Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 41

Sponsored Links

XLI….
(41)

*MunayaMaleek is Five hundred naira only via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta 07082281566*

Alhaji Dawood na kwance a dakin sa yayinda yake fafatawa da zuciyar sa, so yake ya binciko ta ina yayi sake da gidan sa? Ta ina ya gaza da gidan sa? a iya sanin sa yana sauke dukkanin wata bukata ta su, meye laifin sa ta Sa’adah ta zabi kuntata wa zuciya da ma rayuwar sa gaba-daya, duk inda ya kai ga binciko laifin sa bai gani ba, amma daya tuna cewa Sa’adah ta ce ya sakar mata tarbiyyar yaran gaba-daya, sai jikin sa yayi matukar sanyi, tabbas ya yi sake ta nan, saken da yayi yana daga cikin abinda ya sanya Sa’adah yin son ranta.

Ya numfasa da ƙarfi yana ji dama hannun agogo ya dawo baya tabbas daya gyara wasu kurakuransa da kuma taka rawar da uba kan taka a rayuwar ya’y’an sa.
Yana kwance a wanna yanayin, tunanin sa yayi zurfi, har ya kwakwalwar sa ta bankado masa wani sirri daya jima da manta shi shekaru arba’in kenan, jikin sa ya shiga rawa ya mike zaune hannun sa tallabe da kansa.

*Shekaru arba’in baya*
Jahar Akwa ibom
_kauyen Oruk Anam_

Kamar yadda aka sani jahar Akwa ibom na daya daga cikin jahohi masu kyawawan mata, hasken fata da dirarran jiki, domin kafin a kwato yanci turawa mulkin mallaka sune asali a jahar, Allah ya albarkace su da danyen mai, haka zalika suna da cima mai kyau da gina jiki, shiyasa mafi yawan yan garin masu dirarran jiki ne daga mazan har matan.

Matasa ne su biyar sanye da Kayan bautar ƙasa, suna tafe suna hira cikin barkwanci, daga yanayin da suke hirar zai tabbatar wa mutum da cewa suna cin duniyar su da tsinke.

Farin Daga cikin su yace “kai gafa gidan abinci mun samu”

“Haba dai?” Sauran suka fada bakin su a hade.

“Wallahi, gashi can an rubuta mama Edet restaurant”

Suka nufi dan madaidaicin shagon suka yaye farin labule irin na da din nan mai fasali kamar net suka shige, wajen a matse amma haka suka zauna, babu wasu customers a shagon sai mutum daya dake gabzar lomar abinci ko kallon samarin bai yi ba .

Babbar mace ce da a shekaru zata yi 46 ta Mike tana cewa “Edetyyyy where are you, see customers ooo”

“Ma i dey come, see Me for kitchen” zazzakar Muryar matashiyar budurwa ta amsa wa matar data kasance mahaifiya a gareta.
Babu jimawa kyakkyawar yarinya fara mai kira ta zo inda samarin suke, ta gaida su da fara’a wanda hakan dabi’ar ta ce, samari Biyar din nan suka zuba mata ido domin ta ɗauki hankalin su matuka musamman shape din ta.

Ganin basu yi kama da yan garin su ba sai bata yi musu yare ba tace “wetin i go serve una?”

Farin nan yayi saurin cewa “what and what did you have?”

Tace “we get fufu, akpu, eba, Pando, with edikang ikong soup, editan soup, afang soup, ekpang nkukwo soup”

Dukkanin su ba cimmar su cikin abinda ta lissafo, amma yanda yarinyar ta dauke hankalin su ya sanya baza su iya cewa zasu tafi ba, wani gajere daga cikin su yace “bring one one plate for us”

Cikin farin ciki ta koma kitchen din domin kawo musu abincin, maman Edet kuwa dadi sosai take ji ganin ciniki ya zo, dan haka tace “una Weldon oo my son’s”

Suka ce mata “thank you ma” Ita kuwa ta koma wajen zaman ta ta zauna domin Edet ke bawa mutane abinci, iyakarta tayi girkin da za’a siyar, domin ta saka a ranta cewa Idan customers na ganin Edet sabuwar jini kuma kyakkyawar yarinya hakan zai saka suna tururuwan zuwa shagon.

Babu jimawa Edet ta kawo musu akpu da miyar edikang ikong, kowa ta ajiye masa nasa kwanon sannan taje ta kawo musu ruwan sha Dana wanke hannun, fuskar su a yamutse yayinda suke dan fargaban ko ya ɗandanon abincin zai kasance a baki, a tsorace suka kai lomar farko, dadi sosai suka ji yayi musu suka kalli juna sai suka kwashe da dariya, nan suka shiga loma har suka yi take away da zasu tafi, maman Edet kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha saboda dadin wanna cinikin da suka mata.
Daga wanna ranar suka mayar da shagon maman Edet wajen cin abincin su, a hankali shakuwa ta fara shiga tsakanin su, kamar yau bayan sun gama cin abinci Edet ta zo karban Kudi ta ce musu ” a beg wetin be una name” Daga yanda take yawan gurbataciyyar turanci zai tabbatar wa mutum da cewa bata zuwa makaranta.

Suka yi dariya sannan cikin turanci Farin yace mata “I’m Dawood, wanna Kuma Ibrahim, wanna Isma’il, wanna Ahmad, wancan na karshen Yusuf” ta shiga maimaita sunan suna mata dariya saboda yanda take furta su ba dadin ji, domin sunaye ne da bata taɓa ji ko cin karo da su ba.
A hankali Edet ta kamu da son Dawood tun bata sani ba har ta fahimci hakan, duk da ta san akwai matsala da tashin hankali idan mahaifiyar ta ta gano hakan amma bata damu ba, domin a yanda take jin son Dawood a ranta ko menene zata iya yi domin sa, shi kan shi Dawood da ma sauran abokan sa sun san da wanna son da take masa, domin Kulawa na musamman take bashi idan sun zo shagon su, amma ya basar domin ba abinda yake ransa kenan ba, kamar yadda yake da wata manufa a kanta, haka zalika abokan sa.

Duk ranar Lahadi maman Edet bata buɗe shago, ba kuma dan tana zuwa chochi bane, ita din mara addini ce, domin *asari mandu* shine abinda suke bautawa.

Dawood da abokan sa ke tahowa daga wajen diban ruwan garin, gajeren cikin su mai suna Ahmad ke tura kurar ruwan, Edet suka hango ta zo diban itama, cikin farin cikin ganin su musamman Dawood ta taho Wajen su, suka gaisa cikin barkwanci sannan Dawood yace mata bata taɓa kawo musu ziyara
Copers lodge din su, tayi masa alkawarin zata zo da misalin karfe 12, amma maman ta zata ta bar ta ba, sai dai ta nemi abinda zata ce mata , ya ji dadin dabarar data kawo, haka zalika abokan sa da haka suka rabu, tana tafiya suna bin bayan ta da kallo yayinda suke magana kasa kasa su na dariya su.

Da rana ta shirya tayi kyau sosai, tayi wa mamanta karyar zata je gidan kawar ta, kai tsaye ta nufi copers lodge din su Dawood, Isma’il da shine gwanin girki a cikin su ya gabatar mata da abinci da abin sha bata wani tsake ta ci da yawa ba domin ta zama uncomfortable da irin kallon kurillar da su biyar ɗin ke mata.
Ibrahim shine wanda ya fara fito mata da zahirin abinda ke binne a ransu gami da ita tun ranar da suka fara zuwa shagon maman ta cin abinci, ya fara shafa ta kenan ta mike a tsorace, nan suka fahimci Lallai ita din sabuwar hannu ce, ya kamo ta ya danne ta da kyar saboda yanda itama ta gwada masa karfi, sauran suka kwashe da dariya, ta Fara hawaye tana kallon Dawood alamun ya taimake ta domin ta fi yarda da shi, kamar yadda domin sa ta zo, domin soyayyar da take masa, amma ko kallon ta bai ba suka fice waje, Ahmad da yake karshen fita ya kalli Ibrahim dake kan Edet ya saka tafin hannun sa ya rufe mata baki, yace “kar fa ka mata ragaraga ka barmu da ragowa, ka kuma hanzarta, domin awa dayar ka na cika za ka tashi a kanta ko baka so, domin daga ganin ta zata yi zuma” yace yana dariyar shekiyanci.

A takaice dai da daddaya samari Biyar din nan suka dinga saduwa da Edet, Dawood ne na karshe, a tunanin ta bazai mata komai ba, shi din zai tausaya mata musamman da take kwance kamar gawa, amma sai ta ga yafi sauran mata mugun ta kamar yadda yafi sauran dadewa har abokan sa suka soma kwankwasa kofar dakin, zuwa lokacin Edet mutuwa kawai take jira domin ko motsi bata iyawa, abinda Dawood ya gaya mata ɗaya tarwatsa zuciyar ta shine ” tashi ki tafi gida, sannan kada ki ƙara sammanin sake ganin mu, ki kuma cire son da kike min a ran ki, domin ni ban taba son ki ba, Abinda nake so a tare da ke na samu, dan haka baki da sauran amfani a rayuwar ta”

Shock ne ya kamata, amma halin da take ciki ya sanya ta gagara nuna hakan sai idanun ta da suke lumshewa da buɗe wa.

Bayan ya fita ta rufe idanun ta, hawaye Masu zafin gaske suka zubo mata domin ko kuka bata iyawa, shekarar ta Ashirin da uku a duniya, babu Wanda ya taba yaudarar ta, kamar yadda babu wanda ta taɓa so sai Dawood, amma ya yaudare ta tare da abokan sa, abin ya matukar yi mata ciwo, ta kuma fi jin zafin abinda Dawood yayi mata fiye da sauran abokan sa, har karfe bakwai tana kwance a haka, bata san ta ya ba, ita dai ta ganta a mike, ta shiga bin bango har ta fito daga copers lodge din, sau biyu tana faduwa kana ta lallaba ta mike ta cigaba da tafiya, tana jin jini na cigaba da bin kafafun ta, hawaye na zubo mata, ga duhun dare, haka ta dinga bin ta ciciye abin tausayi, faduwa ta uku data yi ta kasa cigaba da tafiya, rarrafe ta dinga yi, guiwar ta ya gugurje da jini, a haka har ta kusa zuwan kofar gidan su inda sama sama take jin maman ta na kuka ga Kuma mutane da take ganin su dishi-dishi na rarrashin ta da alama ta neme ta ta gaji, tayi nadamar karyan data yi wa mahaifiyar ta, tana zuwa kofar gidan nasu, ta fadi kasa gaba-daya, mamanta ta saki ihun kuka tana kiran sunan abin bautar su” Asari Mandu”
Tana jijjiga Edet, Edet ta furta sunan Dawood, sannan wuyan ta ya saki, sai dai mamanta bata ji ba, kasancewar kalmar bai fito ba sai labban ta daya motsa.
Maman ta cigaban da jijjigata da kiran sunan ta amma bata motsa ba, nan suka fahimci Lallai ta mutu.

Ɓangaren su Dawood kuwa sam basu damu ba, domin a ganin su ai ba wani abun suka aikata ba, yanzu lokaci ganiyar samartakan su ne, bayan sun dawo lodge din su da ga yawo wajen goman dare suka tarar bata nan, nan suka zauna kowa na fasaltawa dan’uwana sa yanda yaji gami da ita da kuma abinda suka fi so a jikin ta.

washegari labarin mutuwar mutuwar Edet ya riske su, sun tsorata da jin wanna labarin, amma sai suka maze kamar basu da matsaniya kan abinda ya same ta, bayan kwana biyu suka manta da lamarin ta, sai dai duk suna ganin ta cikin bacci tana hawaye yayinda take kallon su da wani irin kallo mai firgita zuciyar mutum, a haka suka yi fama tsawon wata ɗaya kana suka daina ganin ta a mafarki, har suka gama bautar kasar su suka bar garin na akwai ibom basu kara ganin maman Edet ba Domin tun rasuwar Edet din bata kara buɗe shagon ba.

Wani dogon numfashi Alhaji Dawood ya sauke bayan ya dawo Daga dogon tunanin ɗaya manta da babin sa tsawon shekaru arba’in kenan, lallai a yau ya yarda da maganar da aka ce, *duk abinda kayi wa dan wani sai an yi wa naka* a lokacin yana ganin Kamar sun ci bulus ashe ranar sakamako na zuwa, ashe zai girbi abinda ya shuka, nadamar da bai ba a wancan lokacin ya rufe shi ruf, sai dai lokaci ya kure, yafiyar da bai nema ba a waccan lokacin zai nema yanzu, a ransa yana addu’ar Allah yasa abin ya tsaya har iya haka kada ya je har jikokin sa, domin Allah baya yafe hakkin wani, tabbas yana jin kunyar Ubangijin sa a yanxu, kunya mai tarin yawa, ya biye wa rudin duniya dana zugar abokai ga inda ya kai shi yau, abokan da bai ƙara ganin su ba tun da suka gama bautar ƙasa.

“Innalillahi wa inna ilaihi raju’un!” Ya furta yana fashewa da kuka sosai.

Bayan an gama sadakar arba’in din Shakur, washegari Alhaji Dawood ya shirya tafiya,
Gidan shiru babu motsin komai, kusan za’a ce Shakur ke raya gidan, yanxu da babu shi gidan yayi shiru, plasma kuwa an jima da daina kunna ta.
So yake ya ga Maleek Kafin ya fita, ya fita farfajiyar gidan sannan ya zaga bayan gidan, ya ganshi kamar kullum kusa da kabarin Shakur da alama addu’a yake masa, shima ya tsugunna gefen sa ya shiga yayi masa addu’a sosai kana ya mike ya koma gefe yace wa Maleek ya zo.

Maleek yazo gaban sa ya tsaya kansa na kallon kasa, Alhaji Dawood ya dafa shi yace “zan yi tafiya, ina saka ran a yau din idan na gama abin da ya kai ni zan dawo, ka kula da kanka”

Ya dago kansa a hankali yace “Dad, Ina zaka, will you mind if we go together?” Maleek ya tambaye shi.

Alhaji Dawood ya ji zuciyar sa ta karye, da ce yana son rakiyar Maleek da shi da kansa zai nemi ya raka sa amma har abada bazai iya zuwa da shi ba wajen nan ba.

“No Maleek please stay back, ka karfafa zuciyar ka, ka tuna yanzu bani da wani Magaji sai kai, kai zaka cigaba da riƙe komai nawa idan lokacina na barin duniya ya yi, ka kuma kokarta ka koma Companyn ka hakan nan”

Hakan da Alhaji Dawood yace sai ya saka zuciyar sa bugawa, amma bai ce komai ba, Alhaji Dawood yayi patting bayan sa sannan yace “Sai na dawo”
Yabi mahaifin sa da kallo har ya bacewa ganin sa, ina ma yana da mahaifiya a raye, daya samu sauƙin wani abin a zuciyar sa, amma ya rasa abubuwa biyu masu tsada a rayuwar sa, uwa da Shakur ɗin sa, tabbas ya yi tawwakali, amma mantawa shine abinda Zuciyar sa bazai dauka ba.

Bayan Alhaji Dawood ya sauka a filin jirgin jihar Akwa ibom sai ya tari mota da zai kaishi kauyen Oruk Anam, bayan an sauke shi daidai makarantar da yayi bautar ƙasa ya sallame mai mota, ya shiga bin garin da kallo domin tabbas an samu sauye-sauye masu tarin yawa a kauyen, shi kanshi makarantar an kara gyara ta zuwa ginin zamani sunan Makarantar kadai ya saka ya gane ta.

Shagon mama Edet ya shiga nema yana kokarin tuno yanda yake, sai dai bai gane ba domin gine-gine sun yawaita ba ƙamar wanccan lokacin ba, ya tsaya cikin gajiya, yana cigaba da dube dube ya hango wani mutum da zai kai shekaru arba’in da biyar ya tsayar da shi, cikin sauri Murya ya gaida shi kana cikin turanci yace yana neman Mama Edet.

Mutumin ya dinga maimaita sunan da Alhaji Dawood ya kira cikin son tunowa, sai yace masa cikin turanci “mama Edet mai abinci ko?” Cikin sauri Alhaji Dawood ya gyada kansa cikin jimami mutum yace “ai Edet ta mutu, har yau ba’a san wanda ya yi mata muguntan nan ba, mahaifiyar ta kuma kullum Cikin kuka take har hakan yayi sanadiyar makancewar ta, yanzu kabi can, sai ka sha kwanar dama, zaka ga gidan mai bishiyar mangwaro” godiya yayi wa mutumin kana ya fara bin kwatancan da yayi masa, jikin sa ya kara sanyi musamman daya ji cewa maman Edet ta makance, kansa tsaye ya buɗe kofar da aka dan kare, ya hango wata tsohuwar mata zaune rike da sanda, tabbas itace Mama Edet, duk da cewa ta sauya matukar sauyawa amma ya shaida ta, ita kuwa ta fara lalube tana cewa waye nan da Yaren su, cikin turanci Muryar sa na rawar Yace “Mama it’s me Dawood”

Tayi shiru, ta kasa tunowa mai wanna sunan, ya samu kan wani tsahon turmi da aka kife ya zauna sannan ya shiga mata bayani ko zata fahimta, tabbas ta gane shi yanzu, ta lalubi hannun sa ta kama, Cikin Muryar ta dake rawa saboda tsufa tace “my son, Edetyy ta mutuuuuuu, na rasa yarinya ta, ban san waye ya yi wa mata haka ba, amma kullum sai na tsine masa”

Dam zuciyar Alhaji Dawood ya buga, ya sauka kasa daga kan turmin cikin turanci yace “Mama Please forgive me, ni da abokaina muka yi sanadiyar mutuwar Edet, dan Allah ki yafe min ko na samu sauƙin rayuwa mama”

Mutuwar Edet ya dawo wa maman Edet sabo, ta shiga kuka sosai tana ƙara tsine wa Alhaji Dawood har da jikokin sa tana kuma jaddada masa cewa bai ga komai ba tukunna” hankalin Alhaji Dawood ya tashi sosai, yana rokon ta amma bata saurare shi ba, sai buge shi take da sandar ta, daidai lokacin Wasu dattijai maza uku da suka kasance yan’uwa gare ta suka shigo domin gaishe ta kamar yadda suka saɓa duk safiya kafin su tafi gona.

Cikin yare suke tambayar ta abinda ke faruwa, da kyar ta iya musu bayani, suka yi wa Alhaji Dawood caaa akai kamar zasu rufe shi da duka, zagi ba wanda basu masa ba, su zage shi da yare su masa da turanci, ya dai tsugguna a gaban su yana rokon su yafiya, gaba-daya ya dawo kalar tausayi, babban cikin su yace “ba batun hakuri, Auren ta zaka yi”

A razane Alhaji Dawood ya dago, Cikin tsoro daya bayyana a fuskar sa yace “aure? Taya zan auri wacce ta mutu”

A kausashe mutumin yace “haka tsarin abin bautar mu yake, zaka aure ta, zaka biya sadakin ta, za kuma ka siyi sa da rago Bayan ka bada kudin da za’a yi abinci, Domin biki xa’a yi, bayan ka biya dukkanin wandannan, sai a daura muku aure a rafin asari mandu”

 

*Mu haɗe gobe da yardar Allah, jiya basu kawo wutan ba sai dazu, kuyi hakuri*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button