Mijin Malama Book 2 Page 53
Khalil na tsaye bakin ƙofa ya kasa ɗaga kai ya kalli Ummie dake cewa “Me kayi mata?” Ya ɗan marairaice ya ce “Ummie ba zan cutar da ita ba, matata ce..,” Tayi saurin ɗaga masa hannu fuska a haɗe ta ce “Na san matarka ce, me ka yi mata? Jinin nan na jikinka na mene?” Kansa a ƙasa ya ce “She is bleeding” A gaggauce Ummie ta nanata maganan a fili ta ce “Bleeding?” Kamar zaiyi kuka ya ce “Please ki fara dubata, kafin komai” Ta girgiza kai tare da murɗa handle ɗin Ƙofar bedroom ɗin ta shiga, idanunta ya sauk’a akan Majeederh dake durƙushe fuskarta ta jiƙe da hawayen azaba, sai girgiza kai da yarfe hannu take, wani irin masifaffen ciwo ne yake karta mata a mararta zuwa cikinta, bayanta ya riƙe kamar mai naƙuda, zufa ta jiƙata sosai tamkar wacce ta fito daga wanka. Ummie ta ƙarasa tana kallonta ta ce “Daughter meke miki ciwo?” Majeederh ta kasa magana sai girgiza kai take tana cije baki, a hankali kuma cike da dauriyar data aro ta yaɓawa kanta cikin jarumta a fusge ta ce “Marata Ummie, cikina, bayana Innalillahi, i don’t want to lose my baby”
Ummie ta miƙe tana danna wayarta ta ce “Babu abinda zai faru, sannu kin ji?” Kai kawai ta samu zarafin ɗagawa, Ummie ta kara wayar a kunnenta magana kaɗan tayi kana ta kashe, tana zaune kusa da Majeederh tana mata sannu wayarta tayi ƙara ta kalli Majeederh ta ce “The doctor is here” Sai kuma ta miƙe ta fita, not too long ta dawo tare da wata farar likita kasancewar babbar likita ce kuma Ummie ta faɗa mata condition ɗin da Majeederh ke ciki ta taho da komai na buƙata, injection ta fara yi mata na tsayawar jinin, kana ta mata gwaje-gwaje cikin ikon Allah zafin ya fara sauka jinin ya tsaya jikinta ya saki, Dr ta ce
“Ranki ya daɗe ta fara gyara jikinta zan sanya mata drip jikinta ba ƙwari” Da taimakon Ummie Jee ta wanke jikinta ta sauya kaya, Ummie ta kama hannunta zuwa sashinta ta ce “Dr follow me” Drip aka sakawa majeederh da wata injection ɗin (Allura) mai sauk’e zafin ciwo da sanya bacci (Pain reliever).
Bayan kammala komai Dr ta ce “Ina mijin nata? Ina buƙatar ganinsa urgently” Number shi Ummie ta kira yana ɗagawa ta ce “Zo part ɗina” Suna zaune ya buɗe ƙofa ya shigo basu da tabbacin ya yi sallama ko akasin hakan ya ɗan zauna saman kujera idanunsa akan Majeederh dake bacci tayi fayau, tayi wani irin kyau dan fuskarta har ta faɗa. Dr ta ce “Sir i need your attention” Khalil dai bai kalleta ba, Ummie tayi kamar bata san me ake cewa ba idanunta akan wayarta tana dannawa. Dr ta sake kallon Khalil ta ce “Ni zaka kalla ba matarka ba, ba ta dalilinka ta samu wannan ciwon ba? Ko a matsayinka na likita baka sani ba?, wai ma menene amfanin kasancewarka likitan? Tunda baka san matsayin matarka ba idan tana da ciki, ko kuma kaga wani sauyi a jikinta ka tsaya ka duba duk mene….,” A gigice Khalil ya ce “Stop, enough pls” Ummie waya take dannawa, amma kamar ta yi wa Khalil dariya ko bata kalle shi ba, tasan tambayoyin na Dr sun masa yawa surutun kuma hawar masa kai yake, a hankali ta kalle shi taga duk jijiyoyin kansa sun fito sun yi ɗoɗar a saman goshinsa idanunsa jajur.
“Ki faɗa mini me Zaki faɗa, kina juya mini kai!” Dr ta yi ta kallon shi kafin ta miƙa masa paper ɗin hannunta ta ce “A binciken da mukayi cikin jikinta bai fi wata biyu ba, yana cikin gaɓa ta haɗari kuma akwai rauni a bakin mahaifarta, yanzu Alhamdulillah mun samu nasarar tsayar da jinin dama cikin bakiɗaya” Khalil ya sauk’e ɓoyayyiyar ajiyar zuciya jin unborn ɗinsa yana lafiya, ya lumshe idanunsa yana hamdala ga Ubangiji Dr ta ce “Ya kamata ka ɗauk’e mata ƙafa, ka bata hutu akan gado domin tsananin takurarka ya jawo haka” Dr Khalil ya kalli likitan ya mayar da kansa kan fuskar Majeederh calmly ya ce “Yadda Daddy bai zama silar zubar cikina ba, nima ba zan zama silar zubar cikin Matana ba” Ummie ta tsaya da abinda take jin Khalil yau ya ambaci mahaifinsa kenan all this years tunanin mahaifinsa na ransa ko me? Son baban nasa yake?
“Khalil!” Ummie ta kira shi bai kalleta ba ya sauke kai ƙasa ranta ya ɓaci sosai sai bata nuna masa ba, Dr tayi murmushi tana jinjina ƙarfin hali da zuciyar Khalil ɗin a hankali ta ce
“Bana nufin haka, abubuwa da yawa suna causing miscarriage kamar su; Matsalar sinadarin halittar jariri wannan matsala ce wacce ake samu tun kafin halittar Ɗan Adam ana kiran sa (fatal genetic problems). Infection sanyin mata wanda yake sa ƙaiƙayin gaba, zuban farin abu, ciwon mara da ciwon baya. Sai kuma
Yin aikin ƙarfi: Yin aikin ƙarfi wanda ya wuce misali na daga cikin abubuwan da yake kawo zubewar cikin. Da kuma
Rashin lafiya: Dukkan rashin lafiya mai zuwa da matsanancin zazzaɓi ya kan iya haifar da yin ɓari”
Dr ta ɗan yi shiru tana kallon yanayin Khalil bata da tabbacin yana jinta ma, domin hankalinsa gabaɗaya yana kan Majeederh da yaga tana ɗan ɓata fuska a cikin ɓacin nata, sosai ya ji sanda take cewa “Cikina marata” Sai ya yi tunanin gajiya tayi zata gudu, gefe guda na zuciyarsa kuma yana jin tunda suke bata taɓa nuna masa gazawa ko ragwanta ta wannan bangaren ba, tana ƙoƙari da duk irin yanayinsa wanda hakan ke ƙara sawa ya sota fiye da ko wanne lokaci Likitan ta ce “Shan magunguna:Shaye-shaye magunguna ba bisa ƙa’ida ba, inma na Hausa ko na bature yana kawo zubewar ciki. Sai kuma
Nakasar maniyyi: samun nakasar maniyyin miji ko ƙwan mace ya kan iya haifar da zubewar ciki.
Matsalar bakin mahaifa: Idan mace tana da matsalar bakin mahaifa shima cikin ba zai zauna ba” Khalil ya dakatar da ita da cewa “Oh kina nufin cikin Matana ba zai zauna ba?” Dr ta ce “A’a, ban ce haka ba ina lissafa maka abubuwan da suke haifar da irin halinda matarka ta tsinci kanta ne” Ya girgiza kai kawai yana rufe Idanu, Ummie ta lura Khalil ya raina Dr ɗin gabaɗaya Already ya san abubuwan da take zayyana masa ɗin “Matsalar thyroids ciwon sugar hawan jini rashin ishasshen abinci rashin jini, shan sigari, suma duka suna haifar da zubewar ciki, idan mace nada ciki ga abubuwan daya dace ta rage yi, Jima’i, aikin ƙarfi, kada tasha ko wanne magani, ta dinga ziyarar asibiti akai akai domin tabbatar da lafiyarta dana babyn” Ta kalle shi ta ce “Matarka akwai abinda ya ɓata mata rai wanda ya haifar da tashin hawan jininta, tayi tafiya mai ɗan tsayi kamar ta mota ko jirgi,bayan nan ta jijjiga jikinta for sure, sannan kazo ka ɗora mata da wannan fitinar naka, na rubutu mata some drugs bayan nan kana dubata ka bata tazarar a ƙalla wata huɗu cif kafin ka sake kusantar ta”
Khalil ya miƙe tare da ficewa yana jan tsaki a fili wai wata huɗu kamar wani nakashasshe? Shi burinsa ma ya ɗauke matarsa ya lallasheta ya kuma dubata da kansa, amma bashi da zarafin hakan saboda kaifin Idanun Ummie. Tun ranar Ummie ta raba musu kwana tsakaninsa da Majeederh wajen suhur ne kawai ko buɗe baki, babu abinda ke damun Khalil tun yana ƙarami amma yanzu dalilin Majeederh rauninsa ya fito ƙarara a fuska sai ya daina ma yin suhur ɗin buɗe bakin ma ya daina, daga ƙarshe bashi da wajen zuwa sai masallacin ƙa’aba ya yi ta addu’a da neman yafiyar Ubangiji akan abubuwan da ya yi na baya, hakan nan ya samu kansa da yiwa Daddy addu’a duk da cewa shi ɗin ba musulmi bane da kuma Fulani wacce itama ta kasance uwa a gare shi. Ya hau yin fushin gaske da Majeederh ko waya ta kira shi baya ɗauka, ta rasa ya zata yi a haka har azumi ya shiga ashirin.
Tana zaune Ƙhulud Arzaan na kusa da ita ta ce “Wai kam lafiya kwana biyu Khalil baya zama?” Majeederh ta ɗan yi murmushi sau ta ce “Lokacin ibada, waye zai yi sake da wannan lokacin? Musamman da zamu shiga ranaku mafi girma?” Ƙhulud ta ce “Haka ne, Ubangiji ya amshi ibadunmu ya sanya ba mu yi k’ishirwar banza ba” A hankali ta ce “Amin” Fatymerh Clara dake jinsu ta ce “Ni kam Kspider yana dariya don Allah?” Majeederh ta watsa mata harara ta ce “Me kike nufi?”
“Ina nufin kamar kema baya miki dry, za kiga ko hira ake ya yi ta yin tsaki kenan, fuska a haɗe kullum ga ɗan banzan isa da gadara miskilancin jaraba, sai zuciya kamar kuturu”
Majeederh ta riƙe haɓa ta ce “Au haba? Yayan naki kike faɗawa haka?” Da sauri Clara ta ce “Waye yayan? Ai ki tambayi Ummie ni ta fara haifa kafin shi ya biyo bayana”
Daga bakin ƙofa aka ce “Ita Ummie ta ce haka?” Suka juya gabaɗaya banda Majeederh yana tsaye gabjeje da shi a bakin ƙofa jallabiya ce a jikinsa sai hiramin daya ɗaura a saman kyakkyawar sumar shi, fuska a kame ba walwala ya kafe Clara da kallo
“Ni bance Ummie ta ce haka ba, amma ko Daddy za’a tambaya ya san ni ce babba” A hankali yana shigowa daidai nan Ummie da Mai martaba Ajlaal Sultaan suka fito Khalil ya ce “Opps je ki lahira ki tambayo ok” Jikin Clara ya yi sanyi hawaye ya cika idanunta, tasan Daddy ya ɓata mata rayuwa amma ya sota fiye da komai ya bata kulawa da jin daɗi tattali da soyayya. Shi kansa Idanunsa sun yi jajur ya dubi Ummie ya ce “I got a message on my email from Latifa” Ya faɗa mata haɗuwar Latifa da Mr President da kuma musuluntar shi sai neman yafiyar da yake wajen su da ita kanta Ummie, ya shaida mata su Latifa sun kuɓuta ne a wani daji da jami’an tsaro suka kama motar daga nan ko wacce ta tafi garin su, yanzu haka tana gidan mijinta Aliyu zaman ba yabo ba fallasa. Ummie bata ce komai ba ta juya tare da barin wajen, Khalil ya shige part ɗinsu ko Majeederh bai kalla ba duk da tsananin kewarta da yakeyi yana jin kamar ya jawota ya rungume ya fahimci da sauranta. Miƙewa ta yi tare da kiran number shi sai da ta yi kira huɗu kafin ya ɗauka, ya yi shiru a hankali kamar zata yi kuka ta ce “Man” Ya ce “Kirani da Ibrahim ko Khalil Hawwa’u, tunda baki san darajata ba” Idanunta ya yi rau rau “Ni kuma?”
“A’a ni, faɗa mini dalilin kiran zan kwanta ne” hawayen da take riƙewa ya ƙwace ta ce “You ignored me, bana jin daɗi” Ya yi mata shiru kawai sai ta fashe da kuka, ya yi saurin runtse idanunsa zuciyarsa na bugawa da ƙarfi wato tasan menene rauninsa? His weakness! Ta jima tana rera masa kukan kafin ya ce “Kiyima kanki ƙiyamullaili, ko wacce mace tana neman lada a wajen mijinta da azumin nan amma ke ana hanaki? Kin dage kina ɗaukar zunubi aljannarki na ƙafata fa?” Tana shassheƙar kuka ta ce “Ummie ce, i am sorry” Kamar zai mata ihu sai kuma ya yi ƙasa da muryarsa ya ce
“Ummie! Ita Ummie aure ne da ita yanzu kin san me take na samun lada a waje? Kin faɗa mata wajen mijinki zaki?” Majeederh ta marairaice fuska ta ce “Taya zan faɗa mata haka Man?” Siririn tsaki ya ja sanda zai kashe wayar yana ji ta sake fashewa da kuka, a daren bacci baiga idanun Majeederh ba, ta sake kiran number Khalil a kashe. Ita kaɗai ce a bedroom ɗin bata san ina Ummie ta yi ba, ta rufe Idanunta a haka bacci ya fara fisgarta, can cikin baccin ta ji an rungumeta da kyau tana kwance male male a ƙirjin mutum yana shafa sumar kanta a nutse, a hankali ta buɗe Idanunta tare da yin motsi, ya sake shigar da ita jikinsa da kyau muryarta na rawa alamar taci kuka ta ce “I am sorry..,”
“Its my fault, sorry wifey”
Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya a hankali tare da sake shigewa jikinsa, daidai kunnenta yana sauke numfashi ya ce “Kina da laifi ina da shi, nawa babba ne forgive me, forgive your husband Khalil” Ta yi murmushi tana shafa ƙirjinsa ta ce “Bakai mini laifi ba, kuma ba zaka yi mini ba Love” Ya matseta tsam! Tsigar jikinsa na tashi ƙofofin gashinsa na buɗewa abubuwan da yawa suna masa yawa, komai na jikinsa ya bubbuɗe “I miss you!”.
Clamly ya ce “I see” Laɓɓanta yake ta kallo sai kuma ya ɗauke idanunsa gently ta kamo fuskarsa ya yi saurin matsawa ya ce “No please ba wannan ya kawo ni ba” Ta hararesa yana ƙoƙarin magana ta haɗe bakinsu waje guda, daga ita harshi sukai loosing control sama sama suka ji ana “Aby.. Aby.. Mimi Mimi nina” Da sauri Khalil ya zame jikinsa daga na Majeederh yana gyara zaman rigar ya juya Allah yasa hasken a kashe yake idanunsa ya sauka akan Alhassan dake zaune saman window ya hauro yana ƙoƙarin dirgowa cikin bedroom ɗin, Khalil ya yi sak wato sanda yake haurowa bedroom ɗin Ummie Alhassan ya ganshi? Ya nufi wajan Alhassan yana zuwa wajensa ya kawo kai wai suyi gware Khalil ya riƙe ƙugu, Alhassan ya yi murmushi yana lumshe idanunsa wannan shi ake kira da abin cikin ƙwan ya fi ƙwan, gado mai wahala hali zanen dutse shi da kansa ya san cewa Alhassan suffar shi ne, ya saka ya ɗauki yaron yana saɓa shi a kafaɗa ta gefen ido Majeederh ta dinga dariya ƙasa ƙasa. Azumi na ashirin da biyar suna zaune a parlour bakiɗaya ana tattaunawa akan yadda za a yi sallah da hawa Khalil baya cewa komai idanunsa rufe duk a takure yake bai saba zama waje guda ba,sallama aka yi gabaɗaya suka kalli mutumin kafin kuma Majeederh ta miƙe ta ce “Uncle?” Uncle Ismail ya yi mata tattausan murmushi kana ya ce “Bani ɗaya bane” Ta ce “Da waye? Uncle B? Abbu?” Ya girgiza kai ya ce “Mr no name…
[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *NIMCYLUV*
*_MIJIN MALAMA_*
Book 2 page 107
Final Episode
ArewaBooks: Nimcyluv
Okadabooks: Nimcyluv
Wattpad: Nimcyluv
Facebook: Na’ima Sulaiman Sarauta
Both Twitter and Instagram.
08119237616.