Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 39

Sponsored Links

XXXIX…
(39)

*MunayaMaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, send evidence of payment to 07082281566 (idan baki shirya siya ba, ɗan Allah don’t chat Me)*

“Abdulshakurr!?” Alhaji Dawood ya kira shi da wani irin karyayyen murya daya shake kamar mai yin mura, domin a sa’ilin ɗaya kalli Shakur ɗin ya tabbatar da cewa rai yayi halinsa, Shakur ɗin su mai kyawawan halaye da nagarta ya bar musu wanna duniyar mai cike da rudu da son zuciya, duk da ya san gaskiya amma ya shiga taya Maleek jijjiga shi da kiran sunan shi, shiru Shakur ba zai iya amsa wa ba, daidai nan doctor’n dake night duty tare da Wasu nurses suka shigo dakin saboda Muryar Maleek gaba-daya ya karade wajen da kiran sunan Shakur.

Related Articles

Doctor ya shigo yace “what’s happening sir” yayi tambayar ga Alhaji Dawood, da kyar Alhaji Dawood din ya iya hada kalaman “he’s not breathing”

Likita ya matso kusa da gadon sosai domin duba Shakur ɗin, ya bukaci Maleek ya matsa amma yaƙi, a haka ya duba Shi sannan ya cire abin da ya makala a kunnen sa, kan sa a kasa yace “I’m sorry Alhaji, but we lost him”

Wani irin dummmm kunnen Maleek ya ɗauka, doctor’n na kokarin rufe shi, Maleek ya cakumi hannun likitan yace “why are you covering him? Meyasa kake rufe shi? Ina oxygen na saka masa, nace ina oxygen!?” Yace cikin wani irin Karaji daya firgita dukkanin su in ka cire Alhaji Dawood dake jinjina kai kawai kamar Yanzu likitan ke gaya masa, ya kasa tabuka komai, abin ya zo masa a bazata, duk da Shakur na jinya a asibiti amma ko kusa bai taba kawo masa mutuwa ba, Taya ma zai kawo wa gudan jinin sa mutuwa?

Likita kuwa ya kasa kwatar hannun sa, idanun Maleek sun yi wani irin jaaa yana kallon fuskar Shakur ɗin sa, yayinda likita ya cigaba da kokawa da son kwatar hannun sa amma ya kasa, dama nurses din tsananin tsoro ya sanya tuni suna bakin kofa saidai basu fita ba, domin basu taba ganin mutum da aka masa rasuwa ya birkice kamar mai ciwon hauka ba sai wanna.

Alhaji Dawood ya dago idanun sa, ya kalli Maleek, tausayin Maleek din mai yawa ya tsirgan masa a zuciya, domin dukkanin wani mutum da yasan irin kusancin dake tsakanin su tabbas, zai iya yiwa Maleek din kuka.

Ya shiga gimtse labbansa cikin na juna yayinda suke matukar rawa, ya bude bakin sa da kyar yace “Maleek, free him”

Kamar wanda ya zare yace
“Dad wanna likitan bai san aikin saɓa, sai na kai shi kotu, how will he even dare say my kid bro is no more, yanxu fa muka gama hira, ai ka ga lokacin ko da…”

“Maleek! That’s the bitter truth, gaskiya ce Amma mai matukar daci fada a baki, kana mai dafin saurare a kunnuwan mu, Shakur is gone, gone for ever, sake shi”

A hankali hannun Maleek ya shiga sakin rigar likitan daya fara hada gumi ba tare da ya san hannun sa na barin rigar ba, bakin sa a tsake yana kallon mahaifin sa tamkar shi din Wani sabon halitta ya sauya.

Cikin daurewa Alhaji Dawood ya rike hannun Maleek, gaba-daya ya taho jikin sa, hakan ya saka Alhaji Dawood rike shi gam, dole ya zama bango majinginar Maleek, dole ya karfafa zuciyar sa domin taimakawa Maleek ɗin, Maleek bashi da kowa yanzu sai shi, Maleek kuwa kamar mutum mutumi ya dawo, ƙwaƙwalwar sa ta daina aiki, komai ya tsaya masa cak, kamar yadda kwayar idanun sa suka tsaya cak Baya ko kifta su, sai zuciyar sa dake wata mahaukaciyar bugawa tamkar zata faso kirjinsa ta fito.

Da misalin ƙarfe takwas aka gama dukkanin wani abu ɗaya kamata kafin asibitin suka bada gawar.
Sai dai Maleek yaki bari a dauki gawar zuwa mota, yace da kansa zai dauka ba mai taba masa Shakur ɗin sa, tilas suka barshi amma gani suke bazai iya ɗauka shi kadai ba saboda nauyin da gawa ke yi, amma abin mamaki cak ya Daga Shakur ɗin, suka bishi da kallo ganin yadda yake lafiya kamar bai dauki komai ba, gaba-daya ya dawo kamar wanda ya zare, ya gama fita a hayyacin sa, gani yake kamar mafarki yake, irin mafarkin da yayi cikin daren yau, yana kuma fatan Allah ya farkar da shi.
Da motar asibitin za’a kai gawar gida, bayan sun ce masa ya saka gawar, Ba musu ya saka, ya tsaya yana sauke numfashi, za’a sauke murfin motar ya rike, kana ya dira bayan motar, ya daura kan Shakur a cinyarsa, ya bude fuskar sa, Alhaji Dawood ya dauke hawayen idanun sa sannan ya matso yace “sauko Maleek, sauko ka shiga mota, duk gida zamu tafi”
Ya girgiza kansa ba tare da ya ɗauke idanun sa daga kallon fuskar Shakur da ya kara kyau da haske ba.

Alhaji Dawood ya juyo ga likita yace ” bazai yarda ba, ku barshi kawai”
ya kara matso kusa sosai, ya mayar da farin zanin yace ” karka buɗe shi kuma kaji ko?” Abin tausayi sai yace “saboda iskar mota ko Dad?”

Alhaji Dawood ya kasa rike hawayen idanun sa, yayi kasa da kansa yace “eh” ya bar wajen, Yana addu’a Allah ya bawa Maleek hakuri da dangana domin idan ya cigaba a haka zai iya rasa tunanin sa.

Kafin kace me labarin mutuwar Shakur ya karade garin Abuja da wajen ta kasancewar Alhaji Dawood shahararren dan kasuwa, haka zalika ya’yan sa ma tsanannu ne, har an sanar cewa karfe goma za’a yi jana’izar Shakur.

Tun da suka shigo layin Alhaji Dawood ya ga mutane dankam a kofar gidan sa, mai gadi da ya sha kuka ya koshi ya bude musu gate cikin mutuwar jiki domin Shakur mutumin sa ne, bayan an tsayar da motar a farfajiyar gidan, dreban motan asibiti ya fito, ya zo ya bude Bayan mota, Maleek ya sauko, ya saka hannu zai sake ɗaukar Shakur, sai dai ya kasa a wanna karon, ya gwada iya yin sa amma ya kasa, sai a lokacin wani hawaye ya zo masa, ya saki kuka ya daura kansa a cikin Shakur ɗin, Alhaji Dawood ya zo wajen ya dago Maleek ya rike shi, kana aka samu aka ɗauki Shakur domin yi masa wanka, ya riko Maleek da kyau a jikin sa. Maleek ya rungumgumeshi yana kuka, zuciyar Alhaji Dawood ya karye, dauriyar da yake kokarin yi ya kasa, shima ya saka kuka, mutane suka zo suna bashi baki da masa nasihar illar kuka ga mamaci, baya ga dole shi zai karfafa zuciyar sa domin iyalan sa kasancewar shi shugaba a gidan.

Babban yaron yaya Laraba ne ya zo ya rike Maleek ya nufi cikin gida da shi.
Cikin falon ma mata ne cike a cikin sa, daga na yan’uwan Alhaji Dawood, abokan arziki dama makota. Hajiya Sa’adah dake zaune sanye da zumbulellen hijab ash color da carbi ta kara sautin kukan ta a lokacin data ga Maleek, tayi laushi sosai idanun ta sun kumbura sosai, aka shiga rarrashin ta kan tayi shiru.

_ko da bana nan tare da kai, ina so na kasance tare da kai, Ina son a kowacce safiya bayan ka iddar da sallar asuba ka min addu’a, ko da baka min kullum, kana yi min ko sau biyu ne a sati kaji_

Kalaman Shakur suka amsa kuwwa a kunnen Maleek tamkar yanzu yake gaya masa, sai yanzu ya fahimci komai, sai yanzu ya fahimci abinda Shakur ke nufi, ya mike zai fita, ɗan yaya Laraba ya rike shi, amma ya zame ya fice ta ƙarfin tsiya.

An fito da gawar Shakur kenan shirye cikin tufafin sa na ƙarshe, Maleek yaji kafar sa tayi nauyi kamar an daura masa bulo inci sha takwas, Alhaji Dawood daya taho kiran sa yayi alwala domin sallar jana’iza ya ganshi tsaye, zai masa magana yace “Dad Dan Allah kar a Kai Shakur makabarta” yace Muryar sa na rawa.

“Meyasa?” Alhaji Dawood ya tambaye shi yana riko hannun sa cikin mamakin kalaman sa.

“Haka yake so, ina son cika masa burin sa”

Alhaji Dawood ya jinjina kai domin ya san muhimmancin wasiyyar mamaci, umarni ya bayar da a haƙa rami a garden dake bayan gidan.

Aka kira Hajiya Sa’adah domin yin masa sallamar karshe da addu’a, tana kuka hijabin nan na jan kasa ta durkusa gaban gawar, sau biyu tana buɗe baki domin yin magana sai kuka ya zo mata, ana uku tace “Shakur rabbi ya yi maka rahama, ya karbi bakoncinka, baka taɓa min komai, illa ma nice na maka laifi, ka yafe min Shakur, ka yafe wa mahaifiyar ka, halinka na gari ya bika”.

Maleek yana tsahun gaba a masu yi wa Shakur Sallah, sai dai bai san abinda yake yi, bai kuma san abinda yayi ba cikin sallar domin hankalin sa gaba-daya yana ga makaran da Shakur ke kwance a ciki, har aka gama sallar jana’iza mutane suka watsa daga tsahu Maleek na nan hannun sa rungume a kirjin sa har sai da Alhaji Dawood ya janyo shi kana ya farga da cewa ashe har an ɗauke gawar, amma shi yana hango ta kwance cikin idanun sa, ya runtse idanun sa Yana ji Kamar ya bar duniyar shima saboda yanda komai da Kowa ya fice masa a rai…

Ba dan rai na so ba aka zura Shakur a kabarin sa, bayan ya an yi masa addu’a sosai tare da fata na alkhairi, kamar yadda Shakur ya samu jama’a sosai, haka ya samu shaidu masu kyau, kowa ya watse, ya rage sauran Maleek tsugunne gaban kabarin.
Tsawon lokaci yana a haka kana yace “ya rayuwar mu zai kasance babu kai Shakur,? kaine farin cikin mu, zuciyata radaddi take min, amma ka sani zaka kasance cikin kowacce addu’a da zan yi, zaka iya tafiya a zuciyar mutane, zai yu na daina ganin ka cikin idanuna, amma har abada kana zuciyata Shakur, You will always be remembered and never forgotten. Kwanaki zasu rikide izuwa shekaru, amma zaka kasance a zuciya ta, dukkanin abinda zan yi domin cire zafin rashin ka a raina, daga can Kasan zuciya ta radadin na manne, domin bazan kara rungume ka ba, bazaka dinga min barkwancin ka ba, babu Wanda zan fada wa damuwata kuma, Allah ya jikan ka my blood!” Ya ce yana damkar kasar wajen a tafin hannun sa, hawaye ya sulalo masa, yana matukar hana kansa kuka domin malamin da yayi addu’a dazu ya fadi illar yiwa mamaci kuka, taya zai so ayi wa Shakur ɗin sa azaba sanadiyyar kukan sa, amma zuciyar bata shawara da shi ɓalle ya hanata.

Har bayan sallar la’asar yana wajen, Sallah kadai ke masar sa dashi, anyi anyi ya koma Cikin gidan sai yace “Baya son barin Shakur shi kadai ”

Mutane da dama sun tausaya masa sosai, abinci ma yaƙi ci.

Doctor Abbas ne ya fara samun labarin mutuwar Shakur, mutuwar ta girgiza shi, sai ɗaya yi kuka a cikin motar sa Domin Shakur mutumin kirki ne da zai yi wuya a manta shi, ya kira doctor Aaban ya sanar masa tare da barrister Abrar ya kuma nemi kada su gaya wa Munaya tukunna, Allah yasa Munaya ba mai shiga media bace da babu abinda zai hana ta gani, bai sha wuyar gane gidan ba, sai dai Alhaji Dawood ya samu yayi wa gaisuwa, ya shiga bin mutane dake cike a farfajiyar gidan da kallo bai ga Maleek ba, ya kuma kasa tambaya, tabbas mutuwa ta wuce wasa, duk yanda ta kai da basa shiri da Maleek, amma bazai iya cigaba da gaba da shi ba, ko dan darajar Shakur.

Sai da dare yayi Alhaji Dawood ya ga tashin hankali, domin Maleek cewa yayi a nan kusa da kabarin Shakur din zai kwanta, taya yana cikin gida amma kanin sa na waje.
Da kyar aka iya fitar da shi Daga garden din, washegari Alhaji Dawood ya kira aka masa allurar bacci, domin idan aka cigaba da tafiya a haka depression zai Iya taba ƙwaƙwalwar sa.

*Ranar sadakar uku*
Bayan an yi addu’ar ukun, Maleek ya koma kabarin Shakur yana masa addu’ar da Yaren daya iya tunda ba addu’o’in larabci ya iya ba, Alhaji Dawood kuwa sai a yau ya dauko Wayarsa, sakwani ne wanda baza su kirgu ba yawanci masa taaziya ne da basa kasar, amma ya tsallake Dukkanin su sakamakon wani sako daya ja hankalin sa, Shakur? Ya duba kwanan wata ya ga ranar ɗaya rasu ne, hannun sa na kakarwa ya buɗe sakon.

_dear Daddy! ina fata wanna sakon nawa ya same ka lafiya, kafin nace komai, ina baka hakuri a madadin maleek, Sannan nima ka yafe min, bawa baya wuce ƙaddarar sa, ba kuma komai ya saka muka boye maka ba illa gudun ɓacin ran ku, Daddy, Maleek yana da ya, ita ce yarinyar nan da suka zo asibiti Duba Ni, tabbas ƙaddara ya fada musu ba tare da kowanne su ya shirya masa ba kuma rabon y’a ya shiga tsakanin su, dan girman Allah Kada ka yi fushi da Maleek, ka yafe masa, sannan rokona na biyu a gare ka shine kada ka saki mummy, i know it’s hard to forget, amma ka yafe wa mummy domin tayi nadama, Abu na karshe, ka fada Wa Maleek cewa ya cigaba da zama jarumi mai zuciyar dutse kada ya zama rago idan bana tare da shi, tell Maleek i love and miss him, i love You Daddy, and I love mummy too_
sai da Alhaji Dawood ya ga screen din wayar sa a jike ya lura ashe kuka yake, ya saka hannu ya rufe idanun sa ya fashe da kuka.

Munaya yau da niyyar zuwa duba Shakur ta tashi, ta haɗa masa breakfast tare da yin wanka ta fito ta shirya cikin riga da siket, sannan ta ɗora jilbab Blue color daya dace da atamfar jikin ta, ta saka sandal mai kyau irin na mata Black color ta dauki wayar ta ta fito.

“Munaya!” Barrister ta kira ta.

“Na’am” ta amsa hakan nan taji gaban ta ya fadi.

“Zo ki zauna” tace mata.

Ba musu Munaya ta zauna

Barrister Abrar ta sauke numfashi tace “Munaya matsayin ki na muslima kin san yarda da ƙaddara, kuma yarda da ƙaddara na daga cikin imani, kuma kin san mutuwa gaskiya ce ko, babu bawan da zai tsallake ta”

Ta jinjina kai cikin sauri, domin yawun bakin ta ya fara kafewa da irin maganganun da barrister ke mata Mai cike da daure kai.
Barrister Abrar ta ɗora da cewa “ina so kiyi hakuri, ALLAh’n daya fi mu son sa ya dauke shi, munaya Shakur ya rasu yau ake sadakar ukun sa”

Jin Munaya ne ya dauke kana ya dawo, hawaye tuni suka wanke fuskar ta, innalillahi wa inna ilaihi raju’un take maimaitawa tsakankanin lips din ta, ta kifa kanta a kan Cinyoyin ta ta shiga rera kuka, gaba-daya ji take kamar mafarki ne ko ace karya ne, sai dai wacce ta gaya mata bazata yi karya ba, karya ma irin wanna na mutuwa, alkhairan Shakur da irin barkwancin sa take ta ta hasko wa a ƙwaƙwalwar ta, tabbas duniya is nothing but a beautiful lie.

Gidan gaisuwar duk suka shirya domin tafiya doctor Aaban da barrister hadi da Munaya da little Amnah kasancewar su miemie sun tafi Makaranta ya rage saura little Amnah.
Ko a cikin mota ma Munaya kukan take, bayan sun iso gidan, alhaji Dawood na daya daga cikin rumfar da aka kafa a farfajiyar gidan.

Nan su barrister suka nufa domin yi masa gaisuwa, a kallo daya Alhaji Dawood ya gane su, suka mai gaisuwa ya amsa, amma hankalin sa na ga little Amnah, sakon Shakur na sake ringing a kunnen sa.
Ya sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan yace “ku tashi ku shiga ciki” yace yana kallon barrister, barrister ta mike daga tsugunne da take ta riko hannun Munaya suka nufi cikin gidan.

 

Team Shakur ina mana taaziya 🥺👏

Mu haɗe Monday idan Allah ya kaimu ngd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button