Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 33

Sponsored Links

[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: _*Nimcyluv sarauta 85*_
Duk yadda Khalil ya kai ga jarumta, dakiya da ƙarfin zuciya da wata iriyar murɗaɗɗiyyar zuciya, amma a wannan karan neman su ya yi ya rasa, ganin yadda jikin mutum ya yi pieces a gabansa, kuma matarsa, kuma ƴar abokin dad ɗinsa Chancellor. Khalil ya dinga kallon gawar Debeka wacce ɗan ƙaramin bom ɗin ya tashi da ita, ya juya ya kalli hannunta daya fita fit zuwa wani gefen nada ban, Ikon Allah kawai yake gani deep down na zuciyarsa yana kiran sunayen Allah Adadin iya abinda ya haddace, tunani fal zuciyarsa hakan na nufin Debeka aiki ta kewa Ddmaster bom? Meye haɗin shi da ita? Wacce hujja ce ta sanya yanzu take waya da shi? Something is fishy!. Gimbiya tana tsayen da take bata motsa ba, fuskarta looking ok as always, ba zaka taɓa ganin yanayi mai kama da tashin hankali a tattare da ita ba, a karo na farko ta ɗan kalli gawar Debeka sai kuma ta ɗauke Idanu, a sanyaye cikin rashin damuwa domin idan da sabo ta saba da ganin fiye da hakan cikin izza da jinkimar ta ta furta. “Who is she?” Ta ɗan sauke numfashi tana juya idanunta a taushashe kuma a ɗan kasalance ta ƙara furta “What are you accusing her of?? Ka tattare gawar” Ya yi mata shiru, ta fahimci baya son haɗa Idanu da ita, ta gane kuma firgicin daya shiga duba da yadda naman jikinsa ke rawa ga zufar dake tsastsafowa daga goshinsa, a hankali tana ɗan haɗe yatsun hannunta can ciki ta ce “Ibrahim, ur wife is coming” Khalil ya ɗaga kansa da sauri sai kuma ya kalli Ummi, jin motsi daga ƙofar part ɗin Jee ya saka Khalil zare rigar jikinsa ya goge jinin hannunsa dana ƙafarsa ya cilla rigar bayan kujera, a ɗan gaggauce ya buɗe ƙofar ya shiga daidai nan itama ta ƙaraso ƙofar tana ƙoƙarin murɗa handle ɗin ta ji an buɗe, ta ɗan tsaya tana kallonsa kamar wacce ke shirin fahimtar wani abu, ya san kaifaffan tunaninta sai yaga ta hararesa tana shirin bi ta gefensa ta nufi waje ya yi saurin saka hannu ya kamo ƙugunta tare da dawo da ita baya, ta ware manyan sexy eyes ɗinta a kansa tana ɗaga masa gira, a taushashe ya ce “I need u wife” Ya faɗa a hankali yana mai saita muryarsa a hankali kuma ya murza hancinsa a nata bayan ya yi covering fuskarsu waje guda, mamakin yadda zuciyarsa ke tsananin bugawa da ƙarfi wacce bata taɓa ji ba tayi ta miƙa hannu tare da ɗora shi a saitin zuciyarsa kasancewar ƙirjinsa a buɗe yake kuma a faɗaɗe ya bayyana, ta manne hannun sai kuma ta ɗaga lafiyayyun lumsassun idanunta ta kallesa a hankali ta ce “Your heart is beating way too fast, are you okay?” Ya zubawa fuskarta Idanu, tunaninsa ta yadda zai yi keeping ɗinta busy yake a cikin bedroom ɗin, ko ya sanyata bacci. “Man” Jee ta furta tana riƙe nasa ƙugun ganin kamar tunaninsa ya Kaɗaita ya ɗaga mata gira, ta ce “Ba kaci komai ba, ur food is ready” Ya yi shiru sai kuma ya girgiza kai yana kama kunnenta tare da ɗora bakinsa ya ce “Tunda na sameki na rage ci, abincina kala biyu” Tayi saurin kallonsa ya kashe mata ido ya ce “This is your husband, Ibrahimul-khalil, now I’ll feed on u later I’ll eat the food” Yana faɗin hakan ya sunkuceta yana zare hijab ɗin jikinta, ta riƙe shi kamar za tai kuka ta ce “Khalil, Ummi” Yana kwantar da ita saman gado ya saka hannu ya ƙure a.c yana zare ribbon na kanta ya ce “Who is Ummi abeg? tasan gidan sabbin ma’arauta ta zo, da zaki kyauta kiyi screaming yadda zata ji ta gudu” Majeederh ta ware Idanu ta ce “Ni ina gudun abin kunya” Ya murza bakinta ya ce “Ni gaba na bashi” Za ta yi magana ta tashi ya yi saurin kissing nata yabi ya mayar da ita kwanciyar a hankali ya ce “Kila ciki na biyu zan baki, garin hadari sai ki haifi twins” Jee tayi dariya tana tura hannunta a sumar shi ta ce “Gaskiya Khalil sanda ake topic ɗin Biology bacci kake” Bai sake mata magana ba domin baya hali na fahimta….

Da sauri Khalil ya kunna switch ɗin bedroom ɗin, saboda daman a ƙa’ida baya buƙatar haske,sai yaso zai kunna, ya dinga kallonta ganin yadda take bacci a nutse, kamar yadda ya yi al’ƙawari gashi ya sata baccin, ya ɗan shafa kansa sai kuma ya yi kissing forehead ɗinta a hankali ya furta “Rest of my life” Ya miƙe ya nufi waje, tsaye ya yi a wajan ganin babu gawar ba alamarta ya juya ya kalli Ummi dake zaune saman kujera ta harɗe ƙafa tana danna waya, ba zaka taɓa cewa ta haifi Khalil ba, rashin ganin gawar da jinin yasa Khalil ƙarasawa wajan Gimbiya da sauri yana zama kusa da ita cikin rashin sani da sabo ya ɗora hannunsa a shoulder ɗin Gimbiya yana ɗan leƙa fuskarta a hankali ya ce “Ummie ina gawar?” Ta juya ya kalle shi sai kuma ta kalli hannunsa a hankali ta ce “Ku shirya kayanku, now” Ta miƙe tsaye still tana danna iphone ɗin hannunta yadda yatsunta ke sauka zaka gane wani muhimmun abu takeyi, ya tashi jiki a sanyaye har ya juya ya ji ta ce “Hi Young Man” Ya kalleta sai kuma ta nuna ya je kawai.. Motar su Majeederh ce ta fara fita a sirrince, Jee ta ce Ummie ta bata tayi driving ɗin, ita dai Ummie bata kalli Majeederh ba, da wani irin masifaffan gudu taja motar, kana gani kasan ta ƙware a juya mota ta kuma saba da tsere da ita, bayan tafiyar su Jee Khalil ya fito daga shi sai three quarter daman komai nasa Gimbiya ta wuce da shi, sai ya nuna kamar unguwa za shi ko mota bai ɗauka ba, ya fice a ƙafa fuskarsa da face masks ya jima yana tafiya da ɗan tsalle kamar training yake ya nemi napep ya tsaida ya sanar masa inda zai kaisa, kai tsaye airport ya ƙarasa a nan yaga Mai martaba Ajlaal Sultaan, Zaytoon, Roohan, Ƙhulud, Zoya da Zohal, sai Majeederh dake tsaye gefe, yana zuwa haɗaɗɗan private jet ɗin na sauka, daman suna waiting room, ne duk suka miƙe zuwa bakin vip daga nan suka shiga harabar jirgin, Mai martaba Ajlaal Sultaan da Ƙhulud suna champer ta ɗaya, ta tsakiya kuma Roohan ne da Ƙhulud sai Gimbiya, ta ƙarshe Khalil ne da Matarsa Jee a haka jirgin ya tashi zuwa sararin samaniya ya nufi Saudiyya da su.
Maman Alpha na zaune tana kallon Baby Khalil dake wasan shi, General Alpha ne ya shigo cikin wata Kamfala mai kyau hannunsa zube cikin Aljihu ya zauna a hankali yana cewa “Barka da hutawa Mama” Ta ce “Yauwa General, ka ji meke faruwa?” Ya buɗe ido ya ce “Mefa?” Ta ce “Al’amarin ƙasar nan, wai wasu mata masu shan jini sun bayyana, suna sallama da a taimaka musu da abinci kana basu suke zuƙe maka jini, ga tsadar man fetur, abinci ya yi tsada mutane nata mutuwa” A hankali ya ce “Oops, Allah ya kyauta”
“Yanzu wacce kalar rayuwa muke ciki ne? Anya! Hakan zai tabbata, shin shuwagabanni basa gani ne? Jami’an tsaro suna ina? Hukumar kare hakƙin rayuka da lafiya ta ƙasa da jiha suna ina? Rayuka na salwata, yawan mabarata suna ƙara tu’azzara, ga Shaye-shaye na ƙara yawaita, wai me ake nufi da al’ummar Annabi Adamu ne? Shin sun manta su wad’anda za’a tambaya ne ranar gobe ƙiyama? Suna yini basu ci ba suma? Ko mancewa suke da ranar Yaumal ƙiyamati, tunanin su ba zasu mutu ba?” Ta share hawayen daya cika a Idanunta ta ce “Yanzu fa ƴan mata guda ashirin aka nema aka rasa, ga wata mata data mutu saboda yunwa, Wayyo, innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” A sanyaye General Alpha ya ce “Allah yana gani, stop bothering yourself Maama” Ya kalli Baby Khalil har zai ɗauke shi sai ya fasa saboda wata mahaukaciyar kama da suke da Khalil, nan da nan ransa ya ɓaci ya runtse idanunsa, zuciyarsa na bugawa wani irin zafi da raɗaɗi yake ji a ransa har yanzu kuma bai fidda rai da samun Majeederh matsayin mata ba, yadda abubuwa suka same shi dalilinta ya saka yaƙini lashakka zai sameta ko da ace yana samunta zai koma ga Ubangiji. Jin ƙarar wayarsa ya sanya ya ɗauka da sauri kuma ya miƙe yana ƙamewa tare da ɗaga hannunsa ya sara da ƙarfi ya ce “YES Sir!” Sai ya yi shiru sai can ya ce “Ok Sir, i am ready” Yana gama faɗin hakan ya kira wata number ana ɗagawa ya ce “Oba, oba, oba 012 are you with me?” Aka bashi amsa ya ce “Ready, Major Janar Mohammed Yusuf, shugaban sojoji ya sauka a Kano shi da Field Marshal, zamu je wajan shi tare da kai, abu ne na gaggawa da yiyuwa juyin mulkin sojoji za su yi a Nijeriya, kasan kuma idan hakan ta kasance duk wani Gwamna na jiha sauka zai yi soja ne zai hau” Ya yi shiru jin anyi Sallama Zaleehat ce ta shigo hakan yasa ya kashe wayar suka gaisa da Maman Alpha tana ce mata ya mai jiki saboda Baby Khalil da bashi da lafiya, Alpha ya nufi waje Maman Alpha ta ce “Allah ya tsare” Ya nufi waje sojojin birjik a compound na gidan Uncle Bello, yana ƙoƙarin shiga mota aka ce “General” Ya tsaya sai kuma ya juya idanunsa ya sauka akanta, a hankali ya ce “How are you?” Zaleehat tayi ƙasa da kanta ta kasa cewa komai idanunta ya cicciko da hawaye, Alpha ya ɗan lumshe idanu sai ya buɗe ya ɗan juya yaga ba kowa da sauri ya ƙarasa wajan Zaleehat tare da jawota ya rungumeta ta fashe da kuka ta ce “I am tired, General” Ya rungumeta sosai a hankali ya ce “I am sorry dear am sorry” Kuka kawai take ta ce “But u know i missed you” Ya kasa magana sai kuma ya yi ƙasa da murya ya ce “Same dear” Aaliyyah ce tsaye tana kallon Aliyu daya ɗan rausayar da kansa gefe kamar maraya a hankali ya ce “plz dear” Tayi ƙasa da murya ta ce “Meyasa kake tunanin ga Anti Latifa ni zan iya aurenka? Me ya sa? Haba Yaa Aliyu koba komai akwai alkunya” Ya harɗe hannu a ƙirji ya ce “Oh, now tell me do you love me? Alkunya kike ko so na ne bakya yi?” Kafin ta yi magana wayarta ya fara ƙara ta ɗauka ganin Du’a ce ta ce “Sister Du’a ya kike?” Du’a bakinta na rawa ta ce “Ajiye gaisuwa gefe, na kira number Anti Jeederh baya tafiya” Aaliyyah ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce “Meke faruwa? Lafiya dai? Akwai damuwa ne?” Du’a ta ce “Ke daƙiƙiyar ƙwaƙwalwa ce dake sometimes, check your WhatsApp, ki duba IG account ɗin Northern kiga komai” Du’a ta kashe wayar daga nan tabi kowa na family ta faɗa masa. A tsorace Aaliyyah ke karanta posting ɗin Northern wanda malama ta saki 20 minutes ago, but comment sama da 3k gabaɗaya tsinewa Latifa Omar suke, Aliyu ya matsa kusa da ita ya amshi wayar ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita, tashin hankalin Aliyu yafi na Aaliyyah ya yi baya kamar zai faɗi ya jingina da mota, ganin abinda Latifa Omar ta ce a ƙarshe “Malam bayan hakƙin Majeederh kuma Bestie,nasan hakƙin mijina Aliyu ma ba zai barni ba, na zubar da cikinsa sau babu adadi bisa umarnin boka, na yanke shawarar faɗa miki ko zan samu sassauci daga zuciyata na samu su yafe mini na cutar da Majeederh cuta mai yawa wacce babu wata aminiyar arziƙi da zata iya yin haka, na yarda ni muguwa ce azzaluma, saboda a baya ina baƙin ciki da duk abinda Majeederh take musamman kyan da take dashi da farin jinin data taso da shi, hakan yasa na daƙile farin jinin na mayar da ita mujiya, hatta mijina Aliyu bani yake so ba, ita ce zaɓin shi amma ni ce tubalin rasa muradin zuciyar malama wallahi ni ba aminiyar ƙwarai ba ce….,” Aliyu Sufyan bai ƙarasa karatun ba, yaji wani irin jiri ya kwashe shi ganin zai zube yasa Aaliyyah tare shi ya yi saurin jawota ya rungumeta idanunsa na zubar da hawaye a hankali ya ce “Marry me pls Leeyerh” kukan take itama wallahi sai ta auri Aliyu ko dan taci kutumar uban Latifa zata gane bata da hankali sai ta gigita mata lissafi kuma ba zata taɓa bari Aliyu ya saki Latifa ba, baƙin ciki ne zai sanya zuciyarta bugawa one time.. Gimbiya na tsaye tana danna system a ɗan gaggauce hannunta ɗaya a kunne, a hankali Khalil ya ƙarasa ya kara kunnen shi muryar Dad ɗinsa ya ji yana cewa “Akan rayuwar ƴarki ma jinkimar zakiyi? Ki gaggauta zuwa ko na tura miki da wuyanta, zaki sha mamakina na baki 24hrs” Ba tayi masa magana ba ya ce “Ki amsheta ki bani Abraham, kuma daga nan ki fita sabgar shi kamar yadda kika fita a baya daman ba ciwon shi kika sani ba, i am waiting for you” Yana faɗin hakan ya kashe kiran, Khalil na ƙoƙarin ɗauke kunnen shi ya ji ta kama kunnen ta murɗe da ɗan ƙarfi, ya saki ƙara “Auchhh” Ba tare daya sani ba da kuma soyayyar uwa mahaifiya dake fusgar shi ya faɗa jikinta ya rungumeta a hankali a ɗan fakaice tayi Holding nasa back, da sauri ya saketa yana sakin numfashi, a karo na farko bayan wasu shekaru ta saki wani ƙlkyakkyawan murmushi tana juyawa, Majeederh tayi masa dariya ta ce “Wai meye kake gudunta?” Ya ɗan kwaɓe fuska a hankali ya ce “ban san me zan ce mata ba, ban santa bafa, kunyar ta nake ji” Kafin tayi magana ankira shi daga hukumar NAPTIP Musbah ya ce “Private Investigators ɗin mu sun shaida mana DDMASTER BOM yana Pakistan, zuwa jibi zai ɓace zamu tura maka komai na tafiya nan da 24hrs ka shirya ka tafi don’t let anyone know” Khalil ya jinjina kai saboda Jee dake kusa da shi, Musbah ya ce “And where are you now? Ina buƙatar sanin location, ƙasa, ko Area” Khalil ya yi jim sai ya ce “No, a shirya komai a tura ta waya” Yana faɗin hakan ya kashe wayar, ya ɗaga kansa kenan ya hango Gimbiya a hankali tana fita ta ƙofar baya hannunta riƙe da trolley ga wani ticket da yake gani, tunani yake where is she going to? Sai ya ɗaga shoulder kawai, ya nufi dinning zai ci abinci Jee kuma ta nufi wani part, kasancewar abincin larabawa ne aka zuba wani masifaffan pepper a ciki, ga ba wani ɗanɗano duk so da ƙaunar da Khalil kema abinci baya ƙaunar yaji ko da wasa, gigita masa lissafi yake ko yana ƙarami idan yaci yaji ya dinga hawaye yana zaro tongue yana “Mami pepper, Mami my tongue zai cire” Har wasu ƙananun guraje ke fito masa, ya zubawa abincin idanu ganin rice ɗin ta ɗan yi wani colour gwanin sha’awa ya sanya ya ɗauki spoon, tare da yin bismillah ya sanya a baki, da wani kalar sauri ya cillar da spoon ɗin, wani zufa na yanko masa jikinsa ya ɗauki rawa da ɓari, idanunsa sukai jajur suka fito waje saboda azaba, babu wanda ya fahimta, gashi ya kasa magana sai fito da harshe yake yana dunƙule hannu wata kalar gigitacciyar azaba yake ji tun daga kan yatsar ƙafarsa har zuwa tsakiyar kansa, yana jin har wani tiririn azaba yake ji na fita daga kansa, idanunsa suna ƙanƙancewa tunda yake bai taɓa jin abu makamancin haka ba, shi yasa ba abincin kowa yake ci ba, a hankali ya kifa kansa a dinning ɗin jikinsa duka ya jiƙe sharkaf da wata kyakkyawar zufa wacce tsananin azaba da gigicewa ya fiddo da ita, numfashinsa ya fara sarƙewa tsakiyar ƙirjinsa na masa zafi zafi da zugi, Mai martaba Ajlaal Sultaan da Zaytoon magana suke a hankali hakan ya sanya gabaɗaya basu farga ba, Roohan waya yake dannawa Ƙhulud kuma abincinta kawai take ci, zaton su kuma Gimbiya na sashin ta, Daidai nan majeederh ta fito ƙamshinta a kullum dake alamtawa zuciyarsa zuwanta shi ɗin ne a yanzu ya sanar da shi, ya miƙe da ƙyar jiki na ƙyarma Jee ta ce “Granny ga fresh milk ɗin…,” Bata ƙarasa ba ta ji an damƙota hanka ya jawo hankalin jama’ar wajan. “Khalil lafiya?” Cewar Zaytoon amma ina babu bakin magana Jee dake ƙoƙarin yi masa magana taga ya yi sauri a gaggauce cike da neman ɗaukin jin harshen shi zai tsinke da wani fitinannan wahalallan yanayi ya haɗe bakinsu waje guda…
[

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button