Munayamaleek 37
XXXVII…..
(37)
Haraban asibitin Maleek ya fita da ita, ya dora ta saman motar sa, ta sakala hannun ta a wuyan sa sai zuba take masa, tace mummy ta yi kaza, mummy tace kaza, mummy ta siya mata kaza, idanun sa a lumshe Yana sauraran ta.
Little Amnah ta ga ita kadai ke ta zuba babu bai amsa wa, sai ta kalli fuskar sa, ta ja gashin idanun sa, yayi saurin buɗe idanun na sa, ta kyalkyale da dariya, ya rungume ta yana sakin murmushi, yana matukar son yarsa har matakin da idan ya ganta yana jin damuwar sa na raguwa, ya ciro ta daga jikin sa, ya shiga gyara mata gashin ta daya fito ta Cikin hular da ke kanta, tayi saurin riko hannunsa tace “lah Daddy, mummy ta hanani lalata gashina, ka bar gargaje min” tace cikin salon magana irin ta yara.
Ya sumbaci kamatun ta yace “school zaki fara zuwa, tunda kin zama parrot”
Ta zaro idanun ta tace “payyot fa? A’a Daddy Ni ba payyot bace, payyot fa bakin sa dogoooo ne” bai san sanda yayi dariya ba, abinda ya kan dade Kafin yayi.
Haka ta cigaba da masa hira cikin Kuruciya, ya lalace wurin biye mata.
Sosai Shakur yaji Daɗin zuwan su Munaya, haka ma Alhaji Dawood, a iya yau daya zauna tare da su sai yaji kamar sun zama ahali daya domin sun daɓe musu kewa sosai, har Shakur yaci abincin da Munaya ta Kawo masa da dan yawa, hakan kuma ya ƙara faranta ran Alhaji Dawood.
A lokacin da suka mike domin tafiya, Munaya tayi wa Shakur alkawarin cewa zata dawo, har rakosu Alhaji Dawood yayi bakin kofa, yayi musu godiya kana ya koma wajen Shakur.
Tun daga nesa munaya ke kallon bakin little Amnah dake ta zuba yayinda Maleek ya bata baya.
Haushi ya cika Munaya, ta rasa wanna wani irin naci da so ne, kamar yadda ya nace wa little haka ita ma bata da magana daya wuce shi kullum, hakan na matukar kona mata rai.
Barrister Abrar kuwa haushin Maleek da mamakin sa take, ta kasa hakuri bayan sun gifta Maleek din tace “Ni kam pure heart wanna Yaron kalau yake kuwa? Ace ko gaida mutane bazai iya yi ba?”
Doctor Aaban yace “ke ga son girma kamar gyambo”
Tayi dariya, kana ta gimtse dariyar tace “amma to be Frank abinda yake sam babu tsari bare dacewa, ai ba laifin sa bane, daka barni an dauki mataki a kansa dana sauke masa abinda yake ji, tunda kansa hayaki yake”
“Zai yi nadama wata rana decent one, forget about him” ya fada.
“Kullum haka kake cewa zai yi nadama har yanzu Ban ga nadamar da yayi ba”
“Gaggawar me kike? Ki jira ki gani, Munaya” yace yana murmushi Cikin tsokana.
“Au nice ma Munayar?” Tace tana fashewa da dariya
“Ai na ga kamar kin fita jin haushin sa ma”
“Ba haka bane, Munaya too is hurt deep down, ka san na sha kamata tana kuka amma sai tace min ba komai, kasan irin wanna abubuwan yana da wuyar mantawa, ina taya ta jin tsanar sa wallahi”
“Ashe matata ba iya lawyer da kare hakkin dan Adam bane aikin ta, har da taya fada kina yi” ya ce yana kokarin bude murfin mota.
Itama a xoyale tace “ai duka aiki nane”.
“Amnah muje!” Munaya dake tsaye dan nesa da su ta fada.
Amma yarinyar nan ta gwale ta tace “Ni mummy zan zauna a wajen Daddy na”
Habawa notikan kan Munaya taji yana kwance Wa, a dan tsawace ta ce “will you get down now from there my friend”
Yarinyar ta tabe baki wanda hakan ke nuni da cewa zata iya fasa kuka a ko wani lokaci, ta riko fuskar Maleek tace ” Daddyyy kace wa mummy Ni a wancan ka zan kwana”
“Little kada ki bari na zo wajen nan” Munaya ta gargade ta.
Little Amnah kuwa ko motsawa bata yi ba.
Kamar daga sama ba tare da kuma Maleek din ya juyo ba, murya a daure yace “ki bita a hankali madam!”
Kamar ta rusa kuka, idan akwai kalmar da ta tsana a kira ta toh Madam ne, ta kalli wajen motar su barrister da suke jiran su, hankalin ta ya tashi, ai ba dadi suyi ta jiran su, bayan tuntuni doctor Abbas ya tafi.
A hankali Maleek ya sauke little Amnah kasa, ya durkusa ya riko kafadun ta, fuskar sa ta sanja sosai domin da yana da hali da yarinyar sa babu inda zata je, tare zasu kwana.
Cikin son mata wayo yace “ki je kin ji, zan zo anjima ai, me kike so na siyo miki idan zan taho”
“Uhuhmmm” tace tana makale kafada alamun taki Wayon.
Zai yi magana kenan kawai ya ji an fisgo little Amnah, ya dago kansa ya ga munaya ce, idon sa ya kara ja, Munaya ko kallon sa bata yi ba, little Amnah ta fasa Kuka tana ƙoƙarin xillewa, Munaya ta shiga janta zuwa wajen mota, tana ji yana mata fada kan ta daina ja masa y’a a kasa, yanda ranta ke a ɓaci so take ta kara kuntata masa dan haka ta dinga can little Amnah ɗin da gayya, fuskar Maleek ya sanja kamar ya kaiwa Munaya Bugu haka yake ji, taku hudu kacal yayi ya cim musu, cak taci an ɗauke little Amnah ta waiga cikin sauri ta ga Maleek ne, ya dauke ta yayi gaba, kai tsaye bayan motar su barrister ya nufa, ya bude motar ya ga su miemie a zaune, ya daura little Amnah a kujerar, ya share mata hawaye da hannun sa, ya karasa abinda zai bata domin tayi shiru, kawai ya debo kudi a aljihun sa da bai san ko nawa bane ya sanya mata a hannu, bayan ya kuma rarrashin ta, sai sauke shesheka take, ba dan ya so ba ya cire kansa daga cikin motar, ya zo gifta Munaya ba tare da ya kalle ta ba yace “the next time Zaki kara wanna gangancin da kika yi wa Angel yau, wallahi tallahi You won’t find it funny with me, akan me zaki dinga ja min ita a kasa, dabba ce?”
“Babu abinda ka isa ka yi, me zaka min? Yata ce, ina ruwan ka da rayuwar mu?” Tace masa cikin rashin kunya.
Mamaki ya kama sa yace “haka kika ce?”
“Eh haka nace, idan kana da zuciya stay away from us!”
A zafaffe yace “ke baki isa in shiga rayuwar ki ba, rayuwar yata na shiga ki gyara kalaman ki”
“Rayuwar yata Tamkar rayuwa ta ne, idan…”
Pim pimm taji horn din mota, hakan ya saka tayi shiru, amma ranta a bace yake da bata samu ta mayar masa ba.
Bayan ta shiga motar sai ta kife kanta a jikin kujerar da barrister Abrar ke zaune, Wasu zafaffan hawaye suka zubo mata.
Cikin sigar bata shawara doctor Aaban Yace “Munaya kin san condition ɗin lafiyar ki ko? Bai kamata kina saka damuwa a ranki ba, ki rabu da shi, yarsa ce, duk yanda yake so yayi ta, yayi, he loves her, bazai cutar da ita ba, kin gane ko?”
“Eh Abbi” ta amsa a sanyaye tana dago kanta.
Barrister Abrar tace “a’a pure heart kana bari ta rama wani zubin, abin na sa yayi yawa, kar shirun da ake masa ya zama rainin hankalin”.
Ya dafa kansa yace “shikenan Hanan ta lalata min Mata da ziga mutane” ya fada yana dafe kansa.
Sosai barrister Abrar tayi dariya tana cewa “ba ruwan ta wallahi”
Munaya sai data yi murmushi duk da damuwar da take ciki, domin su barrister na matukar burge ta yanda suke tafiyar da rayuwar su, ta sauke ajiyar zuciya, daidai nan little Amnah ta kwantar da kanta a cinyar Munayan tana kallon fuskar ta a tsorace, munaya ta daura hannun ta a kanta ta rufe idanun ta, “mummy kin ga kudin da Daddy na ya bani” little ta fada murna ganin ta samu fuska, munaya tayi kamar bata jin ta, itama yarinyar sai ta yi shiru bata kara cewa komai.
Maleek kuwa direct dakin da Shakur yake ya nufa. Yana shiga Alhaji Dawood yace “Maleek where have you been?”
“Ina waje Dad” ya amsa yana Zama kusa da Shakur.
“Gashi baku yi sallama da wadannan mutane da suka zo gaida dan’uwan ka ba” Alhaji Dawood ya fada, da alama bai lura cewa ko gaida su Maleek din bai ba.
Shakur ya kalle shi, kasa kasa yace “raka ta kayi?”
“Wa zan raka? Allah ya kiyaye Ni”
Siririyar dariya Shakur ɗin yayi ganin yanda Maleek din ke ɗaukan zafi duk sa ilin da yayi masa maganar Munaya, wanna karfin halin na sa na bashi mamaki, domin ita wacce aka cuta din ma baya tunanin tana ɗaukar zafi irin sa.
Shakur Ya kara cewa “ina ganin wasu abubuwa a cikin idanun ka”
Bai bawa Maleek damar bada amsa ba ya kara da cewa “yanzu gayamin da mai kankat ya shiga tsakani ku ka kamu da infection?”
Maleek ya yi shiru yana son gane ma’anar maganar dan’uwan sa, Sai can ya dafe kansa, yayi wa Shakur wani kallo yace “naughty boy, yaushe ka dawo haka?”
Shakur yayi dariya, Alhaji Dawood yace “me ne kuke tattaunawa haka baku gayyace Ni ba?” Yace cikin jin dadin yanda Shakur ɗin ke walwala, hakan ke kara kwantar masa da hankali,
Suka kalli juna, sai suka yi masa murmushi.
Bangaren Hajiya Sa’adah kuwa, tuni ta kira masu aiki suka dawo, gidan ya dawo hayyacin sa, sai dai shirun da gidan yayi ya dame ta, domin kusan sati biyu kenan bata sanya kowa a ido ba bare ta ji motsin su.
Ta mike daga zaunen da take ta fito falon, kasancewar yanzu tafi zama a daki, banda karar Ac babu wani motsi a falon, ko dai gidan suka bar mata? Cikin sauri ta kauda tunanin a ranta ta fice zuwa haraban gidan, mai gadi ta tarar a zaune, shi ko mai gadi ya cika da mamakin ganin ta, domin a tunanin sa bata gidan.
Ya kauda mamakin sa ta hanyar tasowa da gudu yace “Hajiya Barka da warhaka, ya mai jiki? Ai naje duba shi a asibiti, Allah ya dai ya tashi kafadun sa” mai gadi ya karasa Maganar cikin aihini.
Gaban Hajiya Sa’adah ya buga, tabbas ko ba’a fada Shakur ne bai da lafiya, daga kuma yanayin da mai gadi ke magana da alama yana cikin critical condition, so take tace ina ne asibitin amma sai ta ga idan ta fadi haka abin zai yi wani bambarakwai, taya bare infact mai gadi a gidan ya san asibitin da dan ta ke kwance, amma a ce ita bata sani ba, it doesn’t make any sense.
Sai wata dabara ta fado mata, ta maze tace “Ameen, ina driver ne? Yazo ya kaini asibitin”
Mai gadi yace “toh bara a kira shi Hajiya”
Ta jinjina masa kai kawai, ta shiga nazari, duk da wata zuciyar na fargaban irin tarban da zasu mata, amma zata je domin rashin zuwan ta zai iya sanya jama’a su fuskanci akwai matsala a tsakanin su, musamman ma dangin Alhaji Dawood din, ta koma ciki ta dauko mayafin ta kana ta fito ta tarar da driver na jiran ta, ta shiga ya ja suka fice daga gidan.
Mintuna talatin kaɗai ya kai su asibitin, ta buɗe murfin motar ta fita, har tana son tambayar driver wani daki aka kwantar da shi amma sai tafasa saboda wani tunani data yi, kai tsaye wurin nurses dake reception ta nufi, ta tambaye su suka duba mata Ward ɗin da yaƙe hadi da mata kwantance, bata wani sha wahalar gane dakin ba, fargaba ne fal ranta, amma haka ta daure ta tura kofar dakin…
Maleek ya juyo dan ganin mai shigowa, kasancewar ya bawa kofar baya, Hajiya Sa’adah ta zaro idanun ta tana dafe kirjinta, domin har ga Allah bata san abin yayi muni haka ba, ta fara kuka wiwi, takaici ya kama Maleek, duk wani girma da kimar ta da yake gani a da ya zube a idanun sa, ya mike tsaye, yana nuna kofa, kasa kasa yanda Shakur da bacci ya dauke shi bazai ji ba yace “get out!” fuskar sa a matukar daure.
Hajiya Sa’adah ta share hawaye tace “na zo ganin dana, i came to see Shakur, Dan me zaku ki fada min Abu irin wanna?” Ta fada tana rufe bakin ta da hannuwan ta, tun da ta haifi Shakur bata taɓa tausaya masa irin na Yau ba, toh ina ma ta damu da shi bare taji tausayin sa?.
Maleek kuwa burin sa ta fice, baya bukatar ganin ta a dakin, baya ga haka baya son Shakur ya farka domin tun safe yake fama da matsanancin ciwon kirji daya matsa masa fiye da baya, wanda likita yayi masa allura har bacci mai nauyi ya dauke shi.
A hankali amon sautin Muryar Shakur ya fita, “mummy!” ya fada yana murmushi da alama yaji dadin ganin ta.
Mamaki ya kama Hajiya Sa’adah sosai domin bata tsammaci samun koda kallon arziki Daga gareshi ba, ta taho wajen shi, ta riko hannun sa tace “Shakur ya jiki? Ka yi hakuri ban sani ba wallahi, ba’a gayamin kana asibiti ba”
Yayi kara Mata murmushi kawai, Maleek mamakin Shakur ɗin ya kashe sa a tsaye, hakan ya saka ya kasa magana, wani irin zuciya ne da Shakur?
Ƙarar bude kofa ya sanya shi dawowa tunanin sa, likita ne ya shigo yace “ka tashi ashe, how are you feeling now?”
“Great!” Shakur Ya amsa, ba dan kuma ban baya jin ciwo ba, illa baya son kowa ya shiga damuwa ta Dalilin sa.
Likita ya gama duba shi ya fita, Hajiya Sa’adah data koma gefe ta tsaya tun lokacin likita ke duba Shakur tace “kana jin sauƙi ko Shakur?”
Maleek ya rufe masa baki yace “karka amsa, just go back to sleep”
Ya fada yana haɗe rai.
Shakur yayi dariya a hankali, haushi ya ƙara maka Maleek, sam bai son wanna sakin fuskar da yake mata.
Gaban Hajiya Sa’adah ya fadi data kalli Maleek da kyau yanzu, tsanar ta take hangowa a cikin idanun sa, her biggest fear kenan, tsoron data dinga ji kenan wanda wanna tsoron ya sanya ta debi shekaru masu yawa bata cika burin ta a kansa ba, tabbas shi kadai take gani a idanun sa.
“Ki tashi ki tafi!” yace kamar zai rufe ta da duka, yanda yake jin zuciyar sa kuwa wallahi zai iya mata komai Domin ya fanshe haushin abin data masa, amma idan ya tuno Shakur, his only brother sai ya fasa, domin ya san Shakur ɗin bazai ji dadi ba.
“Maleek dan Allah ka barta kaji”
“No she most live this room” Maleek ya fada a kausashe.
Hajiya Sa’adah kuwa kanta a kasa, banda kuka babu abinda take yi, abu goma da ashirin ne ya haɗar mata.
Shakur kuwa ya ji ba dadi da irin kukan da take, yau mummyn sa ke kuka a kansa? Ita ke tambayarsa jikin sa cikin Kulawa? Kulawar da bai samu ba tun zamanin Kuruciya amma yau ya samu, saidai bai zo masa a yanda yake so ba.
Suna a haka aka kara turo kofar Dakin, wanna karon Alhaji Dawood ne rike da ledoji mai dauke da tambarin gidan abinci, ledar ta kusan subuce wa daga hannunsa, damuwar da ɓacin rai da yake ta kokarin yakicewa ya dawo masa sabo, tsawar daya buga ya sanya Hajiya Sa’adah mikewa a gaggauce kana a firgice, “zuwa kika yi ki karasa min shi? Toh maza ki fice kafin ranki yayi mummunar ɓaci!”
“Alhaji ka min rai, kayi hakuri ka barni dan Allah, ina son zama tare da ku” ta fada tana fashewa da kuka.
Shakur ya runtse idanun sa, sam Baya son tashin hankali, yace “Daddy please ka barta”
“Shakur! bazata zauna ba, zuciyata ba zai dauka ba” ya fada yana dukan kirjin sa da karfi.
“Get out now kafin na kira security su fitar da ke ta tsiya!”
Jikin ta na rawa tana waiwayowa tana kallon Shakur dake kallon ta shima ta fice tana kuka.
“Nonsense!” Alhaji Dawood yace cikin ɓacin rai yana sauke numfashi masifar da yayi.
Ya dawo da kallon sa ga Maleek yace “ga abinci, ka bawa dan’uwan ka, barin duba likita, domin na fara tunanin mu fitar da dan’uwan ka waje saboda yawan ciwon kirjin nan da yake yi”
“Okay Dad” Maleek ya amsa yana mikewa domin daukan ledar.
Yana cikin bawa Shakur abincin sai kuma ya ga yaki cigaba da buɗe baƙin sa, cikin damuwa Maleek yace “menene, ko baka son wanna, na siyo maka wani abun?”
“Please ku yafe wa mummy, tayi nadama fa”
A raunane Maleek yace “Idan ka ga na hakura toh wallahi ka warke ne, na ga an raba ka da na’urorin nan, ka dawo Shakur dina na baya”
Hawaye ya ciko idanun Shakur yace “MALEEK let bygone be bygone, fushi, ko damuwa Babu abinda zai kara mana, ka zata dariyar da nake bana jin ciwon abin ne? Saboda yanda na ganku a ranar nan zuciya ta taki dauka har ya kawo Ni inda nake kwance a yanxu”
Jikin Maleek yayi sanyi, ya ajiye cokalin hannun sa a hankali, zuciyar sa ta kara jagulewa daga hadewar data fara yi.
“Alhaji ka kara mana lokaci, in sha Allah You won’t get disappointed, irin haka ke sake mana guiwa, muna da kwararrun likitoci a nan Nigeria da suke bada perfect treatment wa patient kamar yadda yan wajen ke yi, zuwa jibi dama muke saka ran cire masa na’urorin jikin sa tunda jikin na sa yayi kyau”
“Gaskiya doctor nan da kwana ukun idan Babu Canjin babu abinda zaku ƙara fada yayi convincing dina”
“Toh mun gode Alhaji”
likitan ya fada suka yi musabaha kana Alhajin ya fita.
07082281566