Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 29

Sponsored Links

XXIX….
<29>

*Munayamaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, then your Evidence of payment to 07082281566*

“Daman na san kai din billionaire ne, You don’t have to say it again”

Related Articles

Maleek ya runtse idanun sa Yana kauda kansa gefe, yau duk kalaman daya tsana Shakur ke gaya masa.

Shakur kam bai damu da yanayin sa ba ya cigaba da cewa “amma ka sani, ba komai kuɗi ke samar da shi ba, baka jin ko kunya da maganganun nan naka? Yarinyar nan tun tana ciki bata taɓa jin Muryar ka ba, kazalika wacce tayi wahala da ita baka taba bata kulawa ba har ta haihu, idan ba ta silar doctor Abbas ba bai zama Lallai wanna jaririyar da ma Uwar ta su rayu ba….”

“Karka kara kiran min sunan gayen can, ya faɗa ko nawa ne zan biya sa, Bama shi ba duk wanda yake da saka hannu a kula da Ita should name his or her price I will pay!”
Ya katse wa Shakur maganar sa, idanun sa har wani wutar bala’i suke fitarwa.

Shakur ya girgiza kai, yace “You see your problem, money Money money, you always put money first in anything you say, ba kuma zan gaji da faɗa maka ba, kudi ba sune komai ba”.

Maleek ya shafa kansa, sam ba haka yake nufi ba, Shakur na fahimtar sa a baibai, ya cije labbansa kana yace

“Stop it Shakur! Kafi kowa Sanin cewa bana show up da kudina”

“Amma kalaman bakin ka na nuni da hakan, why MALEEK? Kasan abu ɗaya, ba kowa bane is after money, doctor, barrister Abrar, ko mijin ta, wa kake nufi da wandanan kalaman naka, ko munaya? Kafi kowa sanin cewa that girl ba makwaidaciyya bace, da son abin duniya dabi’ar ta ce da bata dawo maka da kudaden ka ba, Kasani akwai mutanen da suka fi buƙatar kulawa da soyayya fiye da mata’ul hayat(kyalekyalen rayuwa) ko kunya baka ji kace a baka yarka? Who does that, a ina ka taba jin anyi hakan? Yar daka san da zaman ta ko wacce baka sani ba, yanzu idan aka baka yar ya zaka yi da ita? Oh nasan zaka ce zaka yi employing nannies, shayar da ita fa? Shima kana da arzikin da zaka iya dauko mai shayar da ita. Saidai ka manta abu daya su yara musamman jarirai sun fi buƙatar uwayen su fiye da kowa, kuma uwa ta shayar da yaron ta yafi amfani a jikin sa fiye da komai, Bama wanna ba, ka shirya bayyana wanna sirrin ga su Daddy? Think about it, ka kuma sanja dabi’ar nan taka kafin lokaci ya kure maka”

Maleek Ya rasa abinda zai cewa Shakur, dama can yafi shi baki, ba kasafai yake magana ba, sai ya samu kansa da cewa
“Waccen ya fara koya maka rashin mutunci ko, Ni kake fadawa haka?”Maleek ya fada yana nuna kansa da yatsantsa manuniya.

Shakur yayi wani murmushi yana girgiza kansa, ya fahimci wanda Maleek ke nufi dan haka yace “gaskiya ce nake fada maka, kuma shi din mutumin arziki ne, rawar daya kamata ka taka a rayuwar munaya yake yi, tarayya da shi sai dai ya koya maka kyawawan dabi’u, ba kai ya kai mutum ga bata ba”
Shakur ya fada cikin dauriya, domin basu saɓa wadannan rigingimu ba, Wasu abubuwan rufe ido yake ya furta su ga Maleek ko da bai so ba.

“Ba matsala cigaba da yabon bare a kaina, dama ba yau ka fara ba, ina kara fada maka ina son yata a kusa dani, zan….”

Shakur ya dakatar da shi dacewa “sai dai idan Ni Shakur bana raye ne zaka dauki Little Amnah, wallahi baka isa ka mayar da ita marainiya ba, bayan Munaya na raye “.

“Haka kace?” Maleek ya fada yana dage girar sa daya tattare saboda fushi.

“Eh haka nace Maleek, idan har ka cika mahaifin ta, kana kuma kaunar ta kamar yadda idanun ka suka fallasa soyayyar da kake mata, then act like one, ka taka rawar uba a rayuwar Little Amnah” yana gama fadin haka ya cigaba da harkokinsa, a yanda suka gasa wa juna magana idan mutum yazo wucewa zai dauka cewa ko hira suke, domin ba ihu suke ba, sai dai fuskar su duka turbune da ɓacin rai.

Maleek ya juya wa Shakur baya yana tunanin kalaman sa, kansa yayi bala’in daurewa, kalaman Shakur ɗin na amsa kuwwa a kunnen sa, take kansa ya ɗauki ciwo.

Daga wanna ranar basu kara maganar data shafi little Amnah ba, sai dai Maleek ya yi zuru-zuru saboda yanda Allah ya kara jarrabar shi da matsanancin soyayyar little Amnah, tun yana fushi bai amince da sunan da aka sanya mata ba, har ya dawo ya saduda, sunan ya zauna a zuciya da ƙwaƙwalwar sa, a wanna halin suka ƙasance har wata daya.

A wanna bigiren yaji komai zai iya faruwa da shi idan bai sanya yarinyar sa a ido ba, saboda Little Amnah ya dawo da WhatsApp his favorite platform domin kullum cikin sanja dp Shakur ke yi da hoton ta, ta kara wani mugun kyau, tayi bulbul da ita tamkar diyar turawa.

*Sunday*
_5:00pm_

Kamar yanda kowa ya sani Lahadi ranar mafi ya yawan ma’aikata ne, har ma da Wasu yan kasuwa, hakan ce ta kasance ga iyalan Alhaji Dawood.

Alhaji Dawood ne ya bi Shakur da kallo wanda ke sanye Cikin shirin fita, ya lura cewa Shakur ɗin na yawan fita yanzu bayan da hakan ba dabi’ar sa bace.
“Ko dai kayi min suruka ne? Naga this day’s you re always going out”

Hajiya Sa’adah da sai yanzu da Alhaji Dawood din yayi magana sannan ta gasgata maganar sa ta Kuma ankara, ɗan haka ta zuba masa ido tana jiran jin abinda zai ce.

“Ammmm Daddy wajen abokina zani, sai na dawo” Shakur ya fada cikin dariya. Da wanna ya kare kansa ya fita.

Maleek dake kwance cikin tunani a dakin sa ya ji tashin mota alamun za’a fita, ya yaye labule yaga motar Shakur ce, haka kawai jikin shi ya bashi cewa inda zuciya da dukkanin tunanin sa suke nan Shakur ɗin zashi.

Ba tare da ya duba wacce mukullin mota ya ɗauka ba ya fice, Hajiya Sa’adah na masa magana ganin uban saurin da yake ko lura da su a falon bai yi ba.

Hankalin ta ya gagara kwanciya, Alh. Dawood yace “ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai same shi, Maleek is not longer a kid zai iya Kula da kansa, na lura kamar yana Cikin damuwa kwana biyu amma idan an tambaye shi sai yace bakomai, amma idan ya dawo zamu zaunar da shi muji menene damuwarsa”

Hajiya Sa’adah ta ɗan ji dama dama a ranta, duk da haka sai data kira shi sai dai wayar na ringing ba’a dauka da alama bai fita da ita ba .

Sosai yake sharara gudu domin ya cimma Shakur da yake hango motar sa a nesa, sai dai hanyar unguwar daya ga Shakur ya dauka shi sanya guiwar sa sanyi, da alama he didn’t guess it right. Har zai juya ya koma sai kuma yayi kasadar cigaba da bin Shakur ɗin har suka iso kofar wani gida. Ya ga Shakur ya danna horn mai gadi ya bude, Sai kuma ya ga Mai gadi ya washe bakin sa da alama akwai sannaya a tsakanin su.
Wani irin over taking yayi wa Shakur ɗin ya riga shi isa farfajiyar gidan, domin bai so a rufe gate din without him inside the house, Shakur ya taka burgi ya shiga bin motar da kallon mamaki domin wanna zak irin motar Maleek ce, amma meye motar Maleek zata yi a gidan nan, kai ba Maleek bane sai dai wani ne mai irin motar sa, ya aiyana a ransa.

Mai gadi ya taho domin ganin waye wannan ya shigo babu neman izinin masu gidan, shi kuma ba’a sanar da shi akwai bako da zai zo ba. Daidai lokacin shima Maleek ya fito da ƙafarsa dake sanye Cikin silifas waje, Shakur yayi kuri yana kallon kafar mamaki na kara kashe sa, tabbas wanna kafar jinin sa ce Maleek, daidai lokacin da mai gadi zai gifta shi yace “ammmm dan uwa nane tare muke”

“Au TOH shikenan, har da zan masa magana, toh a fito lafiya” mai gadi ya fada yana komawa bakin aikin sa.

Shakur ya fara takawa domin Zuwa wajen motar, ta mirror Maleek ya hango sa, dan haka Sai ya fito gaba dayan sa Mamaki ya kara kashe Shakur daya tabbatar shi din ne da gaske.

“What are you doing here MALEEK?”

“I came to see my angel”

“Angel? Wace haƙa?”

Yau bazai biye Shakur ba, dan Kada ma ya bata masa rai, domin ya fara jin sanyi a ransa tun kafin ma yaga yar tasa.

“My daughter!”

“Ai ba nan take ba, go look for her idan har You really love her”

“Please Shakur! Jikina ya bani Wajen ta kazo” Maleek ya fada Muryar sa na bayyana tsananin so da kuma kewa”

“MALEEK Kana son kanka da yawa, me kake so nace musu, abin bai yi ma’ana ba, ince musu me, a’a gaskiya bazan iya ba”

“Shakur nasan zaka iya min hanyar ganin ta Please, can’t you see your brother is slowly dying?”

Shakur ya masa wata harara, Maleek yayi masa murmushi domin ya san ya amince kenan tunda yayi haka.

Bayan su miemie sun yi murnar Ganin sa domin sun yi sabo da shi yanzu sosai.
Ya nemi waje ya zauna yana cewa “ina mamin ku da anty munaya?”

Hammad yace “ana yiwa baby wakan yamma, barin je in fada musu”

“Yawwa thank you” ya fada yana tunanin yanda zai musu wanna maganar, Yana jin nauyin su sosai musamman ma Munaya.

Bayan mintuna goma sannan ya ga barrister Abrar rike da little Amnah, munaya na bayan ta.

Cikin faram faram suka gaisa da juna, ya kalli little Amnah dake shirye cikin wasu overall dark pink, ta sha farar hoda
Ta jarirai da kwalli, kanta ya sha wani hair band black, she looks so cute, dole duk wanda ya ganta yayi sha’awar daukar ta.
Tsawon mintuna biyar kana ya iya tattara karfin guiwar furta “ammmm barrister, zan dan kai little waje za’a ganta”

“A’ah bako muka yi, kuma ka barshi a waje, ka shigo dashi”

Yayi murmushin yake kana yace “ammmm ba..baban tane”

“What? A’a bazai gan ta ba, kayi hakuri Shakur, i might sound rude”

“na fahimce ki barrister, amma dan Allah ki yi hakuri bazan bari ta jima ba…”

Cikin ɓacin rai barrister Abrar tace “ina ganin girman ka sosai Shakur, i respect You a lot, if not saboda Kai bai isa shigowa gidan nan ba, gaya masa ya tafi bazai samu ganin Amnah ba”

“Allow him decent one” doctor Aaban daya bayyana a falon ya fada.

Fuskar barrister kamar tayi ihu, munaya kam idanun ta a kasa, hukuncin Barr. Abrar din yayi mata daidai, amma kuma bazata iya kin yiwa Shakur alfarma ba, ba kuma ta son yarta ta rabe azzalumin can, jin doctor Aaban ya fara magana yasa ta bar wajen, wasu hawaye dake barazanar zubowa suka cika idanun ta taf.

“Go give him the baby Shakur” doctor Aaban ya kara fada, Shakur ya kalli yanda yanayin barrister ya sanja sai yaji ba dadi, ga munaya ma, ya tabbata tana can tana kuka, cikin sanyin jikin ya fice da little Amnah dauke a hannun sa.

“Pure heart abinda kake babu adalci, ai rainin hankalin sa yayi yawa wallahi…”

“Yaushe kika dawo mafadaciya ban sani ba?” ya tambaye ta a zolaye

“Pure heart kowa ma ya iya fada sai dai idan ba’a tabo shi ba”

“I understand, tun shigowar su na ga duk abinda ya faru ina zaune a balcony, like I said before zai yi nadamar dukkanin halayen da yake, yanzu maganata ta fara bayyana, ba dabarar kowa bace ya kamu da kaunar yarsa, Allah ne ya jarrabe shi…”

Cikin katse shi barrister tace “pure heart waccan mai zuciyar dutsen ne zai kaunace ta, bayan tun tana ciki he never cares”

“Decent one, na gani, i saw it in his eyes, Duk lokacin ɗaya zo a barshi yaga yarsa, ki zuba ido kiga yanda abubuwan zasu cigaba da tafiya kin ji ko?”

Da “Toh” ta amsa, duk da bata ji dadin hakan ba, amma bata iya tsallake maganar sa”

Tun kafin Shakur ya karaso inda yake ya shiga takawa domin cin musu, he’s so eager, a matukar kage yake da ganin ta, damuwar da yake ciki ta rashin fitowar Shakur yanzu ya rikida zuwa farin ciki, domin saura kiris ya biyo Shakur ɗin saboda yanda hakurin sa ya ƙare.
Bai jira Shakur ya mika masa yar ba ya karɓe ta, ya mannata a kirjin sa, ya shaki dadaddan kamshin turaren ta mara hayaniya ta yara a hancin sa, ya ji kamar ya mayar da ita jikin sa saboda so, ya kara rukumkumeta kamar za’a kwace ta.

Shakur yace “hey Mister man ka sassauta rikon daka mata, jaririyar ce fa”

 

 

_kuyi hakuri update ya zo a kurarran lokaci, nayi azumi ne, ban samu na kammala da wuri ba, I’m sorry for the inconveniences, mu haɗe gobe in sha Allah_💖

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button