’u ina son ganinta, ina son faɗa mata wani abu mai muhimmanci a rayuwarta” Malam ya fara addu’a tare da cewa “Ki faɗa mini ko ma mene, ni ne uban Hawwa’u kuma zan riƙe amana” ta girgiza kai ta ce “Al’amari ne daya shafi uwa da ƴarta, da kuma dangina ka je ka dawo mini da Hawwa’u, dole zata ɓukaci sani a lokacin da buƙatar hakan ta zo” Ta dinga rufe ido tana salati gabaɗaya wajan aka fara salati Yaya Bilkisu ta zari mayafi ta ce “Wacce ƙaddararriyar makaranta ce har kusan almuru? Wallahi yanzu zan je na dawo da ita, Allah ya baki lafiya Fulani”
Tana faɗin haka ta yi waje lokacin yaran duk suna makaranta banda guda ɗaya.
A hankali Yaran suke tafiya wajan su biyar, uku a gefe guda biyu a can gefe sai. Wacce ta fi ko wacce nutsuwa ta ƙara ƙanƙame Alkur’aninta a ƙirji tana sauke numfashi, a hankali ta yi kyakkyawan murmushi ta cikin liƙab ɗin dake maƙale a fuskarta. Murmushi daya haifar da lomawar dimple ɗinta guda ɗaya. Farin ciki yau take ta ƙarasa bada haddar Alkur’aninta surar ƙarshe kuma shafin ƙarshe na Suratul Bakrah. Latifa dake kusa da ita ta ce “Majeederh kina dariya ko?” Ta jin jina kai ta ce “Uhm, Mimana na siyo mata alawa, kuma zan ga babyn da zata haifa na samu ƙanwa” Latifa ta ce “Laa Mima haihuwa za ta yi?” Majeederh ta bata fiya hayaniya da surutu ba sai ta ƙara jinjina kan ta cikin siririyar muryarta ta ce “E, ba kiga cikinta ya yi ƙato ba? Zan je na ga baby kuma na ce mata na kammala hadda ta yi mini sadaƙa inji Ya mu’alim” farin ciki ya kama Latifa sosai ta ce “Ai nima zani na ga baby kuma ni ma zan ce na kusa gama haddata” Murmushi kawai Majeederh ta sake yi har ranta farin ciki take na ganin ta riga kowa kammala haddar Alkur’ani ga Mima zata haifa mata ƙanwa. Tuna haka sai ya sa ta lumshe idanu tare da rungume Alkur’an ta na ji tamkar ta yi tsuntsuwa zuwa gida. Amma kamar wacce ake ƙara bayar da ita baya sbd yadda take tafiya a nutse da tarin kamala nutsuwarta ta fi ta wata cikakkiyar budurwar. Tunda kuma ta fara girma Abu ya siya mata Liƙab kamar yadda Ya mu’alim ya bashi shawara sbd kyan da Allah ya yi mata na musamman ne tamkar zara ce a cikin sauran taurari ga sai dai ƴar firit take karatu ya sata gaba Islamiyya da boko ga tarin hadisan da Abu yake ƙara mata idan ta dawo, bata barci sai wajan ƙarfe 1 asuba na yi take tashi ta fara karatu.
Sun zo dai-dai wajan wa su matasa wani ya kalleta ya ce “Yarinyar nan daga gani munin ya yi mata yawa, tunda nake ban taɓa ganin fuskarta ba” Wani ya ce “Kuma dai gata kamar fara ce”
“Ahhab, waya faɗa maka fari kyau ne?” Suka dinga surutu ɗaya ne ya ce “Ni kuma nutsuwarta ke birgeni, idan ba makaranta ba ko aike bata fitowa mahaifinta ya gwammace ya je da kansa, amma sauran ƴan uwanta ga su nan kullum suna fitowa” Latifa za ta yi magana Majeederh ta yi saurin riƙe hannunta tana ƙarawa tafiyarta sauri. Burinta bai shige tayi tuzali da Mima ba tana son jin labarin da a kullum take ce mata yana da muhimmanci a rayuwarta. Yau kuma ta yi alƙawarin bata wannan labarin. Farin ciki ya danne yunwar da ta ke ji.

Tazarar gida ɗaya ne tsakanin gidansu Majeederh da na su Latifa, wannan dalilin ya sa ƙawancan su ya ƙara ƙarfi duk da girmewa Latifa da Majeederh ta yi kuma suka samu nasarar shiga makaranta ɗaya daga ta boko har Islamiyya akwai bambancin fahimta tsakanin su, wanda ya sa Majeederh ta fi Latifa gane komai. Tun da ga nesa Majeederh ta hango Yaya Bilkisu tana zuba uban sauri tare da share hawayen da ke bin idanunta. Cak! Ta tsaya sbd mummunar faɗuwar gaban daya risketa Kur’anin hannunta ya nemi faɗuwa ta riƙe sosai fararen Idanunta masu tsari kwance akan fuskar Yaya Bilkisu har zuwa lokacin data riski tsaiwar ta su.
“Allhamdu lillahi, maza zo muje ƴar albarka” Majeederh ta ƙurawa Yaya Bilkisu Idanu domin Allah ya yi mata baiwar fahimtar abu dalilin da ya sa Abu ya ce psychologist zata karanta bayan nan sai ta koma Islamic studies. “Haba Kulun Majade mu je mana” Kamar wacce take karantar zuciyar Yaya Bilkisu ta ce “Mimana? Mene ya sameta? Ta ce zata bani labarin abu mai muhimmanci, ta ce kafin na dawo zata kawo baby, ta haihu?” Tsoron ya kama Yaya Bilkisu ganin tafarar ɗaya Majeederh ta kasance abin da ke shimfiɗe a fuskarta lallai tunani da kaifin basirar Majeederh ya shige shekarunta. Ta ce “Eh, yanzu ma cewa tayi muje ta faɗa miki wani abu” ta tsorawa mata Idanu sai kuma ta sauke ajjiyar zuciya mai nauyi tana jinjina kai. Sauran ƙannenta Ruma da ɗayar kana ta kama hannun Yaya Bilkisu suka nufi cikin gidan domin suna gab da ƙofar dama. Malam ya dinga girgiza Fulani yana faɗin “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, Fulani faɗa mini abinda ki ke son faɗawa ƴarki Majeederh” Ta ja numfashi da ƙyar tana karanta kalmar shahada ta ce “Malam kayi mini wannan alfarmar kamar yadda aka baka ni ina shekara 15, to ka aurar da Hawwa’u a wannan shekarun domin akwai ɓoyayyiyen abu tare da ita don Allah, don Allah…” Kalamanta suka tsaya sbd ajjiyar zuciya da tayi tana ɗaga idanu sama daidai shigowar Majeederh ya yi daidai da wa’adinin rasuwar Fulani…….. The destiny was just begun!

Duk wata mace yana da kyau ta nutsu ta bi labarin nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button