Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 30

Sponsored Links

XXX…

Munayamaleek is 500 Pay to 3200689860 Haruna Rukayya first bank. Send evidence of payment to 07082281566(idan baki shirya siya ba, dan Allah don’t chat me)

Ya bude rikatattun idanun sa, yayi murmushi, sam Shakur ba zai fahimci yanayin da yake ciki ba, shi kadai yasan abinda yake ji a zuciyar sa gami da wanna kyakkyawar halitta dake hannun sa.

Related Articles

Ya cire ta daga kafada domin ya samu kallon ta da kyau, little Amnah ta shiga yamutsa fuska irin yanda kananan jarirai kanyi idan an fito da su waje, hasken wajen yayi mata yawa har bata son bude idanun ta, tayi mika tana tabe baki irin yanda yara suke idan baza su yi kuka, hakan da yarinyar tayi ya kara burge shi, yayi murmushi, kana ya Yi saurin ɗora ta a kafadar sa, little Amnah ta saki kuka, take ya burkice ya shiga jijjiga ta, cikin sigar waka yake fadin
_oh little baby why are you crying, ooh little baby your mum…._ sai yaki kara sawa, Shakur ya girgiza kai yana sakin murmushi, wato Maleek wani irin murdadden mutum ne, kallon su yaƙe tamkar wanda ya samu tv, a Yau, yanzu right in front of him ya kara tabbatar da cewa ba karamin so jinin sa Maleek ke yiwa jaririyar sa ba, sun yi matukar burge shi da bashi sha’awa, bai taba tunanin msleek zai iya abubuwan nan ba, domin Irin mutanen nan ne da basa son yara bare daukar su ko yi musu wasa ba.

Ya ƙara cire ta a kafadar sa domin bai gaji da ganin ta ba.
Wanna karon ta rufe idanun ta, ta saka hannun ta a baki tana tsotsa, yayi murmushi yana kai mata sumbata a goshi, kumatu da lips dinta da ma curling gashin ta mai cika, ya dago kansa daidai lokacin da little Amnah ta yi dariyar yara.

Maleek Yace “Shakur see see see dariya take”

Shima Shakur ya yi dariya saboda yanda Maleek din ke yi gaba-daya ya birkice kamar ba shi ba, sai hira yake mata kamar da wata babba yake, ya juya ta nan ya juya ta can, ya rike ta, ya manna ta a kirjin sa, da alama little zata yi ciwon jiki a yau.

Suna a haka akayi kiran sallar magrib.
Shakur yace “Kawo ta na mayar da ita, lokacin sallah yayi”

Har Wata bugawa zuciyar Maleek din tayi, a yanda yake ji wallahi Kamar ya gudu da yar nan, yana ji kamar bazai iya tafiya ya barta ba.

Ya dago rikatattun idanun sa daya sauya kamar wani Maraya, Shakur sai yaji wani tausayin sa abinka da jini, akace yafi ruwa kauri.

“Please ka bari na kara ganin ta” ya fada kamar ba Maleek ba.

“Sallah fa ake kira, bai kamata tana waje yanxu ba, kaga muma zamu yi sallah”

Ya kara riƙe yar da kyau, yana matsawa daga gaban Shakur ɗin, sai tafiya yake da baya baya, Shakur ya biyo shi cikin sauri yana rike shi, fuskar sa da dariya sosai yace “kai Maleek, what is this are you doing? Meye haka ina zaka Kai ta?”

“Gida” ya amsa a hankali.

“Daddy da mummy fa? Ka tanadi amsar basu?”

Ya runtse idanun sa, shi fa baya kunyar ko tsoron a sani, tashin hankalin da iyayen su zasu shiga sakamakon maganar yake gujewa”

“Ka gani, amma tabbas zasu sani, wata rana amma ba Yanzu ba, kawo ta na mayar da ita”

“Muje toh” Maleek ya fada.

“Ina zamu je? Ka san dai they won’t allow you in”

“Ba shiga zan yi ba daga bakin kofar can zan baka ita, Nima bana bukatar ganin ta”

“Kai kadai kana tsarguwa da karan kanka, ni kaji na kira sunan Munaya anan?” Shakur ya fada yana danne dariyar Sa.

Maleek ko kula shi bai yi ba, ya yi gaba kamar ya san kan gidan, Shakur ya girgiza kai yana bin bayan sa.

Bayan sun iso kofar da zai sada mutum da falon, Shakur ya mika hannu zai karbi little Amnah, Maleek ya hana shi, kana ya kalli fuskar yarinyar yace “hey angel”
Sai kuma ta bude idanun ta tarr ta zuba wa Maleek din, yayi murmushin farin ciki yana fadin “kalli Shakur, ta san ni daddyn ta ne”

Shakur yayi wata dariya, mamakin Maleek na ƙara kashe sa.

“I love You kinji, zanyi kewar ki” ya fada yana sumbatar kumatun ta, Kamar baya so haka ya mika wa Shakur yarinyar ya koma bakin motar sa yana jiran Shakur ɗin.

Bayan Shakur ya mika little Amnah, yayi godiya ya fito.

Munaya data kasa zaune bare tsaye tun dazu tayi saurin juyowa jin an taɓa kofa za’a shigo.

Ta saki Wata boyayyar ajiyar zuciya ganin barrister Abrar ce rike da little Amnah.

“Hankalin ki ya kwanta yanzu ko?” Barrister Abrar ta fada domin ta gano yanayin da take ciki.

“Munaya tayi murmushi tana rufe fuskar ta da hannun ta na hagu, fargabar data shiga na barin jikin ta.

“Karɓe ta, pure heart ya min fin karfi sai da aka kai masa mata” barrister Abrar ta fada da alamun har yanzu tana jin zafin rainin hankalin Maleek, ga kuma idanun munaya daya yi jaa alamun tayi kuka, hakan ya kara bata ranta, amma bata cewa munayan komai ba, saboda maganar sai dai ya kara saka ta kuka.

Bayan Barrister Abrar ta fita, munaya ta kwantar da Amnah a bakin gado, ta tsugunna a gaban ta, ta sumbaci bakin little Amnah, a lokacin ta ji wani kamshi, kamshin turare daya tuna mata da wani baƙin rana a rayuwar ta, ta ɗauke fuskar ta daga kan little Amnah saboda kamshin sai kara bugar ta yake.

Wasu hawayen bakin cikin ne suka zuba mata, Meyasa a duk lokacin da take ƙoƙarin manta rayuwar ta ta baya, wani abu zai zo ya cigaba da tuna mata, menene ya saka Maleek dawowa rayuwar ta? Eh dole tace rayuwar ta, domin rayuwar little Amnah ya dawo, rayuwar yarta kuma na nufin rayuwar ta.

Ta mike cikin sauri, ta bude wardrobe, gefen inda kayan little Amnah suke ta bude, ta ciro mata wasu kayan, ta cire na jikin ta ta sanja mata, ta shinshina yarta sai taji jikin ta ya daina kamshin amma fuskar ta na ɗan yi, ta rasa wani irin Mayen turare ne wanna sam bata son jin kamshin, ta kara mikewa ta dauko farar hoda ta yara ta shafa mata a fuska, sannan ta fesa wa little Amnah nata turaren, ta kara shinshina ta taji yarinyar bata kamshin turaren amma ita tana ji a hancin ta har yanzu, ta shige toilet ta wanke fuskar ta sosai da sabulu kana ta fito tana sakin numfashi, ta ɗauki yarta zuwa cinyar ta, ta kura mata ido cikin kaunar ta.

Washegari da safe sai ga Maleek a dakin Shakur, ya tsaya daga bakin kofa yace “Shakur har yanzu kana kwance?”

“yanzu fa karfe shida, Ina zaka je haka naga ka shirya?”

“Ka tashi malam, zaka rakani ganin angel”

Cikin zaro idanu Shakur yace ” ka kalli agogo kuwa Maleek? Yanzu kake so muje gidan mutane haba”

MALEEK ya dafe kansa, he’s crazy in love with this daughter”

“Toh idan takwas tayi sai mu je”

“No Maleek Babu dacewa hakan, muje gidan mutane yanxu abin sai ya zama takura, karfe takwas ɗin ma yayi wuri”

“Takura fa kace, wani abin zan tsare musu toh? Yata kawai za’a bani na ganta daga waje”

“Toh sai kaje tunda hakane, baka bini jiya ba, ai kasan hanya ”

“Saboda kasan ba zan iya zuwa ba tare da Kai ba shi yasa kake fadin haka, ka sani cewa ko ina zani You re always by my side, saboda bana jin dadin ko ina if your presence is not there, ba Kuma lallai su bani Ita ba idan basu ganka ba, You no I’m a monster bani da kirki” ya karasa da wani murmushin mai ciwo a fuskar sa.

Jikin Shakur ya yi sanyi, sai ya mike ya yi saurin riko hannun Maleek da har ya daura hannunsa kan handle din kofa.

“Karka kara kiran kanka da mugu ko mara imani, if are a very nice guy, don’t ever call your self a monster again”

Maleek ya jinjina kansa, kana yayi masa murmushi.

Shakur ya mayar masa da martani, kana yace “we will go, amma daga makaranta zan biyo ta Company sai mu tafi kaji”

“Thank you!” Maleek ya fada kana ya bar dakin, Shakur ya bishi da kallo, kana ya sauke ajiyar zuciya ya koma ya zauna.

Daga wanna rana Maleek ya mayar da zuwa gidan doctor Aaban tamkar ibada ba fashi, Shakur tuni ya daina mamaki dan’uwan nasa, barrister Abrar kuwa ganin Irin zuwan da yake tun tana kirga kwanakin zuwan sa har ya zamana ta dawo kirgen watannin, ga mahaukacin siyayya da yake mata yanzu tamkar bai san zafin kudi ba wasu abubuwan ma little bazata iya amfani dasu yanxu ba, amma shi ba ruwan sa, dukkanin abubuwan da ya gani na yara siya mata yake, har Wata rana tana tsaye a balcony suka zo da Shakur as usual taga irin soyayyar da yake nuna wa little Amnah din, daga wanna lokacin ne ta tabbatar da maganar mijin ta daya ce Allah ya jarrabi Maleek din da matsanancin soyayyar yarsa.

Ɓangaren Munaya kuwa tun tyana zuwa tana sanja wa Amnah kaya saboda turaren sa dake kama kayan ta har ta gaji ta daina saboda ta ga zuwan nasa yaki karewa,
Kuma duk zuwan nan da yake munayamaleek basu taba haduwa da juna ba.

Hajiya Sa’adah ce ta saka Maleek a gaba, domin yawan fitan da suke kullum da yamma ya dame ta, hankalin ta ya gagara kwanciya, ta kuma yi iya yinta wurin gano inda suke zuwa ta gagara ganowa har yanzu, tsoro ne fal a ranta, tana tsoron kada Maleek ɗin ya zo ya kamu da son wata Mace.

“Believe Me mum Babu komai ko Shakur?” Maleek ya fada.

Shakur ya kara jaddada mata Lallai babu komai.
Hajiya Sa’adah ta kauda kanta daga kan Shakur a ranta tana jan tsaki, bai san ba shi bane matsalar ta ba.

“TOH ina kuke zuwa, uhmm, Ni bana son ku Fara saka mace a gaba tun yanzu, ku Bari sai gaba, Ni mahaifiyar ku ce, baku da wata bayan Ni, ku gayamin gaskiya”

Shakur ya kalli Maleek, abinda mummy take son su fada bazai yiwu ba, domin sirri su ne da basu shirya bayyana shi ba, gudun tabarbarewar zaman lafiyar gidan su.

“Kawai muna fita yawo ne” Maleek ya fada.

“Amma da bakwa haka, Meyasa sai yanzu, ni gaskiya bana son wanna yawon”

Duk yanda Hajiya Sa’adah ta so su Maleek su daina fitan yammacin nan abu yaci tura, musamman da suka samu goyon bayan Alhaji Dawood, gefe daya kuma Hajiya Sa’adah na nan tana cigaba da fafutikar neman hanyar cimma Burin ta akan Maleek.(aka daddyn Amnah😂)

Bangaren doctor Abbas kuwa, ya dan dakata da gayawa Munaya abinda yace yana zuciyar sa sakamakon shawarar da doctor Aaban ya bashi tunda ya lura da take taken sa kan munaya din, ya bashi shawarar cewa ya bar munaya sai zuwa gaba sai ya sanar da ita koma menene yake zuciyar sa zuwa lokacin ta kara girma, ta kuma ƙara samun nutsuwar zuciya.

A yanzu little Amnah tayi wata goma a duniya, yayinda kamaninta da Maleek ke kara fitowa a kowacce rana.

_Monday_
*11:03am*

Litinin akace tushen aiki, hakan ce ta kasance da dukkanin iyalan doctor Aaban, barrister ta tafi kotu, doctor na asibiti, yaran sun tafi makaranta, gidan ya rage daga munaya sai little Amnah.

Wani irin bacci mai nauyi ne ya ɗauki munaya a falon.
Little Amnah Dake rarrafen ta ko’ina tana Kuma iya rike mutum ko Abu ta mike ta nufi Kofar ganin ba’a datse duka ba har tana dan hango farfajiyar gidan, tana murnan ganin waje ta yi rarrafe zuwa bakin Kofar, ta saka kananun hannun ta ta kara buɗe kofar, da kyau, cikin saurin rarrafe ta fita farfajiyar gidan, tana dariya, ta cigaba da rarrafawa har ta nufi gate, ta ga gate din ma a bude kawai ƙara ta akayi ta zauna kan gwiwowin kafar ta kana ta bude kofar, abinka da yarinta ta shiga murna sosai ganin ababen hawa na wucewa, ta kara rarrafawa ta fita Wajen gate din.
Ta samu gefe ta zauna, ta shiga wasa da kasa tana ci.

Maleek da bai taba makara irin na yau ba ke biyo wa ta layin doctor Aaban, kasancewar titin da yaƙe bi anyi cunkoso yau sosai, sai yayi shawarar yanka ta layin domin ya samu sauƙin isa office.

Tunda ya shigo layin yake ji ina ma ya ga yarsa? Amma bazai iya shiga gidan ba tare da da Shakur ba, Shakur kuma fitar wuri yayi a yau sakamakon morning lecturing da zai gabatar, ya sauke numfashi yana ji ina ma zai iya shiga gidan ya ganta, he just want his daughter by his side.

Munaya ta bude idanun ta suka yi haske da kara girma sakamakon bacci data farka yanxu, ta dudduba falon bata ga Amnah ba, ta mike cikin sauri ta shiga neman ta
a dakunan dake kasa, itace har kitchen amma babu little Amnah, tana kiran sunan ta amma bata ji Amnah ta mata gwaran ci ba.
Munaya ta dawo falon ta durkusa tana leka karkashin kujeru, a lokacin ta ga Kofar falo a wangale, ta tuna dazu data taya barrister Abrar kai jaka mota bata rufe ba, a gigice ta nufi farfajiyar gidan.

Wani irin wawan burki ya taka a lokacin ɗaya zo wucewa ta daidai Kofar gidan, ya ga kamar little Amnah ce zaune tayi bututu da kasa, kodai gizo idanunsa ke masa? No it can’t be his daughter, amma kuma suna kama, ya sauko cikin sauri yana cire seat belt, ya karasa inda yarinyar ke zaune yace “my angel” ta kuwa dago, ta shiga masa dariya tana daga nasa hannu alamun ya dauke ta, yayi saurin daukar ta ya manna ta a kirjin sa, kasar jikin ta ya Bata farar rigar sa da bakin wandon jikin sa, zuciyar sa na bugawa da wani matsanancin ɓacin rai, ya shiga dudduba jikin ta ya tabbatar da cewa babu abinda ya same ta, ya shiga ciccire kasa da wasu kananan duwatsu dake baƙin ta.

Munaya dake ta kiran mai gadi bai amsa ba sai a lokacin ta lura kofar shima gate din ba’a rufe yake ba, meke faruwa yau ne, da gudu ta karasa buɗe gate din ta fita.

Tsayawa tayi cak a lokacin data yi tozali da Maleek rike da little Amnah, zuciyar ta ya shiga tsalle tamkar zata faso kirjinta ta fito.

Shima Maleek ya zuba Mata rikatattun idanun sa masu cike da ɓacin rai, yayinda yake shafa gashin little Amnah data yi luf a jikin sa, bayan shekara ɗaya da Wasu watannin yau munayamaleek suka ƙara haduwa, ya ƙara tuno halin daya ga little Amnah a ciki dazun sai ya nufe ta ba tare da ya ɗauke idanun sa a kanta ba ya daga hannunsa ya wanka mata mari.

Munaya ta kifa tamkar zata fadi sai kuma ta dago hannun ta dafe da kumatun ta, bakin ta a dan bude tana kallon sa da mamaki, wasu zafaffan hawaye ne suka zubo Mata domin ba kadan ba marin ya shige ta.

Ya nuna ta da yatsa yace “na san kin tsane ni, ba sai kin kara nuna min ta hanyar kin yata ba, idan baki san darajar ta ba, nina sani ina kuma son ta, dan me zaki min sakaci da ita har ta fito titi, da ban zo ba fa, ga ababen hawa na wucewa idan aka buge ta fa, ko kuma an sace min ita? Wanna ya zama gangan ci na karshe da za kiyi a kan yarinya ta idan kuma wani abu ya same ta saboda kasar data ci You will see the other side of me”

Mai gadi daya karaso yanzu ya ce “lafiya meke ga faruwa ne, na dan fita siyo katin waya ne”

Maleek yayi wa mai gadin wani mugun kallo kana ya nufi wajen motar sa, ya shiga da little Amnah, ya tada motar da mugun gudu ya bar wajen har yana buɗe musu ƙura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button