Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 1

Sponsored Links

 

_By NoorEemaan_✍️📚

 

Related Articles

_*All thanks goes to Allah subhana wata ala for giving me the life, ability, and strength of writing Munaya~Maleek. Greetings to ummourh na, my mother, my queen, my first love, Hajiya Mama. My sweet siblings, i love You. my fans ain’t excluded also, ina son ku duka, da barzaku nake taka rawa, my Habibty Saudat i know you won’t see this, cos you are not a fan of novels… but get this, i love You so much.*_

*_Ban san yanda zan fasalta muku wanna labarin ba, but it will be the best novel i have ever written, it’s going to be hot hot and hot, Kun san salon labarina, so trust me on this one too guys, sai dana shirya tsaf kafin na kowa muku shi, labarin ya kunshi cin amana, son zuciya, ƙaddara, kunci, mumunan dabi’a, fadakarwa, wa’anzantarwa, da nishadantarwa*.
*And i will be using roman numerals for every chapter, hope you won’t get confused? so guys are you ready? Oya let’s get started_.*🥰

All my novels are available complete at this platforms, usernames are:
Wattpad @NoorEemaan
Arewabooks:nooreemaan

⚠️*Caution*⚠️
🚫Ban yarda a juyamin labarin nan ta kowacce siga ba, ban yarda a karanta ko ɗora min shi a YouTube without my consent ba, ban kuma yarda a maida min shi audio ba tare da sanina ba🚫

*NOTE*
This novel is a total work of fiction, any resemblance of story or life style should be considered as a coincidence please!

In the name of Allah most gracious, most merciful…

 

i…..
(1)

*Tuesday*
8:00Pm

Cikin Wata murya mai rarrabewa hadi da rawa tace “Muna! dan Allah karki tafi ki bar ni kadai a gida” yarinya mai shekaru shida dake tsaye a rubabben kofar wani daki ce tayi maganar tana fashewa da kuka mai matukar ratsa zuciya.

Budurwar da aka kira da Muna dake tsaye a soron gidan ta tako cikin sanyin jiki zuwa wajen yarinyar, ta durkusa a gaban ta, tayi matukar kokari wurin mayar da hawayen da suka ciko idanun ta kana tace “Amnah kiyi shiru, bazan dade ba kin ji, saboda ke zan fita fa, saboda samun lafiyar ki nake wahalar neman aikin nan, kin tuna?, ko bakya so ki warke?”

“Inaaa sooo” Amna ta fada tana murza idanun ta, Munaya ta kamo busassu kana sirarran hannun ta tace “toh ki daina kukan bari naje, akwai koko a daki idan kin ji yunwa ki sha kinji? karki je ko ina” ta karasa maganar tana kokarin janyo mata hular kanta gaba wanda kwalkwal din kanta ya bayyana, domin babu gashi ko daya sak’amak’on lalurar yarinyar.

Ta dauki lokaci kafin ta iya haɗa kalaman
“Ni na daina kula su khairat, bayan idan na fita wasa suna ce min mai kan maza” ta kai karshen maganar da turo labb’anta gaba, Munayan tayi murmushi mai ciwo tace “karki damu da maganar su, zaki warke, har gashin ki ya fito in dinga Miki kitso, kina so ko?”
Amnah ta daga kai alamun eh ta fara murna, hakan ya ɗan sanyaya ran Munaya har ta samu kwarin guiwar mikewa domin tafiya, nan Amnah ta fara sabon kuka, sai Munaya ta tafi da ita, haka Munaya ta fito daga gidan, tana jin sautin kukan tilon kanwar ta har ranta, amma bata da zabi daya wuce fitan, fatan ta dai Allah yasa yau tayi dace da samun aiki…

****

Da ace ƙarfin iko, kudi, da duk wani ababen more rayuwa yana hannu ko wani ruhi, tabbas da ta fi kowane ɗan adam abubuwan data lissafa ko dan su huta daga kyara da suke fuskanta a wajen mutane, sai dai shi arziki riga ne, wanda Allah yaso shi zai sanya wa, daga lokacin data yi wayo ta fahimci mafi yawan mutanen duniya sun fi daraja masu abin duniya ta ji ta kwadaitu da ta zama mai kuɗi, ba wai dan a daraja ta ba, a’a saboda ta iya dauke duk wata bukata tasu, babban abinda yasa take son samun kudi saboda lalurar tilon kanwar ta, numfashi ta sauke, kana a gajiye ta zauna kan wani dakali dake gefen hanya, ta cigaba da sauke numfashi a karo na ba adadi sakamakon tafiyar data sha, domin tun safe data bar gida a yawon neman aiki take amma bata dace ba, ita bata matsa ba ko goge-goge da share-share ta samu zata yi.

“Ya rabbi ka taimake ni” ta karasa maganar tana daga kanta sama wanda hakan yasa ta hango wani katon gini dake tsallaken titi, zumbur ta mike, ta tsakankanin labb’anta ta karanta sunan dake rubuce baro-baro a saman ginin da kyakkyawan rubuta…
” *A.A DAWOOD MOTORS* ”
cikin sauri ta nufi titin not minding ababen hawa dake wucewa, Allah ya bata ikon tsallakawa amma ta samu rabon zagi daga wani magidancin mutum daya kusan yin karo da ita a babur din sa, sam Munaya Bata damu da zagin ba, ta kara tsallake dayan titin ta nufi bakin gate din wajen, tana fatan ta dace a yau, bata san karaya ko gazawa ba, a kullum tana sawa a ranta cewa zata samu aikin yi, Allah zai iya ikon sa a kan su a ko wani lokaci, amma ganin girman Wajen data tunkara ya dan tsorata ta, amma ta dake ta shiga kwankwasa gate ɗin, tsawon mintuna uku kana aka buɗe, wani saurayi dake sanye da blue din riga da bakin wando hadi da booth baki ya bayyana a gaban ta, da alama shine mai gadin, wani kallon sama da ƙasan da mai gadin ya bita da shi ya sanyaya mata jiki, ita ma sai ta bi jikin ta da kallo, ta fara cin karo da kafar ta da yayi bututu da dattin kasa dake sanye cikin silifas dan Madina da har ya gaji da dinki, kana ta kalli kodadden bakar jallabiyar dake jikin ta wanda duk ya huhuje, kana ta kalli mayafin dake kanta wanda gefe daya ya kone, duk yayi Gashi-gashi saboda tsufa, tayi kokarin mayar da kwallar daya ciko idanun ta, ta ɗan risuna tace “ina wuni, dan Allah akwai vacancy? Aiki nake nema”

Taji gate man ya bushe da wata ƙatuwar dariya har Munaya ta ɗan tsorata ta ja da baya kaɗan, sai daya gama dariyar sa, sannan ya tafa hannu yana mai kara kallon ta musamman kafar ta daya sha datti ya ce “aiki kike nema, amma yarinyar nan baki da hankali ko? nan wajen ya Miki kama da wajen wasan yara, toh bari ki ji kaf staff’s din Company’n nan babu mai karamin kwali, daga masu degree sai masters, Ni nan da kwalin degree dina na samu wanna aikin da kyar, dan haka ki kama hanya ki bar wajen nan domin ko a mai goge-goge ba za a dauke ki ba….”

Munaya tayi ƙasa da kanta Wasu zafaffan hawaye suka zubo mata, ta tuno halin da suke ciki, ta kuma tuno cutar dake damun kanwar ta, da a kullum cutar kara cin ta yake, gashi ko sisi na magani basu da shi bare na aikin da za’a mata, da samun aikin nan ta dogara, a sanyaye ta dago zata kara rokon mai gadin duk da da kamar wuya a bata ko da goge-gogen ne kamar yadda ya faɗa, sai taji horn daga cikin Company’n, mai gadi ya tafi da sauri ya bude gate din, wata hadaddiyar mota ta danno Kai waje, hakan yasa ta yi gefe cikin sauri, tana kallon yanda mai gadi yake girmamawa na cikin motar da bata iya hangowa saboda tint ne glasses din motar, har motar ta gifta ta sai kuma ta dawo da baya, aka sauke glass din motar, and then she saw two young handsome Men, daya baki dayan kuma fari, bakin ne kuma ke tuka motar, “Nura!” Taji bakin saurayin ya kwala kiran mai gadi.
“Yes sir!” Nura ya amsa hadi da matsowa wajen motar cikin girmamawa.

“What’s this young girl doing here?”

“Oga, wai aiki take nema” Nura ya karasa cikin Muryar dariya, daidai lokacin farin saurayin ya dago ya kalli inda Munaya take tsaye, kallon kaskancin daya watsa mata ya sanya kirjin ta lugudan bugu, tayi saurin yin kasa da kanta jikin ta na dan k’ak’arwa.

“meye abin dariya?” bakin saurayin ya fada yana bata rai, domin shi kam Munaya ta burge shi, musamman ganin ta karama amma tana da zafin nema.

“Sorry sir!” Nura ya fada cikin kame kan sa.

“Hey! Come closer” ya ce yana yafuto Munaya da hannu, jiki na rawa ta taho amma bata ƙara gangancin kallon farin ba.

“Ya sunan ki?”
“Munaya! Munaya Jabir”
Ya jinjina kai kana yace
“Aiki kike nema right? misali idan an dauke ki aiki a wanna Company’n wani irin aiki zaki iya yi?” Ya tambaye ta calmly.

Ta ɗan saci kallon farin ta ga kansa a kasa yana danna tsadaddiyar wayar hannun sa, ta hadiyi wani yawu, kana tace “ko wanne irin aiki aka bani zan iya yi”

Ya jinjina kai, karsashin yarinyar na burge shi, bai kara cewa mata komai ba, ya kalli Nura yace “take her to Maleek’s office ta jira mu, yanzu zamu dawo”

“Yes sir!” Nura ya amsa cikin mamakin daya gama kashe sa, “Lallai yarinyar nan da sa’a take” ya fada a ransa cikin dimbin al’ajabi daya gagara boyuwa a fuskar sa.

***

Bayan samari biyun nan sun dan yi nisa da tafiya a mota, farin mai suna Maleek yace “what’s the meaning of abinda ka yi Shakur?”

“Ban gane ba” Shakur ya fada acting as if bai gane me Maleek yace ba.

“Shakur don’t force my hanger please, meye amfanin jiran mu daka ce kazamar yarinyar can tayi, don’t tell me aikin zaka bata, because hakan bazai yu ba” ya karasa a zafafe.

“Zai yu Maleek, aiki zan bata, sai dai idan zaka nuna min cewa A.A DAWOOD MOTORS mallakin ka ne” ya faɗa cikin daga sauti.

Maleek Ya kankance ido, hadi da rage murya yace “ka san bana son hakan ko? Komai nawa naka ne, kana da iko da shi, don’t ever tell me that”

“Then ka yarda na bata aikin, kai fa kace kana bukatar ma’aikaciya da zaka dinga aika idan kana bukatar wani abu, gashi kuma an samu”

“Not this type Shakur, tayi datti da yawa, kuma tayi kankan ta, sannan bana jin ko secondary school ta gama, ka kuma san kalar ma’aikatan da nake dauka”

Shakur ya yi murmushin yace “Maleek ka sani cewa komai lalacewar abu idan ya samu gyara zai gyaru, sannan age is just a number, shi aiki da tunani ake yin sa ba da matsayin karatu ba, saboda haka ka bata dama, mu taimaka mata, domin yanayin ta kadai ya nuna cewa tana cikin halin talauci”

Maleek ya yi shiru ya cigaba da danna wayar sa, domin idan yace zai cigaba da magana zasu yi fada da Shakur, abinda kuma baya so kenan, shi kuwa Shakur ya yi murmushi ganin ya ci nasaran shawo kan Maleek, duk da yasan ba wai ya wani yarda bane.

***
“Nura, Nura, ya ne? a’ah! wanna fa, bara take ne? Shine zaka shigo mana da ita har nan? Da alama dai kana son rasa aikin ka ko, domin yanzu boss zai dawo” wata matashiyar budurwa mai Kimanin shekaru ashirin da Shida data fito daga wani office ta fada.

“Toh ai oga Shakur ne ya ce na kawo ta nan ta jira su?”

“Oga Shakur!?” Matashiyar budurwar ta fada cikin mamaki.

“Kwarai kuwa, nima abin ya bani mamaki sosai” ya juyo ga Munaya yace “kinga ki zauna a can ki jiran su” Nura ya fada yana nuna wa Munaya kujeran zama.

Sannan ya dawo kusa da matashiyar budurwar nan yace “Habibah Bari na koma bakin aikin na”

Habibah ta dauke kanta daga kallon kurillar da take wa Munaya tace “toh gashi bata yi kalar masu kuɗi ba bare nace ko kanwar su ce?”

Kasa kasa yace “Haba Habibah, ina wannan fakiriyar da su boss? Kar ki aikata zunubi mana, kawai dai yarinyar ta ci Sa’a ne, musamman da ta samu oga Shakur ya zo yau, kin san shi da saukin kai sosai” ya gama maganar yana barin wajen domin zuwa bakin aikin sa, duk da yana so su cigaba da gulmar amma baya son rasa aikin sa.

Munaya Kam bata damu da maganar su ba, domin ta ji fiye da hakan a wajen mutane, ita addu’ar ta su bata aikin, tsawon mintuna ashirin take zaune a wajen tana cigaba da jiran su, sai zuciyar ta ya raya mata da wanna zaman ai gwara tayi sallah kawai, hakan yasa ta mike zuwa wata kofar zallan glass tana kokarin jan sa ta ga kofar ta buɗe da kanta, ta ɗan ji tsoro ganin kofa ta buɗe kanta, tayi jim kadan, sai kuma ta shiga, kamshi mai dad’i daya cak’udu da sanyin Ac ya bugi hancin ta, a dan kallon data yi wa office din ta fahimci ba karamin kudi aka narka masa ba, kofofi biyu ta gani, ta bude na biyun ta ga lafiyayyen banɗaki ne da bai cika girma ba, shiga tayi da dattin kafar ta, ta yi tsarki, amma ta rasa ina zata danna domin fitsarin ya tafi, haka ta kunna famfo tayi alwalar ta, ba tare da ta lura da sink da aka tanada domin wanke hannu da alwala ba, gaba-daya ta zuba ruwa a kasa, ga dattin kafar data wanke duk ya bata tiles na toilet din, ta fito tana gyara mayafin kanta, duk inda ta taka sai datti ya manne a kasan tiles din domin kasan silifas din ta da dattin ƙasa sosai, tana kokarin daukar wani sallaya data gani a ninke kofar office din ya buɗe, Maleek ya shigo, ta tsorata ainun har sallayar hannun ta ya zame ya fadi, cikin fuska mai dauke da tsananin bacin rai yake bin tsahun silifas dinta da kallo wanda ya gama bata farin tiles din office din sa, “kee!” Yace a kausashe ya nufe ta gadan-gadan…

 

*Wanna labarin daban yake, zai zo da wasu sababbin salo masu yawa, kamar yadda zai fi sauran books dina tsayi*😘😚.

 

 

Kafin mu je ga page na gaba, bari na baku labari akan littafai na dana rubuta behind the scenes ku sha dariya.

*(PAPI NE!)* A littafin papi ne, Hussain Habib Nu’aymah ya kamata na aura masa, amma sai PAPI ya bani tausayi, ya sha wahalar rainon babyn sa, shiyasa na bashi auren ta.😍

*(Mijin Ammi na ne sila)* A littafin mijin Ammi nane sila, kamata yayi ace bayan fyaden da Alhaji shettima ya yi wa Abrar zata dauki ciki ta haihu, Sannan kwakwalwar ta zai tabu fiye da yanda na rubuta amma sai ta bani tausayi, haka zalika doctor Aaban deserve some happiness, shiyasa na takaita musu wahalar…. 😀

And *(Kyautar koda)* a littafin kyautar koda it was supposed to be daddy zai aurawa Fadeelah jameeel ne ba fadeel ba, sai dai Fadeel ya dawo daga neman kudin sa ya tarar fadeelah tayi aure, har ta kai shi ga kwanciya asibiti, amma sai fadeel ya bani tausayi, cos ya sha wahala da yawa, he deserve some happiness too right…? 😃

Then *(Abraham)* a littafin Abraham kamata yayi ace sharrin da madam gloria ta kullawa Aysha na poison ya tabbata har hakan ya kai ta gidan yari, amma sai ta bani tausayi, ooh my innocent Aysha😁 Abraham kuma kamata yayi ace shima ba zai sake tsayawa kan kafafun sa ba sakamakon karfin gubar daya ci, sai dai zama kan wheelchair, amma sai ya bani tausayi shi ma na takai ta masa wahala😃.

*(Rayuwar faheemah)* a littafin rayuwar faheemah kuma yanda na tsara labarin, kamata yayi ace lokacin da jameela ta ga hoton fu’ad har ta nuna wa Mami tana son shi, har mami ta je wajen boko, na so asirin ya ci shi har ya juya wa faheemah baya amma sai ta bani tausayi, kuma ina son ta sosai shiyasa na kawo karshen sharrin mami a hanyar ta na dawowa daga wajen boko😻.

*(Hoorain mai kusumbi the hunch girl)* a hoorain kamata yayi ace bayan kusumbin hoorain ya warke Taheer yaci nasarar auren na ta, amma ina son hamdan sosai ya kuma bani tausayi saboda wahalar da bai saba ba ya shata a duniyar mutuwa saboda Hoorain, and na so awajen da aljanin duniyar mutuwa yace lallai sai mutum daya ya sadaukar da rayuwar sa kafin daya ya iya daukar kwaryar maganin hoorain kamata yayi aljanin ya dauke hamdan tunda shine bako a garin, then Aramani ya dawo da kwaryar maganin kusumbin hoorain, ya kuma aure ta, amma tabbas hamdan zai dawo bayan wasu shekaru tunda shine star, musamman idan su Ammi sun dage da addua, amma sai hoorain ta bani tausayi domin bazata iya jure rashin hamdan ba…. 🤓

 

Kun san meyasa na baku labarin nan?☺
Saboda a *MunayaMaleek* babu wanda zan tausayawa, yanda na tsara haka zan rubuta shi, infact MunayaMaleek will be one of my most favorite novel dana taba rubutawa, dan haka ku biyoni dan jin yanda labarin zai kaya, you will gonna love it guys in Sha Allah, i promise.

 

07082281566

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button