Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 25

Sponsored Links

XXV….

*Munayamaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya first bank. Evidence of payment to 07082281566(Dan Allah idan baki shirya siya ba don’t chat Me)*

Cikin munaya ya shiga wata na 9 amma shiru babu alamun nakuda, Hakan ya dami barrister Abrar har take gayawa mijin ta kodai a ciro babyn tunda wasu ma na haihuwa a 36weeks, ɓalle nata cikin da yayi wata tara cif, doctor Aaban ya kwantar mata da hankali, ya kara da cewar Kada ayi gaggawa.
Lokacin azumin Ramadan ya zo, suka hana munaya azumin saboda yanda ta dawo kalar tausayi, idan yaso ta rama bayan azumin tace zata Iya ta kuma ce ko da bata yi ba bazata iya cin wani abin kirki ba, ba yadda suka iya haka suka barta, a kwana a tashi azumin ya dinga gudu tamkar ba yau aka fara ba, har ana maganar gobe Sallah kamar wasa, ikon Allah kuma munaya bata sha ko ɗaya ba, Dukkanin su sun jinjina ƙoƙarin ta, domin ko shabiyar basu yi tunanin zata iya kai wa ba.

Related Articles

*Ranar Sallah*
Dukkanin iyalan doctor Aaban sun tafi idi cikin kyakkyawar shiga, sai munaya kadai dake gida kasancewar tace ba za ta ba, basu kuma takura mata ba, duk da barrister Abrar bata so hakan domin bata son barin ta ita kadai a gida Musamman da cikin ta ya gama tsufa haihuwar kuma bai zo ba, but she has no option.

Cikin tafiya a hankali munaya ta fito daga toilet jikin ta da lema da alama wanka tayi, ta kara duhu da sirranta sai uban girman da cikin ta ya kara, duk Wanda ya ganta zai dauka yan uku zata haifa, karaf idanun ta suka sauka kan mirror data manta rabon data kalle shi, idanun ta ya Fara sauka a cikin ta tayi saurin dauke idanun ta domin bata son gani, ta nufi gaban mirror ta ɗauki farin kyallen da takan rufe madubin da shi daya zame ta mayar ta rufe fuskar madubin dashi , ta dauki man shafawar ta zata zauna a gado kenan domin ta shafa, kasss taji bayan ta ya amsa, “innalillahi wa inna ilaihi raju’un” ta furta tana cillar da man shafawar ta saka hannu ta dafe bayan ta da shi tana yarfa hannun ta, mararta ya shiga wani ciwo da bata taba jin makamantan sa ba, ta tsugunna kan gwiwowin ta tana cigaba da yarfa hannun, hawaye cabe-cabe a fuskar ta da yayi fayau, kukan da take son yi ma ta kasa saboda tsananin radaddin da take ji, ta hango wayar ta can kan pillow amma bazata iya tashi ta dauko ba, so take kawai ta kira barrister Abrar domin ta taimaka mata.

***
_9:30am_
*Bayan an sauko daga masallaci*

“Pure heart ka kara sauri dan Allah, mun bar munaya ita kadai a gidan fa”

Doctor Aaban ya juyo ga matar sa Yace “duk gudun nan da nake decent one?” Ya fada da murmushi a fuskar sa.

Cikin damuwa tace “hankalina gaba-daya yana ga munaya ne, gaskiya ina ganin ayi mata aikin nan a ciro babyn yarinyar nan ta huta hakan nan, haba wata goma fa ba wasa bane”

Doctor Aaban shi kan shi wanna karon bai ja da ita ba, saboda abinda ya kamata ayi tuntuni kenan, amma duk suna tunanin haihuwar zata zo da yan kwanaki ƙalilan bayan ta shiga wata tara.
Ya kalle ta yace “idan mun koma gida sai ku shirya mu tafi asibitin”

“Eh hakan za’a yi, amma asibitin ka zamu je saboda surutun mutane”

“Ai dama, where else did You think?”

Barrister Abrar ta yi murmushin jin dadi, a matukar kage take da su isa gidan, ta leka su miemie dake bayan mota ta san ba karamin farin ciki zasu yi ba idan suka ga munaya ta haihu.

Har yanzu munaya na nan yanda take ta kasa motsa wa, ta haɗa uban gumi, babu abinda take sai girgiza kai da cije labbanta, ji take kamar zata mutu, fasalta zafin ba mai yiwuwa bane sai wanda ya taba shiga hali na nakuda kawai ne zai fahimci halin da take ciki, ta yunkura a ƙoƙarin ta na son daukar wayar ta ta ji an turo kofar an shigo, Bata san waye ya shigo ba, amma ta ji dadin hakan, at least za’a taimaka mata.

“Munaya!!!” Muryar barrister Abrar kenan.

Munaya ta juyo da birkitattun idanun ta masu cike da hawaye, sai a lokacin wani mugun kuka ya kufce mata. “Mami marata, bayana zai ɓalle, Mami zan mutuuuu, wayyo Allah na”

Gaban Mami ya fadi data ga halin da munaya ke ciki a yanzu data juyo kasancewar ta bata baya ne dazu.

“Innalillahi wa inna ilaihi raju’un, sannu munaya, sannu, yanzu zamu je asibiti” ta fada tana shafa bayan ta, daidai lokacin da aka bude kofar, doctor Aaban ne, ya koma da baya ganin babu kaya a jikin munayan sai towel, ya riga ya fahimci komai dan haka ya dan daga sauti yace “pure heart find her something to wear, ku same ni a mota”

“Toh, pure heart ka daukar min jakar haihuwar ta na hada yana dakin can ka samana a mota” ta fada.
Kana tayi kokarin dago munaya domin ta zaunar da ita kafin ta dauko mata riga, daidai lokacin da Wani ruwa mai yauki ya fashe daga jikin munaya, “innalillahi wa inna ilaihi raju’un” barrister Abrar ta fada duk ta bi ta rude tamkar bata taɓa haihuwa ba, sai dai karancin shekaru da tausayin munaya ne ya sata hakan, gani take she’s too young for all this, taya karamar kwakwalwar ta zai jure zafi irin wanna? Cikin sauri ta dauko mata doguwar ruwa mai yalwa ta sanya mata da hijabi da bai kai kasa ba, rungumo ta a jikin tayi, amma tafiya ta gagari munaya, ji take kamar an sanya mata bulo a kasan ta, cikin lallashi barrister ta ce “sannu, daure ki taka mu fita”

Da kyar suka iya fitowa falo, su miemie suka mike, fuskar sa Tamkar zasu saki kuka ganin mayuwancin halin da munaya ke ciki. Barrister Abrar ta cigaba da tafiya da munaya tace “ku zauna miemie, zan kira mummyn ku hanan tazo ta dauke ku” ta fada ganin yaran na biyo su.
Junior ya Saki kuka yana kiran “anty muyaya” yau kam munaya bata jin sa, su miemie suma suna kiran “Mami” barrister kuwa bata saurari kiran da suke ma ta ba suka fita, doctor Aaban ya riga ya bude musu kofar back seat, da taimakon sa aka saka munaya cikin mota, ya tada ta cikin sauri suka fice, suna hanya barrister Abrar ta shiga lalubo wayar ta, Sai ta tuno cewa ta cilla dazu data ga halin da munaya ke ciki.

Ta mike hannu ta ɗauki na doctor Aaban dake front seat kujerar mai zaman banza.

Ta kira barrister Hanan da mata bayanin hankalin da ake ciki, ita ma hankalin ta ya tashi ta yiwa munaya fatan sauka lafiya da alkawarin zuwa asibitin anjima.

Barrister Abrar ta kalli fuskar munaya dake ta cije labbanta, yayinda rigar ta ya jike tamkar an sheka mata ruwa, tayi mata sannu tana goge mata gumin fuska amma kara tsatsafowa yake, Allah ya bawa munaya wani irin juriya sam bata yi ihu ba, ba tare da ta dauke kanta daga fuskar munaya ba tace “pure heart amma ciro mata babyn za’a yi ko? I don’t think zata iya haihuwa da kanta, I’m afraid kar ta kamu da yoyon fitsari” barrister Abrar ta karasa kamar ta saka kuka saboda yanda munayan ke tayi.

“Muje dai, we will try our best, amma it’s better ta haihu da kanta, babu abinda zai same ta in sha Allah, amma idan ta kasa sai ayi c.s din, addu’ar mu dai Allah ya raba lafiya”

“Ameen, munaya sannu kin ji ko, in sha Allah yau zaki huta” barrister ta fada cikin rawar murya, ta cikin mirror doctor Aaban ya girgiza mata kai alamun kar tayi kuka.
Kana a fili yace “be strong for her” barrister ta gyada kai tana matse baƙin ta da labbanta saboda kar tayi kuka.

Cikin gaggawa nurses suka shigar da ita *maternity Ward* musamman ma da aka ga cewa mai asibitin ne da kansa ya kawo ta, doctor Aaban ya umarci barrister Abrar data shiga office ɗin sa ta zauna, amma ta ki, ta roke shi ya barta ta shiga dakin da munaya take bazata iya zama ba, duk da hakan ya saɓa dokar asibitin amma Ganin yanda hankalin ta ya tashi ya saka ya amince, suna Hanyar shiga maternity Ward ɗin ya ke sanar mata ya riga ya kira Abbas tuntuni tunda yana hakkin sani, ta jinjina kai cikin gamsuwa, shaf ta manta da wani Abbas wallahi.

Suna shiga suka tarar nurses sun sanja mata kaya zuwa na asibitin, munaya na kwance sai juye-juye take cikin zafin ciwo, ta damke gefe da gefen zanin gadon ta cukurkurde cikin hannun ta, kasa kasa Muryar ta ke fita cikin kiran sunan Allah, hawaye kam shabe-shabe a fuskar ta, barrister ta karasa gadon ta shiga shafa gashin kanta dake hargitse,

“sannu munaya”

“Ma…mi…wa..yyo Allah na” take ta maimaitawa, Hakan ya kara ruda barrister, ko a haihuwar ta bata jin ta taɓa irin wanna rudewar da take yanzu.

Doctor Aaban ya kalli nurses biyun da suka kasance Christians ne kasancewar ya bawa musluman hutun Sallah na kwana biyu yace “have You guys checked her?”..

“yes sir, ta kusan haihuwa, mun mata allura”

Barrister Abrar ita kam hankalin ta bai kwanta da wanna haihuwar da aka ce munaya zata iya ba, shiyasa tafi son a mata C.s, amma tayi shiru bata ce musu komai ba tana addu’a a ranta.

Munaya ta fara wani Irin nishi, hakan ya ja hankalin su, Cikin wani irin sauri suka rufa kanta, suka tabbatar haihuwar ce ta zo, nurses suka shiga ce mata “pushhhhh, push harder” munaya kam ta shiga nishi da iya karfin ta hawaye na zuba a idanun ta, ji take kamar ta mutu ta huta da wanna azabar, da dukkanin karfin daya rage mata take nishin, so take kawai ta ga cikin nan ya bar jikin ta, barrister Abrar sai tofa mata addu’a take, kasancewar tayi labour ta gaji Cikin mintuna 15 ta haihu, saukar kukan baby daya amsa kuwwa a kunnen munaya yayi daidai da sumar da ta yi.

Cikin tashin hankali barrister Abrar ta sanar da doctor Aaban munaya ta suma, yace wa nurses da su shirya babyn, ya shiga bawa munaya taimakon gaggawa har numfashin ta ya dawo daidai, sai dai bacci mai karfi ya dauke ta sakamakon allurar, da yayi mata, ya karbi babyn a hannun nurses dake santin kyawun babyn kasa kasa, ya basu umarnin gyara munaya, ya karasa gyara babyn dake sanye da kaya na sanyi farare kal kana ya dora a scale, sai da ya tabbatar babyn na cikin koshin lafiya Sannan ya mikawa barrister Abrar dake murmushi, ta karbi babyn dake ta tsotsan hannu.
“Alhamdulillah, masha Allah) ta furta cikin jin dadi
“Muje, za’a sanja mata daki zuwa na hutu” inji doctor Aaban.
Ta juyo ta Kalli munaya dake bacci fuskar ta fayau kamar wacce ta dibi shekaru tana jinya, kana ta bi bayansa, suka shiga office ɗin sa, kiran doctor Abbas ya shigo wayar doctor Aaban, ya daga, doctor Abbas Yace “gani na shigo asibitin yanzu, ya munaya take, ina fatan ba matsala” ya tambaya a dame.

“Kazo office dina muna ciki”

Babu bata lokaci ya shigo office ɗin, tunda asibitin ba bakonsa bane, ya tsaya daga bakin kofa ganin baby a hannun barrister Abrar, fuskar sa ya fadada da murmushi, at the same time Kuma mamaki yake, bai taba tunanin abubuwan zai kasance haka ba, a kullum fargaban sa ya haihuwar munaya zai kasance? “Ka shigo mana, ka tsaya daga kofa” barrister Abrar ta fada tana dariya.

Ya sauke numfashi yace “bazaki gane ba barrister, where’s munaya?”

Wanna karon murmushi tayi tace “tana dakin huta.

“Alhamdulillah, Allah mun gode maka” ya fada yana karbar babyn, zai iya cewa bai taba ganin cute baby kamar wanna ba, kyawun babyn yayi matukar shiga idanun sa, bulbul babu rama a tare da babyn, ya rufe idanun sa Yana ji tamkar shi aka yiwa haihuwar saboda yanda zuciyar sa ke cike da farin ciki, ya kalli barrister Abrar yace “me aka samu?”

Muryar barrister a sake sosai, hakan zai tabbatar wa mutum da cewa she’s extremely happy tace
“she delivered a baby girl”

 

_kuyi hakuri update ya zo a kurarran lokaci_🙏💖

NoorEemaan
07082281566

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button